← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 66

Sashe 45

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Galadima dake kwance yau yini guda cikin halin ciwon kai da zazza6i, salla Ce kawai ke tadashi, abincima da k'yar ya had'a shayi yasha bayan sallar la'asar, tunda ta shigo yana jinta, saidai baisan wanene ba, shi a tunaninsa ma wanine yazo cutar dashi, jin anyi shiru ankuma k'i magana ya mik'a hannunsa da k'yar ya kunna fitilar dake dirowar gefen gadon.
Baya nad'anyi kad'an danni tsoratama nayi, harma na fara zaton kobaya d'akin, sai kuma na nutsu waje d'aya ina kallonsa, yana cikin bargo ya lullu6e har kansa, janye bargon dake lullu6e da fuskarsa yayi yana kallona ta cikin d'an hasken fitilar.
Idanu ya zuba mata cikeda mamakin yaushe tazo gidan? Ya ciro hannunsa daga bargon yana min alamar nazo.
A hankali na cigaba da takawa, zuciyata cike da d'unbin tausayinsa, koba komai ta sanadina ciwon ya sameshi, na zauna a bakin gadon idona a kansa, hannuna ya kamo cikin nasa dakeda zafi alamar zazza6ine ma a jikinsa. Ina had'iye kukan daya tahomin nace, “Sannu, ya jikin?”.
Idanunsa ya lumshe da cije lips.
Na kama bargon zan yaye yakuma rik'e d'ayan hannun yana girgizamin kai, ahankali yace, “Sanyi”.
Sannu na kuma masa, sannan na zare hannuna zan mik'e, amma saiya rik'oni da sauri, jiyowa nai ina kallonsa.
Ahankali Yace, “Ina zakije?”.
Badan ina kallon la66ansa ba dabama zan fahimci miyace d'inba, Dan banjiba.
Dawowa nayi na zauna, nad'an matsa hannunsa, “zan had'a maka ruwane kasamu kad'anyi wanka, kaci abinci kuma”.
“Zan daiyi wankan kawai?”.
“Abincin fa?”.
Kansa ya girgizamin alamar a'a.
Kamar zanyi magana saikuma na fasa, tashi nayi na shiga toilet, dukda babu wani datti dai sai naga yakamata na wanke, na cire mayafin jikina na tsaftaceshi, na saka air freshener sannan na had'a masa ruwa mai d'an zafi ba canba dai, yanda zai masa dad'i.
Zaune na iskeshi a bakin gadon ya dafe kansa, kallo d'aya namasa na d'auke kai, Dan dagashi sai boxer.
“Ga ruwan na had'a”.
'Dago idonsa yay ya kalleni yana sauke hannunsa daya dafe kai, yanda tawani k'asa dakai kamar tana gaban surukinta, yad'an murmusa danshi kunyar nan tata birgeshi take.
Duk saina takura da kallon dayakemin, gashi kunyar motsawa nake daga wajen, Dan sket d'in jikina ya kamani sosai, maganarsa Ce ta katsemin tunani.
Na d'ago ido naimasa kallon fisha na janye ina fad'in “Towel?”.
“Uhumm”. Kawai yace yana cigaba da kallonta.
Ahankali na dunga tafiya saikace wata mai tatata, Dan inaji a jikina kallona yakeyi har yanzu, saida na d'akko gyalena dake jikin k'ofar bayi na yafa sannan na d'akko towel d'in.
Duk abinda takeyi idosa na kanta, towel d'in da hannunna ya had'a ya rik'e, na kallesa fuska a marairaice ina f'ad'in, “karfa ruwan ya huce yalla6ai”.
Ya zubamin jajayen idonsa ga jijiyoyin kansa sunyi rad'a-rad'a, baice komaiba ya zare towel d'in ya yafa a jikinsa yana mik'ewa da k'yar, saiya kuma bani tausayi, Dan na lura k'arfin haline kawai yakeyi.
Bedsheets d'in saman gadon Na cire bayan Na kunna fitilar d'akin ya gauraye da haske, Na bud'e wardrobe d'in kayansa Na d'akko wani bedsheets d'in Na shinfid'a, Na share d'akin, banyi morping ba tunda darene, nasaka turare sanann Na fita.

