← Book details Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 18

Sashe 4

Sirikata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan sati Daya da faruwar hakan yau su Idiyatu ansamu abinci me rai da lafiya anaci harda kazarsu kasancewar taye ta hada idiyatu da wani tsohon kwartonta dasuka hadu gurin Saida maganin basir, ranar tafita ko tasamo musu abinda zasuci tahadu dashi suka gaisa yace mata kwana2 andena ganinta, nan fa ta labarta masa cewa mijin yartane yagudu yabarta gashi itama yanzu batada jari balle tafara wata sana,a shinefa yace tazo Sudan sakaye se asamu abinda aka bata, ba musu tabisa bayan sun gama yabata 4k,sannan yace takawo yar tata se asamar mata dan abinyi, taye na murna takoma ta labartawa Idiyatu wannan albishir shinefa yau ya dauki Idiyatu ganinta bawata babba bace ya kaita cen gidansa seda sukayi kwana 2 yana gurje Idiyatu sannan yamata sayayya yakawota gida shinefa ake Shan dadi yau.

Sallamar Maza suka faraji suna tsaka dacin dadinsu, wannan karon taye ce taje taduba katti tagani sunyi su biyar tace musu "lafiya kuwa wa ake nema?" Daya daga cikin su ne yace "mata yau wa, adin zamanku yakare ko kufito dakanku ko mufito daku".........

🌹 SIRIKATA 🌹

Na SADIKA IBRAHIM.
Momsani.

Bismillahirrah manirrahim.

Pg din nakune kawayen idiyatu.
Ummu zee
Khadija Musa
Miemie
Reema

Pg07_08

Ja da baya taye tayi tadakata da sudin hannun da take tace "kamar yaya mufito ko kufito damu, banganeba? Nan din gidan mijin 'yatane, gidan sirikina ne zayyad".

Wani daga cikinsune Wanda yadan fisu sauki da alama ya matsa yace mata "hakane gidan sane amma a daa yanzu kuma yasaidashi wa alhaji lawan me kekuna, sannan yabada wannan abawa matarsa Idiyatu", yafada yana mikama taye takarda an nadeta da envelope.

Jikina rawa taye ta amsa tajuya cikin gidan hankali tashe, tana zuwa tamikawa Idiyatu takaddar tace takaranta musu Maza Maza, Idiyatu na tambayarta suwaye a waje amma Ina hankalin taye baya jikinta itade kokarinta taji me ke cikin wannan takaddar Allah yasa de ba abinda take zargi bane, dan ita harga Allah batason auren idiyatu ya mutu..

Tana wannan tunanin ne taji Idiyatu tasaki ihu da ashariya, kuka take sosai dan Allah ne kadai yasan irin son da takewa zayyad. Bakomi wannan takaddar ta kunsaba face Sako daga zayyad kamar haka "*Ni zayyad Abubakar nasaki matata idiyatu murtala sakamakon Allah ya dawo dani cikin hayyacina, dama na auretane bada sanina ba Kuma bada sanin iyayena ba, saboda haka nasaketa saki uku, Allah ya hada kowa da rabonsa na alheri Kuma nayafemata duk zaluntata da tayi Allah ya yafe mana baki daya*"

Wani iru kuka idiyatu keyi kamar ranta ze fita se fatali takeyi da yan komatsansu da suka saura basu siyarba, har abincin duk ta watsar taye se hakuri take bata,Dan itama kadan yarage bata sa kukan ba, suna cikin wannan halin ne wannan kattin mazan suka shigo suka fara musu fatali da yan kayansu waje seda suka watsa komi waje sannan sukace musu "zaku fitane ko se mun fitar daku kamar yadda mukayiwa kayanku? matsiyatan banza maciya amana karuwai, Allah wadaran zuri, a irin taku ba uwa ba Uba ba yar ba kowa tambadadde, in Sha Allah karshen ku baze kyauba kamar yadda na mijinki beyi kyauba" suka fada suna nuna taye, a haukace taye tace " me kuke nufi da kamar yadda na mjina beyi kyauba? Meya Sami murtala ku gayamin?".

