← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 66

Sashe 37

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

.................Kusan mintuna 7 da fitar Nurses d'in doctor yay Knocking, Galadima ya amsa ba tare da ya ajiye wayarba, doctor ya shigo abinsa, Nurse d'aya da sukai akin d'azun Na biye dashi.
Galadima ya d'ago yana kallonsu fuska babu walwala, Dan shifa yafara gajiya da wannan shigi da ficin, amma baice komaiba.
Doctor daya d'an tsargu yace, “Afuwan ranka ya dad'e, dama ina ganin yakamata tafara cin abincine, Dan ruwan da muke saka matane dama yake taimaka mata, to yanzu kuma zata fara shan magunguna insha ALLAH”.
Galadima yad'an sauke numfashi yana fad'in “ok, to amma yaranfa? za'a iya kawosu yanzu?”.
“eh to, sunkai nawa?”.
Yatsu uku Galadima ya d'agama doctor, dukda yayi mamaki saiya danne abinsa, musamman dayaga munayar y'ar k'arama da ita. yace, “Ranka ya dad'e dadai and'an k'ara mana lokaci koda kwana biyune, har yanzu zancen danake maka ba'ason abinda zai cika mata hayaniya a kai”.
Jinjina kai Galadima yayi kawai, alamar gamsuwa.
Daganan Doctor yay d'an dube-dubensa ya bama Galadima Drugs d'in Munayar akan Nurse zata dinga zuwa tana bata kullum.
Doctor Na fita shima ya ajiye wayarsa kusa da ita ya fito, d'akin da Nuren yake ya shiga, yana zaune Aunty Mimi Na bashi abinci a baki, Galadima yad'an hararesa yana fad'in “k'aton banza kacika shagwa6a”.
“Uhmyim” Nuren ya fad'a yana ta6e baki da rama Harar da Galadima ya masa.
Ita dai aunty Mimi murmushi kawai take da wannan rigima tasu dabata k'arewa, dama can inhar Nuren da Galadima Na waje sai kayi dariya, Dan kafin su rabu sai anyi kusan fad'a goma.
Galadima yace, “Ya jikin?”.
“Aini kam Alhmdllh, yanzu kawai maganar gaskiya amin aure, inda Na mutufa shikenan, kukan kwana uku zakuyi a wuce wajen, amma in mat......”
Hannu Galadima yakai zai bige bakinsa, yay saurin duk'ewa, Aunty Mimi ta sanya dariya, Galadima kuwa kwafa yay yana kallon Aunty Mimi, “oh ALLAH, maimakon kimasa fad'a dariyama kike masa? Wannan yaron wlhy fitsararrene, idan kunk'i masa aurenan zai iya zuwa yayi baku saniba ma”.
Nuren ya gyara zama yana hararsa, “Yo angaya maka ni irinkane, soyyaya Na cin zuciyata k'asaita ta hanani fad'e, Malam mufa dama munsan komai, munzuba idone muga yanda wasan zai k'are”.
Murmushin da Galadima bai niyyar yibane ya su6uce masa, ya mik'e da fad'in, “Duk iskancin da kamin ninaso, tunda nine nazo dubaka, idan nakuma zuwa d'akinnan kace ba sunanka Nureddin ba”.
“Ahaf, yo dama sunana Sameer ne?”.
Galadima bai kulashiba, ya kalli aunty Mimi daketa musu dariya, “Auntyna yakamata a sanarma gidansu ta farka, naga har yanzu babu Wanda ya iso”.
Murmushi Aunty Mimi ta masa, ta ajiye plate d'in datake bama Nuren Abinci tana cewa, “babu damuwa, mu barsu har zuwa yammar, tunda kaga har yau basu bada damar a shigaba”.
“Ok, hakan yayi”.
Harzai fice aunty Mimi tai saurin cewa “Abincinfa?”.
Kansa ya girgiza mata yay ficewarsa.

Nuren dake murmushi ya kalli Aunty Mimi yana fad'in “Auntynmu soyayya nacin Guy d'inan yak'i fahimta”.
Dariya tayi “Nuren kenan, ingaya maka sarai yasan yana sonta, shegen son girma da miskilancine kecinsa, amma ai naga alamar yanzu an wuce wajan”.
“A haba? Aunty da gaske?”.
“kwarai ma kuwa Nureddin”.
Hannu yabata suka tafa, yanajin wani sanyi a ransa, da sakama Muftahu albarka a zuciyarsa, danya zama aboki kuma d'an uwa Na k'warai.

