← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 66

Sashe 61

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ranar addu'ar bakwai d'in Innaro muka samu shiga wajen baba mai kanwa ni da Galadima.
Mun iskeshi shima dai lafiyar sai a hankali, dan yanzu ko fitama bayayi, muka gaidashi cikeda girmamawa, ya amsa mana da fara'a, harda tsokanarmu da cewar, “Sai yau nake ganin ango da amarya?”.
Duk murmushi mukayi cikin jin kunya.
Shima ya kuma murmusawa da fad'in, “Mi kukeson Sani y'ay'ana?”.
Nace, “Baba mai kanwa abinda ALLAH ya baka ikon Sani game damu”.
d'an Murmusawa yakumayi yana gyara zaman hularsa, ya nisa cikin sauke numfashi. Yace, “Da farko dai niba maye bane, bakuma muguba kamar yanda wasu sukasha fad'a tun ina yaro, saidai ina tare da wasu aljanu da bansan ta Yaya suka kasance daniba tun k'uruciya. Tun farkon zuwan kakanninki gidan Malam fharuku aljanun dake tare dani suka sanarmin da dukkan asalinsu, harkuma suka rasu da matsalolin da mahaifiyarku taita fuskanta ga marigayiyya, abinda yasa na barsu ban ta6a maganarba saboda komawarsu a wancan lokacin bashida amfani, ina tausayinsu kuma k'warai da gaske, aljanuna sunsha d'aukata su kaini har cikin masarautar su Ai'sha, kullum cikin bibiyar musu ko ansamu canji nake, amma ba'a daceba har ta samu haihuwarku. Abinda yasa lamarin Galadima ya shigo rayuwaki a labarin shine, Maharbi daya taimaki Badi a jeji ranarda ya bama Auwalu babanki abin d'aukar hoto ne. Ba mutum bane wancan maharbi, aljanine yazo masa a suffar mutane, kuma har Badi yabar wajensa shima bai saniba, wannan aljani shine ya ta6a taimakonka a India lokacinda ciwonka ya tashi ka fad'i a titi, shine kuma ya kwad'aita maka wasu zantuka akan matar dazaka aura, a lokacin shekarun su Hussaina 12 kacal a duniya😊, badan yasan itace matar takaba ya fad'a, saidan maka fatan hakan, dan yata6a sanarmin akwai al'amari mai k'arfi dake tattare da y'an biyun Ai'sha, kuma bisa dalilin abinda akabama Auwal abin yake, sai dai shima baisan mineneba, saidai mujura hukuncin ALLAH. tun daga wannan lokacin wannan aljani ya baza y'an uwansa aljanu suna kula da dukkan motsinka Muhammad Sameer, suma su Hussaina haka itada y'ar uwarta har suka kai adadin shekarun girma. Yafara zuwama Hassana a mafarki, amma saiya fahimci batada k'arfin zuciyar da zata iya shan gwagwarmayar rayuwa dakai, hakanne ya sakashi komawa kan Hussaina, amma ita sai aka dace, wannan shine mafarkin da kuka dingayi keda y'ar uwarki Hussaina, nikuma na cigaba da d'oraki mataki-mataki akan kar6ar Muhammad a matsayin miji, Haidar da kike gani yazo har aka saka ranar aurenku ba mutum baneba, aljanine dagashi har iyayensa da sukazo neman aurenki”.
Ba k'aramar zabura nayiba, hartaso bama Galadima da baba mai kanwa dariya.
“Kinga kwantar da hankalinki, ai ko driver dayay masu Muhammad aiki akan satoki ba mutum bane ba, k'arfin jini da ALLAH yabaki kikaso fahimtar hakan kuma, daga ke har Muhammad kunsha mu'amulla da aljanu a matsayin mutane ai har lokacin da ALLAH ya k'ulla igiyar aurenku, aiko cikar taron d'aurin aurenku akwai d'unbin aljannu da suka Halarta a ciki, dukkan bayanan danai muku yanzu zan baku tabbaci, wani turaren tsinke ya d'aga lamusashshiyar katifarsa ya zaro, ya k'yarsa ashana ya kunna, dandanan hayak'i da k'amshi ya gaurasye d'akin, saiga sallama munji a k'ofar d'aki.
Matashin saurayi ya shigo, Wanda Munaya bazata ta6a mance fuskarsaba, wato Haidar, hakane ya sakata zabura ta mak'alk'ale Galadima.
Haidar yay murmushi kawai yasamu waje ya zauna, saiga kuma dattijo da Galadima yata6a had'uwa dashi a India, shima dai da kallon k'urilla ya bishi, basu fita a mamakiba saiga Driver daya ta6a d'akko Munaya lokacin dayace suyi auren Contract shima ya shigo, saikuma mabanbanta fuskoki Wanda sun had'u dasu a mabanbanta gurare, harda masu zuwama Munaya a k'awaye, saida duk suka zauna suka nutsu sannan suka gaisa da baba mai kanwa, Galadima ma dai a d'arare ya yarda yabasu hannu sukayi musabaha, nikam uwar y'an tsoro ai ina mak'ure a bayansa, ALLAH ma yasoni banzo dasu Abdurraheem ba, suna gidanmu.
Baba mai kanwa ya nuna manasu yana fad'in, “Ina fata duk kun ganesu?”.
Duk muka amsa da eh a d'arare.
Dattijon daya had'u da Galadima a India ne yafara magana a nutse, “Muhammad Sameer ya bayan rabuwa da gwagwarmayar rayuwa?”.
Galadima ya amsa da “Alhmdllh”.
Tsoho mai sihirtaccen k'yawu zam jinin indiawa yace, “ka tuna na fad'a maka matarka Ce fitilarka? zuwa yanzu ka tabbatar?”.
Galadima ya gyara zama yana Murmushi har hak'waransa na bayyana, yace, “Lallai ban mantaba kaka, saidaima nabama wasu labarin, nakuma mik'a godiya ta musamman agareku da fatan ALLAH ya had'amu daku a aljanna, ya kuma biyaku da mafificin alkairi bisaga taimako na mussaman da kuka bama rauwarmu ni da matata, duk da kasancewarmu ba jinsi d'ayaba”.
Gaba d'aya suka amsa da amin, haidar ya nema izinin Galadima domin Neman afuwar Munaya. Galadima ya bashi izini.
Haidar yace, “ki gafarceni bisa ga kalmomi masu zafi dana fad'a a gareki a wancan lokacin, hakan ta farune bisa k'ok'arin janyo hankalin mijinki domin jin tausayinki, kasancewarsa mutum mai tausayi da gudun shigar wani matsala ta dalilinsa”.
Munaya ta murmusa tana kallonsu. Tace, “na yafe maka wlhy, kuma komai yawuce, fatana ALLAH ya tabbatar da addu'ar mijina a garemu baki d'aya”.
A tare aka amsa da amin. Mun dad'e muna tattauna abubuwa da dama, kafin daga bisani sumana sallama su tafi, Wanda bai saniba saiya d'auka da gaske mutanene, baba mai kanwa yay mana doguwar nasiha mai ratsa jiki, wadda harta d'arsa tsoro a ranmu, yakuma ja mana doguwar addu'ar. Galadima ya ajiye masa alkairi mai tsoka mukayi masa sallama muka fito, bamu dad'e a gidanmuba muka koma gida jikinmu a sanyaye da abubuwan da suka faru tsakaninmu da baba mai kanwa da su Haidar.

