← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 66

Sashe 40

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A 6angaren Galadima kam suma Alhmdllh, Abie yanata samun kulawa ta musamman ga Dr Erfan Fahad, Dan da iya k'yautatawar yakema Abie abu, kodan sanayyar dake tsakaninsa da Galadima wadda saidaga baya ya tuna wanene Erfan Fahad d'in, sunyi karatun addni wajen malami d'aya a time d'in bazasu wuci shekaru 9 ba, har lokacin da suka kai 17years shi Erfan Fahad iyayensa suka d'aukesa daga wajen Sheaik Mu'azzam Abdul-aziz, saboda zasu koma Kashmir a lokacin, dama aikine yakawo mahaifinsa India, tundaga nan basu sake had'uwa ba sai yanzun, lokacinda Sheaik Mu'azzam Abdul-aziz ya rasu shi Dr Erfan Fahad yazo gaisuwa, amma basu had'u da Galadima ba, a sanann shikuma yana k'asarJapan karatun shekara 2 daya kaisa, saida ya dawonema yakejin rasuwar malamin nasu, gaisuwa kawai yaje yayma iyalansa yaymusu alk'airi mai yawa.
A kullum Dr Erfan Fahad da Galadima cikin hirar tuna baya suke, balle da Dr Erfan Fahad ya d'ebo masa wasu hotunansu suka gani, nanfa suka kuma rikicewa da labari, suna hirar sauran abokansu da rashinjin da sukayi a makarantar.

Rabonsa da jin Munaya tun randa suka tafi, suna gab da shiga Niger sukayi waya, daga nan basu sake ba, sosai yake kewarta, duk ya damu, kwana biyu kawai dabai jitaba, har Dr Erfan Fahad saida ya fahimci yana cikin damuwa, Dan Dr Akash da Dr Ajay sun koma India kan aikinsu.
Amma Galadima yace masa babu komai, Dr Erfan Fahad bai yardaba, Dan haka ya damesa da tambaya, doledai Galadima ya sanar masa.
Aiko ya tasashi gaba da tsokanar wai yace dai soyayya kecin zuciyarsa ba wani abuba, to yarage damuwa, yasan itama laila d'in nacan cikin damuwar rashinsa.
Murmushi kawai Galadima yayi, Dan yafara sabawa da yawan tsokana irinta Dr Erfan Fahad, akoda yaushe yanzu suna tare, idan kin gansu ba tareba to yashiga aikine, yakanbar Galadima a Office, Dan har yanzu ba'a shiga wajen Abie, awata na'ura suka sakashi dake taimakama ga66ansa motsawa a hankali, saboda allurar da ake masa duk bayan awanni 12, a koda yaushe saidai Galadima ya lek'ashi ta Window idonsa yakan cika da hawaye, Dan lallai ALLAH ne kawai zaima Abie hisabi dasu Alhaji Lawan tanderu bawai Alk'alin duniyaba.
Su Momma sunso zuwa amma Galadima ya dakatar dasu, Dan bayason suzo su d'orama Dr Erfan Fahad nauyi, shikuma maganar gaskiya a tsakaninnan aljihunsa yayi k'asa, damma akwai madogara Na business kala-kala da koyaya asiri zai rufu.

