← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 66

Sashe 20

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muftahu ya bud'e abinda ya siyo yana fad'in “Ranka ya dad'e mizakaci?”.
Cikin d'an ta6e baki ya girgiza masa kai alamar bazaici komaiba.
“Okay, to bara na kira Gimbiya meybe ita ta saka kaci”.
Bud'e ido yayi yana zubama Muftahu harara, shikuma ya fuske tamkar bai ganiba.
Saida Muftahu yasha fama kafin Galadima ya yarda yad'anci abinci, rabima duk fura da kayan itatuwan ne yasha. Sunkai 1hour da shigowa ya buk'aci ganin Harun da SD.
Sun fara shiga d'akin da harun yake, bayan Muftahu ya saka key ya bud'e matsawa yay yabama Galadima hanya yafara shiga, takun takalmansa ya saka Harun dake zaune bakin gadon d'akin kansa a duk'e d'agowa, kallon ido cikin ido sukaima juna, Galadima ya janye nasa cike da basarwa yana wani miskilin murmushi mai k'ona zuciyar mak'iyi.
Harun ma janye idanunsa yayi yanajan tsaki, Muftahu kuma ya ta6e baki yana gyarama Galadima kujerar zama.
Galadima ya zauna idonsa akan harun, hannunsa ya mik'a ya kar6i lap-top d'insa dake wajen Muftahu, ya d'orata bisa cinya sannan ya janye idonsa ga harun dayak'i sake kallonsa, lap-top d'in yafara dannawa cikeda kwarewa, cikin seconds dabasufi 10 ba ya d'ora lap-top d'in saman stool d'in da Muftahu ya sake ajiyewa, sannan yay playing abinda ya kunna yana hard'e hannaye a k'irji da zubama Harun ido.
Harun har yayi tamkar zai share sai dai ya kalla lap-top d'in, Wato shine a ranar sunan y'an uku gab da za'a sace yaran shida d'aya daga cikin kidnapers d'in.
“Bibo inaso Ku tabbatar da kun kwashe yaran, karku kar6i wad'anda suke hannun k'annen matarsa, Dan na bogine, baby dolls ne aka sakama kaya irin na yaran domin kauda hankali, Sameer yanada wayo fiye da yanda kuke tsammani, Dan haka kuyi komai cikin kulawa da taka tsantsan, dai-dai lokacin da wutar hotel d'innan zata d'auke, zan kwashe yaran insha ALLAH, harsai nabar cikin hotel d'in ni da ku sannan za'a kunna, ina fata ka fahimta”.
“Eh na fahimta ranka ya dad'e, namaka alk'awarin ko y'ay'an sarkine bana Galadima ba yau saisun kwana a alahira”.
“No, banason su mutu yanzu, sai shi ubansu ya d'and'ana d'acin rashinsu, yana gab da mutuwa sai a kawo masa gawarsu, daganan shima kaga ai sai tafiya shida wannan tatsitsiyar matar tasa y'ar bayi”.
“Okey nagane boss”.
Mamaki ya kama Harun har Muftahu. Zuciyar Harun tamkar zata fad'o waje dan mamaki, ya akai Galadima ya d'auki wannan video d'in, bayan dukkan CCTV cameras d'in dake hotel d'in saida suka saye mai kula dasu na hotel d'in aka tsayar dasu daga aiki........
Murmushin da galadima yayine ya katse tunanin Harun , cikin lumshe idanu da kad'a kai ya gyara zamansa, cikeda izza yace, “Abin mamaki ko? haka nake ni dama, kullum cikin bada mamaki, tabbas 6oyen dakai masa bazai yuwu muganiba, saidai kamanta da koda ace banida hanyar ganin naka idan ubangiji bai k'addaro ruhi na kona y'ay'ana ko matata zai salwanta a hannunka ba babu yanda ka iya, kana tunanin duhu da tsayar da cctv d'in hotel d'in zai baka dukkan dama ko? To kayi kuskure dan Muhammad Sameer kansa cctv ne, eyeglasses d'in dake idona komai duhun waje shi zai haskokane, dan camera d'in jikinsa tana tareda komai, kasan miyasa nabaka damar d'aukar yaran? Saboda hakan yana cikin k'addararsu, nakuma barka dasune danna kafa maka tarkon neman hujja da tabbatar da abinda Muftahu ya sanarmin”.
