← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 66

Sashe 51

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kukan Amaturrahman ya sanya Munaya farkawa, tayi mik'a addu'a d'auke a bakinta ta bud'e ido.
Da Galadima ta fara tozali, ya sakarmata wani sassanyan Murmushi yana wani lumshe ido.
Itama murtani ta mayar masa da sinne kai saboda kunya.
Yace, “Ayi hak'u atashi yunwa mukeji”.
Munaya tad'an 6ata fuska tana kuma jan bargo, “ALLAH barcin nan bai isheniba nidai”.
“Haba my Queen yi hak'uri please ”.
Kamar Munaya bazata tashiba, tadai daure ta tashi zaune tana yamutse fuska, sauka tayi ta shiga bayi tayo brush sannan tadawo.
Ya d'ora mata Abdurraheem daya kafa sabon kuka a cinya.
“Wlhy rigimarka tayi yawa Abdurraheem, ko kad'an bakada hak'uri”.
Galadima yayi Murmushi kawai amma baice komaiba, sai ido daya zuba mata itada yaron.
'Dai-d'ai taringa shayar dasu, yayinda Galadima ke can gefe saman kujera yana waya da latsa lap-top, da alama kiran mai muhimmancine.
Nidai nagama shayar dasu natashi, duk saman sofa Na maidasu Na gyara gadon tsaf, harna kammala bai gamaba, koda nazo shara da Morphing ma yanata wayarsa, nagama kimtsa d'akin fes na shiga bathroom shima Na tsaftace sannan nakoma falon, dukda babu datti shima saida Na kuma gyarawa, ina jiyo hirarsu Momma a k'asa amma banyi yunk'urin saukaba, danni yau bammasan ya za'ayi Na sauka k'asaba, kunyar kowa nakeji wlhy.

A tsaye Na iskeshi yana k'ok'arin d'aura towel idonsa akan yaransa daketa kalle-kalle.
Muka had'a ido ya d'agemin gira da fad'in “zanyi wanka”.
Da to Na amsa masa na shige bayin danna had'a masa ruwan wankan.
Ko kad'an banji shigowarsa ba, saida na d'ago da nufin fita naci karo da mutum, baya nayi zan fad'i yay saurin taroni na dawo jikinsa.
“Nikam kabani tsoro”. Nai maganar a shagwa6e.
“Sorry”. Shima ya fad'a yana k'ok'arin saka idonsa cikin nawa amma nak'i.
Nace, “Ga ruwan, bara naje karsuyi kuka”..
Hannu yasa ya rufe k'ofar yana jana cikin bayin sosai, “Bawani kuka da zasuyi, yau duk zame-zamenki tare zamuyi wanka Matar Sameer”.
Cikin waro ido nace, “Tarefa?”.
Saukar ruwa naji ajikina. Yace, “ga tabbaci ma”.
Inaji ina gani doledai akayi wankannan, Wanda shiriritar da muka tsaya tajamu tsawon lokaci.

Aunty Mimi ta had'a breakfast a babban tire tabama Samha takai musu, taita knocking ba'a bud'eba, saita d'an tura k'ofar ta lek'a, babu kowa a d'akin sai yara a kan gado, saikuma ta jiyo motsin ruwa a bathroom, hakanne yasata fahimtar wanka suke kenan, d'aukar tiren tayi ta shige cikin ta ajiye, a ranta tana fad'in soyyaya ruwan Zuma, duk d'aurewar Uncle Sam da k'asaitar nan tasa Ashe zai iya soyayya, Ashe mu aka raina aita mana mazurai da harara.😂

