← Book details Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 18

Sashe 5

Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka Idiyatu taci gaba dason muhsin da bawa rayuwarta wahala dan shi bemasan tanayiba, shigar ta university yasa takara wayewa tayi kawaye wayayyu Kuma tambadaddu irinta samari kala kala kowa kulawa take yan iskan makaranta kowa tasanshi amma Bata taba Bada kofar fa za a gane Hakan a gidan ba.

Bikin muhsin da zainab yamatso haka akasha biki nagani na fada tunda baban zainab me kudine Hakan yasa yabawa muhsin MD a kampanin San na sarrafa Mai, arziki yakaru Kuma ya wadata idiyatu da komi na rayuwa suna zaune lfy da maman sa har takai matakin 200level lokacin kan har shaye shaye tanayi ba Wanda yasani, Kuma bata dena son muhsin ba kullum kamar Kara mata sonsa ake.

Bayan shekara biyu lokacin takusa yin graduate amma saboda dakikanci c.o dinta sun hana ta yin graduate har an koreta a makaranta batareda su maman muhsin sun saniba, kullum Kuma seta fita dasunan zuwa makaranta. Lokacin muhsin dan sa me sunan Rabil an yayesa.

Wata Rana da daddare Idiyatu tayo gayyar abokanta 'yan dabar makarantarsu Wanda aka koresu tare sakamakon dabancin da sukayi wa wata malama suka mata mugun duka mazan Kuma suka mata fyade Hakan yy sanadiyyar mutuwarta, an Sami nasarar kama wasu yayin da kafin azo kansu Idiyatu ta tattaro su sukazo gidansu muhsin, yasha mamaki matuqa ganin Idiyatu cikin bakaken kaya kamar 'yar fashi, murmushi tamasa tace "kayi mamakin ganina ko muhsin? To ba abin mamaki bane ganin cewa kaki karbar soyayya ta nikuma har yanzu Ina sonka Hakan yasa zan Maka adalci guda shine ko kabani kudade kimanin billion dari ko kuma..... " Takai karshen maganarta tana shafa wuyan zainab alamun yanka.

🌹 SIRIKATA 🌹

Na SADIKA IBRAHIM.
Momsani.

Bismillahirrah manirrahim.

Pg09_10

Pg dinkine Ayshu kawar idiyatu.

Ina Mika sakon godiya ta gareki *YUMNERH* nagode sosai Allah bar tare.

Cikin rawar jiki da murya Muhsin yace "sister dagaske zaki iya kashe rai? Dagaske zaki iya kashe matata zainab? Duk irin halaccin da nai miki a rayuwa,innalillahi wa inna ilaihi raji'un" "shiiiiiiiiiiii"idiyatu tafada tana dora hannunta akan lips dinta alamar ya yi shiru.

"Ai baka nemi zaman lafiyaba tunda kace bakaso na, my friend kinɗly nd silently go nd bring d money i demanded,or else..." tayi fito tana kallon sama tanuna zainab daketa kwakwume yaronta akirji.

Bamusu muhsin yatashi wani daga cikin ƴan daban ya na binsa da wata sharbebiyar wuqa a hannu, sama suka haura har dakin muhsin yajawo side drower dinsa ya dakko wata ƴar jaka karama shaqe da kudi,dama banki ze kaisu besami dama ba yabari har gari yawaye se yakai, mikawa wnn ɗan dabar ya yi,amsa ya yi suka juyo zasu fito kenan sukaji jiniyar motar police, ai jiki na rawa ya ture muhsin ya sakko a tamanin kan kace me sauran ƴan dabar sunfara fita aguje aiko duk wanda ya fiya jikake fass an harbeshi,ashe me gadin da suka daure ne yasami nasarar kwancewa ya yi sauri yakira ƴan sanda.

Jin anata sheqesu yasa Idiyatu tadaki kan zainab da bayan wuqar dake hannunta ai dasauri Muhsin ya yi kan matarsa,kasancewar basuda bindiga ko daya sede wukake da adduna, aiko nan take zainab ta sume kanta yafashe dauke yaron Idiyatu tayi da jakar kudin ta rataya tasawa yaron wuka a wuyansa wanda yafarka sakamakon faduwar da ya yi sanda aka daki mamansa akai, a hankali Idiyatu tafito riqeda yaron tasamishi wuqa a wuyansa fuskarta rufe rub da face mask.

