← Book details Uncle Datti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 52

Sashe 2

Uncle Datti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da ya iso ya tarar Nana a kan kujerar three seaters tana sharar barci sanye take da riga da gajeriyar wando wanda bai gama rude kanta ba, tsayawa yayi for some few seconds yana kallon ta murmushi ne ya d'an sub'uce mishi" lallai Nana sarkin kiriniya ji yanda take ta sharara barcin ta hankali kwance", bin kayan jikin ta yayi da kallon sai yaga ta bala'in yi mishi kyau domin kuwa shekarun Nana bai hana bayyana kyaun surar ta ba, yanda jikin ta ya murje yayi b'ulb'ul zaka d'auka kamar ta yaran larabawa d'innan ne.

Tsintar kanshi yayi da nufar wajen ta ya tsugunna dafff kunnen ta ya hura mata iskaaaa", cikin barcin ta taji, ta d'an yi mik'a kamar zata rashi sai ta gyara kwanciya ta koma ta kwanta.

" Cije libs d'in shi yayi a hankali ya kuma kafe ta da ido, komai na Nana daban ne tana da kyau da kan diri, a hankali ya sa hannu biyu ya kinkime ta ya soma tafiya da ita, yayin da ya maida jakan shi da ya shigo da ita d'aya hannun nashi.

D'akin shi ya nufa ya dire ta a kan bed d'in shi kana ya lek'a d'akin Aina ya tarar da ita kan Sallaya ta idar da sallah kenan tana lazimi.

Zama yayi a kan tafkeken bed d'in ta ya jawo pillow ya kishingid'a yana jiran ta har ta idar ta ninke sallayar ta ajiye tare da zare hijabinta shima ta tana ninkewa lokaci guda tai murmushi tana kallon Datti" barka da dawowa mijina", da murya mai zakin gaske ta fad'a.

Amsa mata yayi shima cikin murmushi kana ya d'an turbune fuska da tsigar wasa yace" shine kika bar min baby angel d'ina a parlour ita kad'ai ko?

Wife mun kusa mu bata fa",.

Ohhhhh damn it!!!!!!!!, na manta Nana batayi sallah ba take barci sai yanzu na tuno ma, mai baby angel tare muke da ita nima sallah ne ya shigo dani amma bari na tada ta".

Kafin ya bud'e baki yayi magana tuni tayi hanyar parlour ko da ta iso bata tarar da kowa ba ta lek'e bayan kujera nan ma babu ita babu alamar ta, nan idanuwan ta suka cicciko kamar zata yi kuka?

Ina Nana ta yi da daren nan ita da ta barta tana barci?

Tsoro ne ya d'an kamata a lokacin da wani tunani ya fad'o mata ta safe kirji tare da waro ido waje" na shiga uku kar dai shigowa gidan nan akayi aka tafi da Nana"?

Kuka ta fashe da shi da gudu tayi d'akin ta ta tarar da Datti a inda ta barshi yana ganin yanayin da ta shigo a firgice yace lafiya kika shigo haka?

Me ya faru?

Banda kuka babu abunda take yi da kyau ta iya bud'e baki tace" banga Nana ba?"
"Kamar yaya baki ga Nana ba?

Ya jefa mata tambaya fuskar shi na bayyana mamaki.

Wallahi na duba kafff parlourn nan babu Nana babu alamar ta, nafi kyautata zaton satota akayi".

Sai yanzu ya fahimci inda ta dosa bai san sanda dariya ya subuce mishi ba har sai da ya kular da ita tace" wato baka damu da b'atan baby angel d'in da kake ikirarin taka ce ba shine ma na zama abin dariya?, ta kuma rushewa da kuka tana tunanin halin da y'ar k'anwar take ciki".

Ganin abun nata dad'a k'aruwa yake yi gashi ko kad'an bai son jin kukan mace balle na wacce take da muhimmaci a rayuwar shi, wacce babu abunda zai iya saka mata da shi sai addu'a domin irin guduwar da ta bayar a rayuwar shi, ba shiri ya had'iye dariyar shi, cikin rad'a yace" yi shiru daina kukan haka matata idan ba su kike ki saka nima na taya ki ba, guess what? baby angel na d'akina tana barci.

Kuka mai d'auke da hawaye ne ya makale mata lokaci guda tace" Dan Allah? da gaske? ya d'aga mata kai alamar "eehh"
Zolayar ta yayi yana cewa" Ashe Ainata ma ta damu da baby angel d'ina amma tafi ganin ganin ina son baby angel fiye da kowa.

Kin san dalilin da yasa nake son Nana?

Ta girgiza mishi kai tare da yin kasa da kan ta tana murmushi kasa-kasa, " sabo da wife d'ina tana sonta bayan haka jinin mu ce ma'ana soyayyar Nana a jinin mu yake".

A tare suka kwashe da dariya daga nan suka d'unguma parlour ta serving d'in shi da abinci dan d'asu suka ci nasu da Nana suna ci suna hira har ya gama daga nan suka nufi d'aki suka shirya tsafffff suka kwanta tare da bama juna baya wanda ya kasance kamar al'adan su ne.

Tana jin Datti na ta sharara barci yana minshari, wannan wace irin bak'in kaddara ne?

Anya zata iya cinye jarabawar da Allah ya rubuto mata kuwa?

Wai ace aure kusan wata uku kenan su kwana ta tare su tashi tare babu abunda ke shiga tsakanin su?

Anya su Ummi sunyi mata adalci kuwa?

Kaiiiiiii!!!!!

