← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 66

Sashe 43

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda Na shigo motar k'amshin turarensa ya faramin sallama, sanye yake cikin milk d'in shadda datasha ainahin aikin masu sarauta harda hula, yayi k'yau, Dan yau a sarakinsa ya fito, muka kalli juna kowa yay murmushi, saida Na zauna sosai su Deejama dake rik'e da yaran suka mik'ominsu, ganin zasumin yawa yad'an matso ya d'auki Abdurraheem da Abadurrahman, idona dukya cika da k'walla, haka suma su Maryamu hawaye sukeyi, haka suka rufemu suna d'aga mana hannu.
Saida motar ta fara tafiya sannan hawayena suka sami damar zubowa.
Galadima da tun shigowata idonsa Na kaina yay murmushin gefen baki, tissue ya Ciro a bayanmu ya matso jikina sosai da d'ago fuskata. Kallonsa nayi, idanunmu suka sark'e cikin Na juna, ya lumshe nasa dake cike da barci da mura wadda ta k'ara musu girma da canja kalarsu jaa kad'an yana girgizamin kai alamar nabar kuka.
Bance komaiba, sai kuma matso hawayen da nayi, yasaka tissue d'in ya gogemin, sannan ya sumbaci saman la66ana kad'an yana jingina kaina da kafad'arsa.
Shiru nayi ina sauke ajiyar zuciya kad'an-kad'an, yayinda shikuma yake d'an shafa gefen kafad'ata daya d'oro hannunsa wajen, saida nasami nutsuwa sannan Na d'ago, kallona yayi muka had'a ido, cikin salon rashin son yayi magana ya kad'a kwayar idonsa alamar yadai?.
Da hannu Na nuna masa yaran nima, dukda bai fahimci minake nufiba baice komaiba.
Hulunan su Amaturrahman Na fiddo a handbag zan saka musu, dan sauri bai barni nayi hakanba dazamu fito, anafa fitowa daga sallar Asubahi akaita mufito-mufito, kuma duk Yaa marwan ne da wannan azalzalar.
Amaturrahman dake jikina Na sakamawa, shima gogan da mura taima murus ya kar6a yasakama mazan yana magana tamkar an masa tilas, “kai garinnan da dad'in zama da wahala, wannan sanyin nikam shiya hanani sukuni”.
Dariyar data tahomin Na had'iye da k'yar ina fad'in “Ai sanyin kam babu sauk'i, sunce idan zafima yazo yashin yaji rana haka suke azabtuwa, garama sanyin, kaji kuwa muryarka fa ta canja gaba d'aya”.
Murmushi yayi ya jingina kansa dake masa ciwo jikin seat batareda ya amsaminba.
Nima sai ban sake magana ba, Na nad'e yaran sosai a showal dukda glasses d'in duk a rufema suke, driver dai nata tuk'insa, ni idan son samunema Na kwanta, Dan barci nakeji sosai, jiya bamuyi wani barcin kirkiba anata hirar bankwana, muna kwanciya babu dad'ewa innaro tafara tashinmu mu shirya.
Seat d'in gaba Na kalla, tunanin maida yaran can yazomin, nakuwa d'aukesu d'ai-d'ai ina maidawa, tunda suna cikin kayan sanyi, kuma barcinsu sukesha, nima ai saina huta ko.
Zamewa nayi Na kwanta tareda d'ora kaina a cinyarsa, ido kad'an ya bud'e ya kalleni da mamaki, “Ina yaran?” ya fad'a yana kallona.
Da hannu Na nuna masa gaban motar, “Amma ai zasu takura a can?”.
A shagwa6e nace, “ALLAH bazasu takuraba, barci nakeji har kaina yafara ciwo”.
Kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru, Dan bayason yawan maganar saboda kansa ciwo yake sosai. Nima ban sake cewa komaiba Na gyara kwanciyata ina lumshe ido, hannunsa ya d'ora a jikina daganan motar ta d'auki shiru, Dan barci tuni yayi awon gaba dani, shima a hakan barcin ya kwasheshi.

