← Book details Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 18

Sashe 8

Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kullum se sunhadu adede kan junction susha hirarsu sannan yasiya mata ice cream da meat pie tayi take away taje suci d uwarta, daganan kan karime yakara girma ita me sa,a ce yarta tasamo me kudi, har maganar aure tashiga tsakanin su basusan me gadi bane, haka yasa babansu yaje nemar masa auren hadiza uwarta tayi Kane Kane tahana ayi kwakkwaran bincike, acewarta su masu kudi basa son yawan bincike, dama mijin nata ta shanyesa haka aka basu auren hadiza,akan sadaki dubu hamsin,tace ai albarka ake nema bayawan kidinba,dogo baban nera shine sunan da duk Yan kauyen dama ita kanta amarya sukasan muktar dashi, aka kaita gidan wannan baturen, kasancewar sa ba mazauniba Kuma yana barin makullin gidan a hannun babban me tsaron gidan wani inyamuri, shine muktar yabiyasa kudi suka hada baki aka kaita cikin gidan da niyyar idan bature me gida yakira ze dawo se yadauki hadiza akan zasuje ganin mamansa, seya wuce sudawo.

Haka kuwa akayi ankawo amarya gidan da kowa seda yaji tsoro anata gulmar karime tasiyarda yarta wa me yankan Kai. Watansu biyar anacin amarci bature yasanar ze dawo, muktar betaba bari mahaifiyarsa tasan irin zaman da sukeyi da amarya ba, cemata yayi ai ogansa ne yabasu daki daya suzauna.

Kuma duk tsawon watannin nan Bata taba zuwa ba, Shima Kuma be Kai hadizaba.

Dawowar bature me gida shiyasa muktar ya tsiri tafiya shida amaryarsa wai zasuje kauye agaida mamansa,.

Seda sukayi kwana 6 akauyen LAMBATA inda iyayensu sukeda zama sannan aka kira muktar kan cewa bature yakoma, shinefa suka tattara ya hau aniyar komawa.

Seda suka kwashe tsawon shekara uku acikin wnn auren karyar, har yau batasan asalin waye Shiba tade lura suna zuwa kauye lokaci bayan lokaci.inda acikin wnn shekarun duk sanda bature zedawo se yasa akwashe kayansu bayan tafiyarsa akai boys quarters,in zasu dawo akwasao amayar,komi nagidan dakayan sawar na matar baturene,ake amfani dashi,.

Yayinda yatare agindin matarsa komi yasamu natane itada uwarta, Yana mantawa da tasa uwar se in bature ze dawo inzasu kauye. Dake becika zuwa ba, seyafi shekara bezoba.

Wani zuwa dasukayine kwanansu uku sukace zasu tafi,
inda mamansu tadage setaje taga inda sukeda zama, aiko DEEJA tace batasan zanceba, seda muktar yayita lallashi shine fa ta yarda da sharadin bazata dade agurinsuba, ya yarda sbd Yana sonta matuqa, duk da haka ita abin bemata ba tana gudun tsohuwa taje tace bazata dawo kauyeba, waya ta dauka takira mahaifiyar ta karime tafada mata komi, aikuwa karime tadinga sababi wai za atakurawa yarta, bashiri tayi gurin nakan tudu akan amallake mata dogo baban nera da mahaifiyar sa,.

Kwanan su biyar da dawowa taga tsohuwa taki tafiya aiko takara Kiran uwarta, uwarce tanuna mata karta nuna Bata son uwarsa agabanasa tanuna ai uwarsu ce gaba daya, daganan tamaida ita yar aiki.
______________________
Wannan shine tarihin kowa nacikin wannan labarin yanzu zamu tsuduma da kyau cikin labarin, muje zuwa.

🌹 SIRIKATA 🌹

Na SADIKA IBRAHIM
Pg15_16
Bismillahirrah manirrahim.

CIGABAN LABARI.....

Bayan Idiyatu takoma gida da sati biyu fatima matar Rabil tafara wani shegen laulayi me zafi sosai Wanda yakai ko tashi bata iyawa, ga wani tari me tsanani idan tafara setayi amai da fitsari a gurinda take, sannan bata iyacin komi. Idiyatu bata temakon ta da komi sede in Rabil na nan y temaka mata, inko bayanan haka zata wuni tana wahala da Jan ciki take zuwa toilet tasamu ta gyara kanta tadawo kafin kace me wani tarin yasake tirniqeta laulayi take me azabar gaske, Idiyatu tasan laulayi take amma Fatima da Rabil basu saniba .

