← Book details Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 18

Sashe 6

Zaujun Majunun Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cike da mamaki yace boy ban gane ba today is what ba, son kenan yaukam ai yaune ko *Barr* ?...yana me kallon *Papa* kai ya gyada alamar eh yana murmushi.

Shikam *Blue* ido ya lumshe sai kuma yabud'e cikin d'an kosawa dasan abashi amsar abinda ya tambaya, sai kuma ahankali yace *Dad* ina nufin yau din wace ranace muke sannan wani wata muke kuma wace shekara muce ciki, domin ina ganin wannan kalandar tayi expired dan hakan ban yarda da abinda yafada'a ba.

  Murmushi *Dad* yai me kayatarwa tareda karban kalandar yakalla, sannan ya kalli *Blue* wanda ke kallonsa yaname san yatabbatar masa dacewa yesss! kalandar nan tayi expired, kafad'arsa yadafa cikin dariyar jin dadi yace my boy kalandar nan batayi expire ba tana tafiya dai-dai tabbas yau asabar 5-6-2021, ya'akai ne boy?...shuru yai na yan wasu dakika sai kuma ya yaro ido cike da mugun bugawar zuciya had'eda tsananin tsoro bakinsa yana rawa yace......

Muje zuwa

*MEENAL or LUFHAT CE*

_ALLAH kasa mucika da imani ameen ya hayyu ya kayyu_

🎍🎍🎍🎍
     🎍🎍🎍
          🎍🎍
               🎍
🎍 *ZAUNJUN MAJNUN* 🎍
(Miji mahaukaci)

*BOOK 2* Page

2️⃣1️⃣to2️⃣5️⃣
🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍

WRITTEN BY

🎍 *AMINA UMAR FARUQ* 🎍

OR

🎍 *MEENAL*🎍

Marubuciyacer

*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*
*HASKE BAYAN DUHU*
*ZAUNJUN MAJNUN part 1*
*TAWAKKALI*
*TASEERI*
and now
*ZAUNJUN MAJNUN part 2*

_SADAUKAWAR GA_

Iyayena abin alfarina ina godiya bisaga tarbiyyar dakukai mu, dan haka ina rokon Allah yasaka maku  da alkairi yakareku daga sharrin mutum da aljani, ubangiji yasa kugama da duniya lfy ameen ya rabbi.

Wannan littafin na kudi ne akan farashi me sauki, 200 naira only zaku iya turo kudin tawannan account no 0047769671 Amina Abdullahi A., sai kuturo shaidar ku ta hanyar yin screenshot sannan kuturo ta wannan lambar 08161850024, sai naji ku.

✍🏼

_Bismillahirramanirraheem!_

"''''''''*D.....a....d.....* kenan da gaske kalandar nan batayi expire ba?...yace tabbas Boy batayi expire ba, "shin my son me yafaru ne"?...naga duk katayar da hankalika gashi bakada lafiya so kanutsu kaji ko?....yakarashe fad'a tareda dafa kafad'arsa,cike da kulawa yayinda shikuma ya gyad'a kai.

"Sai kuma wani irin gumi yashiga feso mashi agoshi" cike da tashin hankali, yace *Dad* yanzu haka naji ajikina cewa banda lafiya sabodama banajin karfi ajikina, saidai pls *Dad* tell me me yasame ni haka it mean wani irin rashin lafiya nayi haka.

       "Wanda alissafin danayi yau kimani shekara daya da rabi kenan, harda wasu watanni ko?...tunda ai mun dawo ne biyar ga wantan shidda shekara ta dubu biyu da ashirin ko my _guy_ ?.., yakarashe fadinda kallon *Bulama*, wanda shima kallonsa yake  kafin yace" tabbas hakane my _ guy_.

        "Yauwa *Dad* to wani irin rashin lafiya nayi haka tsawon shekara daya da rabi harda wasu watanni, nadai san aranan da muka dawo ina saukowa daga jirgi naji kaina yai wani irin masifaffen sarawa, wanda ban ta'ba jin irinsa ba tunda nake arayuwata. 

"To saidai kuma dagan ban sake sanin me yafaru daniba, sai yanzu dana farka nagannin wani irin atsamutse *Dad* sai naga kamar banine fine Boy din nan d'an gatanka ba, yakarasa fad'i cike da shagwa'ba harda d'an turo baki sannan yadora da cigaba dafad'in so pls *Dad* kafad'a mun meye yasa meni wai haka ne eye?.

