Sashe 55
Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun d'azun yake tsaye akanta amma bata saniba, ta Lula duniyar tunani mai zurfi, ga Abdurrahman dake gefenta yanata mutsu-mutsu da k'ananun kuka amma batama jishiba.
Agabanta yay wani durk'uso mai birgewa, yakai fuskarsa daf da tata yana hura mata iska a saman ido zuwa hanci.
Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke tareda dawowa hayyacina cikin zabura, yay azamar damk'e hannuna da fad'in “My Mata!?”.
Ajiyar zuciya na sauke tareda dai-daita dan fahimtar shine, na zuba masa idanu cikin mamaki nace, “Yaushe ka shigo?”.
Murmusawa yayi sannan yamik'e daga durk'uson dayay agabana, batareda ya bani amsaba ya fara k'ok'arin cire farar rigar suit d'insa. Mik'ewa nayi na taimaka masa, sannan nadawo gabansa na warware tia.. 'Din da bottoms d'in pink d'in rigarsa ta ciki. Sai wani faman lumshe idanu yake da bud'esu akaina, bansan miyake tunaniba.
Ina cire bottom d'in k'arshe na rigar ya rik'e hannuna, idanu na d'ago na kallesa, ya sakarmin wani k'asaitaccen murmushi yana matsoni jikinsa sosai, a saman la66a ya furta “Kinyi k'yau sosai, amma mikike tunani haka?”.
Da mamaki na kalli kaina, sanye nake doguwar rigar shadda milk color, anmata simple aiki da brown d'in zare, an k'awatashi da stones, Wanda sune suka fidda ainahin k'yawun d'inkin, sai siririyar sark'a data kwanta a wuyana d'as, nayi d'aurin Maryam babangida daya kuma fidda ainahin suffata ta bahaushiyar asali mai rik'o da al'ada. Yanda nake bin jikina da kallo haka Galadima kebi shima da idanunsa, na maida kallona ga face d'inshi dake kadaran kadahan, bai d'aureba kuma babu walwala sosai tare dashi.
Gira d'aya ya d'agemin sai kuma yad'an ta6e baki yanajan hancina da had'e yatsunsa biyu na k'arshe👌🏻alamar komai yaji.
Nad'an murmusa ina k'ok'arin barin wajen dan naga alamar miskilawan suna kusa.
Ruwa naje na had'a masa, na fito ina goge hannuna da towel.
Durk'ushe na iskeshi gaban Abdurraheem da cup d'in ruwan dana ajiye danshi a hannunsa. Ya d'ago yana kallona dad'an murmushi a face d'insa, “kinsan minake gani a jikin Abdurraheem kuwa?”.
Kaina na girgiza masa alamar a'a.
Kallonsa ya maida ga yaran yana cigaba da murmushinsa. Yace, “Kamannin Abie”.
Takowa nayi Inda suke Nima Ina murmushi mai sauti da fad'in, “Nadad'e da wannan tunanin a raina, saidai nabarma zuciyatane har sai randa zan gansu a waje d'aya, Ashe kaima kana lura?”.
Wata y'ar dariya yayi, wadda tafi kud'i tsada awajensa. Yace, “My Heartbeat ALLAH kin iya haihuwa”.
Ba k'aramar dariya maganarsa tabaniba, aiko nashiga k'yalk'yalawa. Shiko ya shagala da kallonta saboda birgeshi da dariyar tata tayi, burinsa dama yaganta cikin farinciki.
Bayan na tsagaita da dariyar na kallesa Ina d'aga kai da kashe masa ido alamar kallonfa?.
Mik'ewa yay tsaye ya dawo inda nake tareda rank'wafowa kaina yana dafa hannayensa biyu asaman gadon gefe da gefena. Kusancin namu yasakani d'anyin baya kad'an ina kallon cikin idonsa, yakuma matsowa, na matsa, yakuma again, Nina still na matsa, saida na haye gadon sosai shima yay balance yanda yake buk'ata sannan ya kwanto gefena kusan Rabin jikinsa a nawa, har lokacin idonsa na sark'e da nawa. Galadima yay bala'in Sanin sirrin kallo, inhar ya sark'e idanunsa da nawa duk wani hope d'ina nemansa nakeyi na rasa, yatsansa kawai naji saman la66ana yana zagayawa ahankali, santsin hannunsa Dana lips gloss d'in Dana sanya sunayin kamar susa, kasa jurewa nayi na lumshe idanuna a hankali.