Hankalin Rabil duk yakoma kanta yayi2 akan suje asibiti taki satinta daya ciwo yaqi cinyewa ya dauketa bisa dole sukaje asibiti gwajin farko ya nuna ciki wata uku da sati biyu Kuma yana cikin koshin lafiya, farin cikin da yayi baya misaltuwa, agaban Dr yayi sujudul shukur, Dr nata masa dariya tun a asibiti yakira Idiyatu da murnar sa yafada mata atinaninsa zatayi murna amma seyaji akasin haka dan wani irin ashar ta lailayo ta saki tacikin wayar kamar wata yar tasha sekuma ta kashe wayar diff.

Jikin sa a mugun sanyaye ya dauke wayar a kunnensa, dama so yake yafara fada mata kafin yakira mahaifiyar Fatima amma abinda Idiyatu tayi yasa jikinsa yin sanyi harya manta bekira maman Fatima ba.

Biba ma Koda Takoma gida tasami labarin daya kusa juya duniyarta, mijinta Lukman ya auro wata tsaleliyar yarinya budurwa wacce bazata wuce shekaru ashirin ba, yayinda mufida matar Awwal danta takeda cikin wata biyar.

Abin yamata mugun bugu, an shammaceta iya shammata, tanacen tana fafutikar hana matar danta haihuwa ashe mijinta Yaena nan Yana gina mata kabarinta, abi mamakin ma bakowa bace yarrinyar da Lukman ya auro face yar abokinsa datakewa Awwal danta kwadayin aurenta wato Ihsan Tukur dollars.

Suma Biba tadingayi ana zuba mata ruwa, daga ta farfado ta kalli mufida zaune kusa da ita da Dan cikinta Daya fara tasawa Wanda bata taba lira dashiba se yau, gefe Kuma ga mijinta Lukman da yar matarsa ihsan zaune kusadashi se manne masa take kamar mage, tana arba dasu seta koma duniyar sunanta Lols.

Abude yaki ci yaki cinyewa seda aka dangana Biba da asibiti Wanda duk mufida ke dawainiya da ita dan Lukman kamar abin tsafi yatare gindin yar amaryarsa me shegen shagwabar tsiya, sede yazo yadubata yakoma, daga mufida se Awwal suke kulawa da ita tayi kuka hartaba uku lada, Kuma ta kudiri aniyar muddin tana numfashi adoron kasa se ta juya farin cikin Lukman da Ihsan zuwa bakin ciki.

*******************

Abangaren hjy DEEJA kuwa,..

Da Koda Dr yashigo cemasa tayi bawata matsala yana iya komawa sbd mara lafiyar ma ba taji ciwoba muktar yanaji ba yadda ya iya Dr yajuya yatafi.

Family Dr din baturene idan yazo Nigeria, yabada damar aduba duk wani ma, aikacinsa idan bukatar hakan ta taso bisa umurninsa.

A bangaren innar muktar kuwa tanacen daki tanata matsar kwallah bame lallashin ta, yaranta biyu ne aduniya, muktar shine babba se Biba, dukansu gasunan de se gyaran Allah Biba tunda tayi aure mijinta Allah yamasa budi bata waiwayarsu acewarta ai tana musu aike duk karshen shekara, tanacen daga ita se danta, Wanda bata nuna masa darajar suba, shikuma muktar bata ma san inda yasa gaba ba, tarasa gane masa shine wannan gidan nasane ko Kuma uban gidan nasane ya ara masa?, Ita wnn Al amarin yana daure mata Kai.

Ga azababbbiyar matarsa Bata ganin darajar kowa, Bata ganin kimarta amatsayin ta na SIRIKARTA, gashi takasa barin gidan kamar andaureta agidan. Kuma ma ko ba komai ai tanasamun jar miya ga katifar ta me laushin tsiya ga rabar AC Kodan wannan ai tazauna. Takai karshen tunanin ta tana zamewa takwanta akan katifarta katuwa.

____________________

"Assalamualaikum, assalamualaikum".

