← Book details Uncle Datti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 52

Sashe 40

Uncle Datti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaron kamar ya san za'a raba shi da uwar shi ya saki kuka yana mik'a mata hannu ta d'auki shi sai tausayin shi ya kama Nana taje da gudu tana kuka zata k'arb'e shi baba babba ya rik'e ta da sauri......barshi ya tafi da tsiyan shi raino kam kin gama yi mishi sai ya d'aura daga inda kika tsaya.

Tana ji tana gani haka Datti ya tafi da Sadeeq uba kuka d'a kuka uwa kuka.......da dai sauran masu saurin kuka suma suna taya su.

Datti na fita Fu'ad yayi saurin bin bayan shi ya sha gaban shi" yaya ka ga takun",
Nayi amfani da kwakwalwata na cusa maka k'iyayyar Nana a zuciyan ka........., a halin yanzu tafi kowa tsanar ka......., ka san me?

Na raba ka da ita ne dan na cimma burina kuma" kana ji kana gani sai na aure Nana na cusa maka bakin ciki wanda zaka dawwama a cikin ta.

" Wawan shak'a ya kai mishi da hannun shi d'aya yana huci kamar mayunwacin zaki.......

Idan har ban aure ta ba kaima baka isa ka aure ta ba......., bangaje hannun shi Fu'ad yayi ya shige ciki ya barshi.

