← Book details Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 18

Sashe 16

Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuwa tayi bakin kofar gidan takama zata jaa gate din kamar ansa remote taga yabude dakansa ajiyar zuciya tayi takama hanya kanta asama zata shiga jitayi tabuga uban tuntube ta wani abu kamar dutse sauke kanta kasa tayi aiko tayi arba da wani wadan mutum mara kyan fasali ko kadan Wanda ko acikin wadanni muninsa yabaci gashi bakikirin, dafe kirji tayi taja da baya ido waje bakinta na rawa take nunasa ta yatsa "waye Kai? Me kakeyi agidan mu? Innalillahi wayyo nashiga uku" harga Allah tsoro yabata yadda yakafeta da jajayen idonsa kamar maye.

Duk da cewa yaji haushin yadda tayi data gansa sekace wacce taga abjn tsoro, hakan behanashi karewa kyakkawar fuskarta kallo ba, matsowa yayi kamar ze riketa yana fadin "yi ahankali 'yan mata karki fadi" jaa baya tayi taruntuma aguje tabar kayanta yashe agurin gidan me unguwa ta afka kamar mahaukaciya tana haki.
Kallonta iyalan gidan sukayi Wanda suka kasance zaune a tsakar gidan yuuu sukayo mata da idanu gasu da uban yawa, daya daga cikin matan gidan ne tace "baiwar Allah wacece ke kika fado mana haka bako sallama kamar wacce aka biyo?".

Dago kanta tayi tace "inayini baba kandala nice hadizan karime ta gidan mlm audi", " hadiza, hadiza, banganeba wlh", " hadiza me maganin ciwon daji tagidan mlm audi na kan layin habu me kanti".

" O, o haka au kice dani hadizan karime lashe money, to yau Kuma kece aguje haka? ina motocin alhaji muktar dogo baban nera? "Tafada tana kama haba.

Kan Deeja akasa batareda ta amsa tambayar tace "baba kandala dan Allah Ina mamana take naje gidan mu bansametaba wlh sede wasu wadanni ne kawai suke fitowa daga gidan ko shiga bansamu nayiba yanzu ma daya daga cikin sune ya biyoni shine nagudo nan".

" Hahaha hadiza kenan wace irin tambaya ce wnn Kuma tun yaushe kika sa mijinki yazo har cikin garin nan yasiyarda gonakin ku dagidan da kuke zaune aciki kikasa yasiyawa mahaifiyar ki wani gidan acen cikin garin SULEJA? Kozakice duk bakisan da wnn ba? To munan my muka raka karime har gidan ta na suleja ta tare me kyau dashi Wanda mijinki yagina mata, duk gonakinku Wanda kika gada daga gurin mahaifin ki da na mahaifiyarki yasiyar yadauketa yamayar da ita cikin gari wannan gajerun mutanen kuwa sune masu gidanku ayanzu sunansa alh Mande big moo, shiya Siya gidan yau kusan wata uku kenan da tarewarsa, dama mlm audi ya dade da rabuwa da karime lashe money yakoma gidan matarsa Wanda yaransa suka gina da guminsu, yanzu shikam Allah yasa yadawo hayyacinsa yanacen suna zaman lfy da uwar yaransa".

Idon waje Deeja ke kallon baba kandala wacce se yanzu tagama rattaba zancen ta kafin tadasa aya, hannu tadora aka zata zunduma ihu cen Kuma kome ta tuna se tayi shiru, awayance tace "oh gosh wlh baba kandala mantawa nayi alokacin da akayi hakan ina cen Switzerland naje wani taro kinsan matan manya da safgogi may be shiyasa na shafa'a, amma bakomi, toko Zaki hadani da wani cikin yaran nan yakaini cen gidan? sbd saukata kenan daga airport nan nayo direct ko gida banjeba".

Dan jimm baba kandala tayi kafin tace " Koda naji ninasan Kam taya Zaki kwaso jiki kiyonan bayan kin dauke uwarki daga kauye aikam de se mantuwa", yake Deeja tayi kafin baba kandala takara cewa " to gashi ba Wanda yasan guri acikin yaran nan sede idan ni zanzo narakaki barin tambayo me gidan, ince de da motarku me sanyin nan kikazo? " Ta tambaya tana washare baki, " cikin dan mazewa Deeja tace "no taxi nahau dg airport zuwa nan yanzuma inaga sede mudau wata taxi din dan nariga nasallami wancen".

