← Book details Uncle Datti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 52

Sashe 26

Uncle Datti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gyara ta yayi ta yanda zai ji dad'in zuga mata allurar yana cewa" karki ga laifin Datti dan ya so jikin ki, kece mahad'in rayuwar shi, dan haka i'm sorry Nana banda wani hanyar da zan iya taimaka miki........ yana fad'a ya hau kokarin danna mata allurar ajiki...............
*eedatou*
SHINNING STARS WRITERS ASSOCIATION*
'''The more we shine bright the more we educate and enlighten our readers.'''
https://m.facebook.com/110896360504039/photos/a.110896457170696/110898470503828/?type=3&source=45
*UNCLE DATTI*
'''JIKINA YAKE SO!'''
*WRITER OF*
*1.MAGANIN MATA(DAMUWA)*
*2.WAYE MACUCI?*
*3.RAYUWAR SUMAYYA*
*4.UNCLE DATTI(JIKINA YAKE SO)!*
*eedatou
'''Follow and
ote me on Wattpad''': *eedatou*
'''Masha Allah nayi matukar farincikin addu'o'in da kuma yi min da kuma tambayar lafiya ta kun nuns min Ku masoyana ne na kwarai, e.'''
Tsorone ya gama kamata ta saki wani firgiccen k'ara yayin da nunfashin ta ke k'orarin d'aukewa luuuuuuu ta tafi zata fad'i Usman yayi saurin janye allurar yana cewa" innalillahi wa'inna ilaihiraji'un duk ya fita a hayyacin shi cuz tsoro yake karta mutu a hannun shi ta b'ata mishi carrier d'in sannan kuma karyayi kisan rai.

Gani yayi jini ya b'alle mata yana bin k'afar ta abunda kenan ya d'aga mishi yanka kan kace mai ya hada uban gumi, saboda tsabar tashin hankali ya rasa ta inda zai fara" kar dai ace ya committing suicide?

Fita yayi cikin tsananin tashin hankali yana bude kofa Datti da ya had'e kai da jikin bango ya d'ago da sauri yana fad'in lafiya?

Is it successful.......

Maganar ta makale mishi a sanda ya had'a idanu da Usman........

Not really Nana is dying da wani irin murya ya furta maganar tare da kawar da eyes d'in shi gefe tunda yake bai taba jin dana sani ba irin ta ranar have it been bai bada gurguwar shawara ba and kuma yayi hunkurin taimaka ma abokin shi da bai jefa kanshi cikin wannan halin ba".

Ido ya bishi da shi a tsorace ya fiddo su waje zuciyar shi kuma sai kad'awa yake a take ya jikin shi ya d'auki rawa......, bud'e baki yayi zai yi magana amma ya kasa dunkule hannun shi yayi a haukace ya shako Usman" you killed her?

Ka kashe min Nana?

Gara na kashe ka kowa ma ya huta idan ya so nima a kashe ni, fada yake amma kana gani ka san hankalin shi baya jikin shi.

Kuka ne ya kwace ma Datti sosai yayi saurin sakin Usman ya hada kai da jikin bango ya saki malalacin kuka, ganin idan suka ci gaba a hakan anything can happen gashi ko kadan Usman baya son kowa ya fahimci halin da ake ciki and Datti kamar so yake ya tara mishi mutane yayi sauri jawo shi ciki.

Ba k'aramin tashin hankali yayi ba da ya ga Nanar shi a kwance a kasa a matsayin gawa, sai yaji duk ya tsane kanshi.

Rungumo ta yayi jikin shi yana kuka yana girgizata, ranar Datti ya ga tashin hankali marar misaltuwa.

Hawaye ne masu uban dumi suka soma gangarowa a saman fuskarshi suke diga akan fuskarta, a hankali ta ja numfashi ta bud'e ido a hankali tana kare ma d'akin kallo......idanuwan ta ne ya sauka akan jinin da ke zubo mata a take tunanin abubuwan da suka faru ne ya dawo mata...........

