← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 66

Sashe 57

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wad'annan bayin ALLAH yau lallai suna cikin tsantsar farin ciki, ko kad'an Galadima ya kasa gusawa daga jikin Abie, Yakuma k'i kiran kowa, burinsa shima yabasu mamaki tamkar yanda Dr Erfan Fahad yabashi. A yau yay niyyar su juya amma Dr Erfan Fahad ya hana hakan saidai gobe, Dan dare yayi kam a yau.
A gado d'aya Galadima da Abie suka kwana, dukda sunma cinye rabin daren da fira😁.

**********

Hankalin Munaya duk a tashe yake, saboda tanata kiran Galadima yak'iyin picking, tun tana daurewa harta gaza tafara kuka da shiga tsantsar tashin hankali.
Momma Ce ta lura da canjawarta, ta tambayeta lafiya?.
Kasa magana tayi saboda kunya, saida Momma ta kuma maimaitawa sannan tace, “Momma inata kiran Number Abbansu ne yak'i yin picking tun d'azun”.
Ita kanta Momma ta kirashi baiyi picking ba, amma ta d'auka ko wani uzirine yasha kansa, sai yanzumefa hankalinta ya fara tashi itama, waya ta d'auka tashiga kiransa amma babu amsa, kusan kira 10. Cikin firgici ta kalli Munaya da aunty Mimi da itama take kan gwada kiran nasa, amma itama ba'ayi picking.
“Kinga Munaya tura masa massage mu gani”.
Jiki a sanyaye Munaya ta tura massege, amma kusan 30minutes babu reply.
Hankalinsu fa yakai k'ololuwar tashi, amma sun rasa mafita.

*********

Shikam Galadima baima San sunaiba, wayarma kanta baisan inane ya jefar da itaba, gabaki d'aya hankalinsa ya tattarane ga Abie, harkuma suka kwanta barci bai nemi wayarba.

***********

Yau kam inhar wani yay barci a cikinsu to bana kwanciyar hankali baneba, dan kowa damuwa tamasa katutu, dai-dai da Hadiman gidan suma duk a damuwa suke, sai dai tamkar yanda suka saba yauma sun mik'a lamarinsu ga Ubangijin talikai.

*_Washe gari_*

Tunda safe Momma ta nemi Number Dr Akash da Dr Ajey akan rashin jin Galadima, duk sun amsa mata da zasu bincika.

Can kuma su Galadima sun wayi garine da shirin dawowa New Dhalhi, cikin tsantsar farin ciki irin Wanda misaltashi ma 6ata lokacine.................✍🏻

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
[8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*

*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
_____________________
*_Tawan miss xoxo tawa ni kad'ai, wannan gaisuwar takice ke kad'ai da babbar murya my dear, ALLAH ya bar mana zuminci mai d'orewa har Abadan, ke ta dabance a zuciyar bilyn Abdull, ina yinki irin Trillion's d'innan wlhy, na gaisheki da gaba d'ayan ahalinki da tawagar y'an Group d'inki na HOME OF NOVELS baki d'ayansu, alkairin ALLAH yakai gareku har gadon barci My Hafsy🤸🏻‍♀😘👍🏻._*

_______________________

*_BOOK 3_* 👉🏻3⃣0⃣

...............Da asubahi na tashi jikina cike da gajiyar tafiya da wadda boss ya k'aramin, daga sallar asubahi bai samu dawoba, Dan ana fitowa salla dukan ahalin gidan mai ruwa da tsaki sun hallara ne ga yima Abie barka da zuwa dakuma tabbatar da gaskiyar zancen, domin tabbatar musu da kokwantonsu mai martaba yabasu damar ganin Abie d'in tareda shelar Sank'ira. Wannane dalilin yad'uwar zancen dawowar ta Abie har a wajen masarauta.