Fitowar Galadima yaci karo dasu Yassar, ya fad'ad'a murmushinsa, shima yaran sun shiga ransa sosai, k'arasowa sukai gareshi, cikin girmamawa duk suka gaisheshi, ya amsa da kulawa.
“ku bakwa gajiya da yawo?”.
Soshe-soshen kunya suka farayi, Marcel yace, “ai daga gida muke, munzo muk'ara ganin jikin Aunty da Uncle ne”.
Galadima yad'an murmusa yana tura hannayensa duka a aljihu, cikin d'an lumshe ido yace, “kushiga to kugansa”.
“Uncle! Auntynfa? Ta farka itama?”. ‘Ahakam ne mai maganar’
Galadima ya jinjina kai. Yace, “ta farka Ahakam, amma tana barcine”.
Gaba d'ayansu farin cikine ya bayyana a fuskokinsu, kai kace y'ar uwarsuce ta jini, da wannan farin cikin suka shiga d'akin da Nuren yake, shikuma yakoma inda Munaya take murmushi d'auke a fuskarsa.

Dad'an hanzarinsa ya k'arasa gareta, ganin ta farka, zama yay a kujerar suna kallon juna, murya a sanyaye yace, “Kin tashi?”.
Da idanu ta amsashi.
Ya shafa kanta yana fad'in “Sannu, yanzu ina ke miki ciwo?”.
Fuska ta d'an yatsine, ta nuna masa hannunta da kanta.
Cikin tausayawa Yakuma mata sorry, sannan yace, “mizaki ci?”.
Kanta ta girgiza masa alamar babu komai.
Ya d'an 6ata fuska yana fad'in “Ban yarda ba, kinga kuwa yanda kika rame?”.
Murmusawa tayi, itama ta masa alamar wai ya rame shima.
Baki yad'an ta6e, amma baice komaiba ya d'auka wayarsa dake kusa da ita yay kiran Muftahu akan abinda za'a kawoma Munayar kozata d'anci.
Itadai kallonsa kawai takeyi. Ya yanke wayar yana kallonta shima da d'age mata gira d'aya alamar kallonfa?.
Dukda taji kunya saita yamutse fuska irin miye abin kallon anan.
Galadima yay wani miskilin murmushi cikin murya k'asa-k'asa yace, “Really?”.
Ta lumshe idonta alamun tabbabatarwa.
“zaki maimaitamin idan kin warke yarinya”. Yay maganar da wata siga harda cije lips.
Munaya ta kauda idonta tamkarma bata fahimci ina ya dosa ba.

A ranardai haka kowa ya yini cikin farincikin farfad'owar Munaya, gashi anbarsun sunshi sun gagganta, saidai anata musu gargad'in banda hayaniya, tausayin ta duk ya kamasu. Innaro harda hawayenta, aka saka bakin Zane ana sharewa da jemasu Alhaji balala ALLAH ya isa, harda cewa sai an koma kotu an sake sabuwar shari'a an kar6oma jikarta hak'inta.
Shi Galadima ma abin dariya ya bashi matuk'a, yadai had'iye yana duk'ar da kai baiyiba, wannan tsohuwa akwai abin dariya wlhy.
Munubiya kam rungumeta tayi taita hawaye, itama Munayar nayin nata.

