← Book details Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 18

Sashe 1

Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

🌹 SIRIKATA🌹
Story nd writing by: SADIKA IBRAHIM
Momsani.......✍️

Bismillah rahmanir raheem.

*Wannan littafi me suna SIRIKATA kirkirarrene banyi dan cin zarafin wata ko wani ba,Allah yasa yadda nafara a sa,a nagamashi cikin amincin me duka*

Note:*wasu zasuga Ina yawan yin labarai na da garin kontagora,yes hakane sbd Ina alfahari da kasancewata yar cen besides ma bansan kowane gari ba bayan namu😀😀ni kifin rijiyace iya garinmu kawai nasani,Kuma Ina fatar Hakan ze baze Dami me karatuba,sannan Ina fatar darasin dake ciki dasakon da labarin ya kunsaya isa inda ake bukata ngd*🤲

Pg 01_02

Kontagora Niger state.

Zaune suke agaban wani shirgegen mutum yasha babbar riga da rawani hannunsa rikeda katuwar charbi irin me dubu dinnan, idonsa yasha kwalli ranbadau katon mutum ne bakin kirin dashi fuskarsa cikeda gashi buzuzu lebensa manya dasu kamar biredi dan dari da hamsin se mui-mui yake da baki kamar me karanta wani abu gabansa wani farantin kasa ne idan yaja charbin nan se ya dangwala kasa se zare ido yake, sukuwa se kallonsa suke suna jiran suji abinda zece, cen daya gama gungunin sa yace "ke Idiyatu, kozaki mutu matar danki seta haihu Kuma idan kika matsa akan hana faruwar haka to tabbas mala,ika azara,ilu ze ziyarceki,domin akwai rabo me zafi atsakani inkika cika matsa lamba hahahaha margaya Sala"

Jikinta na rawa tace "to Allah yatemaki mlm buzu bawata mafita ne" dole seta haihu? nifa kozanyi yawo tsirara wannan shegiyar bafulatanar banason ta haihu da dana"

Kallonta mlm buzu yayi yace "lalle bakida hankali kikace ko Zaki yawo tsirara ne ko? to ai se kina raye ne Zaki yawo tsirarar ko? Wakika ga yana shiga hurumin ubangiji har haka? Kin taba ganin Sara da sassaqa yahana gamji toho? To ko gurin wa zakije magana guda ce za a fada Miki matar danki seta haihu sede in kudinki za aci afada Miki sabanin hakan, ni kaina duk hatsabibancina bana matsawa akan irin wannan Al amarin saboda da aure da haihuwa idan kadage akan dakatar dashi sekiga Allah ya daukeka anyi babu Kai to mekenan akayi badi ba rai? to badaniba nide na fada miki abinda yake akwai kuma me yuwuwa inkinji kanki in bakijiba ruwanki nide na fada Miki gsky kafurar banza bacemin dagani anan" yafada yana kwalalo mata kananan idonsa da sukasha kwalli.

Jiki na rawa daya matar me suna Biba tace "gafarta mlm ayi hakuri bata sani bane,tayi kuskure ayi mata afuwa yanzu menene abinyi bawata hanyar da za abi?"

Kallonsa yamayar kan Biba yace babu amma za,a iya yima su farraqu da juna ko an haifi yaro ko yarinyar baze sotaba zema iya cewa ba danshi bane ko 'yarshi".

"Yawwa mlm buzu ayi hakan,hakama yayi,to yanzu nawane kudin aikin?"

Yana hura hanci yace "dari uku ne ba yawa" zugurar idiyatu Biba tayi tace "kibada kudin mana kinyi zugum kamar me tunani" sauke gauron numfashi tayi "hmmm Allah temaki mlm ba ragi"?

Idon mlm buzu cikeda bala,i yace "nafasa Miki aikin makwadaddiya 'yar munafuka baqar muguwa tashi kibar min guri kafin na sauya Miki kama marar godiyar Allah"

Jikina rawa Biba tace"Allah ya huci zuciyar mlm buzu me abin ban mamaki batasan ba a tayin aikin ka bane namanta ban mata wannan bayanin ba gafarceni mlm zamu Bada kudin" idiyatu jiki na rawa ta dakko kudin acikin Jakarta tamikosu dubu dari uku cif, duk irin rudewar da tayi da tsoro mlm buzu Daya shigeta besa tayi zuren kudin ba dari uku cif tabashi lols, sannan ta tashi jikina rawa tafita tabar Biba aciki tana Kara bawa mlm hakuri.