Dukda gajiyar dake tare dani bansamu komawa barciba, nashiga k'imtsa gidan iya bedrooms d'inmu zuwa nashi sashen da babu wata baiwa dakeda lasisin shiga. Sauran guraren zuwa kitchen kuma bayina dasukayo asubancin zuwa sashen saboda jin nadawo ne keta k'ok'arin gyarawa.
Na fito da nufin komawa d'akina na tashi yara na musu wanka cikin bayina d'aya ta zube Guywoyinta a k'asa tana fad'in “Ranki ya dad'e ga sak'on kayan abincin salla nan daga sashen mama fulani”.
Cikin d'an mamaki Na kalleta tareda kayan abincin dake jibge, sai naman kaji cikeda k'atuwar roba irin wadda ake tarama mai jego ruwan wanka. Katsemin tunani tayi da kuma fad'in,
“Ki gafarceni ranki ya dad'e, wannan al'adar mama Fulani Ce, a duk daren salla takan aikama kowanne sashe Na y'ay'anta da manyan gidannan irin wannan kayan, yanzu zama a k'araso da sauran, kowane sashe dasu yake abincin salla”.
Kaina Na jinjina tareda zama bisa kujera ina d'ora k'afa d'aya kan d'aya da kallon baiwar dani nama mance sunanta a yanzu. Nace, “Oh, yama sunanki?”.
“Ranki ya dad'e Umimi”.
“To Umimi wace shugabar hadiman sashen nan?”.
“Nice rankai ya dad'e”.
“Ok, ya zamuyi kenan? gashi mun kasance lokacj a k'ure, Dan yanzun kinga kusan 6:23am, bamuda isashen lokacin abincin salla kenan”.
“Ranki yadad'e ki gafarceni, zamu iyayi insha ALLAH, tunda kinga ai munada yawa”.
Shiru nayi inad'an nazari, saikuma Na sauke numfashi ina mik'ewa damata nuni muje kitchen d'in.
Alhmdllh inada kaso mafi yawa Na buk'ata, saidai abinda ba'a rasaba, Umimi nasaka ta tattaro sauran suka shigo da kayan, Dan danan suka fara rage aikin, ni kuma Na fito nad'an rubuta sauran abinda nake buk'ata nabama baiwa d'aya da kud'i takaima Sarkin Mota yabama wani ya sayomin.
Badansu Abdurrahman sun tashiba Na tadasu duknai musu wanka, shirin sune yad'an jani lokaci abinka daba d'ayaba, gashi sunfara wayo, sauk'i nama d'aya Umimi babbar macece kuma Na yaba da tsaftarta. Duk da dai namusu gargad'in jira nazo Na had'a komai da kaina. A gurguje nayi wanka nasaka simple gown dabazata takurani wajen aikiba, nasaka k'aramin hijjab Na fito nabarsu Abdurraheem a d'akin, insha ALLAH bazasuyi kukaba, Dan saida cikinsu yay taf sannan Na fito.
Naji dad'in iskesu sunci rabin aikin, to kusan su 15 kowa da abinda yakeyi. Dannan nasaka hannu nima wajenyin abinda yakamata ace ni nayi d'in, Dan Sarkin Mota yakawomin sak'ona tuni. Sannan ankawo sauran kayan daga sashen mama Fulani.

8:00am dai-dai Galadima ya shigo sashen, saboda yazo yay shirin massalaci, mamaki ya kamashi jin k'amshi ya baje ko'ina, shidai yasan bai tanadi komai d'aya danganci abincin salla ba.
Yana cikin tunanin Sauban ya shigo d'auke da k'atuwar ledar kayanda zai saka, Wanda tun muna India yabada umarnin a dink'a masa su.
Tare suka shiga sashensa da tunanin ko inacan, dukda yasan bazanbar y'an aiki akan girkiba, Dan yakula inada son komai naima kaina musamman girki.
Babu abinda ke tashi sai k'amshi mai dad'i anan d'inma, ga ko ina yayi k'al gwanin sha'awa da birgewa, saidai kuma tsit alamun babu kowa.
Sauban ya Shiga bedroom d'insa da kayan shima yana biye dashi.
Cikin sigar tambaya Galadima yace, “to ina take itada yaran?”.
K'aramar dariya Sauban yayi, yace, “Yaa Sam kasan halin auntyn tamu dai, Na tabbatar k'amshin girkinnan daga sirrin iyawartane, kaga kenan tana kitchen ”.
Hararsa Galadima yayi, Sauban ya rufe baki Dan tuna ta6argazar da yayi.

