← Book details Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 18

Sashe 7

Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Biba tace allanbaran se Idiyatun tazo sunje inba hakaba abarshi dan ita yanzu batada matsalar komi.

A dasauri Idiyatu tace zataje, sbd tayi wani tunani aranta cewar yanzu kilama Muhsin baban Rabil Kila basa garin kontagora a yanzu, fa wannan suka ajiye ranar da zasuje kontagora, shine da akaje gurin malam buzu idiyatu ta nuna halinta na mako lols.

Bayan duk inda zataje da katon hijabi da face mask take zuwa kar azo asamu Wanda yasanta taganta asami matsala.

Wanda ko Biba batasan dalilin Idiyatu ba na yin wannan shigarba ta dauka kawai sbd yanayin garin ne sbd hunturu da ake.....

# Karshen labarin idiyatu da biba#
____________________________
# Wacece mahaifiyar na gwaggo #???

🌹 SIRIKATA 🌹

Na SADIKA IBRAHIM.
Bismillahirrah manirrahim.

Pg13_14

WACECE MAHAIFIYAR NA GWAGGO???

Fatima zarah, shine cikakken sunan ta, yar asalin kauyen Babban rami ce, ana cikin garin kontagora suna zaune da iyayenta acikin garin kontagora unguwar Bagaya babanta principal din makarantar Maidubu primary school ne.

Tayi primary da secondary school dinta a wata makarantar kudi me suna Mustapha Bello comprehensive school.

Tana karamar secondary wato j.s.s 3 sun Sami Hutu me dogon zango shine taje kauyen Babban rami domin tayi hutunta acen tareda kakannin ta, kakanta mahaifin babanta me suna mlm Abubakar shine me garin wnn kauye a wancen lokacin, inda mahaifiyar babanta me suna mama Laure suke zaune a cikin kauyen.

Mahaifin na gwaggo wato Sani yaje hutu kauyen shina kasancewar Shima dan asalin kauyen Babban rami din ne.

Tafito tazauna dan nesa kadan da dandalin inda take hangen yan mata yan kauye da samari anata rawa da gada a dandalin matan rigunansu daban da zanin jikin su hakama Dan kwali daban, itakuwa shigar riga da Zane ne na atamfa ajikinta se wani dan gyale kalar kayanta data yafa akanta tana kallonsu tana murmushi fuskarta Babu digon kwalliya ko kadan, yayinda yan matan kauyen kowacce fuska cikeda kwalliya irinta yan kauye.

Yana gefe Shima cikin kayansa kanana riga da wando masu kyau yau karo na uku kenen yana ganinta zaune akan wannan dutsen ita bata shiga cikin masu rawarba sede tayita kallonsu tana murmushi, sallama yayi mata ta amsa tana kauda Kai gefe, yace "barkanki da hutawa yan mata" bata amsashiba tamatsa cen gefe murmushi yayi yace " Yan mata ke bazaki shiga cikin yan uwanki kuyi rawar ba? " Kallonsa tayi tace " mtwsss did I look lyk a villager's lyk dem? " Koda yake ma ta Ina kasan me nace mtwsss" tayi gaba abinta mamaki ne yacikashi Jin tayi turanci dama a wannan zamanin akwai mace karama kamarta wacce tayi karatun boko har take Jin turanci har haka a wannan kauyen? Ganin bashida me amsashi ne yajuya yabi hanyar tabi da kallo har tayi nisa yacimmata da Dan gudunsa yana mata magana tamasa banza yace " hey young lady koba kyajin hausa ne? "

Juyowa tayi da mamaki tana kallonsa dama yanajin turanci tab ashe akwai me Jin turanci a wnn kauyen, mamakin ta yakasa boyuwa tace "dama kanajin turanci?" "Kadan ba" yabata amsa murmushi sukayiwa juna suka cigaba da tafiya.

"Anan kauyen kikeda zama ne?"
Yajefa mata tambaya.

"Aa Hutu nazo agurin kakannina mlm Abubakar me gari"

"Wow dama kece jikar me gari da akace tazo hutu yar gayu naji anata maganarki agari, Ashe kece"?

"Nice" tabashi amsa.

