Sashe 21
Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyawa tayi a fusace tana ƙoƙarin barin falon taji ya riƙo hannun ta ,a wani irin fusace ta Juyo tana kallon sa . Gani tayi ya miƙe idanun sa hawaye ke zuba . Saurin kallon sa tayi cikin wani irin murya ya furta " Nayi laifi Amrah nayi Kuskure don Allah kiyi hakuri kar ki barni 😭💔 . Hannun ta takai cikin sauri tana tallabo Kuncin sa ,wanda nan taga ya durƙusa a gaban ta yana Daura Gwiwowin sa ƙasa , tare da riƙo hannun ta yana Cigaba da cewa " Ke nake so kullum koda yaushe har mutuwa na . Na zaɓi na bar kowa nayi rayuwa dake ke kaɗai , Amrah kiyi hakuri kiyi Haƙuri Ban san me zance ba , amma Ni mai laifi ne , Wallahi nayi Miki Alƙawari ba zan ƙara giya ba kuma baxan ƙara mu'amala da mata ba . Don Allah ki tsaya tare Dani ki daina furta zaki barni zuciya ta zata iya kamuwa da ko wani irin ciwo Amrah na rasa ki mutuwa zanyi........! Yayi maganan cike da sarewa . Kuka Amrah ta fashe masa dashi tana saurin Rungume sa tana cigaba da rera masa kukan a hankali tare da riƙo sa sosai tana manna sa da jikin ta . Noory ka tashi Nima Fa kawai ina faɗa ne amma ba zan iya barin ka ba ,ba zan iya tafiya ba ko nata fi zan dawo 😄 tayi maganan tana ɗago fuskar sa tare da sakin masa murmushi mai haɗe da yar dariya na son kwantar masa da hankali . Hannun sa ta riƙe tana cewa " Noory taso muje ciki " . Ohk zan kira ki Miki Baba ko? . A'a na fasa sai zuwa gobe .
Mmnteddy .
[9/6, 2:36 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: Book 3
Yar tsakar gida
Tayi maganann tana kallon sa tare da masa murmushi ka manta yanda muka yi da kai ɗazu idan na gama cin abinci.? Murmushi yayi kana yace " Na sani yanzu muje kiyi barci sai kin tashi. Janye hannun ta tayi daga jikin sa tana shagwaɓe masa fuska kana tace " a'a Ni dai sai dai idan har yanzu baka sauka ba ,kuma damuwa a tare da kai shine nan kawai zaka ce haka . Ka manta cewa fa kayi kullum idan kana tare Dani baka da sukuni. Ta ƙare maganann tana kafe sa da Lulun idanun ta . Tabbas maganan ta gaskiya ne , amma kuma baya son takura mata ne ga kuma laifin da yake gani yayi mata . noory tuninn mene kake yi haka .? Dan Numfasawa yayi kana yace " Zan so hakan . Dariya tayi tana riƙo hannunn sa suna nufar Bedroom ɗin fuskar su cike da Annuri tamkar babu abin da ya taɓa shiga na damuwa ko rikici tsakanin su .
**
Yau fa kwana biyu kenan da mutuwar Larai kuma duka Wayoyin Nurayn a kashe yake. Aslam bashi da hali shima ko ƙyayarsa bare yayi zaman makoki . Don yanda Nurayn ya tsani larai da Zuwai haka shima . Wannan yasa ko da yaji mutuwar nata ko gezau baiyi bare yace Allah yajiƙan musulmi . Aslaam wai kana da lafiya wacce ta mutu matar Dad ne fa ? Mommyn Aslaam tayi maganan tana kallon Aslaam wanda yake zaune ƙafan sa a harɗe ya daura bisa Centre table dake gaban sa . Dakatawa da latsa wayar hannun sa yayi kana ya ɗago yana kallon Mommy . I'm sorry Mom ba zan iya zuwa bane . Ohk tayi maganan tana daure fuska kana tace " Zaka iya taimaka mun ka nemo Numbern nurayn don a sanar masu Amrah taxo . Mommy Kin manta ne daxu fa a gaban ki na kira Numbern sa baya tafiya ,but a jiki na nake ji komai lapiya Cox kin san Wancen lokacin bai samu sakewa da matar sa ba , amma yanzu ya samu hakan shi yasa baya son damun ku ne shiyasa ya kashe Wayoyin sa.
Tsayawa Mommy tayi tana kallon sa cike da ɓacin rai tace “ Mara kunya kawai ,tashi yau ko menene tasa ka zanyi Wallahi sai kaje wannan gaisuwar mutuwan . kallon Mom din nasa yayi kana ya mike yana faɗin " Mom bathroom zan watsa Ruwa . ina nan ina jiran ka mintuna sha biyar na baka . Wuce momy yayi yana hayewa stairs tare da nufar Bedroom din sa .
Haka a wannan rana Mom ta tasa shi sai da yaje gidan Ɓaidu ,inda Anan yaga sababbin yan uwan sa wanda bai san suba ma a duniyar sai a ranan . Matan Aure duka yayyun sa ciki har da Yaya Ikilima. Sosai suka nuna farin cikin ganin sa , wanda a da baya ya ɗan share su haka bai sakin fuska ba ,amma ganin yanda wannan taxo ta ganshi wannan ta fita kowa cike da farin cikin sun ga dan uwan sa yasa Aslaaamm sakin jiki da su .