Shikenan sun Rana ta da baby d'inta Datti ya tsane ta tunda har ya nemi ya cutar da d'an shi da ke cikin ta, ba tare da ta d'auke idanuwan ta akan jinin ba cikin zuciyar ta tace" daddy d'inka baya sonka baya k'aunar ganin ka a duniya, ya toshe kofar da zaka shaki iskan duniya........, ta zabura ta hankad'a Datti da bai ma San da farfad'o ba cikin rashin sa'a ya buge kanshi da gefen table na Office d'in, zafin ya shige shi sosai har ya dafe gurin tare da sakin yar k'ara ashh.........ko kad'an bata ji tausayin shi ba ta hau ja da baya a firgice tana cewa i hate you! na tsane ka Datti.......bana kaunar ganin ka again.......

Kalaman ta sun kona mishi rai sosai har ranshi yake jin zafin su fiye da zafin da kanshi ke yi mishi, Yunkurin nufar Nanan yayi yana cewa" karya kike baby baki tsane ni..., kina sona baby ......bana son wannan wasan it really hurts.

Allah ka kuskura ka karaso nan sai na kashe ka, mugu azzalumi kawai ta saki wani irin malalacin kuka mai cin rai, a zuciyanta sai cewa take" they have succeeded in
about my baby", why Uncle.........

Wannan shine soyayyar da kake ikirarin kana nuna min duk irin zaman da muka yi a baya?

Har ranshi yake jin kukan nata ga wani uban ciwon kai da ya addabe shi lokaci guda, ba tare da ya fasa ba ya hau takowa a hankali........Usman shima dai yana jin kanshi cikin wani irin hali taimakon shi d'aya da Nanar bata mutu ba, shine yayi karfin taro Datti" baka da hankali ne?

Baka jin abunda da take fad'a ne?

Do you want to loose your life".

Cikin tsawa yayi maganar cuz komai zai iya faruwa dan ya lura Nanar zata iya aikata fiye da abunda ta fad'a.

Baka jin abunda take fad'a ne?

Barni nake ta kashe ni zaifi min sauki fiye da zazzafar maganar da take fad'a".

Babu yanda baiyi da Usman ba ya ki sakin shi basu san sanda Nana ta fice da sauri ta bar wajen ba.

Tafiya take tana waigewaige kamar wata
mahaukaciya jini na d'iga daga jikin ta lokaci guda
jiri na neman d'aukan ta har ta fito kan titi kenan wani uban jiri ya d'ebe ta ta fad'i k'asa daga nan bata kuma sanin inda kanta yake ba.

B'angaren Datti kuwa hankalin su ya tashi sosai sun duba ko ina basu ganta ba, suna cikin tafiya eyes d'in Datti ya sauka akan jinin, hannun shi har rawa yake ya nuna wa Usman.....na tabbata jinin Nana ne wannan.........,baby ina kika shiga kika barni......duk ya rikice.

Calm down let's follow her footsteps, na tabbata baza ta b'ace mana ba.

Cewar Usman kenan cikin tsananin tausayin halin da abokin nashi yake ciki.

A tare suka hau bin duk inda suka ga jinin har suka fito bakin titi daga nan kuma suka tsaya cirko-cirko, hankalin su ya k'ara tashi fiye da na baya......sosai kansu ya mugun kullewa cuz basu ga wani alama da ya nuna cewa ga hanyar da ta bi ba, illa gani suka yi jinin ya tsaya a dai-dai gefen titi".

Hawaye masu uban d'umi suka fara rolling akan fuskar Datti bai san sanda ya juyo da sauri ba Usman na kiran shi amma ina ko tsayawa bai yi ba ya nufin motar shi........