Kwanaki uku da faruwar haka labarin rasuwar baba mai kanwa ta riskemu, mutuwarnan itama ta girgizamu k'warai da gaske, munkuma jema iyalansa gaisu.
Manyan dake kula da matsalolin gidanmu duk Ubangiji ya d'aukesu, yau babu Innaro babu baba mai kanwa.
Zuwa yanzu kam ko ina su Amaturrahman zuwa sukeyi, sunyi wayo sosai da girma, hakama yaran Munubiya danasu Safara'u datai hak'uri takoma gidan mijinta suke zaune lafiya da kishiyarta da haihuwa yau ko gobe.
Ayusher ta haihu namiji, dan haka muka d'unguma Niger suna k'wanmu da kwarkwata, hardama y'an gidanmu Wanda wanannne zuwansu na farko, sunkuma gano abinda yafi k'arfin shirmensu kuwa, yayinda girman Innarmu yakuma yawaita a zukatansu.
Mun dawo da kwana hud'u Aunty Salamah da Badeerah matar Yaa Fadeel suka sauke, babu nisa tsakaninsu Farhat d'in Nurenma ta juye, Saiga Samha ma ta haife yaranta y'an biyu duk mata, hakama matar Matawalle. Kai wannan abun dad'i da yawa yake, munsha shagulgula sunan kam babu k'arya.
A lokacin ne kuma Galadima yafara k'orafin na yayaye su Abdurrahman wai kona samu nima. Dan gatan da ALLAH yay mana ni da Munubiya muna jerin mata da al'ada ke d'auke musu bayan jinin bik'i har sai sun yaye, amma nasan murzar da Galadima ke min da tuni k'ila ciki na uku na d'auka🤭🤣.
Yanzuma danake kwance a jikinsa dariya kawai nayi. Nace, “su Abdurraheem basu gama yin k'wariba my king, inama laifin sud'anyi 4years haka?”.
Harara ya zubamin da fad'in, “yarinya kinma isa, insha ALLAH gab kike da d'aukar wasu ukun”.
Bance komaiba sai dariya da nayi ina sumbatar goshinsa domin kauda zancen, dan inhar yay zurfi zai zama rigimar da muka sabane kawai, nikuma bana buk'atar hakan.

