← Book details Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 18

Sashe 11

Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aikuwa Sega chief security yana kuka akan sitter din toilet dinsu na ma'aikata, wandonsa a hannu fadi take "nashiga uku yau son abin duniya ta yajamin rasa aikina, Ina zaman zamana nabiyewa wancen shashashan me katon Kai gashi nan yajamin bala'i yuuuuuuhhuiii" yasaki sabon kuka haka yataso dagashi se dan wando da suit wandon suit din rataye a wuyansa, baya cikin hayyacinsa kwata2, haka yadanna kararrawar kiran duk wani me aiki acikin gidan, haka suka sameshi tsaye rataye da wandon suit din sa awuya gashida dan ciki kwai, se matsar kwallah yake, haka yayi gaba suka bisa abaya zuwa falon gidan seda seka Kai bakin kofa sannan yadawo baya yana muzurai yace " meye kuke kallona kamar na cenza muku wani yabude kofar nan Maza yanzun nan.

Acen dakin da muktar da hjy Deeja suka boye kuwa, tasamesa yanata keta zawo dakin duk ya dume da wani gigitaccen wari, s magana take masa yaki kulata jikinsa duk yajike sharkaf da gumi, Fadi take "hubby baka ganin yan fashi ne agidan nan, Amma ka gudo kabarni dasu salon sumin fyade, dubi bakina yadda Daya acikin su ya zabgamin mari"tafada tana turo masa bakinta da yafara tasawa, duk wannan bayanin da take masa hannunta akan hancinta ta toshe sbd warin gudawarsa, snn kasa kasa take magana wai kar yan fashin suji.

__________________

Idiyatu jiki Kam se a hankali duk tafara komawa kamar wata psycho, idan tana zaune kawai sede aga tasaki kuka tana fadin "wayyo Allah na, kidena bina wlh ba danki bane Dana ne wayyo karki daukemin dana" ire iren wannan abin yasa Rabil yashiga damuwa sosai gashi batacin abinci, Shima seya zabge kamar me cuta, idan anason samin sauki sede amata allurar bacci, Shima bawani jimawa takeyiba ta tashi tana ihu akan kar akwace mata yaronta, Se an riketa domin gudu take kwasawa kamar fa zararriya. Seda Rabil yafara amso mata rubutu sannan aka fara samin kanta kadan, domin anyi zarya asibitoci kala kala amma suce normal take kawai stress ne ke damunta da rashin bacci.

Ahaka aka kwashe tsawon watannin biyar, lokacin tafara samin sauki sosai Se dan abinda ba a rasaba, amma totally tacenza kamar ba Idiyatu ba mace tsayayya fara tas ta bleaching, ga kwalliya amma yanzu tazama so silent shagon nata ma tadena fita se yaara ne kezama, Fatima kuwa haihuwa ko yau ko gobe, dan harta wuce edd dinta.

Agidan alhaji Mansur mijin Biba kuwa, danta Awwal yasa anyi mata kafar roba ba inda Bata zuwa da kanta, Amma bazuwa unguwa tunda ta dawo mijin ta yadena kulata baya zuwa inda take amma komi na rayuwa yana Bata, kawai de ita dince tafice masa arai, sbd munanan halayenta Wanda a daa cen betaba lura dasuba se yanzu, da irin yadda tasashi yarabu da kowa nasa harda ubansa mahaifi, daga ita se dansa batason kowa yarabesu.

Dakyar aka samu yafara kulata Shima sanadiyyar haihuwar da matar Awwal tayi tahaifi namiji yaci sunan alh Mansur, shine sanadiyyar kulata da yafara yi, sbd itace takewa me jego da yaronta wanka, dan tahana amaidasu gida, wani irin son yaron take kamar me, hakama alhaji Mansur yana matukar son yaron shine dalililn da yasa idan yazo duba yaron yadaukeshi Yana masa wasa kamar babba yayuta masa magana seta dinga Sanya baki, tun yana shareta har ya fara kulata kadan2.

Bature Hector mansion....

Zaune suke jigum jigum kowa ya yi mukus, an gama rattabawa bature yadda muktar yamaida gidan kamar gidansa, komi da hjy Deeja take amfani dashi na Isabella ne.

