← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 66

Sashe 48

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Galadima ya sakko daga samansa, fuskarsa kawai zaka kalla kafahimci yana tare da damuwa, sanye yake da kayan barci farare sol, wandon yaje har k'waurinsa amma baikai k'asaba, sai k'amshi mai sanyi yakeyi.
Cikin sand'a ya tura k'ofar Momma yad'an lek'a kansa, Munaya kad'ai ya hango zaune abakin gado tana tofama yaran addu'a a tafin hannunsu tana shafa musu a jiki, ya kalli ko ina babu alamar Momma saiya ida shigewa.
Shigowar Mutum kawai Munaya ta gani, tsorata tayi, ta kware baki zatayi ihu yay azamar saka tattausan hannunsa ya toshe bakin, k'amshin turarensa ya sakata fahimtar shine, d'aukarta yay gaba d'ayanta tanata mutsu-mutsu da k'afafu dason yin magana amma babu dama.
Yanufi k'ofa da ita zai fice Momma ta fito daga bayi, daga bayansa kawai yaji ance,
“Sannu shugaban masu iya satar mutane, to saika ajiyeta ai”.
Fad'uwar gaba da kunya dukta lullu6eshi a lokaci d'aya, ya dire Munaya yana susar k'eya saboda kunya, yama kasa kallon Momma d'in.
Itakam bata kuma cewa dashi komaiba tazo ta gabansa ta fita d'akko abu.
Yana ganin Momma ta fita saiya juyo ga Munaya da hanzari. A matuk'ar fusace yay kanta, “K! y'ar rainin hankali ALLAH yau saikin sanarmin minayi miki, inba hakaba a d'akinan zan kwana, bar ganin Momma ta tsaya miki”.
Ja da baya Munaya tayi ganin yana Neman maketa, idonta cike da kwalla tace, “Ai kaima kasani”.
Hannu ya d'aga tamkar zai maketa saikuma ya fasa, ya dunk'ule hannun, “ke wai wace irin mutumce birkitacciya?, ba'a ta6a zama dake lafiyar ALLAH?, kinsan ALLAH wannan karan Abban zan kira Na sanarmawa idanni kin rainani.......”
Cikin kuka munaya ta katseshi, “Dama kasanar masa ai shine ya kamata, kaga shima zaisan tayaya ka aurar masa yarinya, Papi da mai martaba zasusan Neman auren shekara biyu sukaje suka nema kuma suka d'aura.....”
Kansa ya dafe cikin tsantsar takaici, miye kuma nadawo da wannan maganar bayan ta wuce? Kai yarinyarnan y'ar matsalace. Duk a zuciyarsa yake zancen.
Momma da dama duk cikin shirinsune ta fita tai saurin shigowa tana fad'in “Minakeji haka? Waye yayi auren shekara biyu?”.
Duk kasa magana sukayi, munaya Na kuka shiko kunya da nadama dukta rufeshi.
“Waishin bakujini baneba?!”. Momma tayi maganar a tsawace.
“Momma please cool down”.
“Nayi cool down a ina Muh'd, dama abinda ka aikata kenan bamu saniba? Yanzu nan da hankalinka da iliminka Na addini da tarbiyyar da muka baka zakaje kayi auren yarjejeniya da d'iyar mutane? Shekara biyu ta cika kasaketa saboda son zuciya? Wannan d'abi'ar daga ina kuma ka samota? Danba koyarwar addininmu bace balle al'adarmu”.
Jiki a sanyaye Galadima ya zauna a bakin gadon kansa a dafe, itama Momma saita zauna tana kiran Munaya data mak'ure jikin bango tana kuka maiban tausayi. Takowa tayi tazo inda take, saita zauna a k'asa kusada ita.
Momma ta kallesu dukansu, saima suka bata tausayi, Dan takula kowannensu yakamu dason d'an uwansa Na gaskiya, tad'anyi gyaran murya tana fad'in “Muh'd!”.
Kallonta yayi idonsa ya kad'a zuwa jaa kad'an, jijiyoyin kansa da gashin jikinsa duksun mik'e saboda damuwa, sai faman cizar lips yakeyi.
Momma datasan bazaiyi magana ba tunda yahau sama saita cigaba da maganarta, “Muh'd ka fad'amin gaskiya ya akayi ka auri Munaya?”.
Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru yana kallon Munayar da kanta ke a duk'e tana kuka har yanzu.....
“Ba kallonta nace kayiba, amsar tambayata nake buk'ata”.