"To to bakomi aisemuhau kurar Adamu musamu ko titi yakaimu sannan musami taxu din ko?" Tafada tana dauraye kafarta jikina rawa har tamatsu su isa Kila tasami ko 'yar jallop ce me manja taci, dan ita atunaninta idan tasami jallop din manja tasami cimar yan gayun birni, tunda akauyen bakowa ne yake samun arzikin dafa shinkafa agidan Saba, Suma dasuke matan me unguwa tuwon datsar masara shine abincinsu me dan kyau da dadi, Allah yasa mudace.

Koda suka fito akwatunan Deeja kusan guda takwas babu se wani wadan yaro cikin Wanda suka kifar da ita ne sukaga yana Jan dan kit din ta daya rage zeshige gida dashi aikuwa asukwane Deeja ta fafaro ta mauje masa Kai ta amshe akwatinta tana ihun Ina sauran kayanta, sbd idan Bata mantaba harda yan sarkojin Isabella da ba a bataba ta zundume amma gashi babu awaktunan ta se dan kit din da kayan ciki basuda yawa, ihu take tana karawa Fadi take "wayyo nashiga uku sarkokina kayana nashiga uku namutu na lalace", baba kandala sakato tayi tana kallon yadda Deeja ke sambada ihu, tace "kekuwa hadiza wasu irin kayane aka sace haka?" "Wlh baba kandala kayana masu tsada harda gwalagwslaina aciki wayyo nashigesu wlh se anbiyani" cikin gidan su tayi dagudu wanda ayanzu yake mallakin alh Mande big moo (Dan wada)kamar dazu tabude zata shiga Sega wata wadar matar tafito aguje aiko sukayi Karo da Deeja jikake timm takara faduwa itako wannan wadar matar ko gezau batayiba fadi take "luku waya bugeka nunamin hii" wannan wadan yaron yana kuka yanuna Deeja da ke yashe kasa yana fadin "Wagga tabbugan gatanan yashshe akasa ke kada ita" (sakkwatanci suke sbd mutanen Hausa ne).

Juyowa matar tayi kan Deeja tace "mi yammiki kinka bugai?" Se huci take, baba kandala ce tamatso tace "yi hkr jummai wlh kayantane taga luku yanaja shine tadan make masa keya, kiyi hkr idan yakawo sauran kayan cikin gidan kutemaka kubata tafiya zatayi takawo mana ziyara ne,wacce aka kira da jummai wato wnn wadar matar tace " sunanan ciki ina Bata kayanta amma SE luku yarama bugun tammai" , " bakomi inde zaku Bata kayan yarama bakomi" Deeja ce tadago fuska jage jage duk majina zatayi magana baba kandala tamata alamar tayi shiru.

" Matso luku tau nanniyagga rama bugun da tayyima" Aiko ba kunya wadan yaro ya matso kafin Deeja ta ankare ya lafta mata kututturen hannunsa a kumatunta seda taga taurari kafin tadawo daga suman datayi Sega jummai ta dire mata akwatunanta agabanta, da sauri baba kandala takama Deeja wacce tunda tazuba ihu sanda luku yamareta bata Kuma cewa komiba se dafe kuncinta datayi bata Kuma cewa komiba har me kura yazo irn wacce ake daurawa shanaye din nan , aka loda mata akwatunanta se a sannan baba kandala ta sauke ajiyar zuciya tadafa Deeja wacce se yanzu tadawo cikin hayyacinta Bude baki tayi da niyyar magana kawai Sega jini shaa ta hanci da baki, kuka tafashe dashi tanatayi abin dariya abin tausayi ga bakin da kimatun sun kumbure kamar biredi, baba kandala nata bata hkr tace "wannan Marin da luku yamiki shine rufin asirinki, Babu Wanda besan bala'i da masifar jummai wada ba idan tafara masifa akan yaranta tunsafe wlh seku kwana kunayi bata gajiba gata da karfi makar shara'a.