Bamu kuma sanin halin da ake cikiba saida tafiya tai nisa sosai, yara suka farka suna k'ananun kuka, shine ya fara farkawa, ya bud'e ido a hankali bakinsa d'auke da addu'a, agogon hannunsa yafara kallo, sannan ya maida kaina danabi dukna kanainayeshi, yad'an murmusa yana janye gyalen jallabiyar jikina daya rufe rabin fuskata, barcina nake hankali kwance, shi saima yaga Na k'ara k'yau a hakan. Kukan yaran daya fara k'arfine ya sakashi dawowa hayyacinsa, ya shafa fuskarta a hankali yana kiran sunanta.
Munaya batada nauyin barci dama, idanma aka cika surutu a kusa da ita takan farka, tad'anyi mik'a tana bud'e ido, hannunsa nakan fuskata ya zubamin idanu, ni saima kunya ta kamani, naja gyalen Na rufe ina tashi zaune. Murmushi yad'anyi yana fad'in “Duk kin samin ciwon jiki”.
Fuskata Na bud'e ina tura baki kad'an da kallon kaina, ina naga nauyin dazan saka masa ciwon jikin?.
Fahimtar abinda nakeyi dayayne ya sashi cewa, “kina kokwanto ne?”.
Nace, “sosaima”. Nai maganar ina d'akko yaran.
Yanzuma kar6ar biyu yayi, Na dungure kan Abadurrahman ina fad'in, “kun ishi mutane da k'ananun kuka, nima yunwar nakeji ai”.
Galadima dake kallonmu cikeda sha'awa yay murmushi mai sauti dahar ya bayyana hak'oransa a waje, amma baice komaiba.
A nutse Na shayar dasu su duka d'aya bayan d'aya.

Munzo cikin babban wani gari Galadima ya Umarci driver da cewar yasama mana wajen abinci mai k'yau, Dan karsu Aiyaan suji yunwa.
Cikeda girmamawa driver ya amsa masa.
Abinka da driver manya, dukkan wani wajen girma sun sanshi, kansa tsaye ya kaimu wani had'ad'd'en wajen cin abinci, saima kayi gaddamar ba'a Niger d'in yakeba, duk fitowa mukayi, amma Galadima yak'i fita, saida su Abba suka shige sannan, Ayusher da feena sukazo kar6ar yaran, Dan can Yaa Fadeel da Laraba sun kar6i Ameen da Meenal.
Mik'ama Ayusher Abadurrahman nayi, Na bud'e inda Galadima yake Na rank'wafo ina d'aukar Abadurraheem, shima mik'ama Feena nayi, itama Amaturrahman Na d'akkota Na rik'e, ganin ko motsi baiyiba nace, “yalla6ai yadai?”.
'Dan yatsinamin fuska yay saikace wani mace. Na kuma rank'wafowa ina d'ora hannuna saman goshinsa, tausayinsa ya kamani, dan kan akwai zafi alamar bayajin dad'i. Nace, “Sorry my king”.
Idonsa yad'an lumshe yana murmushi.
Nakuma cewa “ka daure muje ciki, sai a nemi maganin mura”.
Nanma baice komaiba, saida yaja wasu seconds sannan ya ziro k'afa, nad'an matsa baya nabashi hanya ya fito.
A raina dai ina jinjina jinin masu mulki, k'asaita da izza tarigada tazama jinin jikinsu, babu yanda za'ayi ka iya rabasu dashi.
Da hannu yayma Drivers d'in alamar su shiga suma.

Mune k'arshe. Shiga.
ALLAH Sarki Yaa Marwan, harya tanadar mana wajen zama, gaskiya babu k'arya wajen yayi tsari, mukam mund'an shiga daga lungu kad'an, su Abba basa ganinmu bama ganinsu, inaga hakanne yasaka Galadima d'an sakewa yaci abincin, dukda bama wani Na kirki yaciba, Dana nuna damuwa saiya kalleni.
“Karfa ki damu, inhar ina mura banajin dad'in komai, haka take wahal dani”.
Cikeda tausayawa Na masa sannu, nima duk saina kasa cin abincin.
Spoon d'in hannuna ya kar6a, da kansa ya koma bani abaki, dukda marairaice masan da nayi akan Na k'oshi bai saurareniba, baikumayi maganaba, saida ya tabbatar Na k'oshi da gaske sannan ya barni.

Kowa yaci ya k'oshi yay nak Alhmdllh, muka fito da ledojin kayan mak'ulashen da Yaa Marwan shima ya saima kowa, dan kud'in abincin Galadima ya biya.

