← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 66

Sashe 41

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari aka gudanar da bikin tarbarmu, Wanda yay matuk'ar k'ayatar damu da sakamu farinciki, munga al'adun daba namuba, su innarmu ansha shiga ta alfarma suda su Abba, Saiga su Abbanmu da sarauta, wai tunda sune mazajensu innarmu anbasu wata sarauta domin girmamawa agaresu, hakama Yaa Marwan, dad'i tamkar zai kashemu, aiko munsha hotuna da nuniya wajen jama'a.
Gashi ni banda ma sakewa, saboda yanzu banason hayaniya mai tsanani kusa dani, da za'ayi kid'a ma sai wajen nabari tilas, dama hayaniyar mutane da surutai harta fara sakani ciwon kai.
Da Galadima ya kirama sai Munubiya ce ta kar6a, ta sanar masa halin danake ciki, duk saiya rikice, yaringa rok'on Munubiya ta kula masa dani sosai.

****************

Kwanakinmu 7 da zuwa cif mukaga anata hidimomi a masarautar, kasa shiru mukai saida muka tambayi dalili, su Badeera suka sanar masa wai wani d'an Sarki ne zaizo dana k'asarmu ta Nigeria.
Mamaki ya kamani, to wanene wannan? Dan nidai ko a jiya munyi waya da gadima kuma baicemin zaizoba, hasalima yana India, tunanin bashi bane ya sakani kauda zancen araina muka cigaba da hidimominmu.
Yanzu kam a masarautar babu inda bamu saniba, Dan kulum su Badeera cikin zagayawa damu suke, har cikin gari saida muka fita sau wajen uku, gaskiya Agadaz tanada abubuwan k'ayatarwa da Tarihi, hotuna kam ai yinsu muke tamkar babu gobe.

Su Hajiya Innaro dai kam an nutsu, ni harma tausayi tafara bani wlhy, Dan haka muka rage iskancin da muke mata, yanda ake bata kulawa da girmamata kawai a masarautar ya isheta kunyar abinda ta aikata, (lallai babu Abu mafi dad'i irin ka sakama mai jifanka da sharri da tarin alkairi) wlhy har Abadan bazai sake sukuniba a gabanka saboda d'unbin kunya da nadama dazata addabi zuciyarsa, Dan kullum zai kasance cikin tsarguwa da tsangwamar kansane. Kunga dai yanda innaro ta kasance a yau.😏🤷🏻‍♀

Sai wajen la'asar sakaliya labari yazo mana wai d'an Sarki nan ya iso, bushe-bushen algaitu irin nasu kawai dake tashi ya tabbatar mana da lallai yazo d'in.
Cikin mu babu Wanda ya maida hankali akan lamarin, danni kwance ma nake Na kifa Absurraheem saman cikina yana barci, Feena da Deejahma suna gefena zauna suna kallon hotunan da mukayo ayawon jiya da muka fita, su Munubiya kam Na tsakar d'akin suna hira da sauran y'ammatan, Ayusher nama Zuhuriyya kitso, Wanda anayi yana warwarewa saboda gashin akwai santsi, sai wata dabara sukeyi a k'arshen kitson.
Bayan sallar isha'i saiga mama Rabi'a ta shigo d'akin da muke, duk muka gaidata, fuskarta d'auke da Murmushi ta kalleni ina canjama Amaturrahman kayan barci dan an musu wanka. “Munaya ta shi kiyi wanka yanzunan”.
Da mamaki nace, “wanka kuma mama? Lafiya kuwa?”.
“Lafiya lau, kedai ta shi kiyi, bama Maryamu ta k'arasa shirya Amaturrahman d'in”.
Nidai duk al'ajabi ya kasheni, ganin duk yawan y'ammatan dake d'akin ba'ace kowa yatashi yay wankaba saini, suma dai Kansu kallon mamaki sukemin ni da mama Rabi'a d'in. Hannuna ta kama muka fice zuwa wani d'akin.

Cikin bayin gidan d'aya ta had'amin ruwan wanka, dama tunda mukazo komai yimanashi akeyi. Mama Rabi'a tacemin “Kinutsu kiyi wanka mai k'yau wlhy, inba hakaba dakaina zan canja miki wani”.
Mamaki kuma kasheni yayi, nadai nutsu nayi wankan fiyema da yanda take buk'ata, ga ruwa nata tashin mayataccen k'amshi, dan wannan masarauta sunsan sirrin k'amshi kam, akwanaki 7 d'inan har turare yafara zaunawa a jikinmu saboda bala'in yawan amfani dashi, motsi kad'an sai ahau tiraraki da turarurruka iri-iri.
Nafito Na iske Ayusher Na jirana wai zatamin kwalliya, zanyi gardama saiga mama Rabi'a ta shigi, dole Na zauna akamin simple, nikaina nasan nayi k'yau, kayan da aka bani Na sanya saida Na kallesu Na sake kallo, dan lafayarsuce ta buzaye datasha wani d'inki mai k'ayatarwa, aka d'oramin bak'ar alk'yabba tamkar ta larabawa, tasha golden d'in aiki daga sama har k'asa, a bud'e take dawasu igiyoyi biyu, can sama dakuma tsakkiya. Nidai narasa bakin magana, dan turarema har neman hawarmin kai ya fara, kai nidai a raina nafara tunanin ko tsafi za'ayi danine. Sai gulma muke da idanu ni da Ayusher, dan babu damar yi a fili ga mama Rabi'a a d'akin.
Hannuna ta kama muka fito, aka had'ani da bayi uku nabin bayana, sai ta hud'un a gabana tana mana jagora, masarautar tayi tsit babu yawan hayaniya, saboda d'an Karen sanyi da ake zubawa, kowa ya shige ciki sai d'ai-d'aiku dake kai kawo.
Wani sashe dakecan gefe shima mai k'yau muka Isa, munsha zuwa ta wajen amma bamu ta6a shiga cikiba, Baiwar tayi sallama, dukda ba'a amsaba ta shiga, mukuma muka cigaba dabin bayanta.
K'aton falone mai tarin k'awa da tsari, Wanda ke tabbatar maka a gidan sarauta kake, ganinai duksun durk'ushe k'asa, Na bisu da kallon mamaki sannan Na kalli inda suke fuskanta...................✍🏻

