← Book details Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 23

Sashe 16

Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba ɗaya gidan an dade , Baba Zuwai ce kaɗai tsaye ta rafka tagumi . Ina ma zan mutu na huta . Abun da ta furta kenan kamin ta juya tana shigewa ɗakin ta . Can sai gata da ƙullin kayan ta wanda basu fi hanci bakwai ba tana ficewa gidan cikin sauri har da waiwaye don tace yanda Annabi yabar gidan duniya to ta bar gidan Ɓaidu .
Lanti ce ta fito daga Dakin ta don duk Hayaniyar da ake yi bata sani ba Kasantuwar barci mai nauyi da ya dauke ta . Tsoro ne ya kamata ganin gidan shiru . Saurin mutsika idanu take yi tare da tunanin a raye take ko kuwa mace ko kuma mafarki take yi ne dai ? Yau gidan ɓaidu ne babu kowa daga yara har manya 🤔Abin gaskiya kam da mamaki . Aje butar hannun ta tayi tana sheƙawa da gudu tare da nufar Hanyar barin cikin gidan .
**
Zaune Ammie Hafsat take akan Sallaya hannayen ta sama tana addu'a idanun ta na zubda hawaye na Godiya ga Allah . Alhamdulillah Allah ka cika mun burina a yau zan tare da Mijina uban ƴana Allah bani da kalmar da zan iya nuna maka na Godiya . ALLAH ga ƴa ta nan Allah ka basu zaman lapiya da mijin ta kasa mata haƙuri da juriya, Allah ka wanzar da zaman lafiya ta har abada tsakanin Amrah da Nurayn, ya rabil alamin ya hayyu ya ƙayyum ya Ya sittiru ya Rahman ka duba Ni ka dubi zuciyar Ƴa ta Allah kasa mata soyayya na koyaya ne ka sanyaya zuciyar ta daga wutar ƙiyayya n mahaifiyar ta . ALLAH Ubangiji ka ƙara mana arziƙi da wadata da kuma lapiya mai amfani . Addu'oi ta fara yi a hankali kana ta sauke hannun ta tana shafa ma fuskar ta . A hankali ta muskuta tana miƙewa tare da nufar inda ta aje hand phones ɗin ta . Kallon screen ɗin tayi tana dan kankance idanun ta na manyan ta don hasken screen ɗin yana taba idanun ta . Latsa nomban Nurayn tayi tana fara danna masa kira.
Littafin Yar tsakar gida na kuɗi ne Complete ₦1000 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 . Sorry for the late update. Sannan kwana biyu kunji Ni shiru bana jin dadin jiki na ne amma yanzu Alhmdlh.
*Anty Aysha Mamanteddy*
[9/5, 2:46 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: Fitowar sa kenan daga Bedroom ɗin sa ransa ba dadi tun jiya Amrah da ta rufe kan ta bata buɗe ba har safiyar yau . Sanye yake daga shi sai ƙananun kaya na shan iska , T.shirt da short nicker wanda bai kai gwiwa ba . Babu abun da kake ji yana tashi daga jikin sa face dadɗan ƙamshin nan nasa dama shi mutum ne ma'abocin son ƙamshi . Suman kan shi ƙwance yake wanda ya sha gyara zuwa sajen fuskar sa wanda yanzu ya ɗan fara yawa kaman ƙasumba . Tsayawa yayi a tsakiyar Falourn ganin har zuwa wannan lokacin bata fito ba , a hankali ya Lumshe idanun sa yana Kai hannun sa tare da shafa Sajen Fuskar sa , Ya kamata a rage wannan suman haka ,ya furta a sarari dai dai wayar sa na fara ruri (Ringing) . idanun sa yakai yana zuba ma screen ɗin lumsassun idanun sa kamin yayi saurin ware su yana Mai daga kiran tare da cewa “ Ammie An tashi lapiya?” . Fara'ar Ammie ne ya ƙaru jin Muryar sa a sake babu wata damuwa da ta fahimta tare dashi don bai nuna mata hakan ba. Nurayn kana lapiya ? . Yess Ammie I'm normal ” . Kina son magana Da Amrah ne ? . Yayi maganan yana mai sauraren jin mene Ammie Zata ce . Ɗan Jimm Ammie tayi kana tace “ Eh Nurayn idan ba damuwa ” . Ohk Bara zan kira ki bana kusa da ita yanzu . Cike da jin wani Sanyin Zuciya Ammie tace “ Na gode Nurayn ALLAH yayi maka Albarka. Murmushi yayi wanda sai da Hushiryar sa ya bayyana kana yace “ Amin ya Ammie ” . Datse wayar yayi yana ɗan rufe idanun sa tare da tunanin to ya ma zaiyi ma Amrah a halin yanzu ?. Wacce shi kan shi take fushi dashi to Tayaya zai hada ta da Ammie .? . Saurin juyawa yayi yana nufar House compound tare da kiran daya daga cikin securities din wannan gida . Kallon shi Nurayn yayi yana cewa “ Spire keys ɗin gidan nan zaka kawo mun ina falour . Ohk sir .... Juyawa nurayn yayi yana shigewa falour yayi da Securitin yayi saurin nufar ɓangaren su don dauko masa makullan .
**
Karo da Baba Yusufu Inna Lanti tayi a zauren ƙarshe na barin gidan , hankalin sa a tashe yake furta " Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Lanti Lanti Yau ba larai larai ta mutu....! Wani irin zabura Lanti tayi tana furta hasbunallahu Wani'imal wakil la'ilaha'illah . Malam yusufa mai kaka cewa? Wata larai din ce ta mutu ?. Rai kenan ba bakin komai yake ba . Cewan Baba Yusufu kana ya kuma cewa " Lanti ki yi maza a gyara Ɗakin ta za'a dawo da ita . Malam Tayaya Larai zata mutu? Ɗazu fa mukayi tsaye a kan ta😭 kawai sai ta fashe da Wani irin kuka mai tattare da nuna tashin hankali da alhini . Shikenan Shikenn Larai ta mutu Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un....Haba Lanti kuyi haƙuri suma suna can a asibiti suna ta ihu mara amfani yanzu addu'a kawai ya kamata kuyi mata . Ba wannan iface ² n ba . Juyawa Lanti tayi tana sharɓan kuka tamkar ƙaramar yarinya hankalin ta ya tashi ainun matuƙa .