Muktar agefe ya sunne Kai kamar wani mumini, ga chief security Shima agefe wannan karon yayi gammo da wandonsa yadora Saman kansa se gyada Kai yake kamar kiski duk abinda Labaran me wanki da guga yafada se ya gyada Kai alamar hakane.

Shi Hector gabaki dayama dariya suke basa, yadda Labaran me wanki ya daddage cikin pidgin English dinsa inda takakare masa yahada da Hausa ya kwaba, yana bada labarin yadda aka hadawa hjy Deeja plan kancewa wnn gidan na muktar ne har akayin auren, da yadda muktar yake biyan chief security kudin hayar gidan komi be gareba kakaf seda ya zayyana,sukansu muktar da chief security sunyi matuqar mamakin yadda akayi yasan duk abinda suka kulla,kamar agabansa akayi komi,kagansa sidi-sidi kamar Wawa ashe da hankalinsa kallon biri suke masa yana musu kallon iccen hawa, sauran ma'aikatan ma kansu mamaki suke sbd wani abin ma basusan yafaruba, sbd dayawansu tunanin su yana basu cewa megidan ne yabawa muktar damar zama adaya dg cikin dakunan part din ashe muktar dinku na Allah duka gidan ya mamaye tareda sahalewar chief security.

Dadin dadawa ma hatta kayan sawar Isabella be bariba komi da komi hatta kayan hausawa Wanda Hector yabayar ayiwa matarsa bella daniyyar idan sunzo Nigeria tadinga sawa sbd shigar hausawa ta atamfa na birgeta, se yabayar ayima ta akwati kusan biyar yaso yamata surprised dasu, to su muktar yakwashe yabaiwa hjy Deeja take sakawa,.

Isabella, Danielo, Fredrick, duk kallonsu suke dansu bakomi suke fahimta acikin bayanin da Labaran me wanki yakeba, bature Hector kuwa tsananin mamaki yahasa magana, gabaki dayama karfin halin muktar ne yake Kara daure masa Kai, idan be mantaba a lokacin da ya temaki muktar yabashi aikin gadi lokacin haka yazo kofar wannan gidan kamar almajiri kullum seyazo amma su chief security da sauran masu tsaron kofar gidan sukoresa kamar kare amma haka ze wanke kafa gobe yadawo sbd kawai yanaso adaukesa aiki,.

Watarana yadawo daga unguwa yaga anata dukan mutum a kofar gidan sa, ashe chief security ne yasa yaransa suka Zane muktar saboda sungaji da nacinsa, shikuma yaki dena zuwa shine suka zanesa, haka Hector yamusu kaca kaca har yakusa korar su, sbd yadda suka yiwa muktar rudu rudu da jiki, dukda kasancewar sa nasara bayason wulaqanta mutum, haka yadauki muktar yakaisa asibiti aka masa treatment din ciwukamsa, sannan ya tambayesa meyasa kullum yake zuwat masa kofar gida gashi masu gadi sundakesa, cikin marairaita muktar yake fadawa Hector cewa shi bakone a garin besan kowa ba yaxone ko zasu temaka subashi Koda aikin gadi ne shima yadingayi yasamu yarike kansa, kasancewar muktar yanajin turanci cikin harshen turanci yake fadawa Hector damuwarsa, haka yaji tausayinsa yace yakoma gida idan yaji sauki yadawo shi zebashi aiki, yamika masa katinsa yace yakirasa, Kuma yabashi kudi dayawa domin yakula da kansa har zuwa lokacin da zedawo amsar aikin.

Dahaka muktar yafara aiki agidan bature, farko wuya yakesha gurin su chief security sbd sunji haushi ankaro musu me gadi suna bakincikin yasami alherin da suke samu sbd Hector bashida keta Sam kusan dubu dari yake bawa duk masu masa gadi a wata, shiyasa suke masa mugunta, seda Hector yamusu barazanar kora dukkansu snn muktar yasami lfy ashe kwallon shegene tsiyarda ke wandonsa tafi kaefinsa.

Sauke ajiyar zuciya hector yayi, yayinda Danny ke sake tambayar sa "dad is everything alright? U have been quite for while, wat r dis people saying? I can't understand anything".

