Sashe 14
Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Idan ba muyi haka ba bulus fa yaci kenan , sannan kar ku manta bako ne yana jin labari zai gudu. Yanzu Meye mafita ?. Kallon kallo suke ma junan su kana daga bisani Lanti tace kowa ya dauki abun bugun ƙwarto mu tafi .....😹 .
**
A hankali take sauke ƙafafun ta daga stairs din tana saukowa zuwa tsakiyar Falourn Mom Sa'adah . Gaba ɗaya Nusaiba ta sauya tamkar ba ita ba , babu kuzari bare karsashi . Har yau Bata ƙara ganin Dariya daga Mommy Sa'adatu ba ,tun faruwan wannan al'amarn . Hannun ta tasa tana gyara Hular kan ta , kamin ta juya tana nufar Kitchen don nan ne kaɗai zata tadda Mom Sa'adah da wannan sanyin Safiyar . Tsayawa tayi tana kasa shiga ciki ,sam ta rasa da Wani baki zata fara ba Mommy haƙuri don ta yafe mata akan bisa Abubuwan da ta aikata . Ja baya tayi tana jingina da bangon Wurin a hankali take tunano abubuwan da suka faru da yawa a wannan wuri , da farkon haɗuwar ta da Amrah wanda bata jin zata taɓa Mantawa da wannan rana a rayuwar ta . Rintse idanu Nusaiba tayi tana tuno da kalon tijaran da suka shirya ma Amrah , da irin Abubuwan da suka yi mata da nanaa . Wasu irin hawaye ne suka fara bin Kuncin Nusaiba a hankali take furta " Ban san ita din jinin mu Bace , wallahi rayuwar Amrah abin tausayi ne , Tausayi take bani....kawai sai ta fashe da kuka tana zama nan ƙasa tare da cigaba da kukan ta don ta rasa meke damunta da rayuwar ta .
Yau Adamu ya haɗu da sharrin gidan ɓaidu .
Mata ne su kusan goma sha suka faɗa masa Ɗaki ko wacce da abun duka , wannan muciya wannan takalmi wannan sanda kowa da Abin dukan ta . Su Salamatu sune sahun gaba , wanda suna shiga Salamatu tayi baya da gudu tana faɗin " Ya ilahi ALLAH . Kawai sai matan suka hada baki suna fadin " Ƙwarto....! . A razane cike da tsoro Adamu ya miƙe daga Ƙwancen da yake tsirara tuffffff dama haka yake zama shi ga dan iska . Rufe ido Salamatu keyi wai kar ta ga haramun nan take Safara'u ta karbi muciyar hannun Salamatu tana faɗin " Ai a hakan zamu ci uban sa dukan sai yafi shigar sa ......topah yau ake yin ta . Mu tara a next page don jin yanda zata kaya .😍
**
Ƙwance take sanyin Ac na ratsata wanda sosai Take jin sanyi daga cikin Zuciyar ta . Amrah ce kwance a 2str na Falourn idanun ta na a Lumshe , tunanika ya addabi zuciyar ta . Haka a ko wacce rana sabon kewa da Soyayyar Nurayn ƙara samun gurbi yake a zuciyar ta . Motsin taku taji wanda hakan bai saka ta ta ware idanun ta ba har sai da ƙamshin sa ya fara Mata sallama . Cikin sauri Amrah ta ware Lulun idanun ta tare da zuba su a fuskar Nurayn, wanda ta ganshi yana takowa zuwa inda take . Sauke ƙafafun ta tayi kasa tana mikewa daga tsaye tare da bin sa da wani irin kallo , ƙwallah na ciko idanun ta. Ƙyau ma ya ƙarayi abin sa ,wato dai da gaske ne ya cire Ni a lissafin rayuwar sa ...........!
Littafin Yar tsakar gida na kuɗi ne ₦500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan book 1&2 kk buƙata complete ₦500 👌🏻 .