A hanyarsu ta barin kauyen ma haka Biba keta sababi kamar zata ari baki, "ni wlh Idiyatu wannan halin makon naki yana bani mamaki da haushi, haba ayi mutum me shegen son abin duniya haba Dan Allah, ga bakin Hali,ga son abin duniya duk ke kadai kika hada wannan abin ga hassadar tsiya wacce koni da muke tare baki raga min ba,to wlh nagaji da mugun halinki sekace ke kadaice bayerbiya adoron kasa kinuna kinfi kowa son abin duniya,to wlh nagaji da halinki,gurin malamai kusan uku kikamin wannan abin inbanda ke ma ai ranar biyan bukata rai ba abakin komi yake ba keda zaki samu makudan kukade Amma kike ta wani tsumulmular fidda dubu dari uku haba dan Allah wannan ba girmanki bane"

Idiyatu de ba baka se kunne ita gsky ba haka taso ba taso ace kwata-kwata Rabil be Sami da ko daya a duniyaba,ita gsky acikin agenda dinta babu da ko 'ya saboda tana ganin ko bajima koba dade Rabil ze waiwayi wannan yaron, musamman idan ta tuna yadda yake bala,in son yaga da ko 'yar sa aduniya,yasha fada mata cewa idan Allah yabashi da ko ya ze raba dukiyarsa biyu yaba wannan dan ko 'yar, kenan ita ko oho to bazata taba bari Hakan ta faruba bayan tabiyo ta karkashin kasa ta rabashi da danshi ko 'yarshi to zata hada harda makirci da tuggi gurin ganin ta hanashi amsar wannan abin da za,a Haifa masa. Da wannan tadagawa Biba daketa zuba kamar kanya hannu tace "pls sararamin hakanan,inace duk jirgi daya ya kwasomu? Kefa kadanki ne kike zubarwa matar danki da ciki Kuma kika lakaba mata sharrin cewa itace batason haihuwa har seda kikasa danki yasaketa Kuma kika aura masa wata itama Baki cenza zani ba haka kike sashi yanata aure aure kamar daddawa, to sahirtamin hakanan ehe"

Haka sukata yiwa kansu tone tone har suka fito titi sannan suka cigaba da kitsa yadda zasu Kara zage dantse gurin ganin sun Hana sirikansu zaman lfy.

___________________

Unguwar dadin kowa.

Masifa take kamar zata ari baki bakinta har kumfa yake kamar an kada mata Omo aciki saboda bala,i, wayace kare a kunnenta fadi take " wlh na gwaggo ko ka maidoni minna nan ko kuma kaga bacin raina iskancin banza da wofi, nizaka nunawa aure to sannu tattabara wlh idan har bazaka kaini minna ba kaima sede ka tattaro karuwar matarka Kuma juya kudawo nan indinga ganin ku,inga wacce waina kuke toyawa acen din azo nan ayi agabana ingani, ga dakin da muke ajiyae itace cen ashare muku ku zauna, ai dama daga Kai se ita tunda taki haihuwa sede aci akai masai se uwar kiba da take narkawa kamar jaka," Dan tsayawa tai tana sauraron me ake fada kafin ta lailayo wata uwar ashariya ta narka zanci burar...... Dan kaniya kawai na gwaggo ni kake fadawa naji tsoron Allah? Ni na gwaggo? To idan ban daga Maka nono akan karuwar matarka ba me nake,kace mudi me walda bada jini ya haifeni ba" sekuma tasaki kuka "yiiiiiii na gwaggo ba lefinka bane nasan an gama dakai an wanke Maka buje ka shanye a jiqa Maka jinin al,ada kasha wayyo ni Allah na na gwaggo yiiii"

Gidan baban nera.

Gidane na Gani na fada, gidane me shegen kyau hawa biyu kamar gidan wani me muqami yahadu gidan over kamar a turai.

