Sashe 9
Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tunani yayi kancewa bari yaje ya dubata, ko banza fishida iyaye babban zunubi ne balle uwa,koda yashiga shashen nata wayam babu kowa ko Ina arufe mamaki yakamashi to Ina taje da sassafen nan? Babu me bashi wnn amsar, juyowa yayi yakoma sashen su yana trying number din Idiyatu amma is not reachable.
Abangaren idiyatu da Biba kuwa a hotel din Abuja suka kwana tun asuba suka gama Shirin su na tafiya nijer dake tun dare sukayi booking flight Wanda ze tashi karfe takwas.
A airport takwas din tamusu suka Lula se kasar nijer, cen cikin wani kungurmin daji, a wani karamin kauye wajen gari ne sosai sunkashe kudi sosai kafin su Sami drop din taxi din da ze kaisu gurin bokanyar, a hanya suka tsaya suka dauki wani mutum Wanda shine zeyi musu rakiya har kauyen, mutumin Idiyatu ne run a Nigeria suka San juna, shi dan nan garin Niger ne.
A gefen hanya me taxi y saukesu dan garin ko shinshinin kwalta babu, da kafa suka fara takawa har zuwa cikin dajin ga nisan tsiya duk sun gaji Amma sbd taurin rai da mugun nufi ko alamar gajiya basu nuna ba.
Dede wani katon iccen kuka me ban tsoro ga duhu inuwarsa ta mamaye katon Fili acikin dajin dede wannan iccen suka tsaya, se gani sukayi wnn mutumin yafara cire kayansa yana ajiyewa agefe, seda yayi zigidir sannan ya kallesu sunyi tsuru tsuru kamar kace arr su fece aguje wage katon bakinsa yayi seda suka firgita wata mahaukaciyar dariya yakece da ita seda dajin ya amsa nan take wannan mutumin yazama wata katuwar tsuntsuwa yatashi sama yabarsu nan jikinsu na wata irin makyarkyata, duk sun jiqe jikinsu da fitsari Biba harda zawo tasaki.
Dajin ne yadauki wata irin Kara kamar na ihun mace, daganan basu Kuma ganin komiba se duhu....
*Tofa Ina su Biba da Idiyatu suka kawo kansu? Mugun nifinsu Ina yajefo su? Kude kuci gaba da bibiyar labarina anan ne zakusan wane ruwa wadannan matan suka ballowa kansu*
Share fisabilillah 🤲
Momsani ......... ✍️
🌹 SIRIKATA 🌹
Bismillahirrah manirrahim.
Pg17_18
A mugun firgice Idiyatu ta farka daga mummunar mafarkin da take, tafarko da ihu da wulle wulle harseda ta fado dg kan gadon hotel din da suka kama a Abuja itada Biba, ihunta ne ya farkar da Biba ta tashi agigice itama tana neman gurin buya.
Wayar Idiyatu ce tadauki Kara har seda ta firgita jikinta na karkarwa ga wata zufa data wanke mata jiki kamar tayi wanka, ga zaninta da takeji da danshi alamar kamar tayi fitsari a kwance, wayarce ta sake daukar ruri alamar ankara kira da sauri Biba ta dakko wayar tamikowa Idiyatu wadda jikinta be bar bari ba har yanzu.
Amsar wayar tayi jikinta na masifar rawa faduwa kasa wayar tayi ta dakko hannu na rawa ta dauka, muryar Rabil ce ta dakin dodon kunnenta inda yake cewa "assalamualaikum mom Ina kika shiga baki kwana a gida ba? Hankalina yatashi sosai dana duba banganki ba, baki fadamin Zaki fitaba balle ki kwana"
Tattaro yar ragowar jarumtarta tayi tace "son Ina nan cikin garin Abuja ne Biba kawatace batada lfy an kwantar da ita asibiti shine nazo, sorry hankalina yatashi shiyasa ban fada maka ba amma in Sha Allah nan da karfe 2:00 na rana zan dawo".
Seda yamata magana kafin ya kashe wayar.