Yauce rana ta farko dana shigo kitchen da nufin dafama miji abu, sainakejin karsashi da alfaharin nimafa yanzu matar aurece tamkar kowacce mace, natashi daga matar Contract yanzu, wasu hawayen jin dad'i suka zubomin, nasa bakin mayafin Na share, a kayan da mukazo dasu Na ciri kayan k'amshi, ina d'auraye tukunya laraba ta shigo, juyowa nai ina kallonta.
Tace, “ya jikin nashi?”.
Ajiyar zuciya nad'an sauke. Nace, “da sauk'i iya, amma kwance Na iskeshi rijib ga zazza6i, zan dafa masa ruwan zafinne da d'an abinda zaici”.
“ALLAH ya k'ara sauk'i, dama mura bata masa da sauk'i, dan yasha zuwa can yanayi kota sameshi a can, namiki karambani Na dafa ruwan zafin gashinan”.
“Nagode iya, wlhy babu wani karbani, taimako dai, mun saki aiki ga gajiyar tafiya”.
Dariya tayi tana gyara tsayuwa. Tace, “Aini gajiyarnan kam ta gudu, ras nakejina, kunedai dayake ba wahalar kuka saniba koyaya kuka motsa sai jiki yayta ciwo”.
Nima dariya nad'anyi, ina cigaba da had'a komai akan k'aramin tire.
Laraba tace, “To yanzu Yaya za'ayi kenan da abinci? Kinga dai ba'a barshi da yunwa ba?”.
Nace, “Iya ga Muftahu can ya tafi samo masa abincin”.
Tace, “To shikenan hakanma yayi”.
'Daukar tiren nayi natafi kai masa.

Har yanzu bai fitoba, mamakin dad'ewarsa ta kamani, ajiye tiren nayi a k'aramin table glass d'in dake gaban gadon nima Na zauna ina tsumayen fitowarsa. Kusan mintuna 3 da zamana saigashi ya fito.
Ban kallesa bama gudun karnaga abinda yafi k'arfina, kaina a k'asa ina wasa da stones d'in jikin mayafina.
Shikam tunda ya fito idonsa Na kanta, ya zauna kusa da ita yana tsane ruwan fuskarsa zuwa kai da towel.
Kallonsa nayi kad'an, ganin bathrobe ce a jikinsa saina samu nutsuwa.
Da hannu yay min nuni da mansa, na mik'e Na d'akko, amma saiyak'i kar6a.
Nad'anyi shiru da tunanin miyake nufi?...
Katsemin tunani yayi da fad'in “Manma nizam shafa?”. A hankali yayi maganar, kuma fuska babu walwala.
Ni mamakima yabani, amma to da banzo ba waye yake shafa masa?, bance komaiba na zauna kusa dashi ina zuba man atafin hannuna da mutsukashi, kunya tasa narasa dama ina zan fara?.
Lura da hakan dayayi saiya mik'amin hannu kawai, banida za6in daya wuce cika umarninsa, anutse na shafa masa man dan banida yanda zanyi.
Kaya na d'auka masa marasa nauyi, ya tashi zaune daga kwanciyar da yayi ya saka, nidai kauda idona nayi gefe harya gama.
Natashi na had'a masa tea d'in da ruwan kayan k'amshinan, yana zaune akan sofa ya zubamin ido saikace wata television, dana mik'a masa mug d'in saiya had'a harda hannuna ya rik'e, da ido namasa alamar da zafifa cikin marairaicewa.
Shima saiya min nasa salon da ido alamar da gaske.
Nakuma narke fuska tamkar zanyi kuka, zame mug d'in yayi yana wani miskilin murmushi.
Ya d'ora cup d'in akan bakinsa yana kallon yanda take tatta6a tafin hannunta, a ransa yace hajiyar tsiwa kenan, andawo koya kuma zamu kwashe?.
Tea d'in yamasa dad'i, Dan saiya tuna masa da inno, itace kan masa wannan had'in inhar yana mura, yanasha yana kallona a k'asan ido, saika rantse kuma ba kallon nawa yakeba, amma ni inaji a jikina.
Knocking k'ofar da akaine ya sashi kallon cctv, ganin Muftahu da Dr jalal sai ya juyo ya kalleni da alamar tuhuma. Uffan bance da shiba, na mik'e da nufin fita na bud'e musu saiya dakatar dani ta hanyar d'agamin hannu.
Komawa nayi na zauna, shikuma ya mik'e rik'e da mug d'in ya fita.
Ajiyar zuciya nad'an sauke ina binsa da kallo.