Dagananfa muka damk'i hanya babu sanya, dan burinmu mu Isa Nigeria a yau, wancan zuwanma dan bamusan inda muka dosa bane.
Aikam dai tafiya tayi riba, dan salla kawai muka tsaya mukayi, Azuhur da la'asar muka had'a muka kuma damk'ar Hanya, bayan magrib muka shigo Nigeria, nanma mun tsaya munyi sallar Magrib da isha'i, daganan muka cigaba, abinci ma sai saya akayi kowa yaci a hanya.
Yanzunma dai Galadima baici Na kirkiba, dan bayajin dad'in bakinsa, da gaske Mura batai masa da wasa kam, dam duk bashida wani sukuni.
Sai wajen 2am muka shiga namu garin, zuwa lokacin kowa yayi ligif, ga gari tsitt, sai motoci jefi-jefi Na matafiya irinmu, saikuma manyan motoci masu d'aukar kaya.
Gidanmu aka nufa, saida aka fara saukemu harsu mama Rabi'a anan, Fadeel Yaa Marwan da Abbansu ne kawai aka nufi gida dasu su kam, shima Galadima masarauta aka juya dashi, sama-sama mukayi sallama Na fita, tausayinsa Na cin zuciyata, yana buk'atar kulawar matarshi matuk'a, amma ya zanyi.

Duk y'an gidanmu sunyi barci, sai tsirarune suka fito y'anson ganin dami mukazo?. To babuma abinda aka fitar daga mota, kowa dagashi sai handbag d'insa ya fita.
Koda muka shiga kowa wajen kwanciya ya nema, dukda sashen namu yad'anyi k'ura, amma bamu damuba, Inda zamu kwanta kawai muka karkad'e.

*****************

Galadima yana shiga gida ruwan zafi ya had'a yay wanka, kozai sami sauk'in ciwon da jikinsa ke masa, yad'anji dama-dama kam, ya nema kayan barci masu kauri ya saka, dan muma dai nand'in cikin sanyin ake, gadonsa ya haye, ya shige bargo yana sauke numfashi da k'yar, babu dad'ewa barci yay awon gaba dashi.

*Washe gari*

Bamu tashiba sai kusan 12, su innarmu ne kawai suka tashi da wuri, y'an gidanmu anata shigowa musu sannu da zuwa, kowacce jikinta saiya fara zanyi, dan yanda muka dawo 6ul-6ul damu kad'ay ya Isa basu amsar muna cikin k'oshin lafiya, kuma inda mukaje wajene mai daraja.
Duk wadda ta fita saita nufi gidan Innaro da nufin mata sannu da zuwa, ammafa dason jiyo gulma.

Tab hajiya Innaro mai abin mamaki, zama tayi tiryan-turyan tana basu labarin garar arzik'i da wacece Inna. Ta rik'e ha6a tana tafa hannaye da fad'in “Yo Niko koda naji wannan halin dattako Na Ai'sha, Ashe jinin sarautace , shiyyasa duk shirmenkunan bata shigarsa, maganama saitaso ta kula maiyinta, duk shirme ya rufe mana idanu bamu fahimtaba, lallai yau naga tushen arzik'i Na gaskiya ba hayeba, nayarda da masu iya magana dakance duk Wanda yace shine to bashi bane wlhy.....”.
Innaro dai taita zuba musu labari babu k'ak'k'autawa, sukam sun kume motsin kirki summa kasa, a yanda su inna suka dawo kawai ya Isa ya tabbatar musu da gaskiyar innaro d'in.

Tunaninsu bai kuma birkicewa ba saida aka shiga fiddo tsaraba daga motocin da muka dawo dasu, kowacce saita shige d'aki ta koma lek'e ta window itada y'ay'anta🤣.
Zarah da siyama da har yanzu suna gida, a sanyaye suka shigo gaida su inna, duksun rame sunyi duhu, dan kowacce tana son mijinta, amma gidajensu sun gagaresu komawa, dan bayan tafiyar su Munubiya saiga takardun saki daga mazajensu su duka.
Duk munyi mamakin yanda sukai laushi da fita hayyacinsu, amma bamuce komaiba, muka tarbesu kamar yanda muka saba a ko yaushe. Nidai wlhy duksai tausayinsa yama kamani.
Su Ayusher sukai shirin tafiya gida, iya abinda zasu iya d'auka suka had'a Yaa Marwan yazo ya kwashesu..
Suna tafiya nima sai hankalina ya koma ga mijina, waya Na d'auka Na kirashi dan naji Yaya jikinsa, harta yanke bai d'agaba, nakuma kira dai...
Chapter 43 · 0% Book details