*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻

[8/22, 8:29 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*

*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*

*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_

*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣4⃣

.................A hakimce yake kishingid'e saman lallausan dardumar data k'awata k'yawun falon, Rabin jikinsa duk akan tum-tum, gabansa da butar shayi ta buzayen asali, gakuma mitsi-mitsin kofuna saman wani k'yak'yk'yawan tire k'arami, gefe Bowl ne Na glass cikeda kayan itatuwa, saikuma kwanika 4 dake rufe Wanda bansan minene a cikiba, gefensa yaransa ne duka ukun kwance duk nad'e cikin showals, yanda nake binsa da kallon mamaki haka shima yake bina da kallon mamakin canjawa da k'ayatarwar da shigar ta k'aramin.
Sudai bayinnan sun lalla6a tuni sun fice abinsu.
Cikin d'age gira ya sakarmin Murmushi yana min nuni da hannu wai nazo gareshi.
Tamkar mai tsoron a kamata tana satar naman miya haka nake tafiya garesa, dan kallon da yakemin ba k'aramin haddasamin kasala da sanyin jiki yayiba.
Na k'arasa gabansa ina zama a kasalance, zaman danayi ya kalla, ya min jinjina irinta saraki👍🏻.
Kallon kaina nayi nima, dan banga minayi ba dahar za'amin wannan jinjinar.
Cikeda k'asaitarnan tasa yace, “Kallon fa?”.
Ajiyar zuciya Na sauke, dan narasa bakin magana, ya tashi zaune sosai yana janye tum-tum d'in dake a tsakkiyarmu, ya matso jikina sosai yana wani shinshinata da lumshe idanu, murya a sark'e yace, “Amaryar Muhammad Sameer wannan k'amshin yayifa 100%”.
Yanda yay maganar a dokin wuyana saida tsigar jikina ta tashi, cikin magana d'ai-d'ai nace, “Wai dama Kaine d'an Sarki da aketama wannan shirin?”.
Murmushi ya saki, ya matsar da bakinsa saitin kunnena a wani salo yace, “koban cancantaba ne?”.
Kaina Na girgiza masa alamar a'a.
Ya kuma shigewa jikina sosai, “Wai miya kashe bakin tsiwarne haka yau?”.
“Mamaki mana”.
“To miye abin mamakin? Ni d'in ko zuwan nawa?”.
Nace, “Duka”.
Wani miskilin murmushi ya saki, ya lalubo hannuna dake 6oye cikin alk'yabbar ya saka nashi ciki yana murzawa da wani salo, juyawa nayi Na kallesa muka had'a ido, idanunsa duksun wani k'ank'ance, ya sark'e nawa yanda nakasa koda motsi balle samun damar janyewa, akan la66ansa yace, “I miss you”.
“Humm” nafad'a nima a hankali INA kauda kaina gefe.
Hannunsa ya sak'alo ta bayan wuyana ya matso da fuskata dab da tashi, numfashinmu Na had'uwa waje d'aya, kasa jurar kallonsa nayi saina lumshe idonuna Na bamik'a masa wuya 100%, yayi duk yanda yakeso, dan da gaske missing d'in nawa mai yawa Nagano cikin kwayoyin idanunsa.

Da sauri yarima Issufu da Yaa Marwan suka koma baya, dan dama suna tare da shine aka aiko kiransu, sunata sauri su dawo dan karsu barshi cikin kad'aici, ashema yana tare da matarsa. Sunyi sallama takai 6 jin ba'a amsaba sukayi tunanin kobaijibane, shiyyasa suka shigo Kansu tsaye, dan basuyi zaton samunsa da kowaba, ALLAH ma ya sosu k'aramin gani sukayi🤭😂.

Yareema Isaufu da mamaki ya kasheshi ya kalli Yaa Marwan yana fad'in, “wai dama duk yarannan masu kama da juna sunada aure?”.
Murmushi Yaa Marwan yayi, ya dafa kafad'arsa, “biyu sunada aure mana, su tagwayene, ina auren Hasaanar, shikuma Yarima Sameer yana auren Hussaina, d'ayar itace bata da aure, dan nasan Ayusher kake nufi, tunda Feena bata kaisu girma da shekaruba, amma miyasa kamin wannan tambayar?”.
Yareema Issufu yay k'aramar dariya yana cewa “zan sanar maka amma ba yanzunba, saida safe Na banbancesu”.
Komai Yaa Marwan baiceba yay murmushi kawai suka cigaba da tafiya.
Chapter 41 · 0% Book details