← Book details Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 23

Sashe 9

Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

7-8
Cikin Sauri Amrah ta fara ƙoƙarin ƙwace Jikin daga na Nurayn wanda sai a sannan ya janye bakin sa daga nata , har kuma a lokacin bai Juyo ya kalli inda Aslaam yake sirfa masifar shi ba , wani Hausan nasa ma abun dariya ce don ba fitar da ita yanda ya dace yake yi ba . Still hannun sa yasa yana shafa Gyefen Kuncin ta cike da Wani irin soyayya mai kidimantar da bawa da kuma Bama zuciya tausayin sa ƙwarai,don shi sam idanun sa a rufe suke . Ba tare da Su Mommy Aslaaamm sunji mai yace mata ba sai dai bakin sa da suka ga ya motsa a Miskilance kamun ya juyo yana kallon Aslaaamm wanda ya gama fusata da Al'amarin Nurayn a cewan sa “ Wannan shine rainin hankali da tacewa....Ɗan jan iska Nurayn yayi yana furzar da Huci kana ya kalli Amrah wacce har a lokacin idanun ta Basu tsaya sa zubda Ƙwallah ba , haka kuma bata daina ƙoƙarin son zame hannun ta daga riƙon da yayi mata ba. Idanun sa ya kafe ta dasu wanda Ganin hakan yasa Amrah dakatawa da kiciniyar ƙwatan kan ta . A Miskilance yana ɗan kuna haɗe giran sa wanda ya saba sakata ladab idan yayi mata hakan nan take natsuwar ta ke dawo mata , da hakan ya saba yi mata koda kuwa yana buƙatar ta ne , don dole zata amince masa sai daga baya ya dawo kaman haka ya dinga kwantar mata da kai . Yace next time ba zai ƙara ba 🤔kuma bashi zai hana shi idan ya ɗebo jarabar nasa ya😜kun dai gane . Cike da miskilalliyar Muryar sa ya furta " menene...?

Ba Amrah bace ta saki Baki na Mamaki Mommy Aslaaamm ma Juyawa tayi suna haɗa ido da Aslaaamm , wanda Ganin hakan yasa Aslaaamm nufar sa yana kai hannun sa tare da ƙoƙarin ɓanɓare Amrah daga riƙon da Nurayn yayi mata . Wai ka san me sunan abun da ka Shigo kana mana kuwa ? . Kallon Aslaaamm Nurayn yayi kana ya sauke hannun sa daga na Amrah yana ja baya kaɗan. Sai kuma ya ɗan saki Murmushin nan nasa da zan rasa na Meye ma , Ɗan motsa laɓɓan sa yayi yana Lumshe Sexy eyes ɗin sa tare da Girgiza kan sa yana furta " Aa Aslaam sai ka faɗa . A ƙufule Aslaaamm ya furta " wannan shi ake kira da brain washing. Ka iso mana gida ka kama riƙe mana Yarinya kana aikata haramun ko ka manta ba matar ka......kaiiiiiii.....!! Nurayn ya wani daka ma Aslaam gigitaccen Tsawa wanda sai da kaf ilahirin Falourn ya amsa . Nan kuma take idanun sa suka fara sauya kala tamkar damusa . Da gudu Amrah ta yi bayan Aslaaamm tana kokarin shigewa jikin sa ne , Nurayn ya furta " Na rantse da Allah yau sai kun bani matata...! Babu inda zan tafi sai da Amrah , matata ta ce . Ni mijin ta ne kuma na Sunnah kai ne zan tuhume ka akan riƙe mun hannun ta da kayi matar kace kana da iko da yin haka n ne. ?

Amrah shiga ki dauko Mayafi mu huce .

Da Sauri Mom Aslaaamm ta nufo inda Nurayn yake don ta tsorata da al'amarin sa , Nurayn please ka saurara, ka Natsu kaji . Ƙwantar da hankalin ka . Mommy me yasa zaki basa Haƙuri ? Kalli fa yanda ya faɗo mana gida, sannan wai magana yake na taɓa masa jikin matar sa .? Aslaaamm enough...! Ya isa . Ai gaskiya ya faɗa matar sa ce . Bana son ƙara jin bakin ka , wuce ciki . Wani irin kallo Aslaaamm yayi ma Mom yana ƙoƙarin bude baki yayi magana ta kuma daure fuska tana masa Umarnin ya basu wuri ,don ta fahimta idan ta zuba ido to za'a yi abun da ba'a so...! Cike da jin zafin Nurayn Aslaaamm ya wuce yana ƙoƙarin barin cikin gidan baki daya ba tare da yama san inda zai nufa ba . Ran sa a ɓace yake babu abin da yake gani na Nurayn baƙi Fache sharara fuskar Amrah da yayi da Mari .

Nufa motonn sa ya yi yana mata key tare da danna horn yana ficewa daga Gidan baki daya .