Ina cikin aikin Sauban ya shigo, bayin duk suka zube suna gaisheshi, da farko nama zata ko Galadima ne, saida Na waigo naga Sauban.
Bayan ya d'aga musu hannu dabasu izinin tashi ya kalleni yana fad'in “Aunty gimbiya kinsani jin yunwa mai yawa da wannan k'amshin girkin naki”.
Murmushi nayi kawai ina wanke hannayena, nace “ALLAH Yaa Sauban akwaika da tsokana, ya gajiya”.
“Ai tabi gado wlhy, tare muka shigo da Yaa Sam fa”.
Nace, “Ok". Coffee Na had'a masa a k'aramin filas Na d'ora a tire mai k'yau da mug daduk abinda zai iya buk'ata.
Kar6a Yaa Sauban zaiyi nace, “A'a kabarsa Na hutar dake nikam”.
Yay murmushi, “shikenan Aunty, inagafa nima zuwa zanyi Na shirya yau idin Na musamman ne ga jama'ar masarautar gagara badau”.
“Gaskiyane Yaa Sauban, ALLAH yasa yau asamo mana amaryarmu”.
Dariya yayi yana yunk'urin fita, “lallaima Aunty d'an k'araminnan dani wazai ban y'arsa?”.
Ban samu bashi amsaba ya fice, Nima sashen Galadima Na Shiga INA murmushi.
Babu kowa a falon, Dan haka Na wuce bedroom d'insa.
Sallama nayi kawai Na shige. A bakin gado Na iskeshi zaune d'aure da towel, da alama wanka zai Shiga. Murmushi mukaima juna. nace, “Afuwan my King, aiki ya d'auke hankalina bansan ka shigoba”.
Murmushi ya kumayi yana wani lumshe ido, Na ajiye tiren saman k'arim copy table d'in gabansa sannan Na zauna kusa dashi Na kwantar da kaina gefen kafad'arsa bayan Na sumbaci damtsen hannunsa”.
Shima saiya karkato fuskarsa gareni ya shafa tawa fuskar da tattausan hannunsa, cikin magana rad'a-rad'a yace, “miya kaiki aiki keda ke tare da gajiya?”.
Idanuna na d'ago na kallesa ina murmushi, nace, “my king ai yakamata ace anyi abincin salla a sashen Galadima, wannanfa shine karon farko da zakayi bikin salla da matarka a masarautar nan, bai kamata ace anyishi babu wasu alamuba ai OK?”.
Yanda nai maganar da kashe ido d'aya saida tsigar jikinsa ta tashi, yad'an lumshe ido da sumbatar goshina, sannan ya rad'amin “ALLAH yay miki albarka” acikin kunne.
A saman la66a na amsa da “Amin”.
Ya tambayeni yara nace, “suna d'akina, maybe ma sunyi barci. Bamu tsaya 6ata lokaciba muka Shiga na taimaka masa da wanka, sannan muka fito nahau shiryashi, dukda lokaci yaja a nutse nake masa komai, danshi ma'abocin son komai a nutsene, bayason gaggawa ko yawan sauri koda a magana ne kuwa.
Inamasa shiri yana shan coffee, kaga d'an gatan Munaya.😂
Tsaf na shiryashi cikin farar shadda daduk salla yakanyi amfani da ita wajen idi, nakawo babbar riga na saka masa sannan na fesheshi da turare, ajiye mug d'in hannunsa yayi yana d'aukar hularsa zanna bukar daketa maik'o yay mata kari ya kafa bisa kansa yana dai-dai tawa.
Alk'yabbar dazai sa nagama feshewa da turare sannan na matsa ina kwantar masa da sajensa dayasha gyara da cumb, shikuma yana saka link d'in hannunsa.
Kusan tare muka gama, na kama hannunsa na d'aura masa agogon dabai San da shiba.
Da mamaki ya kalleni amma saina janye idona ina murmushi da fad'in “Happy salla nane nida triplets d'inka”.
Rasama mi zaice yayi, sai kallon agogon da koshi da kansa iya mak'urar za6ensa kenan. Yakai hannu zai rik'oni nai baya kad'an ina girgiza masa kai, Dan nasan makomar rik'onin.
Cikin marairaice face nace, “please kabari saika dawo kawai”.
Wani miskilin murmushi yayi yana cije lips.
Nima na murmusa da nuna masa Alk'yabbar.
Kansa ya girgizamin a hankali yana mai shafa agogon Dana d'aura masa da d'ayan hannunsa. “kibarta zasumin nauyi da yawa, idan zamu fita gaida Governor zan saka”.
Ido d'aya na kashe masa da had'e yatsuna👌🏻alamar yayi.
Ya murmusa shima yanamin jinjina👍🏻.
Ban barsa ya fitaba saida namasa photo biyu, sannan na rakoshi har falon k'arshe, inda Muftahu da Matawalle ke jiransa, suma sunsha wanka mai birgewa, tamkar ka sacesu ko anguna ranar aurensu.
Galadima ya kareni da bayansa tareda min alamar na koma. Baya buk'atar su ganni kenan. Nima saina juya ciki kawai. Yayinda nake jiyosu suna masa Sheri da kod'a wankan nashi.
Chapter 57 · 0% Book details