        "Cikin murmushi jin dad'in me tabbatar dacewa yaronsa yasamu lafiya kwarai da gaske, *Dad* dafa kafad'arsa yayi tareda cewa my Boy wannan maganar me tsawoce, yanzu abinda nakeso dakai shine kaje kai wanka kadauro alwala sai ka'iskemu masallaci.

tunda kaga ankira sallar magrib idan muka dawo sai nafad'a maka komai ko?, cikin sanyi jiki yace to *Dad* sannan suka tafi masallacin "Shikuma yanufi daki jiki ba kwari zuciyarsa cike da tunanin wani irin ciwo yayi haka, tsawon wannan lokacin batareda yasani ba.

******

"Koda *Bilal* yashiga daki tsaye yayi agaban mirron yana kallon kansa sosai yake mamakin yanda yakoma haka, ahankali yashafi kasumbar fuskarsa sannan yafurta Oh! god what happen to me ne wai eye?...see me fa like mad, yana me sake kallon jikinsa tareda nunawa yana kuma turo baki cike da shagwa'bar dayasaba yima *Dad* still yana sake shafa 'kasumbarsa.

    "Sai kuma take wata zuciyace, tace" dashi shi wai ba *Dad* yace" kayi wanka kaje kai sallah ba tukun na idan kuka dawo sai yafa'da maka komai ba eye?.., da sauri yace yesss! tareda nufar toilet din cikin kankanin lokaci yahada makanshin ruwan wanka dayaji turaruka kasan cewar shi ma'aboci san kamshi,

sannan yashiga yai wanka yafito bayan yadauro alwala da sauri yagoge jikinsa da towul, ba tareda yashafa maiba saidai bayan yagoge jikinsa da towul sai yafesa body spray perfume me tsananin kamshi, sannan yasa farar jallabiya tareda daukan farin casbi, yasa wani silifas fari me kyau sannan yafita da sauri domin yaji ana fadin adaidaita sahu.

******
       "Bayan sun idar da sallar sannan suka fito saidai *Bilal* bai fitoba yana chan yanata zuba addu'a hakan yasa suka tsaya jiran fitowarshi, inda *Bulama* yake cewa *Dad* da *papa* kungani ko nafad'a maku "my _guy_ yana addu'a sosai, koda muke U S idan mukayi sallar magrib sai munyi isha'i.

sannan muke fitowa daga masallaci kuma sai my _guy_ yadade yana addu'a sannan mufito, kawai dai Allah yatsara cewa sai hakan tafaru dashine, murmushi *Dad* yai cike da jin dad'in jin haka, yayinda *Papa* yace tabbas hakane kasan duk abinda Allah yatsarama bawa, cewa ai sai abu kaza yasameshi arayuwarsa tofa babu makawa sai yasameshin, dan haka sai dai muce Allah yatsare gaba.

"Sannan kuma ku cigaba da addu'ar nan aduk inda kuke sai kuga Allah yana tsareku daga dukkan abin cutarwa, saboda haka Allah yatsaremu baki d'aya duk suka amsa da ameen. "Sannan *Dad* yace yauwa dan Allah ina rokonku idan zan fad'ama "Boy abinda yafaru dashi bazan fad'i cewa nayi masa aure yana cikin wannan halinba, da sauri  *Papa* yace  *Dr* saboda me?...

yace *Barr* saboda nasan Boy bazayaji dad'in hakan ba, nikaina nayi dana sanin aura mashi "yarinyar nan wacce inda nasan cewa batada tarbiyya da bazan aura mashi "itaba, ai Son yaga yanda muka kwashe dasu saboda rashin d'a'a har mahaifinta yana sa'insa dani, alhalin yasan "yarsa tanada ciki amma yabawa d'ana auranta dan haka banason "yasan da zance dan Allah kunji?.

    "Cikin sanyi jiki *Bulama* yace insha'allah bazaya taba saniba, *Dad* saidai nikam inagani kamar cikin jikin sis *Beenazar* na my _guy_ saboda fa tare suke kwana *Dad* kaga komai yana iya faruwa, kai ya girgiza tareda cewa a ah son hakan bazata faruwa tunda bashida lafiya, dan haka besan ta yanda za'ai yaima mace cikiba sam banashi bane tunda kana ganin saida *Bebe* ta aunata, dan haka mubar zancan nanma  atsakani mu kawai.

"Ahankali *Bulaman* yace to *Dad* insha'allah bazamu fad'a mashiba saidai idan kaine kabukaci muyi hakan, shikam *Papa* baice komai ba sai gyad'a kai dayai domin yarasa abinda zayace cikin wannan magana, saidai aransa yanaji kamar "mutanan nan sunfi  *Dad* da *Bebe* gaskiya.