Yiiiii yiiiiii Ihun Zulai da Sauran Ƴammatan gidan ya katse su Wanda haka suka jeru a tsakar gidan suna wani irin kuka . Lanti ne ta kalle su wanda take shiga da tabarma dakin Larai kamin tace " Kuyi hakuri Yarannan ALLAH yafi mu son ta shi ya dauki Abin sa. Hannu takai tana sharce ƙwallahn da suka taho mata kana tace " Addu'a shine yafi kamata muyi mata a yanzu . Amma Ni kaina mutuwar Larai ya taba Ni ya bani mamaki , ba ciwo ba komai ɗazu fa muka gama fitowa daga Ɗakin ta . Zulai ne ta katse ta cikin kuka tana cewa " Likitoci sunce dukan cikin jikin ta tayi tayi wannan ya haddasa mata ɓallewar jini wanda hakan gashi ya zama sanadiyar rasa rayuwar ta . Kuka suka kuma fashewa dashi suna kiran sunan Allah tare da furta" Allah yajiƙan ki Inna Larai.

Miƙewa Zulai tayi tana faɗin " Baba Zuwai wai barci take yi ne ,duk abin da ake bafa ta sani ba . Hajara ce ta kalli Zulai kana tace " A'a kaman fa ɗazu naga ta fito badai tayi magana bane . Nufar Ɗakin Baba Zuwai tayi tana furta " Baaba baaaba....! Tana daga labulen tare da kutsa kan ta . Kusan mintuna Uku sai ga Zulai ta fito tana kara kwarma ihu tare da cewa “ Mun shiga uku Baaba ta bar gidan nan wallahi babu kayan ta . sakin tabarma Lanti tayi tana cewa " Wani irin tabar gida? Ki dai kara dubawa . Cikin kuka Zulai ta furta da gaske Bata babu kayan ta . Kasa magana Lanti tayi kan ta gaba daya ya kulle . Muryar Hajara ne ya katse su tana cewa kila itama asibitin taje , yanzu mu kira su Anty Ikilima mu sanar masu da rasuwar Inna Larai .
**
Motsin Ƙofan da take ji ne yasa Amrah ɗan cabe baki hankalin ta kwance take cigaba da shafa cream din tana bin jikin ta dashi , a zuciyar ta tana cewa"Kayi ka gama , Ni snacks da lemun fridge Dina zai ɗauke Ni tsawon kwana ki biyu zuwa uku ,daga nan ka gama nacin Naka.......Saurin juyowa tayi jin an bude ƙofar shigowa Nurayn yayi wanda hakan yasa Amrah saurin miƙewa tsaye . Sam ta manta da yanda take . Don daga ita sai bra da Pant ko kaya bata saka ba . Ita a dole ga mai rayuwa ita kaɗai . Hannun ta duk cream Bata riga ta shafa ba .

Wani irin murmushi taga yana mata yana bin dukan ta da kallo ta ƙara ƙyau ta ko ina dama kuma abun ka ga kyaƙyƙyawar mace . Wow 😍 ya furta yana kallon ta tamkar ya samu tv. Ɗaure fuska Amrah tayi tana hade giran sama da ƙasa. Me ya kawo ka Bedroom ɗina kuma ina shiryawa.? . Ɗan Haɗe Gira yayi yana ɗaga mata Wayar sa tare da Ɗaga mata Gira “ Da Ammie nake so kuyi magana ” . Magana...? Nace mata mene.? To Ni ina ruwa na da ita wai .? . Ohhhh ALLAH . Y furta a zuciyar sa a sarari kuma shan kunu yayi yana cewa " Yanzu gudun ki ya kare zaki yi abun da nace Miki ko kuwa sai na dauki mataki . Haaaaahhh🫨 ta bude baki tana kasa ce masa komai tare da kafe sa da ido . Rufe bakin yanzu zan kira ta ki gaishe ta . Ba zan amsa ba . Tayi maganann tana juya kan ta tare da kallon wani ɓarayi da ban tana cigaba da cewa “ Wani mataki zaka ɗauka ?”..

Ita dai kamin tayi Wani yunƙuri ta ganshi ne a gaban ta yana fizgota tare da faɗawa jikin sa . Hannun sa taji yana ɗaurawa a tsakiyar bayan ta tare da Shafawa yana wani irin sauke Numfashi . Idan baki yi ba ,kin san fyade...? Haaaaahhh bude baki tayi da sauri tana waro idanun ta waje tare da saurin gyada masa kai alamun eh . To shi zan Miki. Yayi maganan fuskar sa babu wasa . Dama ai lokacin nan fyaden kake mun kullum 😢 tayi maganan idanun ta n kawo ruwa tsoro na kamata . Dariya ne ya kusa kamasa ,amma sai ya dake cikin Muryar sa yake fadin " A'a Ni ba fyade nake Miki ba Amrah, Yanzu ne idan kika ƙi yi mun abun da nake so zan Miki fyaden . Kuma kin ga dai daga Ni sai ke ne .
Chapter 16 · 0% Book details