"Amin wa alaikimussalam, haba mutum kamar makaho inata amsawa ko ba ajibane? Waye? Shigo ni nariga nazauna ban iya tashi wlh".

Sanyo kansa yayi cikin dakin bakinsa dauke da wata sallamar, "wanake gani haka kamar nagwaggo? Aa maraba, maraba da babban bako yaushe a gari dan albarka? Tafada tana leka bayansa ganinsa shi kadai abin yaharziqata tafara banbamin fada, "Ina ita rasa kunyar take? Wato shine kazo Kai kadai dan karkazo da matarka na cinyeta wato ga bakar mayya ko? Wlh na gwaggo idan baka fita idona akan wannan munafukar matar taka ba ko hmmmm"

"Dan Allah ki hkr mama batajin dadi ne shiyasa na barta amma wlh har kuka seda tayi akan mutaho tare ninace tayi zamanta tunda batada lfy"

" Rasulullahi manzo dan Amina, na gwaggo yaushe kazama sallamamme sbd ba uwarta bace ni shiyasa kahanata zuwa wato dan karkazo da ita nahata komawa ko? To wlh ko kaso ko karka so se kadawo da yar iskar yarinyar nan cikin garin nan, wato ga yar Lele ko? Juyar mace har wata abin lallashi ce, amma balefinka bane zan San abinyi".

Shide kansa akasa bece komiba harta gama kunfar bakin tagama, sede yace mata " kiyi hkr mama".

Agefen oganniya idiyatu kuwa, tana kashe wayar takira mlm buzu tace " mlm maganarka ta tabbata wannan tsinanniyar cikine da ita", dariya yayi ya ce mata " me na fada miki tuntuni? seta haihu Koda zakiyi menene, Kuma wannan karon kisaurari abinda ze biyo baya" kit ya datse Kiran, safa da marwa takama yi acikin dakin nata, agaskiya bazata sabu ba taya zata bari matar Rabil ta haihu? In tabari ta haihu Hakan yana nufin duk dukiyar da yatara takoma mallakin abin da aka haifar masa, ita kenan ta tashi a tutar babu? No hakan bame yuwuwa bane bazata taba bari Hakan ta faruba bari tasan abin yi.

Idiyatu ta manta maganar mlm buzu akan haihuwar Fatima, cewa inta matsa tofa ajalinta nakusa.

Daga waya tayi takira Biba, a lokacin Biba tanacen tana saqe saqen yadda zata wujijjjiga rayuwar mijinta da Ihsan amarya sa.

Kiran idiyatu ne yashigo wayarta inda nan take ta dauka, ba sallama tafara magana "Biba nashiga uku Fatima cikine da ita, da gaske maganar mlm buzu ta tabbata".

Sauke ajiyar zuciya Biba tayi tace "ke matsalar ki jaririya ce akan tawa, ko kinsan irin ta addadancin da natarar agidana?, Ko kinsan irin wulaqancin da Lukman ya aikata min?" Hawaye ya biyo kuncinta take ta fashe da kuka nan talabartawa Idiyatu irin halinda take ciki da irin yadda Lukman ya banzatar da ita, dakuma labarin cikin matar danta Awwal Wanda batasan dashiba se yanzu.

Wata irin ashariya Idiyatu ta lailayo tace " kan babban bujen dakarkari, mu za aiwa haka? Biba idan bamu miqe tsaye ba to lalle wata tonon asirinmune yatsaya".

"To yanzu meye abin yi?" Biba ta tambayi Idiyatu,"abinyi shine kudi Zaki tanada muhau jirgi muje cen kasar nijer akwai wata bokanya nasan da munje gurinta komi yazo karshe".

"Yaushe zamuje dan ni inaga yau bazan iya bacciba" cewar Biba.

"Gobe gobe kishirya cewar Idiyatu"

Koda rabil suka dawo dg asibiti direct dakin su suka wuce fushi yake da Idiyatu Jin batayi murna da samun cikin da Fatima tayiba se yayi fushi a tunanin sa zatazo tasamesa tunda batason bacin ransa ko kadan, Amma shiru har garin Allah yawaye, ganin shirun yy yawa ga sashen ta shiru kamar ba mutum aciki
Chapter 8 · 0% Book details