*Anty Aysha Mamanteddy*
[9/5, 1:00 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: Wani irin murmushi taga yayi yana ware mata hannayen sa tare da furta “ Come and hug me ” . Wani irin kallo Amrah tayi masa tare da jin mamakin rainin hankali irin na Nurayn . Yanda yaga ta tsaya masan tana faɗawa duniyar tunani yasa shi Takowa zuwa inda take yana sanya hannayen sa tare da Rungume ta har yana ɗan rage tsawon sa tare da kokarin kissing din ta , saurin janye jikin ta tayi daga nasa tana kokarin Matsar da kan ta baya ,taji ya kuma rike hannun ta duka biyun cikin ɗan yin ƙasa da Muryar sa ya furta “ Yau ina cikin farin ciki Amrah , Ammie da ....Ya isa haka Noory .! Ta katse shi tana kallon idanun sa kana tace “ Burin ka ya cika , Baba na ya Maida Ammie matsayin matar sa . Kayi farin ciki ba ? Shine zaka zo mun a yau tun da Abin dake fata ya tabbata , to indai rayuwar farin ciki ne tsakanin mu babu . Kasa mata magana yayi ba don komai ba sai mamakin furucin nata ,wanda bai taɓa kawowa zata iya faɗa masa makamancin su ba . Cike da salon sa na son ganin ya dakatar da fushin nata ya yi saurin takawa yana ƙoƙarin haɗa ta da jikin sa ya Rungume amma sai tayi kuma janye kan ta da ƙarfi tana juyawa a fusace tare da basa wuri tana nufar Bedroom din ta . Wani irin gumi ne ya fara tsatstsafo ma saman Goshin sa . Idanun sa sun fara zafi sam bai kawo zai tadda hakan ba , bai kuma taɓa ganin ɓacin ran Amrah ba , bare kuma akan sa. Humm ....Wani irin Gwauron numfashi ya ja kamin ya sauke yana furzar da zazzafar huci kana yayi saurin bin bayan ta . A bakin Bedroom ɗin ya tsaya yana kai hannun sa tare da murɗa Handle Door ɗin but unfortunately yaji ƙofar a rufe alamu tasaka key ta rufe . Cikin Wani irin murya na sarewa da ban haƙuri ya fara kiran sunan ta “ Amrah... Amrah please ki buɗe ƙofan, zan faɗa Miki wata magana kiyi Haƙuri ki buɗe mun ” . Jin shirun ta na kusan mintuna biyar bata tanka sa ba yasa shi ƙara kiran sunan ta yana mata magiya amma duk a banza . please Amrah I can't without you....Noory ya kamata ka dakata da Wa'annan wasannin kwaikwayon naka haka .! Ba zaka iya ba tare dani ba ka tafi ka barni fiye da kwanaki takwas yanzu kazo mun da Wa'annan zancen naka marasa Amfani. Yanzu na fahimce ka sosai kuma na gode da yanda kake yi mun ko ba komai You teach me a lesson . Hakan ma ya wadatar . Muryar Amrah ya katse shi wanda take maganan cike da daga murya da masifa wanda bai san ta da shi ba , tabbas yasan yau ya kaita maƙura .
Amrah Nine fa Nooryn ki don Allah , katse maganan nasa yayi yana furta “ Ohk na fahimce ki , Nasan nayi Miki laifi but pls ki buɗe mun sai ki hukunta Ni Kinji baby na.? Noory Wannan wasan da ka sabamun a da baya ne , amma a yanxu kallon ka nake yi kar ba zaka ƙara raina mun Hankali ba . Lumshe ido Nurayn yayi yana Haɗa kan sa da Ƙofar a hankali, idanun sa sun sauya a dai dai wannan lokacin . Tabbas ya fahimci Amrah ta gane inda ya dosa , kuma ta nuna masa ba zata amince da komai da yake buƙata ba . Amrah ke fa matata ce , kin san fushin Allah zai hau kan ki saboda ina buƙatar ki kuma kina ƙoƙarin ƙaurace mun Zina kike so naje nayi .?