Muftahu ya d'age gira saboda kallon tsana da Harun ke masa.
Murmushi Galadima ya kumayi yana cigaba da fad'in “ka kira matata tatsitsiyar yarinya y'ar bayi ko? Saikuma abin mamaki ita wannan y'ar bayin, tatsitsiyar ce ta zame maka RAINA KAMA, dan lallai gashi zakaga GAYYA. itace ta haskomin kai a cikin madubin fik'irarta tunkan Muftahu ya sanarmin, takuma koyamin yanda zan fahimci makircinka da nagartar Muftahu, tabbas na yaba ma basirarka Harun, kanada basira k'warai da gaske, tunda kasan kanka kake a jikina kana cin dunduniyata, ni matsayin aboki d'an uwa mafi kusanci nake kallonka, kamar yanda mahaifina yarink'a kallon mahaifinka, ashe kud'in duk kaskane a garemu, nayi imani da cewar lallai ku jarabawane a garemu, kamar yanda k'addarar auren Munaya tazamema rayuwata alkairi, a kullum cikin aibanta Muftahu da bak'antashi kake a gareni, ashe kaine bak'in ba shiba, mimuka muku ni da mahaifinane haka da zafi? Nawa suka biyaku kuke cutar damu.............?”.

“Sameer!!”. Harun ya kirayi sunan galadima cikin fushi, ya mik'e tsaye sunama juna kallon ido cikin ido shida galadima, cikin matsannan ciyar tsanar juna.
“Kabar alfahari magen matarka tamaka bajinta, shawarama zan baka ka janyeta cikin wannan hargitsin, danko ubanta daya shiga a had'ari yake balle ita karan kad'a miya, wlhy Sameer ban ta6a k'aunarka ba, bakuma zan ta6aba har abadan, domin tsakanina dakai BASHIN GABANE, dan haka banida lokacinka yanzu har sai Camera ta dawo hannunmu, bar ganina anan a rufe, akwai mai sarrafa dukkan tunanina a waje, yarage naka kanemi hanyar kare Surukinka kafin aikinmu yazo kansa...”.
A fusace Galadima ya mik'e shima yana dunk'ule hannu, amma sai Nuren daya shigo yanzu ya rik'eshi, “relax my brother, kainefa ka ta6a fad'amin ba'a maidama abokin gaba murtani da murtani, sannan ba'a bashi damar sanin sirrin yak'i sai an had'u a filin daga”.
Galadima ya saki hannunsa daya dunk'ule da bakinsa daya cije, yatsunsa ya kad'a suka bad'a k'ara d'as! 'Das! Sannan ya zagaya hannunsa a wuya alamar I will kill you.
Cikin d'aga murya Harun yace, “d'an halak ka fasa Sameer!”.
Daga Nuren har Muftahu da Galadima babu Wanda ya amsa masa, a falo suka tsaya, Galadima ya Nufi d'akin da SD yake batare da yace uffanba,
Nanma dai Muftahu ya bud'e masa, ya shiga cikin tsananin fusatar da Harun ya sakashi. zauna suka iske Alhaji Darma cikin kujera yana duba jarida, kaikace a d'akinsa yake.
Galadima ya taune lips nashi tamkar zai hudasu da hak'ori, zuciyarsa Na k'una, lallai sai Harun da ubansa sun k'are rayuwarsu a jail inhar yana numfashi, dan barin irinsu a duniya had'arine babba, musamman a gida irinna sarauta.........
Nuren ya katse masa tunani ta hanyar yima SD magana.
cikin ta6e baki Alhhaji Darma ya kalli Galadima yana wani murmushin mugunta, ya ajiye jaridar hannunsa tare da hard'e k'afa.
A bakin gadon Galadima ya zauna, ya kalli Alhaji Darma, sosai Darma ya tsorata da rinannun idanun Galadima, amma saiya dake.
Galadima daya lura da rikitar Darma ya murmusa, cikeda k'asaita ya d'age girarsa, “Alhaji Shehu kenan, angaya maka mutum yakanci bashi ya kwana lafiya, duk wata jarumta da zaka aro kasama ranka tuni nagama bitar karatu a kanta, karigada ka shigo ramin damusa iya gudunka babu wajen 6uya, bama duk wannan ba, minene had'inka da surukina? Sanann minene yasa kuka kashe mijin y'ar uwata? Dan ko tantama banayi da hannunka a cikin kisanshi!!”. Galadima ya k'are maganar cikin matsanancin tsawar data rikita Alhaji Darma.