Daya daga cikinsune ya dubi idiyatu a wulaqance yace " ranarda yadawo aranar yaga lokacinda tsohon kwartonki yadauki diyarki Idiyatu acikin motarsa, dama ai yasan wannan mutumin kwartonki ne, to sekuma gashi yagansu da Idiyatu sunshiga hotel din colony, aranar ne yarugo aguje dan yasamu wannan mutumin yamasa warning kan cewa meyasa ze dunga bin uwa da diya, Aiko Yana Hawa titi wata kanta tabi ta kansa nan take kafafunsa suka fita daga jikinsa, muduk Muna wurin muka taso da sauri dan mukawo masa dauki, a lokacin ne yaketa kwarara ihun azaba, Yana fadin a je a dakko masa yarsa Idiyatu tashiga wancen hotel din na colony tareda tsohon kwarton uwarta, shin batasan kwarton uwarta bane,? Se ihu yake kafin ayi wani yunkuri ya kama aman jini ta hanci ta baki, Koda aka isa asibiti dashi rai yayi halinsa, kuma me motar da ya bigeshi be tsayaba ya gudu, muma da muka kaishi asibiti Muna ganin ya mutu muka zame daya bayan daya muka gudu ato bame kudin da ze biya ayi masa wani abin, anan ne mukasan abinda yake faruwa kude kunyi asarar rayuwarku".

Yakai karshen maganarsa yana wani karkace baki irin na yan jagaliya.

Wani irin ihu Idiyatu tasaki nan take ta sume agurin itakuwa taye kamar an zare mata lakka ta dena motsi agurin, seda wannan samarin suka fara balbalin masifa kan cewa zasu kaisu waje sannan taye tayi kamar an mintsineta ta tashi dagudu tayi hanyar waje tana ihu irin nasu na yarbawa idan an musu mutuwa, ihu take tana gudu kamar zararra har takawo kan titi itama tana Kiran sunan murtala tana cewa ta shiga uku se kallonta ake kamar kwancen hauka tana gudu tana ihu, wani me Hilux ne ya shararo aguje yayi tafiyar yaji da raye ji kake timm ta tashi sama ta fado nan take tasami kariya a hannun ta na dama da cinya, kanta ya fashe, ganin haka mutane suka taso ruuu akayi kanta wannan me motar Daya bigeta ya fito hankali tashe yace "Dan Allah kutemaka min nakaita asibiti" haka aka kama taye batasan inda kanta yakeba aka kaita general hospital...

Koda wannan samarin sukaga Idiyatu taki farkawa suka dibo ruwa a katon buket suka lema mata, numfashi taja se Kuma ta tashi tana dube duben inda zataga taye, daya acikin wannan samarin ne yace mata ga uwarki cen tafita da gudu tana ihu kamar ta haukace seki tashi ki bita ko kuma yanzu mu fitar dake

Da gudu itama ta fita tarufawa uwarta baya, haka tayita gudu tana ihu tana Kiran sunan uwarta, wani saurayi ne ya tsaida ita se Kuma take kamar zata shide bala,i goma da ashirin itakam yau Taga ta kanta duniya tajuya musu baya kamar juyin waina a tanda, wannan saurayin ne yagaya mata abinda ya faru da taye dakuma kaita asibiti da akayi, Kara rushewa tayi da kuka idonta har yafara rufewa saboda kumburi, rokarsa tayi yatemaka mata yabata ko dari biyuce, tausayi tabashi matuqa ya dakko dari biyar yabata, gdy tayi ta tare napep ta wuce asibitin da aka Kai taye.