" Ni sunana Muhammad Sani Lawal, ni jikan dagaci Lawal ne nazo hutun karshen shekara ne agurin kakannina kasancewar sukadai suka rage min, narasa iyayena a hatsarin mota, inada mata da yara biyu mata farisa da Farida".

Kallonsa take da mamaki be Santa ba amma yake gaya mata duk wannan kamar wata wacce suka dade dasanin juna.
Murmushi yayi yace "kina mamakine Jin na fada Miki abubuwan da suka shafeni ko? To ba abin mamaki bane tunda kike zuwa kallo dandali kullum Ina lura dake bande tana miki magana bane se yau nide nayaba da hankali dakuma nutsuwarki Kuma nide kinmin amatsayin mata sbd haka idan badamuqa zanzo dakaina gurin kakan naki na nemi izinin zuwa wajenki idan ba damuwa Fatima zarah".

Mamaki sosai yabata Jin yakira sunan ta , murmushi yasake yi yace "jinayi ana cewa sunan jikar me gari Fatima zarah Kuma yar gayu ce"

Murmushi ne yasubuce mata, har seda tadara batareda tasaniba.

Dede lokacin suka kawo kofar gidan me gari tamasa sallama zata shige yace" Baki bani amsaba Ina je inga kaka?"

Aguje ta ruga cikin gidan tana kulle fuska, itakam ya birgeta sosai gashi dan gayu gashi ya iya turanci, sannan yafada mata gsky yanada mata harda yara, itakam bata shirya auren me mataba amma yabirgeta sosai.

Kwanci tashi soyayya me karfi ta kullum tsakaninsu batareda tasaniba itade tasan kawai suna shiri sosai amma basoyyya take ba.

Seda tayi wata uku cur Babban rami sannan tayi azamar tafiya lokacin ne kuma tayadda tanason Sani sosai, ada bata Sha awar auren me mata Amma yanzu gsky tanason Sani sosai.

Hakan yasa tabashi dama yaje yaga kakanta shikuma yasanarda mahaifinta Wanda ita kadai Allah yabasu, be jaba saboda yanawa mahaifinsa biyayya sosai yace duk abinda akayi Dede ne.

Ahaka kakan Fatima zarah da kakan Muhammad Sani suka yanke komi na auren Fatima da sani ansa lokacin biki nan da wata uku masu zuwa.

Ahaka aka daura aure Fatima zarah isah da angonta muhmmad sani Lawal. Kasancewar da sunan kakansa yake bearing.

Seda Fatima ta kwashe shekaru biyar Bata haihuwa lokacin harta gama secondary school ta dora da university, lokacin yaran uwar gidan sani naima uku mata, takara haihuwa bayan auren fatima, daganan Bata karaba, seda Fatima takai 200lv sannan tahaifi danta namiji santalele me kyau sosai kamar tayi kaki ta tofar aka sa masa suna Sufyan.

Aranar sani yi yayi kamar ba a taba masa haihuwa ba seda yayi sadaka da rabin kudin account dinsa raguna biyu y yanka akayi sadaka Sanna ranar suna aka yankawa Sufyan raguna biyu da katon saa, itade naima idone nata batada hayaniya ko kadan hakama yaranta me hayaniyar dayace batula wacce aka Haifa bayan auren fatima.

Haka Sufyan ya taso cikin kulawa kamar me kowa sonshi yake gashi bulbul abinsa kyakkawa, yannensa mata sunaji dashi komi suka samu Sufyan.

Mahaifiyar Sufyan takasance masifaffiyace sosai fadane da ita kamar me, ga Neman fitina yayinda uwar gida naima takeda sanyi batada matsala da hayaniya ko Fatima ta takaleta Bata kulata har ta gaji tabari daga baya dataga ba riba seta koma kan yaran Abu kadan duka da fada kuma tahanasu daukar Sufyan gashi sunason daukarsa amma tahana wai karsu yarda shi.

Harta gama karatunta na university tasami aikin teaching lokacin ta yaye Sufyan yana tafiyarsa ko ina, agidan take barinsa gurin naima.

Bayan shekara goma..

