← Book details Uncle Datti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 52

Sashe 29

Uncle Datti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ganin yanda ranta ya fara baci ta hau fad'a sai ta hau bata hak'uri tare da yi mata alkawarin baza ta sake yin kukan ba".

B'angaren Datti iya wuya hankali ya gama tashi sai baza ido suke yi a kafafen yad'a labarai amma shiru, Fu'ad ma yayi iya nashi kokarin na bada guduma dan nemo inda sahibar shi take abu amma abu yaci tura, tsakanin shi da d'an uwan shi babu wani kyakkyar alaka da ace baiyi halin b'eran ci ba da babu abunda zai saka su cikin wannan halin".

Kuka iya kuka yake yi a duk sanda tunanin ta ya fad'o mishi a rai sai yaji duk duniya babu wanda ya tsana kamar Datti.

Su Umma da Abba duk sun juya mishi baya, Alhaji ma ya fita harkan shi anyi anyi ya fad'a laifin da ya aikata amma ya ki hakan ya dad'a hasala su".

A b'angaren k'anwar shi ce kadai da Ummi da kuma baba karami yake samun sauki amma duk da halin da yake ciki kowa yayi banza dashi, ai ba yaro bane da har za'a ta tambayar shi yana raina wa mutane wayo".

Idan ya shigo d'akin tsohuwa cewa yake su neman mishi Nana idan ba haka ba shima guduwa zaiyi ya shiga duniya, ko tausayi baya bata tayi mishi tatasss da zagi"shi yayi sanadiyar gudun shi zai nemo ta ai shi ya san sirrin da ke b'oye wanda ya kasa bayyana wa".

Itama Aina bata ragar mishi ko kad'an babu kalar habaice-habaicen da bata yi mishi ta mata da cewa a baya dear d'inta ne wanda ta d'auki dukkan yardar ta ta d'ora mishi".

Duk da irin mugun haushin shi da take ji ko da wasa bata fad'a wa su baba Babba cewa kashe Nana yayi ba........, ta zuba mishi ido ne har zuwa tsawon lokacin da zai d'auka da kanshi ya fallasa komai.

Wata ranar Alhamis da rana da misalin karfe d'aya Fu'ad ne ya shigo d'akin tsohuwa za shi wajen Aina kasancewar tunda ta koma gidan a b'angaren tsohuwa take zama.

Tarar da ita yayi akan kujera ta d'aga ido tana kallon ceiling hankalin ta baya jikin ta bata san ma ya shigo ba har ya nemi wuri ya zauna.

Jin motsin mutum a kusa da ita ya sa ta saurin d'agowa ta dube shi tana had'a ido da shi hawayen da take kokarin mak'alewa suka samu daman gangarowa saman cute face d'inta".

"Yanzu shikenan Fu'ad Nana ta barmu kenan har abada?

Ba mu ba sake had'a ido da ita?

Shikenan ya kashe mana Nanar mu?

Maganar ta dake shi sosai a zuciya sai ji yayi shima hawaye ya hau zubo mishi, a yanda take maganar duk ta karye mishi zuciya".

Cikin dishashiyar murya yace" Kin ga gawar ta ne?

Ko kinji labarin wanda ya samo gawar ta?

Tayi saurin girgiza mishi kai".

"Me yasa kike zargin cewa ta mutu bayan ba ki da wata cikakkiyar shaida akan haka".

" Share hawayen ta tayi ta ta d'au hanky a gefen kujerar ta fece majina murya na breaking
tace" Baka.....ga.... ab......n da na.....ga..ni ba Fu'a....d, da ido......na naga jiki a Jikin Datti, ya shigo shi kad'ai bacin tare suka fita, wan......nan hujjar kad'ai ya tab.......batar min cewa mutu.......wa tayi ku.....ma shi ya kashe ta........

Shiru yayi shi kad'ai tare da hard'e hannayen shi yana nazartar kalaman ta har ta gama.........Tabbass akwai k'amshin gaskiya a maganar Aunty Aina dole d'an uwan shi na da hannu akan b'atan Nana........., dole ne ya zurfafa bincike ya gano gaskiya idan har Datti yana da hannu akan b'atan Nana sai yayi sanadiyar yankewar jin dad'in rayuwar shi".

" Mik'ewa yayi yace" babu komai Aunty insha Allah sai na bi dukkan wata hanyar da zan bi na kwato mata y'ancin ta wannan alkawari ne".

"Kana ganin zaka iya?"
Indai akan Nana ne zan iya yin komai ki kwantar da hankalin ki ba zai ci bulus ba he must pay for it", yana gama fad'a ya sa kai ya fita".

A main parlour suka had'u da Umma Datti ya tusa ta a gaba yana mata sambatu har taji zuciyar ta ya fara cika da tausayin shi shine ta sa kai ta fita ta bar mishi d'akin".

"Yauwa Fu'ad dama kai nake nema", yayi saurin karasowa ya zauna a kan kujera ya sadda kanshi kasa yana wasa da farcen yatsan kafar shi.

Zama tayi a gefen shi ta kafe shi da ido cikin tuhuma" maganganun da ka fad'a ranar sun rikita min tunani musamman da naji kana cewa bamu yi dana sani yanzu ba, sai zuwa gaba zamuyi, d'an uwan ka ma yak'i fad'a mana laifin da ya aikata har yayi sanadiyar guduwan Nana ta barmu, don Allah idan akwai wani abu da kuke b'oye mana ku fito fili ku fad'a mana".

Idanuwan shi ne suka kad'a zuwa launin ja ya d'ago kai yana kallon mahaifiyar shi da rinannun idanuwan shi wanda babu alaman fari a ciki".