Wannan me motar shiya biya komi da akayiwa taye, dama sauri yake zeje meeting wani gari segashi Kuma wannan Abu ya faru, yana zaune a reception yana waya Sega idiyatu ta shigo da kuka wii Wii dasauri ta tambayi wata nurse ko an kawo wata mata me suna taye, hatsari tayi, nurse din tace batasaniba Amma de ankawo wata takakkarye sede batasan sunan ta ba, tanuna mata block din yan hatsari dasauri idiyatu tanufi block din tana zuwa kuwa taga taye kwance kan gadon marasa lfy an daure mata hannu da kafa da Kai kamar ma Bata numfashi, dasauri cikin kururuwa tanufi gadon da taye take Kai se ihu take abinka da yarbawa lols, nurses ne suka fara yimata fada kan cewa zata tayar da marasa lfy ba a son hayaniya sannan idiyatu tayi shiru se hawaye take.

Tana nan zaune tayi tagumi sega wannan mutumin da wata mata babbar mace sunzo wurin direct gadon taye suka nufa matar nata alhini tana magana, idiyatu de batajin mesuke cewa sbd tadanyi nisa da tana waje ne suna ta cikin dakin,tasowa tayi tazo wurin tana kallonsu, babbar macen ce ta kalleta tace "sannu ko yarinya yar uwarkice ko?" "Mama na ce" cewar Idiyatu, "Allah sarki Dan Allah kiyi hkr kinji tsautsayi ne Dan Allah kiyi hkr in Sha Allah zata samu lfy" cewar matar,daga Kai idiyatu tayi wannan mutumin Kuma ya matso kusa yace "kiyi hkr sister wlh ban ganta ba inata sauri" " bakomi" tafada tana share hawayenta.

Kwana2 dayin hatsarin taye tarasu Idiyatu tayi kuka kamar bazata denaba daga baya tayi hkr tabar wa Allah.

Wannan matar da danta ya bige taye da mota su suka dauki idiyatu suka Kai gidansu saboda tausayi suka riqeta.

Yau watan ta biyar taredasu, bayan tabasu labarin karya tace musu batada kowa se mmn ta babanta yadade da rasuwa tun tana karama, tayi aure Shima mijin ya rasu shine gidan da suke haya aka koresu, sbd bakin ciki shine mmn ta ta fito tana kuka shine muhsin yabigeta da mota. Sunan wannan saurayin Daya nige taye da mota muhsin.

Saurayi me kyau yanada rufin asirin sa Dede gwargwado, a cikin watannin nan biyar yasamowa idiyatu gurbin karatu a FCE bayan yasiya mata jarabawar gama secondary, tayi jamb shine yasata a makarnta, suna zaune lfy da ita kamar ta Allah ba abinda tarasa, ahaka tafara son muhsin kullum tana dan nuna masa amma kamar baya ganewa ahaka aka fara batun auren muhsin dawata yar uwarsa me suna zainab, ranarda aka Kai kudin sadakin sa Idiyatu seda tayi zazzabi. Shiko bemasan tanayiba kanwa ya dauketa.

Tasami sabuwar kawarta wadda tayi amakaranta tafada mata damuwarta, kawar me suna zahida tace kifada masa mana maybe ya fahimta.

Da wannan tasamesa ya dawo da daddare yana Shan iska a barandar dakinsa tasamesa Tasha kwalliya, takai masa coffee tahaishesa bayan gaisuwa tai shiru yace "sister akwai abinda kk so ne?" Dama haka yake kiranta, kanta akasa tace "yaya dama..... Dama uhm uhm cewa nai uhm ko zaka iya aurena? Wallahi Allah ya jarabceno d sonka me tsanani narasa yadda zanyi na fada Maka, gashi anata Shirin aurenka da wata".

Kallonta yake sosai kamar meson gano wani Abu a fuskarta, seda tagama ya ce " kiyi hkr sister gsky ni banjin zan iya aurenki, besides ma xainab yar uwa tace, tun tana yarinya aka bani ita, so kiyi hkr Allah yabaki miji nagari, sannan kimaida hankali akan karatunki kinji, kicire wannan maganar aranki Babu ita dan ba abune daze yiwuba".

Idonta cikeda kwallah ta tashi ta ruga aguje tana kuka, tausayi tabashi ya girgiza Kai dan de Allah yagani Bata masa ba, shibama rashin asalinta ya dameshiba aa kawai Bata masa ba.
Chapter 4 · 0% Book details