Jikin Idiyatu na rawa ta tashi aguje ta afka toilet ba soso ba sabulu ta watsa ruwa tafito aguje kamar zomo se guje guje take, ba sallar asuba har karfe 10:00 na safe, ta hau hada kayanta a cikin yar Jakarta Biba de se kallonta take cen de takasa hakuri tace " wai idiyatu ban gane mikiba kin tsoratani da iface ifacenki yanzu Kuma kin kama guje guje kamar bera yaga mage Sanna Kalli gadon ki da alama fitsari kikayi akwance, baya ga haka kin hau tattare kaya gashi naji kina waya cewa nanda karfe 2 na rana kinkoma gida, me kike nufine? Batun zuwanmu nijer din fa? "
Idiyatu ba baki se hada kaya take duk a tsorace take, Biba de abin ya isheta amshe jakar Idiyatu tayi tace " kinsan Allah sekin fadamin abinda kike Shirin yi".
Idon Idiyatu jajur cikeda bala'i tace " bani jakata Biba, yau koda zankoma insamu Fatima ta haihune wallahi wallahi bazanje nijer din nan ba, kinkosan bala'in da nagani? Kinsan abinda nagani cikin mafarkina gameda zuwan mu nijer kuwa? To wallahi sede ke kije nikam bazaniba in Sha Allah yau agidana zan kwana" takai karshen zancenta jikinta na bari dan har yanzu yadda wannan mutumin yazama wata katuwar tsuntsuwa yana mata gizo acikin kanta da idanunta.
Cikin muryar lallashi Biba tace "haba kawata kinfasan kudirinmu, kinsan abinda zekaimu garin nan bakaramin abu bane taya haka kwatsam dagayin mafarki Wanda kowa yasan ba gaskiya bane sekice kinfasa tafiya? Dan Allah kiyi hakuri kidaure muje mudawo, Dan wlh ban hakura ba Kuma bazan hakura ba, duk abinda Lukman yamin Sena masa fiyeda yadda yamin, Sena gana musu azaba shida munafukar amaryarsa ke hatta iyayen ta bazan barsu ba".
Idiyatu Bata tsaya wata wata ba ta dauko wani kati acikin Jakarta tabawa Biba tace "duk abinda kike nema gameda zuwa kasar nijer idan kika kira wannan lambar an gama, Amma nide bazaniba nafasa Kinga tafiya ta Allah yabada sa, a". Taja Jakarta tayi waje drop tadauka na mota daga Abuja zuwa ibadan, sbd babu jirgin da ze tashi a lokacin itakuma duk bala,i yau seta kwana a ibadan cikin gidanta.
Biba kuwa ba Bata lokaci Kuma batareda ta damu da tafiyar Idiyatu ba ta fara gwada Kiran wnn numbers din na jikin katin.
_________________________________
Kontagora Niger state.
MUHSIN BAGO'S RESIDENTS...
Tsaye take ajikin window din dakin ta dage Hawa na uku, idonta sanye da glasses fari medicated, Jan numfashi tayi tana sauke ajiyar zuciya sakamakon Jin hannuwa akan kafadarta, "my zee wai yaushe Zaki dena wannan tunanin ne umm? Kullum kuka da tunani tsawon shekaru 30 haba dan Allah karki kasance mara tauhidi mana, Allah daya bamu Rabil yafimu sonsa shiyasa ya amshesa, kisawa ranki dangana, Dan Allah kindeji abinda Dr yace akan ciwonki ga idonki ma sbd kuka har sun fara samin matsala, pls kibarwa Allah komi, gashinan Allah yakara baki wasu yaran har biyu ga Aziza ga Radiya, Kuma duk Allah yabasu mazaje kowacce tayi aurenta sbd haka dan Allah kidena damuwa kinji? Kuma Rabil in Sha Allah me ceto ne"
Da hanzari tajuyo tana dora hannunta aka bakinsa tace " a,a yarona yana raye be mutuba in Sha Allah yakusa dawowa gareni yarona is still alive he's alive he's aliveeeeeeee" se tazube ajikinsa tana mimmikewa kamar me farfadiya, innalillahi "zainabbbbb Kinga abinda nake gaya Miki ko? Innalillahi yayi saurin lalubo gefen drower din gefen gadon ya dakko wata allura nanda nan ya tsira mata ita a hannunta dede jijiya, nan take jikinta yasaki sekuma ta tafi duniyar bacci, bacci me cikeda mafarkan danta tilo namiji wato RABIL....