Gaya masa abinda muktar yy briefly, cikeda mamaki suka juyo suna kallon muktar Wanda zuwa yanzu jikinsa har diga yake da zufa, rigarsa tajike sharkaf da zufa.

Wani kukan kura Deeja tayi ta afka kan muktar tana.....,

Barka da sallah once again ma people.

Momsani...... ✍️

🌹 SIRIKATA 🌹
Na SADIKA IBRAHIM.

Pg 21_22

Bismillahirrah manirrahim.

A yanzu Biba ta saduda kamar ba itaba tanata fama da kafar robarta, amaryarta ma tsohon cikine da ita, Biba tayi kuka kamar me tayi takaicin yadda duniya tajuya mata baya, ahakan ma tagode wa Allah tunda alh Mansur be saketa ba, daya saketa batasan Ina tanufaba sbd har yanzu batasan inda iyayen ta suke ba baban ta bata samin wayar sa, mamanta Kuma tunda Awwal yaje akace masa tabi muktar basu sake Jin duriyarta ba, gashi ita Biba saboda tsananin rashin zumuncinta ko abaya bata damu da muktar yayanta ba, saboda kar yarabeta tasami nakasu acikin dukiyarta, shiyasa bata taba sanin inda yake aiki ba acikin garin Abuja gashide agari daya suke amma batasan yadda yake rayuwa ba.

Ko aurensa batajeba sede ta tura masa kudi, Shima seda Awwal yayi ta magana sannan tabashi acct number din muktar yatura masa makudan kudade yace ga gudunmuwar mamansa nan, aiko Biba tayi bakin cikin yawan kudin da Awwal yabawa muktar, shikuma d kudin yayita facaka a lokacin bikinsa da hjy Deeja.

Shikuma alh Mansur har yau sama sama yake da ita balle yadamu da ita da damuwarta.

Kullum tana tunanin Ina iyayenta suka shiga suka barta da duniya gashi yanzu tana ta koya mata darasi alokacin da yadace, shikuma Awwal danta kasuwancinsa yasha masa Kai, kullum ta Allah ze shigo yadubata ya gaisheta yatambayi bukatunta idan yafita kuwa se tayi bacci ma yake dawowa, hakama iyalansa kullum suna hanyar gaisheta da dan jikanta yaro me kyau bulbul dashi,.
**********************

Idiyatu jikinta alhamdulillah tasami sauki sosai sede duk tayi la'asar tadena batun bin bokaye duk shafe shafen mai yanzu babu duk tayi baqi tarame shagonta ma tadena fita yara ke zama aciki suna kula mata da shagon.

Yau Fatima matar Rabil ta tashi da wani azababben ciwon nakuda ankaita asibiti abu tun safe har yamma tayi tagalabaita matuqa batada sauran wani kuzari idiyatu ana gefe da charbi se jaa take dan yanzu batada aiki se istigfari, mahaifiyar Fatima ma haka Rabil kuwa duk ya susuce yafita hayyacinsa kamar shike nakudar, yakasa Sanya komi abakinsa tun daren jiya rabonsa d cin wani abu sede ya amshi ruwa yasha ragowar ya tofa addua abaiwa Fatima tasha amma haihuwa shiru.

Har likitocin sun fara Shirin yimata aiki dakayar aka samu Rabil yasanya hannu aka shiga da ita aiki tanata neman gafarar sa, Idiyatu se hawaye take itama tana neman gafarar Fatima.

Haka aka gungurata Saman gadon asibiti zuwa theatre room.

Anyi aiki lfy anciro mata yaranta biyu duka Maza, masu tsananin kyau abin haryaso firgita doctors din dayan yaron idonsa ocean blue kyakkawa sosai kamar ba jaririba, dayan Kuma bezo da lafiya ba yazo da ciwon zuciya gashi yafi kyau ma, shi ko kwayar idonsa basu samu ganiba dan ko kuka yakiyi, gasu manya kamar ba twins ba, they look identically.

Cikin kwarin gwiwa tarda murnar samin nasara wata nurse tafito da sauri tazo gurin Rabil tace "yallabai albishirinka"?
Chapter 11 · 0% Book details