Zamansa ya gyara a sanyaye yace, “Momma ku gafarceni, dama nasan duk daren dad'ewa wannan ranar saitazo, nasan nayi kuskuren aikata abinda Addinina bai koyar daniba, hakama al'adata idan taji zata k'yamaci hakan, saidai wlhy a wancan lokacin banida za6in daya wuce hakan, ban ta6a tunanin son wataba, damuwar mahaifina da ciwonsane kawai agabana, banta6a kallon mace dawata siga ta soyyayaba balle tunanin aure, dukda fad'a da kukemin akan nayi aure a kullum. Bayan jaridar nan ta fita saina shiga rud'ani da zargin an aikotane dama gareni, wannan daliline yasani tunani sakawa a satomin ita Na ajiyeta harsai ta sanarmin wanene ya sata, amma sai Muftahu ya nunamin Sam hakan ba mafita baneba, dama kawai Na aureta, maganarsa ta sakani d'aukarsa mahaukaci, Dan haka namasa gargad'in karma ya kuma yinta, nidai kawai a d'akkomin ita Na tuhumeta. Shikuma yace Sam bazai bani goyon baya bisaga wannan gangancinba, k'yalesa nayi da nufin zan nemo Wanda zaimin aikin. Saidai kuma Nureddin kawai gareni, shikuma a time d'in yana Italy. Kwatsam sai wani tunani yazomin a zuciya da gamsuwa da shawarar Muftahu, Dan gaskiya yafad'amin, inhar wani yasan tana hannuna duniya zata d'auka abinda yafaru a jaridar nan gaskiyane Na aikata d'in, amma idan aurenta nayi bakin kowa zai mutu, inada kuma ikon sata tayi komai takuma sanarmin Wanda ya sata. Wannan ne dalilin dayasani bincike akanta, har nasamu aka d'akkomin ita Na sanar mata buk'atata. Da farko k'in abincewa tayi, amma daga baya bansan dalilinta Na amincewarba. Wlhy Momma kinji Na rantse ban aureta dannaci zarafinta ba, kuma harga ALLAH banso kutse cikin mutuncintaba, wlhy Muftahu ne ya zuba mana pills a hollandia muka sha, ALLAH kuma ya k'addara zuwan yarannan ta wannan silar, tundaga randa Na aikata mata abinda babushi acikin yarjejeniyarmu nayi nadama, nakuma gane kuskurena, tunkuma a lokacin nafara tausayinta, tsakanina da ALLAH badan Na amfanu da itaba Na aureta, saidai nasan koda fad'a mata nayi bazata aminceba, zata d'auka bisa wancan dalilinne nace ina sonta, amma nasha nuna mata inason nata, saita dunga sharewa, bansaniba ta fahimcenine kokuwa bata fahimtaba, wlhy Momma tsakanina da ALLAH nakeso Munaya, kuma nayi nadamar aikata abinda Na aikata, na tabbatar bazanma ALLAH wayoba, ikonsane ya aikata yanda yaso a lokacin dayaso d'in”.
Momma tayi murmushinsu na manya tana kallon Munaya, “Na fahimceka Muh'd, amma adalci d'aya zan maka bisaga wannan gangancin naka, adalcin kuwa shine ka saki Munaya a warware auren Contract, saika koma ka kuma Neman aurenta na gaskiya ga iyayenta, ka kuma sanar musu mika aikata musu a farko, kanemi afuwarsu, shima takawa da mai martaba kaje ka sanar musu abinda ka aikata, nikuma namaka alk'awarin zan tsaya maka wajen ganin dawowar Munaya gareka”.
Kasak'e yay yana kallon Momma da wannan tsarin nata, toshi mahaukacine dazaiyi wannan gangancin? Ai kowane irin hukunci zai d'auka amma banda na saki wlhy.
“wai kobaka jini bane?”. Momma ta katse masa tunani.
Narke mata fuska yayi tamkar zaiyi kuka, “Haba Momma Dan ALLAH, yanzunan dakanki kike fad'ar haka? Nidai kimin dukkan hukunci dakikeso amma wlhy banda na saki, bazan iya aikata wannan gangancinba, nayi kuskuren farko amma na biyu kam yana dai-dai daku rasani baki d'aya, wlhy inason matata ina k'aunarta har cikin raina, ni na amince zanje nasami su Abba da papi na sanar musu, nakuma nemi afuwarsu amma banda maganar saki please ”.
Shiru Momma tayi tak'i tanka masa, saikuma yabama Munaya tausayi, ita dama burinta ya amince yayi kuskurenne.
Haka yaytama Momma magiya amma tak'i tanka masa, shikuma ya nace.
Saida Momma ta tabbatar yayi ligif sannan tace, “To ga adalci na biyu tunda ka nace, idan Munaya ta amince ni banida matsala ai, nabaka minti goma kacal zanje na dawo”.
Tashi Momma tayi ta fita tana gumtse dariya, saida ta fita tayita sosai, dama akwai randa Muh'd d'inta zai risina irin haka akan mace, Muh'd dazai aikata laifi bada hak'uri ya gagaresa koma yafi Wanda yayma laifin zuciya da fusata, itakam babu abinda zatace da ALLAH sai godiya, Munaya tagama mata komai data zama sanadin canjawar yaronta mai masifar tauri da tsauri.
Chapter 48 · 0% Book details