← Book details Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 23

Sashe 4

Yar Tsakar Gida Book 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lumshe idanun sa yayi yana ware su a hankali kana yakai hannun sa yana ɗaukar Lemun dake Gyefen sa yana ɗan sip on kaɗan , kana ya sauke Amrah....! Ya furta sunan ba tare da ya san zai Ambata ba . Saurin Rintse idanun sa yayi yana Dafe kan sa tare da saka hannu yana hautsina suman kan sa Wanda yayi tsawo da cika tamkar na larabawa. Oh my god..! Ya furta kana yasa hannun sa yana ture laptop ɗin dake Gyefen sa. Ƙwantar da kan sa yayi bisa Resting chair din yana Lumshe idanun sa tare da cizan laɓɓan sa da ɗan ƙarfi na kasa . Nikam Ganin wannan hali da ya fara shiga yasa Ni saurin Matsawa ina ƙara duban sa da kyau, don daga shi Sai Jogging Pant da da wata riga irin nasu ta maza mai kamar shirt . Sauke Numfashi yayi yana saka hannun sa tare da kama ɓangare guda na zuciyar sa dake buga masa da Sauri da Sauri , wanda abun ka ga likita tuni ya san inda damuwar tasa take. Idanun sa sun kaɗa sunyi jah , Amrah kin sauya Ni , kin chanja Zaid , a dai dai gaɓa kuma kin tafi kin barni , Are You going to leave me forever? Or you will come back my lab ? Please stay with Zaid forever...! You make my eyes shine I love you more ❤‍🔥 dear. Wani irin huci ya saukar yana ware idanun sa kana a hankali ya sauke karatun sa yana Zura Room silipers din tare da nufar Bathroom room don ya watsa Ruwa ko yaji sanyi a zuciyar sa .

Ganin haka yasa Ni Uwar teddy saurin kautsa kaina don na nado maku lissafin dake ciki , just to be make you happy my fans. Jin daɗin ku shine nawa , be happy always my people 🥰 .
Ƙwance yake cikin baf din idanun sa a Lumshe ruwan ya kawo masa har wuya alamu hakan ya fi masa da daɗi yana samun sassauci daga cikin Zuciyar sa . Kusan Mintuna Goma yana a haka bai motsa kana daga bisani ya fara ware wannan tsayayyun idanun nasa yana zuba su a Toilet mirror din dake hasko masa kan sa.

Gizo yaga fuskar ta nayi masa wannan yasa shi kara ware idanun nasa Sosai amma kuma sai ya fahimci gizon nan naga ne wacce yake yawon gani . Bin Mirror din da kallo yayi yana tuno da Haɗuwar su ta Farko yanda ta faɗo masa Toilet yana kwance kaman hakan , Da kuma yanda ta urince tana masa ihu tare da sakin tarkacen kayan goge ² n nata wanda a Wancen lokacin ta Shigo don gyara masa Privacyn nashi . Yar Murmushi yayi yana faɗin Ina Son ki Amrah na , You're my favorite my baby love, Ina so mu kasance forever real life couple 😢 . But how ......? Ya furta yana rintse ido tare da tuno da best friend din nashi Nurayn.
**
Ɓaidu House
Gidan jarfa...😂
Cikin Ruwa Inna Larai ta koma gida don da kyar kwarton nata ya barta ya rabu da ita . Gaba ɗaya ta gama salɓewar ciki ya ɗashe yayi laga laga . A wani irin tattale take tafiya tamkar Yar kaciya .
Gidan shiru kasantuwar ruwan da ya ɓalle da wannan daren ,wannan yasa koda ta Shigo babu wanda ya lura har ta shige daki . Sai da ruwan ya lafa ne ta fito tana nufar madafi ( kitchen) tare da gyara rushin Murhu tana daura ruwan dumi . Ashhhhhh ta Furta tana dafe ƙasan ta dake mata zugi anji dadi ansha aiki ana kuma jin jiki . Nikam nace Wannan ma kaɗanne al'ƙur'an.

Larai me ya faru naji kina faɗin ashh.? Muryar Baba Zuwai wacce ta ke ta Safa da marwa a tsakar gidan ya katse Larai , cikin sauri Larai cike da kame² ta Furta “ wuta na taka Zuwai ” . ALLAH sarki Sannu kiyi a hankali dare yayi nisa .