Haka ya ja yaron shi ya bar gidan daga bakin k'ofa ya tsaya yana k'are ma gidan kallo zuciyan shi nayi mishi zafi.......
*eedatou*
SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''
https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45
*UNCLE DATTI*
'''JIKINA YAKE SO!'''
*eedatou
```Follow and
ote me on Wattpad```: *eedatou*
~Attention pls akwai mistake a page na baya, idan akace gobe ne auren Fu'ad da Nana har aka kore Datti a gidan, ga abunda zan saka a wajen" lokaci na tafiya gashi yanzu bukin Nana na dad'e matsowa", ban sani ba na saka wancan laifinane da ban editing ba ku min uzuri ku gyara, ngd.~
Mota ya shiga da Sadeeq a hannun shi ya had'e kan shi da steering motar yana rusar kuka har da majina........su Umma basu mishi adalci ba da suka raba shi da Nana sannan suka raba Sadeeq da mahaifiyar shi..........., kallon Sadeeq yayi a lokacin har ya gaji da kuka yana sake ajiyar zuciya..........rafa suman kan shi yayi sai yaji sabon hawaye ya sauko mishi" kayi hak'uri son nayi sanadiyar kawo ka duniya ciki kazamin rayuwa..........., da ace ta hanyar aure aka same ka da baza raba ka da uwar ka ba.......hawaye msi d'umi yaji ya sauko mishi sai ya k'asa tsare su..........da kyar ya iya d'aga ya jan mota ya bar gidan..........

Ba shi ya tsaya a ko ina ba sai a gaban wani makeken shago na ga ya parking ya fito da Sadeeq a saman kafad'an shi ya shige ciki........,
Shopping yayi ma yaron sosai na kayan abincin yara da rigunan sawa da wando, kayan wasa da dai sauran su daga nan ya nufi gidan shi.

Tun a hanya Sadeeq ya fara barci har suka iso bai tashi ba ya samu ya kwantar da shi ya koma gefen shi ya kwanta tare da jawo shi jikin shi sai ga hawaye ya fara kwaranya a fuskan shi.

Cikin dare yaron ya farka yana ta sandara kuka sosai kamar ranshi zai fita.......,
Datti ya tashi a firgice ya d'au ledar da ya shigo da shi ya had'a mishi costant yana bashi a baki maimakon ya karb'a sai ya hau kawar da kaiiiiii shi dai mamar shi yake bukatan gani a lokacin.

Hawaye na bin fuskan Datti yana d'aga k'afa da kyar dick d'in shi na mishi zafi amma ba sosai ba yaje ya d'auko zani a d'akin Aina ya goya shi yana yawo da shi a parlour duk Sadeeq sai dad'a k'ara kuka yake kamar zuga shi ake.....hankalin Datti idan yayi dubu ya mugun tashi......" Shi kam ji yake ya ma fi yaron bukatar bukarta hakuri kawai ya fishi.

Rasa inda zai yi da shi ya kunce zanin da sauri cikin daren ya zare car key d'in shi ya nufi gidan su Alhaji ya hau buga musu k'ofa su bud'e, duk suka firfiito cuz daga d'akunan su suna jin kukan yaron karancewar dare ne".

Zubewa yayi a gaban Nana ya mik'o
mata yaron hawaye nata kwaranya a idanuwan shi" don Allah ki k'arbi d'an ki kar ki bari a raba ki da shi........ba don hali na ba ki rik'e Sadeeq kina jin irin kukan da yake yi ki tausaya mishi........help me, help me please i beg you".

Fu'ad na ganin sai tausayin shi ya kama yaron da yana da halin baiwa Nana d'anta da yayi.

Wani mahaukacin kuka taji ya zo mata tana so ta k'arb'i yaron har ranta tafi bukantan shi a kusa da shi.......me yasa su Ummi basa tausayin ta basa tausayin Sadeeq dan ya kasance ba d'an sunna ba?

"Umma taci ka fammmmm da shi sosai " Ya san ba zai iya rik'e d'an ba ya haifa ?wa ya ajiye da zata yi rainon shi?

Tsabar b'acin rai ji take kamar ta wank'a ma Datti mari.....bai ji kunyar abunda ya aikata ba shine yake cewa a rik'e mishi d'an shi".

" Kaiiiii Abubakar ka fita a idona na rufeeeee, wai ba anyi maka iyaka da gidan nan ba?

"Ummi don Allah!!! don Allah ki taimaka kar kiyi min hakan.......ki sassauta min hukuncin nan ya min sauri da yawa ba zan iya d'auka ba".

" Baba na san kaiii zaka fi Umma fahimtar halin da nake ciki......kaima namiji ne kamar ni.......baba ka san jarabawar da nake ciki na lalura ta......, ka fahimtar da ita cewa ba laifina bane, laifin k'addara na ne........tasssss ya ji an d'auke shi da wani mahaukacin mari wanda ya gigitar da shi saura kad'an ya saki Sadeeq ya fad'i k'asa Nana na ganin haka tayi tsalle ta rik'e Sadeeq tana kuka wi-wi, shi kam da ya tsorata ya dad'a k'ara sautin kuka ya gama sadakarwa cewa zai fad'i ne.

"Rungumo shi ta yi tsammm jikin ta tana mai jin tausayin shi a ranta har take nadamar kin biye ma Datti da tayi lokacin da, shi kam Sadeeq sai ya manne a jikin ta ya hau ajiyar zuciya.

Scene d'in ya matuk'ar ba ma Aina tausayi sosai sai ta hau ba ma Umma hakuri.......please Umma ku tausaya wa yaron ba dan halin uban shi ba......" Saurin katse ta tayi cikin fushi" kee rufe min baki kin fini sanin abunda nake yi ne?

Idan kika kara saka baki a maganar nan sai na hada da ke naci mutuncin ku........marar kishin kanta
kawaiiii.

"Ke Nana wuce ki shiga cikin gida".

Zata tafi kenan baba babba yace" mik'a mishi d'an shi........,kwalla ne ya zubo mata ta hau sharar su......."babu yanda ta iya haka ta mik'a ma Datti Sadeeq, cikin wani irin hali Datti yace" kema kin goya bayan na tafi da shi kenan?

Kin goya bayan a raba ki da d'an ki......., kin manta da ranar da cike da cikin shi kike cewa a bar miki d'an ki da hannun ki zaki raine shi.......zaki yi mishi gata ashe irin gatan da zaki yi miki kenan?

Nana idan na k'i Sadeeq yana ciki ke kika so shi har ya zo duniya wani riba zaki ci in kika rabu da shi idan kika rabu da shi?

Dama kin haifo shi ne dan ki mishi tab'on da zai nuna mishi baida gata?

A yanda yake maganar muryar shi har tsarkewa yake yi, a take jikin shi ya d'auki rawa............,
Yanda take jin maganar shi
a ranta kamar diran kifiya........, ba k'aramin ratsa mata kwakwalwa yake.........bata da wani zabin da ya wuce ta bi umurnin iyayen su, haka tana ji tana gani ta mik'a mishi d'an cakkkkk ya rik'e hannun ta ya had'a da nashi suka matse Sadeeq gam a jikin shi" Son ka taya ni rokar mana mommy karta guje mu we really need her by our side............, karta bar mu muyi maraicin ta.........", sai hawaye ya gabgaro ma yaron kamar ya fahimci abunda uban yake fad'a ya hau mik'a mata hannu yana so ta d'auke shi..........,matsanancin kuka ne ya kwace mata ta shafa tare da bashi peck tace" i'm sorry for letting you go, forgive your me son", tana gama tayi d'aki gudu.

Wannan k'aron sai da zuciyoyin su ya k'arye saboda da tsananin tausayin yaran, Ummi ce dai sarkin kuka ta shige gida da sauri tana sharar kwalla.

Aina kam sanda Datti zai tafi da Sadeeq ta rushe da kuka tana rik'e k'afar baba babba tana pleading d'in shi kar a bari Datti ya tafi da d'an baba yace sai dai tayi hakuri dole ne ya d'auki hukunci komai tsananin zafin shi shi zai saka gaba idan ya ga wani mai hali irin nashi ya bashi shawarar.

Haka suka koma gida tana waiwayen Datti" duk da dai ta san cewa yaci amanar ta, ya ci amanar zumunci amma yana tsananin bata tausayi........., some times ma idan ta zauna tana tunani sai ta ga kamar ba laifin shi bane......., ace a bama kura ajiyar nama kura kuran nan ya tabbata yana tsanin bukatar naman me zai hana ya ci........., ko ace majinya ci ne ciwon ajali ya kama shi sai akace ga maganin da zaiyi amfani da shi dan ya warke......duk talaucin shi sai anyi yanda akayi aka samo maganin dan ya warke.

Da wannan take k'afa hujja take ganin ya kamata a sassauta mishi hukunci yayi mishi sauri da yawa...., sai ma take jin kamar idan aka aura ma Fu'ad Nana hakan bai dace ba.........., cikin daren ta lek'a d'akin Alhaji cikin sa'a ta same su tare da tsohuwa tana sharar hawaye tace" don Allah Alhaji ku sassautawa Datti hukuncin da kuka d'auka........, ba dan shi ba ko dan lalurar da ke damun shi.........

Idan har Nana ta kasance magani a gare shi me zai hana a bashi auren ta ni na hak'uri da shi ko da na kasance tare da shi ba amfanin da zai yi min kuma ba zai daina bibiyar Nana ba.........., ina so ku duba magana ta da fuskan fahimta ba wai goyon bayan shi nake yi ba hasalima tausayin shi nake ya had'u da jarrabawa kala-kala.
Chapter 40 · 0% Book details