Saida ya zauna cikin kujera sannan yabama su Muftahu izinin ahigowa.
Duk suka zauna suna masa sannu, ya amsa musu cikin d'aga kai da basu hannu sukayi musabaha.
Magunguna Dr jalal ya bashi na mura. Sannan ya buk'aci yimasa allura, amma saiya nuna bayaso.
Cikin dafe kai yace, “bar Allurarnan Jalal, bara nasha maganin kawai”.
Murmushi Dr jalal yayi, Dan yasan dama Galadima bayason allura. Basu wani dad'eba sukai masa sallama suka fita.
Fitarsu dana gani yasani fitowa falon, kallonsa nayi ina zama, shima idonsa a kaina, da hannu ya nunamin ledojin da Muftahu ya ajiye.
Bance komaiba na bud'e, d'aukar d'aya nayi na fita, na kaima laraba dakema su Abdurraheem shirin barci.
Cikin tsokana tacemin “kodai murufe d'akinmu kawai”.
Dariya nayi na fita ina fad'in “kai iya yanzufa zan dawo”.
Inajiyo dariyarta daga falo. Nidai nashiga kitchen na d'auki plate da spoon na koma wajensa.
Farfesun kifi na zuba masa, dan zaifi masa sauk'in ci, da farko ma cayay bazaiciba, saida naita rok'onsa harda kwalla sannan ya amince nabashi da kaina, yad'anci babu laifi, nabashi drugs d'in da Dr jalal yabashi”.
Koda yagama sha saiya jingina jikinsa da kujerar yay shiru, yad'anji dad'in jikinsa kam ba laifi, falon saiya d'auki shiru, muna a hakane kiran Momma ya shigo wayarsa.
Yabud'e idanu yana d'aukar wayar, yay picking, gaisawa sukayi, bansan mitace da shiba daga can najidai ya amsa da “Insha ALLAH goben muna hanya”. A hankali yake maganar saboda kansa, bama su dad'eba ya yanke wayar ya mik'e, hannu ya mik'omin alamar na kama.
Banyi musuba na saka hannuna cikin nashi ya mik'ar dani, bedroom d'in muka koma, ya zaunar dani bakin gadon sannan ya cire kayan jikinsa, ya hau gadon ya kwanta.
Nidai k'in kallonsa nayi, saida ya kwanta sannan ya kirayi sunana a hankali can k'asan mak'oshi, kallonsa nayi.
Yace, “Please mammatsamin jikina kozai rage ciwon da yakemin”.
Tausayi yabani, dan haka banyi musuba na hau gadon sosai nafara masa tausa a nutse, idonsa ya lumshe yanamai jin dad'in tausar, ahankali drugs d'in dayasha yafara cin k'arfinsa, barci mai nauyi yay a won gaba dashi, saida na tabbatar barcin yayi nisa sannan naja bargon na kuma lullu6a masa har saman kafad'a, nai masa addu'a na mik'e Na lalla6a na fita a d'akin bayan na kashe masa fitila.

Koda na koma d'aki laraba har tayi barci, nima shirin kwanciyar nayi kawai na kwanta, cikeda kewar y'an uwana da jiya iyanzu duk muna a tare😔.

********************
Chapter 45 · 0% Book details