Humm Zuwai yanzu haka zamu kasance kenan? Anya an mana Adalci? Mu gama wahala yaran mu sun girma , mijin namu ya dawo ya zama babba a ƙasa , wai amma daga ƙarshe sai ayi mana wannan sakayyar, me muka yi ma Malam Adamu da zafi ne?. Humm Gwauron numfashi Baba Zuwai ta sauke kana ta kalli Inna Larai tana cewa “ abu ne wannan ma da bazai taɓa yiwuwa ba ai ” . Kaman ya ba zai yiwu ba ? , Bayan gashi yanzu fa mu sakakku ne ?.

Wani irin Dariya Baba Zuwai tayi wanda sai da Ni kaina na tsorata . Cigaba da sha'anin ki zuwa safe zamuyi magana . Eh ..? Inna Larai tayi Maganan tana sakin baki na Mamaki. Ke dai sai da safe . Cewan Baba Zuwai tana Juyawa tare da shigewa dakin ta hankalin ta kwance . Da ido Larai ta bita har ta shige kana ta ce " tabbas nasan wacece Zuwai , idan kika ga tayi wannan dariyar to ta taka dutse . Alhamdulillah zamu cigaba da zama matan Kanol Auwalu Ɓaidu kuma babban Dan kasuwa A yanzu Alh Muhammad tama . Tafe hannu tayi kaman zautacciya kana tace yi dama hauka muke yo dama hauka muke yi mu bar wannan arziƙin ?. Yanda zai kara Auren Hafsartu to muma haka za'a maida namu.

**
Kuka Ammie Hafsat keyi a ƙasan Carpet din Hajiya Kaka tana faɗin “ Hajiya nayi nadama , Hajiya na shiga uku ...Yau yar ciki na ce take faɗin ta tsane Ni ta tsane Ni Hajiya, wallahi a ƙwayar idanun ta na ga ƙiyayya ta ....Wani irin kuka ta kuma fashewa da shi tana kama hannun ta tare da cigaba da sharɓan kuka tamkar ran ta zai fita . Cike da tashin hankali irin na tsofaffi da daga Hankali Hajiya Kaka ke kallon Daddyn Nurayn da Mom Sa'adah wacce ita dai yanzu abun tun yana bata mamaki da ta'ajibi da tsoro al'ummuran sun dake daga Zuciyar ta . Tagumi ta saka ta koma tamkar ba ita ba , Muryar Hajiya kaka ne ya katse su tana cewa " Ban gane ba , wai Meke faruwa ne ?. Kallon Hajiya kaka Daddy yayi shi kan sa ya rasa me zaice . Nan Muryar Ammmie Ya kuma katse ta tana cewa " Hajiya ƴa ta nake SO.! Wallahi ina jin soyayyar ta Tamkar bugawar Numfashi na . Hajiya Amrah ...! Cike da hikima ta tsufaffi Hajiya kaka tayi Saurin dafa Ammie tana mata Addu'oi, don har a lokacin bata da Fahimta komai ba . A tunanin ta soyayya ce ta uwa da ɗa ya taso mata , a hankali cikin Sanyi da kwantar da hankali Hajiya kaka tace " ai Hafsah kinyi kokari na jinjina Miki da kika iya tafiya Tsawon shekaru kika manta da rayuwar Yar ki akan Wancen dangin matsiyatan talakawan, amma yanzu faduwa tazo dai dai da zama . Inshallah zuwa gobe A aika a taho Miki da yar ki . Dama anyi masu haka ne don halin su ,su kuma san ita din zuri'ar su ce .

Hummmm Wani irin Huci Mom Sa'adah ta sauke tana bin Hajiya Kaka da kallo kana ta katse ta cike da sanyi tana cewa" Hajiya Kin san yarinyar da nurayn ya Aura?. . Kayya Manta da wannan Maganan Hajiya Sa'adatu , zuwa safe mayi ta , ba dai ance an raba Auren ba , kin ga yanzu auta na bata da sukuni. Kallon Daddy Mom Sa'adah tayi kana tayi masa wani irin kallo na ƙarshen tikatiki. Humm Hajiya anyi sakin , Amma ai itace Amrahn , Yarinyar Ammie Hafsat jikar ki , itace amrah wacce take matsayin yar ƙanwar Daddyn Nurayn na jini... Innalillahi wa'inna ilaihir raji'una Allahumma ajirni.....Dauke maganan Hajiya Kaka tayi tana komawa tare da zama jaɓar bisa Sallayar ta tana wasu irin Addu'oin zuci hannn ta tasa tana dafe Kirjin ta da ƙarfi kana Ammie ta kara fashewa da kuka tana saurin mikewa tare da Nufar ciki .
Chapter 4 · 0% Book details