← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 66

Sashe 19

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“humm yalla6ai nakula duk yanda bawa yakai da samun komai Na rayuwa saikaga wata damuwa ko tawaya mai kutse acikin al'amuransa, bana manta maganar nan taka da kata6a fad'amin wani lokacin murmushin da jama'a kanyi iyakarsa fuskane, amma zuciyarsu sune kad'ai sukasan sirinta, lallai wannan gaskiyane, amma kasan mike birgeni da k'aramin k'warin gwiwa a rayuwata koda ace Na tsinci kaina a fagen sanyin jiki?”.
Galadima yace, “uhm-uhm”.
Munaya ta sauke wata sassanyar ajiyar zuciya da Galadima yajita har cikin ransa, yayinda wani Abu ya tsarga masa ta cikin kai har zuwa yatsan k'afa, ya gyara kwanciyarsa yana jiran jin mizatace.
“Komai girman fad'uwa inhar da yak'inin HAK'URI dana k'arfin ZUCIYA to lallai akwai tagomashin sirrin samun NASARA, hak'uri da juriya basa ta6a zama fad'uwa, inhar kaga bawa yayi hak'uri babu kuma NASARA a ciki to lallai hak'un nasa kad'anne, sometimes gaggawa aikin shaid'anne, saikuma ansha wahala ake shan dad'i, abinda kawai muke kasa fahimta shine riba akan sameta ne a muhalli biyu, walau a duniya kokuwa a lahira, duk wadda bawa ya samu sunanta nasara, amma kowa yafi fata da samun ta duniya, saidai ta lahira ita yakamata mufi d'oki da addu'ar samu, meybe tazame mana tsani Na zuwa inda bamuyi zatoba, hikimar Ubangijice yabaka nasarar anan kokuma a can, Dan babu yanda za'ayi a zalunceka mai kowa da komai sarkin Rahma da jink'ai ya bari, bai yarda da zalunciba, yakuma haramtashi agaremu mu bayinsa”.
Wasu k'ananun hawaye suka gangara ta gefen idon Galadima, fuskarsa d'auke da murmushi, yayinda kalaman munaya ke tasiri adukan magudanar jininsa da zuciya, wata nutsuwa ta musamman daya rasa tashiga ratsashi da bashi k'arfin gwiwa, a hankali yace, “ke y'ar baiwace matar Contract”.
Dukda maganar k'arshe ta sosa zuciyarta saita murmusa, cikin kuma kwantar da murya tace, “Ni a suwa Mijin contract ”.
Ya d'an dara batare daya shiryaba. Yace, “one-one kenan?”.
Munaya tayi dariya tana fad'in “nidai bada manufa na fad'aba”.
“Fad'i gaskiya dai yalla6iya tsiwa”.
“Gara mai tsiwa da miskili, koba komai akansan muna waje ai saboda tsiwarmu”.
Galadima ya kuma Murmusawa. Yace, “ki kiyayi randa zan kamaki ALLAH”.
Itama dariyar tayi. Tace, “yalla6ai ka fad'i wani Abu nabaka k'yauta mana”.
Yay d'an jimm tunanin mikenan?, saikuma yayi ajiyar zuciya yace, “mikenan?”.
Cikin wani salo Munaya tace, “R. Ita kawai nakeson ji a harshenka”.
Lallai yarinyarnan taga gadon barcinsa wlhy, yay maganar a zuciya fuskarsa na k'awatuwa da murmushi. yace, “Okay, kibari sai ina gabanki”.
“Tab, Indai ba yanzuba na fasa”.
“uhmyim, miye na karayar hajiyar tsiwa?”.
“Aiba karaya nayiba, lokacin kawai kabari ya wuce, ni karmafa yarannan suma su gadoka”.
“Dai-dai kenan ai y'ammata, kokin manta k'yan d'a ya gaji ubansa”.
“Humm Alfahari kenan, ita uwa an rainata”.
Dariya tabashi, amma ya daure baiyiba. Yace, “keda kike gudunsu mizaisa su gadoki?”.
Munaya ta d'an ta6e baki, cikin juya idanu tamkar tana gabansa tace, “yanzu kana ina?”.
Murmusawa yayi saboda basar da maganar da tayi. Yace, “kinason ganinane?”.
“A'a, son sani kawai nake”.
“Humm, naje tad'i to”.
Shiru munaya tayi, sai kuma ta d'an dara, “Yalla6ai kasan wani Abu kuwa?”.
“Saikin fad'a”.
Cikin danne dariya tace, “irinku kwantai kukeyifa, sai anyima y'ammata tallarku asamo mai taimakonku ta aura, kaima nasan saisu takawa sunmaka haka.....”. Sai yaji kitt, ta yanke wayar.
Wani k'asaitaccen murmushi ya saki yana shafa kumatunsa, ya d'ora wayar saman cikin sa yana fad'in “lallai yarinyarnan kin girma, zaki tabbatar nayi kwantai kuwa”.
Daga canma Munaya dariya taketa k'yalk'yatawa, harta tada Meenal, Mununiya datun d'azun take kallonta ta bayan labule bata saniba tayi murmushin jin dad'i itama tana share hawaye, tanason y'ar uwarta sosai, sannan wayonta da iya mu'amullarta na birgeta, tabbas Munaya tanada tsiwa, amma tanada wayo, inhar zaka takurata bazata ta6a raga makaba, amma tanada tausayi dason ganin farincikin wani koda ita zata rasa nata farincikine, gakuma son girma uwa gyambo, tanason komi zaka mata ka nuna muhimmancinta a gareka, a fili tace, “ALLAH yakawo farinciki mai d'orewa a ratuwarki kema y'ar uwata”.