★★★★★★★★★

Rayuwa ta cigaba da gungurawa dai-dai gwargwadon iko, yau da dad'i gobe babu, soyayya nida mijina ba'a magana.
Shekarun Abie biyu kenan da dawowa cikin ahalinsa, yayinda kunnen kowa na masarautar gagara badau yake a bud'e dan sonjin makomar sarautarsa. Saidai kuma tsit babu wani bayani.
Yay shiri yaje har prison wajensu Harun jikin su Alhaji Mansur yayi sanyi matuk'a, Wanda sukaso ya k'are rayuwarsa tamkar gawane a gabansu, lallai duk saurin Bawa da son nuna k'arfin iko sai ya jira ALLAH, Abie baice dasu komaiba ya juyo ya fito, shiruma maganace ga mai hankali.

A 6angaren mai martaba sunata fafatawa ne shida mama Fulani tun dawowar Abie, yanason tado da maganar sarauta amma mama Fulani ta kasa ta tsare, ta hanashi.
Yayinda gimbiya zulfah keta k'ulunboton asirce-asirce agefe dan kar mulki ya koma wajen Abie, duk da batada wata fawa a masarautar yanzu, saboda tunda wancan abun ya faru mai martaba ya hanata shiga turakarsa, babu kuma wani Abu dayake mata a matsayin matarsa, bai kumace ya saketa ba, dan kowa yasan Sarki a k'asar Hausa baya saki, saidai idan mutuwa ta raba. Da farko tashiga damuwa tamkar tayi nadama, amma dawowar Abie saita kuma birkicewa, musamman da Matawalle yay aure matarsa kuma ta haifi mace, duk zugarta dason 6ata Galadima a wajen y'ay'anta Matawalle baya d'auka, saima yakuma kusantar Galadima suka d'inke waje d'aya, su wambai ne dai ma sai kuma rura k'iyayyarsa suke a ransu, har Momma da Abie haushi sukeji, duk da jansu a jiki da sukeyi a banza, uwarsu da mama Fulani sun rigada sun hure kunnuwansu.
Ganin abin zai kwa6e mai martaba ya shirya taro na manyan masarautar, harda gayyar papi Wanda ayanzu shima lafiya take Neman yimasa k'aranci, saboda girma, dan yanama shirye-shiryen yin murabus ya d'ora mahaifinsu Nuren.
Mama Fulani batasan da wannan taronba ko kad'an, dan mai martaba bai nuna mataba ko da a fuska.
Chapter 61 · 0% Book details