Sashe 13
Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Book 3
Littafin na kuɗi ne ₦500 book 1&2 book 3 ₦500 duka ₦1000 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .
Ga masu buƙatar Audio books ɗina zaku iya subscbing to my YouTube channel #maman teddy tv .
#Bonus
Ba don komai yasa nayi wannan shafin bonus ba face masu yaɗa maganann ƙarya akaina 🤨 .
Akwai maganan da naji yana yawo a media kan cewa Ni maman teddy na daina rubuta littafi, a jiya mutanen da suka kira Ni ALLAH yayi yawa da su . Ina godiya da Soyayyar ku Wallahi kun nuna mun nakai inda Ban zata ba , a yanda kuka yi ta kirana a jiyan nan. Ban da Masu mun magana ta hanyar tagging dina a wasu grps wasu kuma sun biyo Ni private suna mun Tambayan wai shin da gaske ne ance kin daina rubuta littafi🤔. Don Allah wai masu yaɗa wannan ƙarya kun Meye riban ku nayin hakan ..? Meye amfanin shi don kin bude ido yau kin ga babu mamanteddy a media ribar me kika tsinta kika samu ? Dama wata rana duniyar ma duka barin ta za'a yi Bama littafi ba ko rubutun shi , Amma kawai ki zauna ki shara karya da zance just because nayi wasu yan kwana ki bana online, na samu matsala Shikenan ke har kin samu damar watsa labarin ƙarya 🙁 to kin yi kokari ...Masoya na ku sani nice dai taku maman teddy Kuma Ni ban daina rubutu ba ina nan , idan na daina rubutu wa zai ƙarike mun littafin Yar tsakar gida🤣. ku ƙara gyara zama don nan ba da jimawa ba zan sakar maku sabo mai dauke da zazzafar salo , don haka rubutu yanzu na fara indai da rai da lapiya ✍🏻 . Taku har abada Anty Aysha Mamanteddy
08081202932.
15-16
Wani irin kallo Baba Adamu keyi masa irin na tausayawa da kuma rashin sani kana yace “ Abun da Larai tayi maka Auwalu ALLAH ya saka maka ”. Subhanah...! Yaya , ƙwarai wannan shine ƙarshen Abin da zan iya cewa kenan, don cuta sun cuce mu sun zalunci kan su. “ Cewan Baba Adamu yana kallon Kanol wanda idanun sa ke akan Baba Adamu yana sauraren kalaman sa tare da rasa Fahimtar inda suka fuskanta . Yaya meke faruwa ne ?. Alhamdulillahi . Kaga Yanzu ne zan faɗa maka komai da ya faru tun daga ranan da ka bar cikin gidan nan har Izuwa yau da muke zaune tare Dani da kai . Gyara zama Kanol yayi yana mai gyaɗa kan sa irin nasu ta manya , anan take Baba Adamu ya fara kora masa labarin tun daga Farko har ƙarshe na gidan Ɓaidu . Duka a ciki babu abin da yafi ɗaga mawa Kanol Hankali tare da saka Zuciyar sa zullumi da Tausayi irin Rayuwar Ƴar sa Amrah . Tabbas a yau yasan Waye Nurayn da kuma gudummawar da ya taka a rayuwar ta , dole a Wancen ranan ta nuna tana son ganin sa duk da laifin da yayi mata amma sam bata ji ƙiyayyar sa ba . Wani irin bugawa ƙirjin Kanol yake yi da ƙarfi tamkar zai fito ya tarwatse . Wani irin gumi na karyo masa a hankali yake sauke Hular kan sa , cikin wani irin sarƙaƙƙiyar murya ya fara cewa “ Yaya don Allah a rufe wannan Maganan kar a bari maganan larai ya fita duniya , ko ba komai dole za'a danganta ta da iyalina , ta zauna har lokacin da zata haife cikin jikin ta . Ita kuma Zuwaira za'a bata Ɗaya daga cikin gidaje na nata ne har abada , ta zauna can har Allah ya bata wani mijin, Ni dai taimako daya nake so shine maganann Larai a rufe ta a cikin gida . Girgiza Kai Baba Adamu yayi cike da Jajantawa don Abin da ya faru da larai hakƙi ne da kuma mugun tan ta , tare da sharrin ta duka sune suka komo mata.
**
Misalin ƙarfe biyu da rabi na yinin wannan rana aka mai da Auren Kanol ɓaidu da matar sa Ammie Hafsat wanda farin ciki har a halin Ɓaidu ba'a Magana . Su Zuwai kuwa an koma tamkar mujiyoyi kwakkwaran motsi bata iya yi daga inda take ,kullum tana cikin ɗaki tana kukan zuci .