Haka tayita tallaba Deeja har tayi shiru lokacin da suka iso cikin gari anfara Kiran magrib suka tare taxi yakaisu har kofar gidan da akace muktar yasiyawa karime maman Deeja akofar gidan suka ganta zaune tanata sheqa bala'i itada wani busasshen mutumi yanacewa yabata nanda jibi kota bar masa gidansa kota Nemo kudin hayarsa tabashi...

Tikashi me Hakan ke nufi me wnn mutumin yake nufi bayan ance wnn gidan na karimene mamar Deeja, baba kandala ke tmbyr kanta.

Suna wnn tunanin me taxi yace abarshi kudinshi, juyowa Deeja tayi tacewa baba kandala "kibiyasa mana kinata kallona", "kamar yaya nabiyashi Kode kibiyashi bake barakoba ?" Ko kallon inda suke batayiba,aiko me taxi yafito yafara nade hannun riga yana karkace Baki yace "yane ko abani kudina konayiwa mace zigidir wlh" kafin kace mekenan Deeja tazaro dubu biyu Wanda suka saura mata acikin yan kudinta tabashi, ya amshe Kuma yaki bata cenjin dari biyar dinta yace ladan Bata masa lokacin da sukayi,.

*************************

Jiki ba kwari idiyatu ke kallon Rabil Wanda tun jiya shekaran jiya data kawoshi ranga ranga sau daya kawai ya farka, drip ne kawai ke dawainiya dashi, duk ya zabge yarame kamar yayi kwanaki yana jinya,.

Gurin su Fatima taleqa Suma jikin alhamdulillah gobema ake sakaran basu sallama, tayi sallama tunda su maman inaya suka amsa basu Kara mata mgn ba sbd atunaninsu tadauke kafane sbd danta yace bashida alaqa da yaran, fatimace kawai take mata mgn.

Juyowa tayi garesu ta fuskancesu tace "kugafarceni dan Allah nadauke kafatame kwana2 sakamakon nayi tafiya naje nahadu da baban Rabil wato mahaifinsa, namuku karyar cewa baya raye dan Allah kugafarceni akan hakan, mahaifinsa yana nan araye naboye mukune sbd wani dalili nawa Wanda nan bada jimawaba zaku sanshi, amma yanzu naga kamar bukatar yazo ga dansa yatasone shiyasa natafi cen gurinsa Kuma cikin rashin sa'a nasamu baya kasar yabar kasarnan gabaki daya ba tabbacin ze dawo nan kusa".

Maman inaya ce tace " Amma ko kin cuci wannan yaron dakika kashe masa uba bayan yanada ransa,"sababi take kamar zata ari baki wai dan ma bataji ainahin abinda Idiyatun ta aikataba. Dama harda haushin dake cinta tasamu tasauke wa Idiyatu duk da haka bawai ta huce akan Rabil bane tana nan tana jiransa yazo yasameta, seta masa kwando kwandon rashin mutunci.

..........................

Muktar yanzu ya shiryu lafiyar Allah suna zaune da mamansa lafiya lau, babansama yadawo dg kontagora ashe dama yana zuwa lokaci zuwa lokaci, a lokacin da sukecen gidan bature, har yanzu jikin muktar begama sakiba daga dukan da yasha a hannun sojojin nan.

Biba kuwa a yanzu babu abinda yake bukata samada iyayenta, kullum kuka take kamar karamar yarinya batada aiki se Kiran akaita gida gurin mamanta, zuwan Awwal sau biyu lokacin basu dawoba, yauma kamar kullum haka ta matsa musu da koke kokenta na fama bashiri alh Mansur Wanda ayanzu shikansa tausayin Biba yake tarame tayi duhu dukta fice a hayyacinta, batacin abinci se an matsa takeshan ruwan Lipton, yasa aka tattarata akasa amota hardashi da matarsa wacce yake jego satinta uku kenen da haihuwa aka dunguma aka tafi se gidansu Biba acen garin SULEJA dake bawani nisane dashiba dg Abuja zuwa SULEJA bawani Nisa.
Chapter 16 · 0% Book details