Galadima ya murmusa da bud'e baki da k'yar yana fad'in, “Kin cancanta, kin cancanta zama matar Muhammad Sameer Munaya, ked'inki da dukkan halayyarki irinta Muhammad Sameer ke buk'ata ga matarsa, ko ayarda ko kar ayarda nasan nama sauran maza zarra, dan matata tafi ta kowa, kinzama fitila mai hake gabana da bayana, kinzamarmin bango abin jingina lokacin danawa yanemi rushewa, shigowarki rayuwata na dai-dai da farkawata daga nannauyan barci mai cikeda rud'ani, nabaki dukkan zuciyata ki jani a sannu danna cigaba da ribantuwa da ni'imomin da ALLAH ya azurtaki dasu, I love you so much Munaya, I love you har a aljanna matsayin uwargidan matana”.
Bansan lokacinda hawayen farinciki suka fara zirarominba, na bud'e idanuna dakai hannu saman kwantaccen sajensa ina shafawa a hankali, cikin wani yanayi nace, “Ka cancanci fiye da haka mijina, dan kanada zinariyar zuciya, kaimai tarin tsoron ALLAH ne dabin dokokinsa, a wannan zamanin samin matashin saurayi mai kud'ad'e da mulki a hannunsa dabaya wata masha'a abune mai wahala, baka kasance mazinaci ba, baka kasance mai shaye-shaye ba, ko sigari wannan bakasha, kulum cikin Neman halalinka kake Dason k'yautatama iyayenka dana k'asa da kai, kaimai ibadane, salla bata wuceka, mai yawan tsayuwar dare, mai yawan bitar littafi mai girma dake d'auke da zancen ALLAH ne, mai yawan sadaka da taimakon mutanen da bakuma had'a addiniba, bakada wata majalissa ta abokai daza'ace gaka cikin jerin masu cin naman wani ko zind'en wani, abinda ke gabanka da Wanda ALLAH ya halatta maka kawai kakeyi, mijina tayaya bazaka samu nasaroriba a rayuwarka? Ubangiji mai ni'imane ga dukkan Wanda ya ra6u samun ni'imar, babu wani Bawa dazai tsinci kansa a ta6ewa inhar yabi dokokin Ubangiji da koyi da manzon tsira, babu cuta mafi rad'ad'i da ciwo kamar bijirema Umarnin ALLAH Wanda ayanzu shike wahal da matasan duniya irinka, burunsu kawai su hole su mori k'uruciyarsu, sun manta babu tagomashi mafi k'yak'yk'yawan farashi irin morar k'uruciya bisa ga Umarnin ALLAH, yadda da k'addara, samu ko rashi, tsayawa matsayin da ALLAH ya ajiyeka, kaucema dukkan wata bad'ala, matasa sune k'ashin bayan al'umma, lalacewarmu ta saka al'ummar tafiya a karkace a halin yanzu, da'ace zamu gyara da kowa ya mik'e, dolene Momma da Abie suyi alfaharin samun d'a irinka, dolene Aunty Mimi da Yaa Sauban suyi alfaharin samun d'an uwa irinka, dolene su Samha dasu Amaturrahman suyi alfaharin samun Uba irinka, dolene k'asarka da addininka yayi alfaharin samunka, saidai duk nice nafisu sa'a da alfaharin samunka a matsayin miji uban y'ay'ana, inaji inama y'ay'yana su gaji k'yawawan hallaya da d'abi'u irinna mahaifinsu, saidai kash ina cike da fargabar tsoron kalmarnan ta bahaushe dakance *Bakowanne tauntsu bane ke raira kukan gidansu* wani tun a koyan tashi yake canja salo. Mijina ka more, ka matuk'ar morewa da k'yawawan hallaya, irinku kunada tsadar samu a cikin al'umma, da mutane zasu gane dasun fuskanci ba k'yawun fuska dana jiki bane abin alfahari, zinariyar zuciya da hallaya shine abin alfahari da d'agawa, saidai kash, burin samarin yanzu da y'ammata k'yawun fuska dana halitta, nauyin aljihun wayewa, basa tunanin mika tara mizaka taras, sannan mika barma bayanka da ahalinka Wanda ko bayan shekaru aru-aru tarihi bai Isa mantawa da kai ba, da inada dama sainabi matasan mata da maza dukna musu allura sunzama kamarka mijina, inasonka, ina sonka, zan fad'a a hankali, nafad'a da k'arfi, na fad'a da kuwwa, na fad'a da ihu agaban kowa kuma, Kaine duniyar Munaya, Kaine farincikin Munaya, zanta k'aunarka har randa nufashina zaibar gangar jikina, nakumayi fatan ganina a cikin matanka dake aljanna Muhammad Sameer”.