Allah kana ji kuma kana gani..........., Allah kasa tsare min mutunci na kar biyayyar da nayi ma mahaifana na auren mijin da marar bukata wanda ko kad'an mace bata gaban shi ya yi silan jefa ni ga hallaka........., ka kare ni da mata masu irin matsalata daga sharin son zuci............, tana kayo nan wani tsiririn hawaye masu d'umi wanda zafi da rad'ad'in kamar ana narka d'alma ne suka suma bin kyakkyawar round kuncin ta d'aya baya d'aya.

WAIWAYE ADON TAFIYA
Aina'u Muhammad Kabeer Danbaba da Nana Halima uwar su d'aya uban su d'aya kuma mahaifan su duk suna raye.

Mahaifiyar su mutuniyar Katsina ce haififfiyar garin mamaga ce da ke karamar hukumar Jibia.

Mahaifin su Kuma Alhaji Abubakar haffaffen garin Bauchi ne su uku ne a wajen mahaifan su rak, yana da wa sunan shi Alhaji Isma'il wato mahaifin Datti da kuma autar su Hajiya k'arama usulin sunan ta Halima wato Nana sunan ta taci cikin su ita ce bata tab'a haihuwa ba".

Datti wanda asalin sunan shi Muhammad wato shima sunan mahaifin Nana aka saka mishi, su hud'u ne a wajen mahaifan su, shine babba a wajen iyayen su, sai Ilham yayi aure a nan Bauchi take da zama a unguwar Federal low coast, sai Fu'ad wanda yannzu yaka yake zangon k'arshe a makarantar jami'a da ke Bauchi wato ABUBAKAR TAFAWA BALEWA UNIVERSITY, bayan haihuwar shi mahaifinyar su bata kuma samun ciki ba sai da Fu'ad ya kai shekaru goma sha d'aya kafin nan aka haifo Mardiya wace zasu yi sa'a da Nana".

Sunan mahaifiyar su Datti Maryam ne amma ana k'iran ta da "umma" ita kuma mahaifiyar su Aina sunan ta Murja ana k'iran ta da "Ummi".

Mahaifin su Alhaji abubakar wato Kabeer D'anbaba da kuma mahaifiyar su Sa'adatu wanda akafi dani da tsohuwa duk suna da ransu, kasancewar family d'in Kansu a had'e yake yasa suke zama a family house d'in su dan su kara dankon zumunci amma y'ay'an su kuma suka amince su zauna a duk unguwannin da suke so".

Marsala ta farko da Datti ya fara fuskanta shine; so tari idan yana tare da friends d'in shi yana yawan jin labarin cewa duk namijin da balaga ya kamashi yana wet deals da dai sauran su, abunda yafi d'aure mishi kai tunda yake bai tab'a jin feelings, ko tayi wet dream ba, hasali ma mace bata gaban shi kuma bai d'auketa amatsayin komai ba.

Wannan marsala tun yana d'aukan shi k'arami har ta kai ta kawo ya girmama yafi k'arfin tunanin shi ya fara tunanin ko aljana ce ta aure shi, wannan dalilin ne ya saka har ya kawo munzalin aure bai tab'a yin budurwa ba, a gida anti anyi ya nemo mata a had'asu aure tun yana boye musu har ya yanke hukuncin Samar da iyayen shi halin da yake ciki game da mata.

Hankalin su ya matuk'ar tashi sosai da suka ji labarin babu kalar maganin da basu nemo ba da na gargajiya da na bahaushe duk sun nema amma shiru, gashi a lokacin yana aiki a asubiti suna gudun kar mutane su mishi mummunan fahimci kun san zaman namiji da kud'i babu mata ana d'auka fasiki ne, da wannan tunanin baban Aina ya yanke hukuncin nema mishi auren Aina a wajen baban shi tare da goyon bayan matar shi domin kare mishi kima da darajar a idon duniya.

Da farko mahaifin Datti bai nuna goyon bayan shi ba a cewan shi za'a cutar da yarinya ne a nakasa mata rayuwa daga k'arshe ya hakura ba dan komai ba sai dan su tsohuwa sun nutsar da shi a cewan su idan ba jinin shi ba wa zata amince ta zauna da namiji irin shi?

A haka har aka d'aura auren ya rok'a a bar mishi Nana wacce tun haihuwar ta taji yana son yarinyar sosai tamkar cikin su d'aya da ita.
************************************
CIGABAN LABARI
Rik'e yake da waya a hannun shi ya shafe kusan dakika biyar sai kai komo yake a d'akin shi kad'ai jefi-jefi yana cizon yatsa.

Ba komai ne yake damun shi ba illa sanin kanshi ne tunda yake wato tun da ya fara falin balagan shi har zuwa yanzu dai-dai da kwana d'aya bai tab'a jin sha'awar mace ba, lokuta da dama idan suna hira da friends d'in shi har mamakin su yake wai idan suna kallon blue film suna jik'ewa amma gashi yau kusan goma kenan ya downloading yana kallo amma ko gizau bai ji ba.

Tsaki mai karfi ya sake tare da yin wurgi da wayan a kan gado ya d'au car key din shi ya bar gidan a gaggauce ya wuce chamber d'in su, a gefen wani garden ya tsaya yayi parking ya fito tare da yin ma mortar key, ya tarar da friends d'in shi su uku suna hirar su cikin raha, ko sallama bai yi ba ya nemo kujera ya zauna suna ganin su suka mik'a mishi hannu suna cewa" man yane ka shigo ba ko sallama".
Chapter 2 · 0% Book details