Muhsin kenan mahaifin Rabil Wanda Idiyatu tasace sa tun yana yaro, zainab mahaifiyar Rabil takamuda cutar damuwa(depression) dakuma cutar jijjiga (seizure) idan ta tuna da Rabil nan take zata Sami attack tafara jijjiga Hakan yasa seda likitoci suka Samar mara da allura wacce dazarar ta fara jijjigar idan ayi mata ita take samin bacci Koda zata farka Kuma normal ne kamar bata yi ba.
Acikin wnn yanayin takara haihuwar mace aka Sanya mata Aziza seda tayi shekaru biyar sannan ta haifi Radiya wacce daga kanta bata Kuma haihuwaba, tsakanin Rabil da Aziza shekara ukune sbd sanda aka sace Rabil shekararsa biyu Kuma alokacin zainab nada shigar ciki Wanda basu San dashiba se bayan faruwar al'amarin Wanda iKon Allah ne kawai yasa cikin be fitaba shekarar Aziza ashirin da tara, Radiya Kuma 25.
Dukkansu sunyi aure, Radiya tana aure a sokoto tana auren Abubakar Sadik zayyad.
Itakuma Aziza tana aure nan cikin kontagora unguwar GRA phase 1.
__________________&
Karfe uku na rana Biba ta sauka a garin nijer a cikin birnin niamey.
Da kwatance wannan mutumin harta kusa isa inda yake tana kan mashi suna waya, Dede wani karamin kauye Sega gungun shanaye wani bafulatani yana kiwonsu,wasu shanaye guda biyu ne suka hauro kan hanya suna ta fada wanna fulanin yayi yayi sunki rabuwa har kan hanya sunata fada, jama a se gudu ake dan bil hakki suke fadan kamar bazasu dena ba, shikuma dan acabar da Biba tahau irin yan takife din nan ne ya fafaro aguje da ita ji kake cuss anyi Karo da dan acabar daya dauko Biba da wannan shanaye.
Salatin mutane kawai Biba takeji akanta daganan Bata Kuma sanin inda kanta yakeba....
****************
Nigeria......
Se karfe taran dare sannan Idiyatu ta isa garin ibadan, duk ta galabaita tun dare rabonta da abinci gashi an tarbi wani daren,sallamar me mota tayi ta hau mashin yakaita gida, da sallama tashiga gidan inda tasami Rabil da Fatima zaune a garden din gidan tayi matashi da cinyarsa, yayinda shikuma yake Kara Kiran number din idiyatu tana fara ringing segata ta shigo gidan afujajan, se haki take duk tayi zuru zuru, dasauri Fatima ta tashi Shima da saurinsa suka tarbota Fatima duk da batajin karfin jikin ta amma dasauki ta daure ta amshi jakar Idiyatu suka nufi part dinta tana gaba suna baya Rabil tana tambayar ta akan dadewar ta bawan tace darana zata dawo, fada masa tayi a mota ta dawo shiyasa ta Dade har suka karasa part dinta yana tambayar ta jikin kawartata.
SULEJA. Gidan alhaji muktar.
Yana kwance dakin amaryarsa ta kanainayeshi ta hanashi fita se uwar shagwaba take zubawa wai seya mata goyon Doki, ba musu y ajiye gwiwowinsa akasa yace tahau yanata yawo da ita aransa yana tunani wai da girmansa amma shine yakewa yarinya goyon Doki sbd kawai ya aureta kamar a da ba ladabi take masa ba, baba sama baba kasa tana sunne Kai amma yanzu ta zanzare wai shi take sawa Doki gashi yakasa yimata gardama dan wlh tunda yakwashi garar amarci yake bala, in ji da ita baya iya mata musu gata da kyau yar karama fara tas da ita fa iya shagwaba Kuma abin mamaki kamar ba yar me kudi sosai ba ta iya girki sosai Kuma tana kokarin ibadan.