Kasa magana Galadima yayi, sai bakinsa ke motsi alamar buk'ar firta wani Abu amma yakasa, idonsa yacika taf da kwalla, lallai hikimar zancema baiwace ga mace tagari, dashi kawai zata iya mallakar mijita babu boka babu Malam, dan gashi Munaya tasamu dukkan nasarori, ya rungumeni tsam a jikinsa tareda d'ora bakinsa saman la66ana, hawayen dayake rik'ewa suka gangaro saman fuskata. Banyi yunk'urin ko motsawa ba nabashi wuk'a da nama yayi yanda yakeso ni halalinsace..........😘👍🏻
*_Hummmm, lallai matar kwarai rabin addini, ya ALLAH kabamu damar zama matan kwarai ga mazajenmu😢🙏🏼_*.
*******
Bayan shud'ewar wani lokaci muka dawo daga duniyar da muka tafi, kunya duk sai ta kamani, nakasa had'a ido dashi.
Galadima ya murmusa yana kama hannuna zuwa hanyar bayi, banida za6in daya wuce na bisa kawai. Yauma dai tare mukayi wankan, nad'an sake dashi fiyeda d'azun da safe. Muka fito na taimaka masa da shafa mai, yasaka kaya marasa nauyi. Nima da taimakonsa na kimtsa sannan na sauka nemo masa abinda zaici dukda magrib ta gabato. Babu kowa a falon sai Khaleel dake homework. Sannu namasa shikuma ya gaisheni, nace, “Ina Samha my boy?”.
Yace, “Aunty yanzu aunty Dhibiya tazo suka fita”.
Agogon falon na kalla da mamakin fita a yanzun? Halan batasan Uncle d'inta ya dawoba?.
Bance komaiba na wuce kitchen.
Da taimakon kuku na shirya masa Abu mara nauyi, na had'o saman tire ina fitowa. Samha data shigo tad'an kalleni a firgice, nima kallon mamaki nake mata da tuhuma.
Nace, “Daga ina haka?”.
Kame-kame tafara na lalubo amsar dazata bani, wadda alamunta ke nuna k'aryace kawai zata fad'a.
Girgiza kai nayi kawai nai gaba abina ina fad'in “Zanso sanin mike tsakaninki da Dhibya Samha? wannan abotar taku k'arfinta yafara tsoratani”.
Banjira amsarta ba na haye saman benen.
Gudun karya fahimci wani Abu na daidaita kaina tunkan na shiga, nasan inhar yasan raina ya6aci akan Samha ne sai taci k'aniyarta, nikam ba buk'atata ba kenan, nafison sanin tsakaninsu da k'awartata kafin na rabasu.
Tsaye na iskeshi rik'e da abin salla, na ajiye tiren saman table d'in gaban sofa sannan na kalli agogo. Yanda banyi magana ba shima baiyiba, na nufi bayi nayo alwala nima, tsaye na kuma iskeshi yana jirana.
Bayan mun idar da sallah na kallesa ina fad'in “Abinci yalla6ai”.
Harara ya zubamin da rankwashi, na dafe wajen ina kwa6e fuska zanyi kuka.
Yace, “Yalla6ai d'inan bazai bar bakinkiba ko?”.
Dariya namasa da gwalo inaja baya, “Yo ba sunanka baneba”.
“Da kika rad'amin ko? Zan kamakine ai”.
Sanin halinsa yasani fad'in, “Toyi hak'uri bazan sakeba”.
“Harkin karaya kenan?”.
“Ba doleba, kamun nakane ai bamai sauk'iba”.
Dariya sosai tabashi, amma ya had'iye abunsa kawai yayi murmushi yana cizar lips.
Munaya tace, “Wato a rayuwa duk d'an Adam zaka sameshi dawata d'abi'a data zame masa jiki”.
Kallona yayi da alamar tambaya, amma baice komaiba.
Mik'ewa nayi tsaye ina cire hijjab da fad'in, “Cizon lips yazama maka jiki, harya zama d'abi'ar dake yawan birgeni agareka”.
Lips d'in nasa ya ciza sannan ya saki wani k'asaitaccen murmushi da girgiza kai, Munaya kenan sarkin k'uruciya. Yafad'a a zuciyarsa yana mik'ewa shima.