Zaune suke tana kwance jikin sa yana latsa wayar sa wanda kunnawan sa kenan kira na shigo masa . Ɗagowa tayi tana kallon Nurayn Wanda ya ɗan ɓata fuska yana cewa “ bana baƙon number ” . A'a NOORY ka dauka yau fa kwana hudu Wayoyin ka a kashe suke . Baka san waye ba please ka dauka . Jin maganan nata yasa shi daukar kiran yana sakawa amsa kuwa . Assalamu alaikum. Muryar Kanol Ɓaidu ya katse wanda duka basuyi tsammani ba . Kamin Nurayn yayi magana Amrah da sauri ta miƙe daga ƙwancen tana faɗin " Baba kaine.? . Murmushin sa taji yana cewa" Amrah Nine tun da kin manta da Baba da kowa ma . Baba Ina Mommy da Ammie ya Aslaam fa .? Duka suna lapiya . Bara nayi magana da Nurayn . Kallon Nurayn tayi wanda ya fara gaisar Da kanol cike da girmamawa. Bayan sun gama gaisawa ne Baba Kanol ke sanar masa da mutuwar Larai wanda daga ji Amrah ta zabura tana saka ihu tare da Fadin " Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un .....Datse kiran Kanol yayi jin ihu ta ,wanda hakan yasa Nurayn saurin riko ta yana ƙoƙarin rarrashin ta . Don shi dai baiji komai don larai ta mutu ba . Da kyar ya samu ya iya shawo kan ta , a haka a wannan rana ta kafe masa sai taje gida . Da yammaci wuraren 5:30pm suka isa gidan Ɓaidu .
Farin ciki ba'a magana gurin iyayen nata ciki har da Ammie Hafsart Amrah ta chanja ko ba'a faɗa maka Nurayn bata kulawa tayi ƙiba dumurmur daga Ni kasan da shigan ciki da Hutu . Tamkar ba Amrah ba wannan yar tsakar gidan . To Allah kenan mai yanda yaso da daukaka wanda yaso . Ƙarshen zalunci wahala kam Amrah tasha amma kuma a yanzu fa sai dai maliya suyi kuka. ƳAR TSAAKAR GIDAA Gata yau a raye bata mutu ba tare da gatan miji ɗaya tamkar da dubu Nurayn . A ranan taso ta kwana amma Nurayn ya mutsike ido shifa da matar sa zai koma . Haka dole Amrah ta biyo sa don tasan bazai iya barci ba tare da ita ba a gyefen sa .
A haka rayuwa ya cigaba da tafiya bayan wasu yan lokaci Baba kanol yasa aka fara cire tobalin ƙasan gidan ɓaidu ko wani ɓangare aka bi ana rushewa tare da Ɗaura ginin bulo da bulo . A yan watanni aka gama gine gidan Ɓaidu ya koma wani irin Katafaren gida kaman estate House kowa da bangaren sa . Haka baba Kanol ne mai daukar nauyin cin su shan su komai na al'umman wannan gida . Ya'yan sa maza da suke su kusan Hudu duka ya fitar dasu kasan london karatu . Yayin da matan ya'yan sa da sukayi Aure Ya basu kudi masu kauri don suyi jari su kulla kan su . Rayuwa kenan kana naka ALLAH na nashi .
Bayan watanni Tara .
A hankali suke saukowa daga Stairs din Nurayn na riƙe da hannun ta yana gaba kaman dan jagora . Amrah na bayan sa da ƙaton cikin ta wanda haihuwa Yau ko gobe a kowa Ni lokaci . Ji yayi ta ja hannun ta ta tsaya tana kama hannayen ta duka biyun wannan yasa Nurayn juyowa yana kallon ta . Shagwaɓe fuska tayi tana masa alaman yayi mata kiss 😘 da bakin ta . Murmushi ya sakar mata mai nuni da narkakkiyar soyayya takowa yayi yana Hayewa Stairs din da take kana ya sumbaci saman Goshin ta yana kuma yin ƙasa tare da sumbatar Gyefen kuncin ta ,ƙasa taga yayi yana ƙoƙarin kama laɓɓan ta nan ta saki Murmushi tana ture shi tare da kama hannun sa suna yin ƙasa ....dariya suke yi cike da nuna soyayyar juna suna nufa falourn gidan .
Handle Door ɗin falourn suka ga an murdo sanye take cikin shiga na kamala Abaya tayi Rolling sai dai gayunan yana nan , fuskar ta cikin wannan crazy glass din da ta saba sakawa . Oyoyo.....! Amrah tayi Maganan tana saurin takawa inda Nusaiba take .... Fuskar ta dauke da fara'a ta sauke Gilashin fuskar ta . Oyoyo Maman Twins ya nauyin jikin Bara na ƙariko huta daga nan . Dariya Amrah tayi tana dakatawa Nusaiba na isowa inda suke . Hugging din Amrah tayi tare da yin ƙasa tana dafa cikin jikin ta . My Unborn babies How far how are you......? Murmushi Amrah tayi tana faɗin " Kema kin zama Noory kenan .? Ɗagowa Nusaiba tayi tana kallon nurayn kana tace " Ya Nurain laifi nayi maka baka ce mun komai ba ?. Yanda tayi maganan dariya ma ta bashi . Ni da bakya ta kaina Amrah kawai kika gani tun shigowar ki . Ohhhh to kishi kake yi da hakan ?.