Lokacin Sufyan yana ajin karshe ta primary a school dinda Fatima mahaifiyar sa take koyarwa, ana musu graduation na gama primary 6,angama sunkama hanyar zuwa gida suka hadu da hatsari inda nan take mahaifinsa Sufyan wato Muhammad Sani Allah yamasa rasuwa, itakuma naima tasami matsalar Karaya a cinyoyinta duka biyu, yaran kuwa babbar ma tarasu me suna zainab, se tabiyun me suna fatiha, se batula da autansu Sufyan da Fatima mahaifiyar Sufyan din su babu abinda yasame su, Fatima ce ma tabugu akanta Shima ba sosaiba.

Wannan ahalin sunji mutuwarnan matuqa Fatima kamar bazata dena kuka ba, ahaka akayi arba'in inda bayan tagama takaba zata koma bakin aikinta, abokan marigayi suna temaka musu da kayan abinci harta gama takaba takoma bakin qikinta, alokacin ne Kuma akamata transfer zuwa wata makaranta tareda mukamin principal.

Itake riqeda yaran naima uwar gida ita yan uwanta sun dauketa acen gurinsu take jinya tace abarmata sauran yaran zata riqe, tacigaba da zama agidan mijin nasu itada yaran.

Haka rayuwa tayita shurawa inda Sufyan ya girma yannensa mata duk sunyi aure a hannun fatima, Shima aurensa yamatso se shiri suke ba kama hannun yaro auren dan gata Sufyan, Fatima tana nan da azabar masifarta Babu abinda ya ragu sema karuwa da yayi.

Bayan auren Sufyan da shekara daya aka fara samun matsala da Fatima uwarsa, acewarta bataga amarya Aisha tana amai da tofar yawu ba, me ake nufine, ita tanason jikoki sbd haka idan ma planning suke to adena bataso.

Tun suna daukar abin da wasa, suna cewa ai Allah ne bekawoba har Aisha tafara gajiya da abin, A shekarar su biyu da aure ne abin Fatima yafara tsamari badama Aisha tasake se habaici da masifa, Anki haihuwa se shegen cii kamar gara da katon kashi kamar yan firsin amma anki haihuwa.

Dalilin da Sufyan na gwaggo ya dauke matarsa suka koma inda yake aiki wato garin Minna.

Sunan na gwaggo da ake kiransa kuwa yasamo asaline alokacinda aka yaye sa aka Kaisa wurin mahaifiyar Fatima wacce ake cemata gwaggo itace take kiransa da na gwaggo shine sunan yabisa har girma.

WACECE HAJIYA DEEJA???

Hadiza lashe money shine cikakken asalin sunanta.
Yan asalin kauyen SULEJA ne suna Nisa sosai da cikin gari tana zuwa tallah cikin gari Amma idonta akan manyan motoci, duk wacce ta wuce seta auno kanta aciki wai itace me wnn motar, kullum tana mafarki da kula lissafin dukiyar rano, seta gama iyayi abakin titi tukunna take zuwa tallarta. Kyakkawar gaske ce fara kamar ba a kauye takeba, sede shigarta ce kawai zata sheda maka daga inda tafito.

Tallar maganin daji take amma idonta idon me kudi itada uwarta karime mayun kudine gasuda munafircin tsiya, da tsananin Munafurci uwarta karime tasa mijinta yasaki matarsa uwar yayansa, takawo agolar yarta hadiza Kuma ta gallabi yaran.

Ahaka wata rana tana talla tahadu da muktar yayan biba alokacin yana aikin tsaron wani katon gida,nawani baturene ana cikin garin SULEJA, balefi yana da kyau ga karya, ahaka ya yaudari hadiza lashe money da motar da ya tuko ta wannan baturen,yazo gari kasancewar baya zama sede yazo yakoma,shiyasa yadauki motar yabashi yakaimasa gyara gurin makanike shine ahanyarsa ta dawowa yahaduda hadiza lashe money, batawani yi karatu ba shiyasa batasan ma anar kayan jikinsaba, Dan kayane irin na masu tsaron kofar mall, ko restaurant haka, irin uniform din nan na masu gadi.
Chapter 7 · 0% Book details