“ Cike da mamaki gami da Ɗaga Murya Lanti ke cewa “ A'a Malam ,wallahi wannan ba mafita bace, ta yaya zaaa ce mu sanya ido har ta haife dan shege ,bayan cikin jikin ta ƙarami ne tasss za'a iya zubar dashi , sai mu bari yazo duniya. ? A'a fa wannan bai ma yi ba , ku dai ƙara Tunani . Yanzu abun da za'a yi a ganina shine a samu Larai ta faɗa waye mai cikin don a sani . Shiru Baba Adamu yayi yana gyaɗa kan sa don maganan matar nasa akwai abun dubawa ciki . Tom Shknn yanzu zan samu sauran mazan gidan sai muyi Magana. Bani Ruwa a buta nayi alwala . To malam . Lanti ta furta tana muskutawa tare da nufar inda take aje butocin ta don ta basa .
**
Zaune Nurayn Aslaam Zaid Suke suna shan Lemun Exotic tare da ɗan taɓa fira , gyefe guda snacks ne kowa da abun da yake buƙata , fuskokin su na kalla inda ƙarya ne na hango wata matsala,duk da Kowannen su akwai abin da yake saƙa ma Zuciyar sa ,amma da yake akwai su da gogewa ta rayuwa da wayewa sam sun ƙi Bayyana ma junan su hakan . Wayar Nurayn ne ya fara ruri alamun kira wannan yasa shi Miƙa hannun sa zuwa mini Centre table din Dake Gyefen shi .
“ Hello...”
Nurayn kana ina ne ? Nurayn komai ya kammala , yau mafarkina ya zama gaskiya Nurayn, na koma hannun miji na Uban ƴa ta wanda na dade Tsawon sheƙaru ina bulayi na ƙi Aure Ba don komai ba sai don .....wasu irin Ƙwallah ne suka Gangaro Kuncin Ammie Hafsat wacce take Tsakiyar Falourn ta tana masa wannan maganann gaba ɗaya idanun ta sun rufe da farin ciki . Ta rasa da wane zata yi sharing wannan farin cikin nata sai dan ta Nurayn . Congratulations mom . Ya furta yana sakin murmushi tare da datse kiran yana Juyawa tare da kallon Inda su Aslaam suke . Yesss Alhamdulillah , ya furta yana sakin wani ƙayataccen Fara'a kana yace “ a yau an maida Auren Ammmie” .
Murmushi Aslaam yayi kana ya miƙe yana takowa zuwa inda Nurayn yake yana hada hannun sa da nashi tare da furta " Na taya ka farin cikin hakan . Na gode .! Uhmm dan juyawa yayi yana kallon ɓarayi guda tamkar mai tunani kana ya kalli Nurayn yana mai cewa " Amma yanzu dai zaka dawo da Amrah ko? . Ɗagowa duka suka yi suna kallon juna har da Zaid kana daga Bisani su fashe da wani irin dariya mai tattare da bayyana tsananin farin ciki da annuri da jin dadi . Yanda suke dariyar Ni kaina sai da nayi mamaki tamkar basu bane Wa'annan marasa kirkin wanda Fara'ar su baka gani bare kuma ta kai ga har dariya irin haka 😹 . Murmushi Nurayn yake yi burin shi ya cika yau Zai je don yaga Babyn nasa wacce ta gama galabaita da rashin shi .... Yau duk ƙin ta dole ta haƙura dole kuma ta ƙaunaci ammie ,a cewan Sa kenan ...!
**
Mata ne cike a ɗakin Larai ciki har da Lanti a takaice Karkatakaf iyaye mata ne na cikin gidan Ɓaidu tsaye a kan larai sunyi mata caaaahhhh kowa da Abun da yake fadi masu kuka nayi masu zagin ta nayi . Yanzu dai duk ba wani magana ba , a zubda cikin nan shine mafi alheri . Cewan Salamatu tana kara gyara curin daurin dankwalin kan ta wanda ta naɗa shi kaman gammo . Aka zubar da ciki ai Mutuwa Zata yi sheƙaru fa sunyi nisa . Cewan wata daga ciki su ,inda Inna Lanti ta furta " Da wani masifar ai gwara wani. Astagafurullaha inda Nine ai gwamma mun mutuwan da rayuwar sai na fi zaɓin mutuwa ta yafi mun alheri .
Yanzu Larai taimakon kan ki Zakiyi ki faɗa mana wanda kuka yi wannan aika² n tare . Cike da matsanancin kuka Larai ta fara masu kwatancen Adamu wanda farin sani sun san shi baƙo ne yazo daga Wani ƙauyen Bauchi . Laha'ila ha'illahu.....dakin ya amsa yayin da Nan take Salamatu ta furta " yanzu larai wannan karamin jaririn yaron ne yayi Miki ciki? Yanxu larai wannan dan cikin naki ne har kika Wangale masa kafa ya danna Miki Accilarn sa . Gaskiya larai kin cuci kan ki da yaran ki Wallahi .
Sharrin shaiɗan ne ,Nima bannsan ya akayi ba , ƙaddara da....don Allah Larai bar mu haka . Cewan Lanti tana daga mata hannu kamin Salamatu tace " Tom yanzu zuba ido zamiyi ko kuwa mu je masa ne muci uban gindin iskancin nasa ?. Don yau sai yasan shi ƙaramin ƙwarto ne dan uban sa . To ai su malam sunce basa son maganan nan ta fita .