Bayan mun gama shiriritarmu muka fito fuskar kowannen mu d'auke da farincikin kasancewa da juna, yaran duk sunyi barci, ya zauna gaban mirror yana fad'in “Kashmir fa zamu wuce yanzunan”.
Da mamaki na kallesa ina fad'in, “Kashmir fa?”.
Hannuna ya kamo ya d'orani saman cinyarsa, yawani k'ank'ance idanu yana kallona, “To bakece kika Sani dawowar doleba my Queen, tunda nasamu kin sauka ai saimu koma tare”.
Hannuna na d'ora saman kwantaccen sajensa dake jik'e da laimar ruwa ina fad'in “Kai dai ka koma abinka, ALLAH inajin kunyarsu Momma”.
Murmushi yayi ya kama hannuna yad'an ciza.
Kukan shagwa6a na sanya masa ina yarfe hannun.
“O, my Heartbeat ingani yayi jini?”.
“Ai saina rama”. Na fad'a ina lalubo nasa hannun nima.
Dariya ya sanya da k'ok'arin 6oyewa, kad'an garage mu fad'i daga saman stool d'in, Dan yamana kad'an. yakuma cizona a kunne kad'an.
Kukan shagwa6a na kuma sanya masa da fad'in bazan yardaba.
Biyemin yay mukai tayi yana dariya da zagaye sofa akan saina kamashi na rama, amma yak'i tsayawa, gashi dagamu sai towel, saida ya tabbatar nayi laushi sannan ya fad'a saman Sofa yana dariya da sauke numfashi, jawoni yay na fad'o jikinsa nima ya rungumeni.
“Sorry Yalla6iyana bazan sakeba kinji, inga kunnen shima koya huda”.
Na turo baki gaba da mik'a masa kunen, “Bagashi harda jiniba”.
Nanma dariya ya sanya, “Yaushe kika koyi sharri kuma?, saikace wani mai hak'orin zaki”.
Dariya nayi inad'an dukan k'irjinsa kad'an. Nace, “wama yasani ko irinsa gareka, ALLAH akwai zafi”.
“Rakinki yayi yawa my Queen, nidai tashi kibani abinci naci, fita zanyi Akash na jirana, kinsan d'an matsalarnan bikinsa yataho”.
“A lallai kace munada shan shagali”.
Hancina yaja cikin tsokana yace, “idan baki fara laulayiba sannan ko?”.
“Laulayi kuma? Nami?”.
“Na abin cikin kwan mana, kina tunanin banyi ajiya bane jiya?”.
Sauka nayi daga jikinsa ina fad'in “Ka rufan asiri my King, ina zani da wad'annan ma dake gabana?”.
“Duk ki had'a mana babie na”.
ALLAH ya kiyaye na fad'a a zuciyata, a fili kam bance uffanba.
Tsaf muka shirya kanmu, sannan mukayi breakfast a makare.
Yayi k'yau cikin fararen suit, sai zabga k'amshi yakeyi, nikam sket da Riga na lass na sanya, kusa dani ya zauna, ya sanyani jikinsa yay mana photo, sannan ya sumbaci la66ana.
Nad'an murmusa da maida masa murtani, cikin lumshe ido yace, “Thanks my Everything”.
Far nayi da idanu cikin kissa nace, “ALLAH ya tsaremin kai”.
“Amin” ya fad'a yana mik'ewa. Ya matsa ga yaransa dake barci duk ya sumbaci kumatunsu sannan muka fito..
Iya falon saman na tsaya ina masa adawo lafina.
Harya fara taka steps d'in ya tsaya, juyowa yay yana kallona, “Wai kina nufin iya nan zaki tsaya?”..
“Nidai wlhy kunyar su Momma nakeji”.
Dariya tabashi, amma sai baiyiba, yay murmushi yana cigaba da sauka abinsa.

Shi kansa dai daya sakko k'asan sai kunya ta kamashi, ganin Momma da Aunty Mimi duk suna falon, saiya samu kansa dak'in yarda su had'a ido.
Aunty Mimi Ce kawai tayi k'aramar dariya, amma Momma yitai tamkarma batasan inda ya dosaba, saima ta shiga yaba kwalliyarsa da tambayarsa sai ina kuma?.
Ganin Momma ta share shima saiya fuske yay mata tamkar yanda ya saba, yasamu ya fice abinsa.