Kallon Nurayn Mom Aslaaamm tayi kana tace " Zauna ka huta sai ka ....No need Mom , ya katse ta yana sauke mata idanun sa kamin ya cigaba da cewa " Amrah zaki bani yanzu mu tafi . Ni na sake ta , kuma na maida matata . Haahhwww 😨 Mom Aslaaamm ta bude baki na Mamaki kana ta ga ya juya yana kallon inda Amrah ke tsaye dauko Mayafin ki mu wuce . Wani irin kallo Amrah ke bin sa dashi nan take Zuciyar ta ya fara ƙiyasta mata anya Ƙwaƙwalwar Noory ba fara samun matsala ba . Abubuwan nasa sun fara wuce gona da iri . A'a ba zata bi ka Nurayn. Muryar Mom Aslaaamm ya katse shi wacce tayi Maganan cike da sanyi. Ohk ya furta yana juyawa tare da maida hannayen sa cikin Aljihu . Mommy Amma Ni mijin ta ne ? . Yayi Maganan yana kafe Mom d idanun sa wanda cike da rashin Fahimtar me zai yi Mom Aslaaamm tace " Eh kwarai haka yake . Gani tayi ya juya yana kama hannun Amrah tare da kokarin jan ye ta daga Falourn yana nufar Hanyar fita. Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Nurayn wai kana lapiyar kuwa .? I'm not ....!! Ya furta cike da ƙaraji wanda yasa Amrah fasa ihu tana kiran sunan Mommy tare da kai hannun ta tana kokarin kamo Mommy wacce tayo kan Nurayn tana faɗin " Nurayn wannan fa ba abu mai kyau bane . Nurayn.....! Kallon Mom Aslaam bai yi ba ya nufi da Amrah Farfajiyar gidan , Mommy na binsa wanda nan take securities suka taso masa suna attacking din sa da bindigogi .

Wani irin kallo Nurayn yayi masu kana ya saki yar dariya wanda sai da Amrah ta kara tsorata . A da baya yanda taga sunyi attacking din sa tayi tunanin ta tsira ne Dole zai barta anan , amma ganin irin murmushin da nurayn yayi yasa ta ƙara fashewa da kuka don sarai babu halin sa daya da bata sani ba . Noory na tambaye ka So na kake yi yanzu ko kuwa ƙina kake yi.? Hannun sa yasa yana Fiddo da wani abu mai kama da card yana daga masu wanda Ganin hakan yasa Securities din saurin ƙasa da bindigogin nasu sun san mallakin sunan nasa tun ba a Nigeria ba , sun kuma san wani shahararren ne da America ma jin shi sunan shi take bare kuma nan gida Nigeria 🥵 . Tsoro ne ya kama Mommy cikin sauri ta dubi securities din tana Cewa " au barin sa zaku yi ya tafi mun da Ƴa ta .? .

Juyawa Nurayn yayi yana sakin ma Mom murmushi kana yace " Mom na gode sai mun sake haɗuwa . Noory me kake yi haka .? Wannan ba so bane hauka ne .! Amrah ta furta tana mai daga Muryar ta da ƙarfi wanda Ganin haka yasa Nurayn bude motonn yana tura ta tare da rufewa cikin wani irin mahaukacin gudu ya bar compound din tare da ficewa yana ɗaukar hanya.....ihu Amrah keyi haka Mom Aslaaamm wacce take ta kwaɗa kiran sunan Nurayn Amrah .....A moton Amrah kuka take tana furta " Wannan sam ba so bane noory ka daina so na wannan ƙiyayya ce....! “ Da wuri haka ? , Humm ,Zaki maimata wannan Maganan taki Amrah ,Duk da kinyi shi a lokacin da bai dace ba ”. Muryar Nurain ya katse ta wanda jin haka yasa Amrah Fiddo da idanun ta tana masa Wani irin kallo na rashin Fahimta . Gani tayi ya sakin mata Murmushi yana maida Kallon sa Driving ɗin da yake yi . Noory me zaka mun ? Ka maida Ni wurin Mommy kar .....Yi mun shiru Amrah.! Ya katse ta ba tare da juyo ya kalli inda take ba .

Itace ta haife ki Mommy Aslaam din .? Me yasa zaki ce Kada Dad ya maida Auren Ammmie Hafsat? . Wani irin kallo Amrah tayi masa Fuskarta na narkewa, hannun tasa tana share hawayen da ke Zubo mata kamin kai tsaye ta furta " Saboda na tsane ta .! Ohhhh da kyau.”. Ya furta yana yi mata wani kallo mai kama dana Rainin hankali dama ya iyasa. Lumshe idanun sa yayi yana ƙara ware su a bisa Kyaƙyƙyawar fuskar ta kana yace " Wannan ma zaki maimaita shi kuma sai kinyi kuka da idanun ki Amrah, babu duka babu faɗa rayuwar mu ce zamu sauya ma salo😎❤‍🔥. Muryar Amrah ne ya hau Rawa na kuka mai cira , Noory ka chanja me nayi maka Ni to...? Ammie na kika tsana...! Dole ki so ta , Dole ki ƙaunace ta dole sai kinyi hakan Amra. Dama baka da tausayi na .? Ta yi maganan tana kwantar da Muryar ta na sarewa wasu irin Zafafan ƙwallah na cigaba da Zubo mata , Shikenan ta saka Noory ya tsane Ni ...ta Furta Maganan a zuciyar ta a zahiri kuma tana mai fashe masa da Wani irin kuka na ta shiga uku....!
Chapter 9 · 0% Book details