Dukya rud'e yarasa ina zai kama, cikin in ina yace, “Ni sharri zakaimin bansan komai akan mutuwarsa ba”.
Galadima yay dariya, saikuma ya gimtse fuska. Yace, “Okay, babu hannunka amma kake tursasa yarinyarsa Samha ta dinga d'akko maka sirrikana tana kawo mata? Kullum kana ma yarinya barazana da mutuwa ko? Alhaji shehu aini tun ranarda mijin aunty Mimi zai koma ga ALLAH naga idonsa ya tsaya cak akanka lokacin da numfashinsa ke bankwana da duniya na d'ora alamar tambaya a kanka, sai kuma yanda kake kaffa-kaffa da Samha a gaban mutane, yayinda itakuma take a d'arare dakai, dukkan wayar dakake mata kana sakata sato maka sirrina INA kan sani, dan nine da kaina nake ajiye mata tagani danta tura maka batareda ita kanta ta saniba, shiyyasa na jata jikina fiye da kowa a gidanmu, duk abinda Sameer zaiyi cikin ilimi yakeyinsa Darma, koda yake bamuzo wannan matakinba, miye had'inka da surikina?”.
Alhaji Darma dake a rikice saboda tsoro da tashin hankalin zantukan Galadima ya had'iye yawu da k'yar yana fad'in, “B..babu ruwanka da abinda ke tsakanina dashi kuma”.
“Hummm". Galadima ya fad'a cikin cije lips, wayarsa ya d'akko ya kunna wani recording daya nad'a a wayar Darma ranar da suka kamoshi kafin su d'akkoshi.
Waya yake da wani cikin tsananin fusata, “Boss wai miyasa bazamu aika shegenan barzahu ba idan yak'i bamu Camera d'innan? Tunda munada hanyar da zamubi mu kar6a d'in, Nibansan miyasa kuke cewa abishi mataki-mataki ba, kasanfa y'arshi yaronan Sameer take aure, yanada hanya mai sauk'i dazai bashi camera d'innan, shi wancan banzan Alhaji Halluru babu tsiyar da y'ay'ansa zasuma mutane, kullum sai tsarin banza yake mana”.
“Karka damu Alhaji shehu, mu bashi damar k'arshe daya buk'ata, tunda ya tabbatar mana a wannan karon zai kar6o camera d'in ta hanyar matan y'ay'ansa, yana son takara, yakuma San inhar burinmu bai cigaba shida takarar Governor saidai kallo”.
“shikenan boss, bara naje ance nayi bak'o”.
“Ok ngd”.

Galadima ya gimtse recording d'in dai-dai nan yana murmushi da kallon Alhaji Darma dake tsuma dukan jikinsa na 6ari.
Cikin d'age gira Galadima yace, “wannan ma ba matsalata bace? Kasanfa shikad'ai ya isheni hujjar gurfanar dakai gaban K'uliya, shikenan babu girma babu mulkin da ake mana Homa da tak'ama dashi right? ”.
Mi Nuren zaiyi kuwa inba Bushewa da dariya ba, dan yatuna Alhaji Shehu ne yafad'ama Galadima maganarnan randa suka kamoshi.
Cikin Fusata Darma yake kallon Muftahu da Nuren dake dariya, ya mik'e tsaye yana nunasu da yatsa, “y'an samari lokacin dariyarku baiyiba, dan camera d'in da kuke farfagandar nema tana gab da zuwa hannunmu, kunga kuwa ai kune abin dariya”. Ya k'are maganar da kwashewa da dariya.
Dukda furucinsa ya daki zuciyar Galadima bai nunaba, saiya mik'e yana murmushi da kallon Darma. Yace, “lallai kaine ka cancanci ayima dariya, indai camera ce tadad'e da zuwa hannuna”.
Yana gama fad'a ya fice, su Nuren suka kuma sanya dariya, dukda yanayin Galadima ya tabbatar musu akwai matsala. Sunama Alhaji Darma dariya suka fice abinsu daga d'akin.
Chapter 20 · 0% Book details