***************

Ni dai kam nakasa sauka kasa, ganin kad'aici da kewar Galadima zata fara addabata saina d'auki waya na kira innarmu, hayaniyar danaji a gidan yasani tambayar mike faruwa?.
Innarmu tace, “To sarkin son gulma basai kinjiba, ya kuke?”.
Dariya nayi, nace, “Kai innarmu Dan ALLAH kid'an gumtsamin”.
“O ni Ai'sha ALLAH ya shiryeki Munaya, wato dai bazaki canjaba kekam?”.
Nanma dariyar nayi harda k'yalk'yatawa, “Kai Innarmu na canja mana, kinsan gidan namune sai a slow, nasan dai yanzu duk kin wuce da iskancinsu d'innan?”.
Itama dariya tayi daga can. Tace, “Ai tsakanina da kowa yanzu sai girmamawa, ni dariyama suke bani, Safara'u ce wai mijinta zai k'ara aure, shinefa inaga ta tada hankalinta taita zuba masa rashin kunya ya shashshek'a mata mari, to jiya dai a gida ta kwana, kinsansu da gutsiri tsomar tsiya, wai Jamila tashiga gaida Hadiza ta iske suna gulma itada Mero, shine taje tasanarma uwar tasu, wannan yakawo wanan fad'an da kikeji, Maman safara'u babu hak'uri tafito tanata zaginsu da fad'in ai ko auren Safara'u mutuwa yayi ba kanta farauba, tunda ga Siyama da Zarah nan a gida tun kafin ita. Shinefa suka kaure fad'a da cin zarafin juna”.
“Tofa, ALLAH ya k'yauta to, tosu su mom indai banda take laifinka ka hango na wani ai baikamata su zauna yida waniba ganasu y'ay'an zaune, anriga an koyama yaran gidanan d'aukar gulma wlhy, yanzu kamar jamila tasan ta d'auki zance takaima mamansu, to su Abba duk basa nan innarmu?”.
“Wlhy suna nan, kuma duk sunajinsu, shiyyasama danaje nabad'a hak'uri sau d'aya naga sunk'i saurarena nai dawowata d'aki, Aryaan na kwance yana fama da zazza6i gara Nazo natattali yarona yafimin”.
“hhh innarmu kinaji da autaras d'innan nakifa, ALLAH yabashi lafiya, sukuma ALLAH ya dai-daita komai. Hajiya Innaro fa?”.
“Tana gidanta mana, bama tajin dad'i kwana biyunnan wlhy, tana fama da ciwon k'afa, ki kirata ki gaisheta, dan jiya gwaggonku Safiyya ma tazo itama”.
“To su Innaro kodai gangarawa za'ayine? ALLAH yabata lafiya”.
“Ja'ira saidai tsohonki ya gangara, amindai to, ai dama sauk'i”.
Dariya nayi kawai.
Daganan muka cigaba da hirarmu wadda ta shafemu, nan ma innarmu ke sanarmin Aunty Salamah tazo gidan ansaka aurenta.
Cikin tsantsar farin ciki nace, “Innarmu dan ALLAH da gaske?”.
“To Munaya ana wasa da maganar aurene? Nasanma zata kiraki ai”.
Farin cikine sosai ya mamaye zuciyata, nace, “ALLAH sarki Aunty Salamah komai nada lokaci, anata surutun ta tsufa agida batayi aureba, gashi ALLAH yakawo iyakar, lallai aure da Haihuwa duk lokacine dasu, duk saurin mutum saiya jira ALLAH, ALLAH yabama sauran y'an matanmu mazajen aure nagari masu addini da nagarta, suma mazan haka”.
“Amin dai Munaya”. Inna ta amsa itama cikin farin ciki..
Nace, “Innarmu zancen Ayusher fa itama?”.
“Itama kwanannan sukace min zasuzo akan maganar, dan kawu Mani ma munyi waya dashi d'azunnan, tsohuwar nan ce tarasu mai ciwon hannun nan, shinema ya dakatar dasu”.
“ALLAH sarki Innarmu, badai wadda tabama yara maganin ciwon kai ba?”.
“Aiko dai ita, ashe kin ganeta, ALLAH ya d'auke kayansa shekaran jiya wlhy, Abbanku ma zasuje gaisuwa su dukansu harda Baba mai kanwa ”.
“Wayyo, to ALLAH ya gafarta mata, amma shi baba mai kanwa ina yaga k'arfin wannan doguwar tafiyar innarmu?”.
“Ai ba'anan takeba Munaya, dayake ALLAH yabashi lafiya, yace insha ALLAH saiyaje yaga tushena”.
“ALLAH Sarki baba mai kanwa, ALLAH yak'ara lafiya da tsawon kwana”.
Inna ta amsa da amin.
Munsha hira sannan mukai sallama.
Chapter 51 · 0% Book details