Zaune take akan daya daga cikin Maka makan kujerun da aka kawata falon dashi tasha less peach color hannunta yasha zobunan diamond masu kyau farar mace me kyau wiyanta sanyeda wata siririyar sarka idonta sanyeta gilashi Kara karfin gani (*medicated*) falonko yagaji da haduwa komi na falon black nd white ne tun daga kujerun Wanda suka kasance set uku har zuwa curtains da center carpet,kafar ta Daya akan daya hannunta daukeda glasscup tana siffing din strewberry jus akalla zatayi Shekaru 37 zuwa da takwas, wata dattijuwa ce zaune akasan carpet din kusada kafafunta kanta akasa kamar zatayi mata sujjada tace "hjy dije lemon yayi Dede ko?" Cikeda fusata da izgili tace "sede in kece dije ko kuma tsohuwar ki bade ni ba, ni sunana hjy DEEJA ko kokuma kice beauty kamar yadda danki yake fada"

Kan wanna dattijuwa akasa tace to "jija kiyi hakuri hjy jija" afusace DEEJA tawatsawa wannan tsohuwar lemon dake hannunta tasa kafa ta shureta tace "jeji zakice ba jija ba uban waye jija? Matsalar dan kauye kenen kina zamanki akauye inda yafi dacewa dake Amma saboda kawai son atakuramin daga zuwa gaisheki kika kwaso kafa kika biyomu kamar gidan ki, Koda yake gidan danki ne bakida iko dashi balle kizo ki share duwawu ki zauna, dan naki ma nikeda sitiyarin juya rayuwarsa da duk abinda ya mallaka. Kuma inason kisawa ranki cewa ukubata itace ajalinki fitinanniyar tsohuwa kawai kwadayya mtwsss "

Tasa kafa ta take yatsar wannan tsohuwar tajuya zata wuce kanan sukaji sallama abayansu wani mutum ne yashigo da alama shine me gidan yasha babbar rigar wata danyar shadda sea green se kamshi yake fuskarsa daukeda fara,a yake cewa "barkan kude da gida" idonsa yasauka akan matarsa abin sonsa durkushe gaban mahaifiyarsa tana kokarin dagata ta tashi tana fadin "ayyah inna seda nafada Miki kidinga kirana idan Zaki sakko Saman matakalar nan saboda santsin tiles din kar ya kada ke ga jikin tsufa sannu kinji daure ki tashi"

Ai dasaurinsa yakaraso yakama mata suka daga inna suka zaunar Saman kushin, Fadi yake "inna bakideji ciwoba ko? Sannu" yafada yana zaro wayarsa daga cikin aljihun babbar rigarsa ya dannawa likitansa kira ringing daya ya dauka yace "pls Dr kazo kaduba min inna tsantsin tiles ne y dibeta ta Fadi,ok sekazo" ya ajiye wayar yamaida dubansa kan inna daketa sharar kwallan, yayin da DEEJA ke gefe tana zuba mata uwar harara ganin ze juyo ne yasa taci gaba da goge idonta kamar me hawayen gaske tace" sweetheart nacewa inna tadinga min magana idan tanason wani abu base tafito ba saboda bata Saba taka tiles ba kar taje ta Fadi gashi yanzu ta Fadi har ma jus dinda ta dakko ya zube mata ajiki Kila zata Sha ne tunda kaga ai basaba shansa tayiba may be ma gurin Shane zakin yadebeta tafadi batasan takawo gurin steps ba" tafada tana share kwallan karya.

Memakon yaji zafin maganarta akan mahaifiyarsa sema Jin yayi takara kima a idonsa gani yadda ta damu akan faduwar mahaifiyar tasa harda kukanta.

"Bakomi beauty zata kula next time ai in Sha Allah,ok stop wasting ur preasious tear umm" yafada yana janyota jikinsa kamar ba agaban uwarsa yakeba Yama manta da wata inna agurin seda Dr yayi sallama tareda Neman izinin shigowa shine ya tuna da inda suke yayi saurin sakinta tareda bama Dr izinin shigowa, Koda suka juya wayam ba inna ba dalilinta...
Chapter 1 · 0% Book details