"Ummaaaa", kiyi hakuri nima ba zan iya fad'a miki komai ba a halin yanzu, a baya babu irin shawarwarin da ban baku ba kuka yi banza dani, idan mai laifi bai amsa laifin da yayi ba ba zaku gamsu da abubuwan da zan fad'a muku ba cuz a baya ma ba d'aukawa kuka yi ba, and kuma banda shaidar da zan tabbatar muku da ita".

Dogon numfashi ta ja ta sauk'e a hankali" shikenan tashi ku tafi amma ka sani kai da d'an uwanka kun jefa zukatan mu cikin zullumi".

Mik'ewa yayi za shi d'aki dai-dai lokacin Datti ya fito daga d'akin Umma cuz ya gaji da zaman jiran ta hakan yasa ya fito ko zai ganta".

Fu'ad ya ga yanda ya zafge ya rame har ya fara kashin wuya idanuwan shi sun fito waje sosai, tsaki mai k'arfi ya ja yayi shigewan shi ko ufan bai ce mishi ba sai ma cewa yayi d'an ba k'ara ba yace abun nashi ba saiti ba ya samu yarinya yana ta danna mata ga irin ta nan, akwai
ranar kin dillacin".

Ko ta kanshi Datti bai bi ba domin bai da lokacin da zai tsaya yana kula Fu'ad bayan da nashi matsalar da tafi komai d'aga mishi hankali.

Zai yi wajen Umma ta d'aga mishi hannu" ka kuskura ka k'araso nan sai ka had'u da fushi na, haka ya mak'ure a guri d'aya hawaye na rolling a saman fuskar shi d'aya bayan d'aya".

Da ta gaji da ganin shi a cikin wannan halin ta tashi ta bar shi a wajen,
haka yayi ta tsayuwa da ya gaji ya fita ya bar gidan tunda basa tausayin shi bayan ya fisu jin zafin rashin babyn shi mai d'auke mishi lalurar shi, ta tafi ta bar shi da tsananin kewan ta da na dumin jikin ta sannan kuma ga garuwar da yayi kullum cikin radadin rashin ganin ta.

Cikin dare Aina ta fito main parlour she was taste a lokacin and babu ruwan sha a fridge d'in tsohuwa gashi baza ta iya hakuri har zuwa safiya kafin ta sha ba kawai ta fito ta hamma ta nufi fridge d'in, har ta d'auka zata koma taji motsin mutum a bayan ta.

Datti ne da tun shigowa ta yake kwance ciwon ciki ya addabe shi ya rik'e ciki yana murd'e murd'e shi kad'ai".

Tana had'a ido da shi ta tamke fuska kamar yana ganin ta tayi sauri zata bar wajen dai-dai lokacin cikin shi yayi wani irin murd'awa zufa ya fara sassako mishi cuz of tsabar azabar da cikin ke yi mishi, cikin sarkewar murya yace" help Aina i'm dying ".

Juyowa tayi da baya zata tafi ta ga ya rarrafo ya rik'e k'asan rigar ta da wani irin dishashshiyar murya nana jan numfashi da kyar yace" please ki taimaka min mutuwa zanyi", ciki na ciwo wife, karki tafi ki barni cikin wannan halin".

Jikin ta ne yayi mugun sanyi a sanyaye ta d'ago ta dube shi sai taji zuciyar ta ta karaya sosai, he really needs her help, and dole ne ta taimaka mishi even though he killed her sister but she can't afford to loose him", shima wani b'angare ne na jikin ta".

Tsuguna tayi ta d'ago shi da kyar tana fidda numfashi duk ta jigata ta taimaka mishi suka bar parlourn,
D'akin Fu'ad ta shige da shi suka tarar har ya fara barci ta taimaka ma Datti ya kwanta a gefen Fu'ad d'in, kafin nan ta tapping d'in shi da hannu".

Fu'ad!!!!!!

Fu'ad!!!!!!, ya bud'e ido a hankali yana kallon ta tare da mik'ewa ya zauna yana mitsik'e ido".

Ga mamakin shi sai ganin Aina ya a gaban shi, in a surprised mood yace" lafiya Aunty kika taso ni cikin wannan dare?

"Ina fa lafiya Fu'ad, hannun shi ta kama ta manna a saman wuyan Datti yaji zafi rad'a ba shiri yayi saurin janye hannun shi ya koma zai kwanta, bai ma san da Datti a d'akin ba sai yanzu".

Muryar Aunty Aina yaji cikin rud'ewa da magiya tace" don Fu'ad mu taimaka mishi kar shima mu rasa shi kamar yanda muka rasa Nana".

"Had'e rai yayi sosai ya sha murrr, duk da irin duhun da ke mamaye da d'akin bai hanata gane hakan ba yace" Allah aunty ba zan taimaka ma wannan azzalumin ba, mugu marar imani mai halin akuyan ci".

Duk da irin jin jikin da yake yi bai hana shi jin zafin kalaman k'anin nashi ba, rutse ido yayi sai ga hawaye ya biyo baya......

Me yasa Fu'ad yake neman bashi ciwon kai ne bayan ya tabbata da shine da irin kaddarar shi da sai yayi abunda yafi hakan......, amma duk da ya san komai me yasa ba zai d'auki k'addara ba?

Me yasa ba zai yarda cewa ba shine ya d'ora ma kanshi son jikin baby ba?

"Haba wannan wani irin rashin imani ne Fu'ad, dan uwan ka ne fa kake gaya mishi haka?

Yau ko makiyin ka ka tarar a cikin wannan halin baza ka fad'a hakan ba, ba'a gaba da ciwo ko ka manta ne?
Chapter 29 · 0% Book details