★★★★★★***★★★★★★

Bayan kwana hud'u da farfad'owar Munaya jikinta yayi k'yau Alhmdllh, Dan tana samun kulawa ta kowanne 6angare, ciwukan jikinta ne kawai basu gama warkewaba.
Aunty Mimi da Laraba na a d'akin, Dan kowa ya tafi, suna zaune d'auke da su Abdurraheem da ake kawowa su yini yanzu, sai dare a koma dasu.
Munaya tana zaune ne a gadon datake jiyya an saka mata filo ta jingina, abincin da aka zuba mata taketa faman jujjuya cokali a cikinsa, tasaba kullum Galadima ke bata abincin, gashi yau tun safe da'aka kirashi ya fita bai sake dawowa asibitinba har yanzu, dukta damu, da taji motsin tahowa za'a shigo d'akin saita zata shine, sai anshigo taga bashi bane sai haushi ya kamata, Munubiya data fahimceta tsaf taita gumtse dariya har suka tafi, su Aunty Mimi hankalinsu gaba d'aya yanaga yaran, basusan mitakeyiba.
Turo k'ofar da akayi ya sakasu kallon k'ofar gaba d'aya, dan k'amshin turarensa yafara musu sallama kafin shigowarsa, wayace manne a kunnensa yana magana a hankali, hannunsa d'aya cikin wandon aljihun Ash color d'in shaddarsa daketa maik'o, Munaya daketa sauke k'ananun ajiyar zuciya tunda taji k'amshinsa tad'an saci kallonsa, shima idonsa a kanta, gira ya d'aga mata, tai saurin janye idonta tana tura baki kad'an.
Murmushi yayi ya zauna a bakin gadon kusada k'afafunta yana cigaba da wayarsa, yayinda yakema Amaturrahman da aka kwantar kusada ita wasa, yaran sund'an fara wayo, Dan idanuwa k'yar suyita kalle-kalle, kwanakinnan da suka dawo shan nono sunyi y'an k'u6ul-ku6ul dasu abin sha'awa.
Munaya dai tafara tura abincin da k'yar, sai wani faman had'e rai takeyi, shidai Galadima dariya na cinsa a rai amma baiyiba, saidai ya saci kallonta ya maida idonsa ga Amaturrahman data rik'e d'an yatsansa gam daya saka a d'an hannunta, kaikace tasan minene.
Sudai Su aunty Mimi da laraba suna cigaba da hirarsu, Dan laraba na bata labarin halinda su Abdurrahman suka shiga a kwanakin da Munaya bata farfad'oba ne.

Galadima ya ajiye wayar yana d'aukar Amaturrahman da fad'in, “O my lil princess I miss you”. Ya k'are maganar da sumbatar kumatunta, sannan ya juyo suka gaisa dasu aunty Mimi dake kallonsa shida babyn tashi abin sha'awa.
Cikin tsokana aunty Mimi tace, “Ai dama shirin kiranka nake danna kula my k'anwa bazataci abincin nanba sai kana kusa”.
Galadima ya juya yana kallon Munaya data waro ido tanajan mayafi ta rude fuska Dan kunya, dama aunty Mimi suna kula da ita kenan, itakam taga idi.
Galadima yace, “A lallai Aunty Mimi da gaskiyarki fa, kamarma kuka tayi?”.
“kad'an dai ya rage tayishi my k'ani, tun d'azun ina lura da ita, rabin hankalinta naga k'ofa”.
Laraba da Galadima sukayi dariya, ya kuma kallon Munaya data kasa d'ago kai ta kallesu.
Galadima ya had'iye dariyar dake Neman kufce masa, ya ajiye Amaturrahman d'in yana matsowa kusa da ita, Murya k'asa-k'asa yanda su Aunty Mimi bazasujiba yace, “Any problems my Princess?”.
Munaya ta saci kallon su Aunty mimi, ganin basa ganinta saita tura masa baki kad'an tana matso k'ananun hawaye.
“O my God”. ‘ya fad'a a hankali yana d'ora tattausan hannunsa saman nata, cikin wani salon daya saka tsigar jikinta tashi ya kar6ar spoon d'in. Babu shiri ta sakar masa.
Yakuma k'asa da murya yana d'ebo abincin da fad'in, “nifa kibarmin shagwa6arnan kokuma humm”. ‘ya k'are maganar da ciza lips yana jifanta da wani kallon mai cike da sirrika’.
Waro idanu Munaya tayi tana kallonsa baki bud'e. Abincin ya zuba mata yana kashe mata ido d'aya.
Kunya ta kamata, Dan wlhy Galadima bashida kunya ko kad'an, kad'an daga aikinsa ya aikata duk abinda yazo masa a rai d'in, danta San halin kayanta sarai.
bata k'ara yarda sun had'a idoba har yagama bata abincin, ya d'akko d'an Basket d'in da drugs d'inta ke ciki yana dubawa.
Aunty Mimi data kasa hak'uri ta mik'e tana tawa, “Oh ni Haneefa, dama abinda ya hanaki cin abincin kenan da gaske dai tun d'azu kiketa cuna baki my k'anwa”.
Munaya tai saurin jan d'an gyalen dake yane bisa kanta ta rufe fuska saboda kunya dataji, Aunty Mimi ma akwai iya 6aro zance, kuma ta Fiske abinta.
Laraba tayi y'ar dariya itama tana bin bayan Aunty Mimi suka fice, itakam dai birgeta sukeyi sosai, komai nasu a nutse.
Chapter 37 · 0% Book details