Ganin haka ƴan sandan sukaja da baya suna cewa "you are under arrest young woman, ki ajjiye yaron nan ko kuma muyi harbi" kara seta wuyan yaton tayi da wuqar hannunta aiko yasaki kuka muhsin yace "dan Allah karki cutar da yarona,baimiki komiba pls ki bani shi kitafi da kudin, i promise u ba wanda ze harbeki pls" yakarasa yana zamewa kan gwiwoyinsa, ko ajikinta haka tacigaba da tafiya da yaron yanata tsala ihu ga wuqa a wuyansa har tafata jimasa ciwo.

Tana kaiwa waje tashige motarsu taja aguje tabar wurin aguje,aiko suna ƴan sandan suka rufa mata baya,haka taketa tsala gudu acikin wnn daren,gudu take iyakar iyawarta,bata tsaya ba har seda tabacewa ganin ƴan sandan nan,shiyoyin asuba takawo maƙera, Rabil ya yi kuka har ya gaji ya yi bacci, wani kauyen makera tashiga wani karamin garine babu yawaitar mutane.

Koda gari ya waye tasami wasu ƴan tsirarun mutane tafada musu cewa ita bakuwace, tana neman gidan da zata saya ne,ƴan kauye baruwansu ganin ta da yaro kuma tafada musu dantane tabaro garinsune sakamakon fadan hausawa da yarbawa a garin ibadan.

Gida madedeci tasamu tasiya, haka tabawa wani saurayi agarin sako yazo cikin gari ya siya mata komi na abinci da kayan da Rabil ze saka,komi na abinci tasiya motar kuwa wani guri tasamu taboyeta acikin kauyen.

A cen bangaren su muhsin kuwa an baza jami'ai tako ina neman Idiyatu an rufe kowacce hanya da tashoshin mota,hatta airport ko ina an baza nemanta. Sam tunaninsu be basu zata iya zuwa kowane kauye ba ganin irin maƙudan kudin da ta amsa fiyema da yanda tayi demanding.

Zainab tayi kuka kamar idonta ze fita itade koda yaushe batada abin fadi se sunan ɗanta Rabil da Idiyatu.

Wani abin mmk shine an nemi hoton Idiyatu ko daya babu ataredasu,shidama muhsin bashida hotonta a wayarshi,mama ce hotonta dayawa amma abinda yabawa kowa mamaki shine babu hoton idiyatu ko guda a wayar mama,su dama ƴan sanda basusan fuskartaba, wayon tsiyane da ita ko a school bata hoto bata yadda da hoto ko video ba,hakan yasa aka rasa ta yadda za,a samo koda me kama da ita,har school anje ko alamar takaddunta babu balle asami koda irin ɗan karamin hotonta na passport.

Haka Idiyatu tayi ta zama a wannan kauyen dako sunansa bata saniba sedaga baya da hankalimta yakwanta ta aminta cewa koda wasa baza a iya zuwa nan dasunan nemantaba sannan tasan sunan ƙauye, har tsawon shekara hudu lokacin sana,arta ta tireda yabunƙasa sosai,Rabil kuma ya yi girma abinsa shekararsa shida cikin na bakwai yaron akwai wayo sosai betaba sanin ba idiyatuce mahaifiyarsa ba tsawon wnn shekarun ba abinda yarasa yana zuwa islamiyyar garin tareda yara ƴan uwansa harda ƴar primary din garin wadda a yanzu an ɗan sami cigaba a garin har boko akwai sannan an musu famfuna ga wutar nepa da sukeda ita available.

BAYAN SHEKARA GOMA.

A wannan lokacin Idiyatu tayi haramar barin garin BODIN SADAU,shine kauyen da take zama da Rabil ɗanta, takoma ibadan da zama acen tasa shi a makarantar boko ta Barrak da islamiya.

Rabil yarone me matuqar hankali da nutsuwa,bagashiga abinda ba bu ruwansa,sannan becika tsawwalawa akan lamariba ko wanne irine,baya shiga abinda ba bu ruwansa ko kadan.

Wani abin al ajabi shine Idiyatu tanason yaron Muhsin da ta sace tamaidashi ɗanta,tabashi ilimi sosai na boko da islama.

Har ya yi sauka, afannin boko kuwa yana shekarar kashe a secondary, idiyatu makwadaddiyar mace ce ga zafin nema,duk yadda kake da ita bakacin abinta ta sauƙi,ta iya maida taro yakoma sisi,amma akan ɗanta Rabil zata iya kashe ko nawane.