   "Domin kuwa ayanda *Bulama* yafad'a mashi tabbas "sunada gaskiya tunda kwakwalwarsace batada lafiya, ba gangar jikinsa ba daza'ace bazaya iyayin tarayyar sure da mace ba to amma tunda sunce haka bakomai, insha'allah gaskiyar zatayi halinta ne komai daran dad'ewa.

Sannan yace karka damu *Dr* insha'allah bazamu fad'a "mashiba, yakarasa fadi yana kallon *Dad dashima yake kallonsa cikin murmushi yace nagode Allah yabar zumunci yace ameen ai bakomai.

"Dai-dai lokacin da *Blue* din yafito hannunsa rikeda casbi yana ja cikin nutsuwa, kallonsa sukai duk suka saki murmushi shima ganinsu tsaye yasashi sakin murmushi, domin yasan tabbas shi suka tsaya jira cikin sanyi jiki yakarasa gurinsu yana me fadin "eyya *Dad* shine baku tafiba ku katsaya jirana ko?...,yakarasa fadi tareda mika masu hannun sukai musabiha.

*Bulama* da *Papa*, yayinda yamikama *Dad* hannu cikin murmushi yasaka hannunsa cikin na *Bilal* din tareda jawosa jikinsa yace munyi laifine damuka tsaya jiranka ko *Boy*?....cike da shagwa'ba yace no *Dad* banufina kenan bafa, to me kake nufi my darling boy umuh?...yana me rungumeshi sosai akafad'a yanajin so da kaunar tilon 'dansa har cikin jinin da jijiyoyinsa,

inda suka fara tafiya ahankali cike da nutsuwa, yayinda su *Papa* suke biye dasu aransu suname jinjina kaunar dake tsakanin uba da d'ansa fiyeda yanda sukema junansu".

"Yace *Dad* nufina dasai kutafi idan na'idar sai na iskeku ko?...,yace "eh hakane to aikaga yanzu munsamu ladan jiranka da musabihar damukai, sannan kuma gashi zamu tafi tare muna fira gwanin sha'awa ko *Barr*?...cikin murmushi yace kwarai kuwa dai-dai lokacin dasuka shiga falon bayan sun zazzauna sannan cikin 'kaguwa *Bilal* yace *Dad* pls tell me yace ok my *Boy*.

*******

          "Saida *Dad* ya gyara zama sannan cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, yafara yafad'a mashi duk abinda yafaru tun daga ranan dasuka dawo daga kasar waje, sukuma sukaje airport daukarsu har kawowa yau din nan saida yafad'a mashi inda cikin hikima ko kad'an maganar *Beenazar* be fito aciki ba.

   Saidai duk irin wahalar dasukai dashi tun daga kan *Dad* aunty *Bebe* da *Bulama* *Papa*da kasashen da aka kaishi dan yasamu lafiya harda mom dinsa, duk saida *Dad* yafada mashi komai inda *Bilal* din yaketa kuka cike da tausayin kashi danasu", na irin wahalar da suka sha akansa.

   "Rungume *Dad* yai yana fadin *Dad* hauka nayi kenan?...cikin tausayinsa yace tabbas son hakane, saidai malam yatabbatar mana cewa yimaka akai ta hanyar tura maka aljani yasaka nata d'abi'ar yara, cikin sheshsheka yace *Dad* "wanene kuma me nayi masa"?...

Son Allah masani kuma insha'allah sai yaga abinsa, da yardan Allah kayi hakuri kaji my darling *boy* kai ya gyad'a yauwa to kayi shuru kadaina kukan hakanan kaji?...yakarashe fad'i dashare masa hawaye, yace to my *Dad* nagode sosai Allah yabarmun kai cikin murmushi yace ameen son.

"Sannan yamike ahankali ya'isa gurin *Papa* tsugunnawa yai agabansa, sai kuma yakwantar dakansa akafafun *Papan* cike da shagwa'ba yace *Papaaaa!* cike da kulawa yasa hannunsa akan lallausan suman kanshi yafara shafawa tareda fad'in my Lovely son ya'akai ne?...yace thanks so muchhh!, yace son for what?...

cike da shagwa'ba yace no *Papaaaa!* for everything dakai mun so i love u so very muchhh!, cikin murmushi yace no son don't thank me is my work to do everything for u, sannan nima inasonka sosai kaji yarona?...kai ya gyad'a yauwa sannan inason kasake yin riko da addu'o'e sosai kaji?...to *papa*, yauwa hakan zaya kareka daga dukkan abin cutarwa, to *papa* nagode sosai insha'allah zan cigaba dayi sosai.
Chapter 6 · 0% Book details