Amin munu😘☺.

★★★★★★★★

Tunda Muftahu ya shigo yakebin Galadima da kallon mamaki, ganin yasake yanata fara'a tamkar ba shine a matsananciyar damuwa yanzunba, ya zauna zuciyarsa na addu'ar samun mace tagari, dan lallai *MATAN KWARAI RABIN ADDINI ce*.
Galadima ya hararesa yana tashi zaune, “malam lafiya ka k'uramin ido?”.
Dariya Muftahu yayi sosai, yace, “to miye na tsarguwar ranka ya dad'e, wlhy kuna sha'aninku kaida gimbiyarka, yanzu nan harta saukeka daga hawa saman da kayi”.
Filo Galadima ya jefama Muftahu, shikuma ya cafe yana dariya.
Galadima ma murmushin yayi yana danna kiran Sauban. Dan yasan har yanzu yanacan cikin damuwa. Hasashen nasa kuwa yayi dai-dai, Dan har yanzu muryarsa a cinkushe take. Amma jin ta Galadima a sake sai farinciki ya kamashi, cike da zumud'i yace, “yaya an dace ne?”.
Murmushi Galadima yayi mai sauti, yace, “muna fatan hakan autan Momma”.
Alhmdllh Sauban yashiga jerowa, saiya saki jikinsa kuma harda tsokanar Galadima yana dariyar k'eta.
Galadima dai murmushi yakeyi yana girgiza kai, ya yanke wayar zuciyarsa na addu'ar ALLAH ya saka farinciki a zuciyar Munaya fiye da yanda ta sakasu. Massage ya tura mata sannan ya kalli Muftahu yana gyara zama.

Munaya na kwance har yanzu takasa fita, tunda tasamu Meenal ta koma barci saita lumshe ido tana dulmiya duniyar nazari, shigowar sak'one ya sata bud'e ido ta jawo wayar. Ganin Galadima ne saita mik'e zaune babu shiri, sak'on ta bud'e.

_“Kin yaudareni da zance banko tambayi yaya jinin jikina sukeba yalla6iya, to ki shafamin kansu._
*_ALLAH ya sanya farinciki a rayuwarki fiye da yanda kika Sani_*.

Wasu hawayen farinciki suka gangaro a kumatun Munaya, bata ta6a tunanin shirmen datake masa yanayin tasiri a zuciyarsa ba, Dan bai ta6a nuna mataba, a fili ta furta “ALLAH na gode maka dana zama sanadin saka wani bawa naka farinciki a lokacin jarabawar damuwa ta lullu6e jinsa da ganinsa da zuciyarsa”.

Amin munaya, muma Ya ALLAH kabamu ikon bama bayinka muminai gudunmawar farinciki mai amfani koyaya ne, amma bata hanyar sa6onka ba ko take k'a'idar daka shinfid'a mana, amin👏🏻😭.

*************************

Muftahu da Galadima suka fito, yauma bai zauna bayaba duk yanda Muftahu yaso hakan, dama yay masa maganar zama bayan hararsa yayi, dole yaja bakinsa yay shiru yana murmushi.
Wani wajen cin abinci Muftahu ya tsaya, ya kalli Galadima dake kwance jikin seat ya lumshe ido yace, “ranka ya dad'e Dan ALLAH ina zuwa”.
Kai Galadima ya jinjina masa kawai batareda ya bud'e idoba, Muftahu ya fita, mintuna 15 saigashi ya dawo hannunsa d'auke da ledoji, ya bud'e seat d'in baya ya ajiye, sannan yadawo mazaunin driver yana maba Galadima hak'urin jira.
Baice dashi komaiba, Dan tuni yama lula wata duniyar.
Gidan gonar Nuren suka nufa, inda su Harun suke a ajiye, a falo suka yada zango, ko ina k'al yake a tsaftace ga k'amshi, cikin masu kula da gidan gonar ya shigo d'auke da wankakkun y'ay'an itatuwa masu k'yau, zubewa yay yana kuma kwasar gaisuwa, Muftahu ne kawai ya amsa, Galadima hannu ya d'aga masa.
Chapter 19 · 0% Book details