Haka taci gaba da zama a garin ibadan cikin unguwar sabo,inda duk hausawa sunfi yawa a gurin.

Rabil yafara soyayya da wara yarinya ƴar makotansu fulani ne, yarinyar marainiya ce babanta ya rasu, Fatima shine sunanta, Idiyatu batason yarinyar ko kadan acewarta fulani mugayene.

Ahaka soyayyar fatima da Rabil tayi nisa sosai har manya suka nemi yaturo.

To anan nefa akeyinta,dama a koda yaushe idan Rabil ya tambayi Idiyatu ina ƴan uwansu da babansa, seta ce masa basuda kowa a rikicin fulani da makiyaya na cen kauyen da suka baro aka kashe kowa nasu,hakan yasa be takura kansaba sbd Idiyatu ta masa komi a rayuwa tazama uwarsa,ubansa,danginsa,hakan yasa baya wani damuwa.

A shagonta na saida drinks dake ita bata zauna hakaba tun kudin da tayowa baban Rabil fashinsu take jujjuyawa kuma se Allah yasawa abin albarka,dawowarta ibadan tabude babban shago kato nasaida duk wani nau'i na drinks ba bu kalar da bata siyarwa.

A cen tasami wani mutumi cikin wadanda suke sana'a tare tabiyasa akan yaje nemawa Rabil ɗanta auren Fatima duk da cewa ba wani son ta takeba amma yaxatayi tunda ɗan lelenta naso.

Itama ɓangaren Fatima wani maƙocinsu ne ya amshi matsayin babanta tunda ana zaman mutunci,abinka da auren marasa asali cikin ƙanƙanin lokaci akasha bikin Fatima da angonta Rabil.

A lokacin Rabil yafara kasuwancin saida shaddodi kala kala da yaduka different design.

Daga baya ma da abin ya yi albarka harya bude katon shago ana kawo masa kaya daga garuruwa daban2,da kasashe.

Cikin shekara biyu da auren Allah yamasa wani irin nudifi ya bunƙasa sosai.

Sede har lokacin babu alamun ciki atareda Fatima, abinda basu saniba shine.......

# FLASH BACK#

Wata biyar kafin auren Rabil Idiyatu taje wani shopprite ta sai mayukanta na bleacing,wanda Rabil ya yi fama akan ta dena taƙi, tana tafe tana zaɓen wanda yamata tana ƴan wakokinta,taji an dafata tabaya ance wanake gani kamar Idiyatu kawata..

Juyowar da zatayi idonta yasauka fess cikin na Biba kawarta.

Mamaki,tsoro, da shock su suka rike Idiyatu na ƴan mintoci, seda Biba taɗanyi waving hannunta agurin idanun Idiyatu sannan tayi firgigit tadawo daga dogon tunanin da ta lula,kawai seta fashe da kuka tafada jikin Biba,kuka take mecikeda kissa da makirci,fadi take "ki gafarceni kawata, dan Allah kimin aikin gafara an cuceki kuma an cuceni nima, sebayan tafiyarki nagane cewa ashe malamin da muka kaiwa aiki ashe akaina ya yi aikin ba akankiba, nima wlh bada sanina hakan tafaruba,kuma bayan tafiyarki zayyad yadinga kuntata min,dukan yau daban na gobe daban,wahala kala kala ba bu wadda bansha ba a hannun zayyad ga tsohon ciki yabarni dashi karshe yamin duka kuma yamin sakin wulaqanci babana saboda baƙin ciki yafadi yamutu,bayan rasuwarshi da wata daya mamana ma takasa juran rashin mahaifina itama tarasu,haka naita wahala nikadai babu matemaki daga bayan nakama wanki da surfe har Allah ya saukeni lafiya na haifi namiji daga nan nacigaba da wanki na da surfe har Allah yamin arziki nadawo nan da zama,yanzu hakama auren yarona saura watanni kadan".

Se yanzu tasauke numfashi daga karyar da take shararowa........

🌹 SIRIKATA 🌹

Na SADIKA IBRAHIM.
Momsani.

Bismillahirrah manirrahim.

Pg11_12

Biba kallon Idiyatu kawai take da madaukakin mamaki, Amma bata bari Hakan ya nu na ko a fuskartaba.
Chapter 5 · 0% Book details