Wani irin wawan reverse yayi saura k'iris ya rage ya buge Usman ya tsaya a gaban shi yana yunkurin tsayar da shi cuz a yanda ya ga Datti ke cin uban motar anything can happen cuz ba a cikin hayyacin shi yake sarrafawa ba.

Datti inaaaaa ko tsayawa bai yi ba a d'ari ya fisgo ta ta ya bar wajen da mahaukacin gudu har yana bad'a k'ura................

Gida ya nufa ya ko gama daidaita parking bai yi ba ya nufi parlor ya banko kofan da karfi Aina na zaune akan carpet tana yankan farce ta mik'e a da sauri a kuma razane ta tsorata sosai.

Ganin Datti tayi a cikin yanayin da tunda take bata tab'a ganin shi a ciki ba........sai surutai yake like he wasn't in his senses" Nana ki fito na san gida kika taho
baza ki gudu ki barni ba........dan Allah idan hiding kanki kike karna ganki dan kin tsane ni ki fito na ganki ko da sau d'aya ne nayi miki alkawarin ba zan sake tak'ura miki ba".........Zuba mishi ido Aina tayi da mugun mamaki" dear ba tare kuka fita ba ai bata dawo ba".

What?

Ya fad'a da wani irin murya yana zaro ido waje, " kina nufin kice min bata taho nan ba......

Ohhhh Aina stop please joke apart, this is not the right time to joke........
sai ya hau dube-dube ko zai
ga hanyar da Nana zata
fito".

Ji tayi zuciyar ta ya mugun kad'awa ta had'iye miyau mai d'aci, duk da dai cewar bata fahimci abunda ke faruwa ba amma jikin ta na bata ba lafiya ba, to idan ma lafiya ne ina me yasa yake tambayar inda Nana take bayan a tare suka fito?

Me yasa ya shigo gida cikin wannan halin?

Cakkkk maganar ta ta mak'ale a sakamakon ganin stained na jini a gaban rigar shi ta hau bin shi da birkitaccen kallo shima bin inda take kallo yayi da sauri.......tsam bai lura da hakan ba......., Magana take yi kamar ta mai stammering tace" Ina.....ka samo wann....an?

Idan kashe ta kayi kayi gaggauwan fad'a tun kafin na aikata mummunar abu akan ka".

Kuka mai tsananin k'arfi ya kwace mata cikin sheshsheka yace" nima ban sani ba........bansan inda take ba...........

Aina ki yarda da ni ban kashe ta ba".

Idan ba kashe ta kayi ba ina ka kai min ita?

Baka da wani hanya da zaka kare kanka Datti you better tell the truth.

Inalillahi wa'inna ilaihiraji'un Aina kanki d'aya kuwa?

Da bakin ki kike cewa na kashe Nana?

Me ta tsare min da har zan kashe ta bacin kin san irin son da nake mata?"
Toshe kunnuwan ta tayi cikin sauri ta fashe da wani irin malalacin kuka mai cin rai" me yasa ba zan yi zargin ka ba bayan na san cewa a tare kuka fita, and kuma ka dawo kai kad'ai ba tare da ita ba?

"Yana jinta tana sambatu ya fice ya bar gidan ya nufi gidan su Ummi, da Aina ta san irin halin da yake ciki yayi imani ba zata tab'a jifan shi mugayen kalamai ba, cuz duk yafi kowa jin zafin rashin Nana a gare shi, ta ko ina idan ya rasa ta kamar ills ne ga rayuwar shi".

Da taimakon Allah ya samu ya iso gidan.

D'akin tsohuwa ya nufa ya tarar da parents din su gaba ki d'aya a d'akin suna tattaunawa.....yayin da Fu'ad ke kwance a kan carpet ya d'ora k'afa d'aya bisa d'aya yana latsa waya, fuskar shi kuma na kallon bakin kofan d'akin".

Kallo daya Fu'ad yayi mishi ya d'auke kai kamar bai ganshi ba yaci gaba da abunda yake yi a waya".
Chapter 26 · 0% Book details