Yauma suna asibitin, Dr Erfan Fahad ya shiga wani aiki, Galadima ne kawai zaune a office d'in cikin k'ananun kaya, yana zaune a kujerun dake cikin office d'in daga can gefe, k'afarsa hard'e bisa teble d'in tsakkiyar kujerun, ya d'ora laptop yanata aikin Company daya zamana saita nan, harma Na Hukumarsu dake nan Nigeria, wato (DSS). Idonsa Na saye cikin medical eyeglasses mai haske, sosai yayi zurfi a aikin, alokacinne kiran Munaya ya shigo wayarsa, amma yay burus yacigaba da aikin tamkarma baijiba harta yanke, kuma kira Munaya tayi, nanma yak'i d'auka.
Bata gajiba tacigaba da damunsa, cikeda jin haushi ya kalli wayar yana jan tsaki, mamaki ya kamashi ganin Number d'in dabai saniba, baima ta6a ganiba, yanzunma harta yanke bai d'aukaba.
Idon Munaya harya fara tara kwalla.
Cikeda Damuwa takuma kira, shikuma ya d'auka cikeda k'uluwar an dameshi.
Kawai saita sakar masa kuka.
Kasa motsawa yayi, Ya kuma kasa magana, Munaya tace, “Ni zakama wulak'anci ko? Shikenan sai anjima”.
Zaiyi magana k'itt ta yanke wayar. Kansa ya dafe yana fad'in “O ALLAH my mata bansan ke baceba”. Kiranta yayi amma tak'i d'auka harta tsinke, saida yakuma kira sannan ta d'aga, itama tana gab da katsewar, harma ya fidda ran bazata d'agaba.
“Shikenan kin rama ko?”. Ya fad'a a hankali cikin taushin murya da nuna kulawa a gareta.
Munaya ta d'an tura baki kamar tana ganinsa, amma batace komaiba.
Ya murmusa yana ajiye lap-top d'in ya sauke k'afafunsa. “Kinga bara Na kiraki video call, gara naga dai ma ya kika koma”.
Bai jira cewata ba ya yanke wayar.
Dad'i sosai ya kamani da jin k'arin k'aunarsa, Wanda ban ta6a tunanin kalloma zan isheshiba shine yake damuwa idan Na damu..........
Kiran ya katsemin tunani, Na d'aga amma saina saka hannuna Na kare idona, bakina da rabin hancina kawai yake gani.
“Haba my mata please mana, ko saina miki kukane?”.
bakina nad'an motsa da turashi gaba kad'an alamar eh.
“Humm kinga duk randa Na kama bakinnan zai min bayani dalla-dallane”.
Cire hannuna nai babu shiri ina kallonsa, ya kashemin ido d'aya.
Nai k'asa da idona ina fad'in, “ALLAH ya shiryaka, nidai babu ruwana”.
K'asaitaccen murmushinsa yayi yana gyara zamansa, “Anya kina missing d'ina kuwa?”.
Fuska Na marairaice masa kalar tausayi, nace, “sosaima kuwa”.
“uhmyim to inga idon”.
d'an kwalina naja Na rufe fusakata ina dariya.
Yace, “Nifa wannan kunyar a ringa ajiyemin ita gefe sai ina buk'atarta, ina my children's?”.
“Nayi k'yautarsu”. Nayi maganar ina bud'e fuska.
“Dakin birgeni, kinga danazo tun anan saina tanajin wasu abin cikin kwan”.
Share zancen nai kamar ban fahimtaba, nace, “yaushene zakazo to?”.
“Kina missing d'inane?”.
“Sosaima ALLAH kuwa”.
Dad'i ya kamashi, cikin lumshe idanu yace, “ina tafe soon, sai kunyi kwana 5 sannan zazo nayi kwana 1 mu dawo Nigeria ki tattaro kayanki miyo gaba”.
“To ALLAH ya kaimu, ya jikin Abiena?”.
“Abienki nata samun kulawa Alhmdllh, muna kuma hango nasara sosai, Dan Abokina yasan aikinsa sosai ”.
“Alhmdllh, ALLAH yasa iyakar wahalarce tazo, muma muga Abie d'inmu Na tafiya da k'afafunsa, yadawo k'asarsa ta haihuwa inda mak'iya basa son zamansa, bak'inciki dukya kashe shegu”.
“ALLAH ya tabbatar my Queen, guntsamin mana, Yaya kuka iske Niger d'in?”.
Cikin tsumud'i nace, “karkad'e kunnenka kasha labari yalla6ai”.
“Na karkad'e da k'yau yalla6iya”.
Cikin Nutsuwa Munaya ta shiga zayyane masa komai, tun yana al'ajabi yakoma mamaki, Yakoma tausayi, ya koma murna da nuna tsantsar farinciki.
Yace, “ALLAH Sarki innarmu, Ashe ita jinin girmace, shiyyasa ta kasance mai dattako, lallai yanzu Na fahimci ina kika kwaso halinnan naki, dama nadad'e ina tunanin anya baki shafi jinin masu sarauta ba, jan
da son girma yayi yawa”.
“kai ba'ace naka yayi yawaba sai nawa?”.
Murmusa yay yana shafa girarsa d'aya. Yace, “toni minayi kuma?”.
“Ai idan zan lissafo maka sai kud'inka sun k'are ban gamaba”.
“Sheri dai zakimin kawai yalla6iya, inasu Abdurrahman wai?”.
“Tab ai wad'annan inba yunwa sukejiba ganin su wahala yakemin ni kaina, ai saikazo kawai kadai sha mamaki, duk yanda zan musalta maka a yanzu hasashe kawai zakayi”.
“Ina tafe insha ALLAH, koma Dan Na d'akko matata Na gudo, amma yanzu kam dole saina nema izinin shigowa”.
“Meyasa?”.
“Kinta6a ganin jinin mulki yashiga wata masarauta bada neman izini ba? Hakan tilas ne, yak'e-yak'en dake faruwa a masarautu yakawo wannan sharad'in, zuwa yanzu kuma yazama babbar Al'ada mai k'yau”.
“Lallai, to yanzu tayaya zaka nemi izinin?”.
“Zaki gani bari lokaci dai yayi. Yanzu mizan samu Na rage zafi?”.
Cikin salon narkar dashi Munaya ta juya idanu tana fad'in “Mikakeso?”.
“Gaba d'ayanki wlhy”. Ya fad'a cikin marairaicewa.
“Indai nice dama takace ai Muhammad Sameer”.
Lumshe idanunsa yayi yana cije lips, yaune ranar farko daya ta6ajin sunansa a bakinta, “Please sake fad'a naji”.
“Mid'in?”. ‘Nafad'a cikin d'an waro idanu’.
Ya wani marairaicemin kamar k'aramin yaro, yana k'ank'ance idanunsa da suka sauya kala. Yace, “Sunana”.
Yanda yay maganar cikin sanyi da kasala saida tsigar jikina ta tashi, kamar yanda ya buk'ata nakuma maimaita masa a kasalance.
“My Queen ina k'aunarki da yawa, zan tabbatar miki hakan randa kika dawo gareni, jinake duk duniya nafi sauran maza morewa da samun nutsatstsiyar mace mai tarin baiwa da tarbiyya, Har abada Na mallaka miki Muhammad Sameer da komai nashi, ki yi yanda kikeso dani my Heartbeat”.
Kwallan farin ciki ya cikamin ido. Nace, “My king tukwiycin wannan k'yauta sai ina kusa dakai, Dan tsadarta yakai tsada, tukwiycinta mai girman darajane, kuma zan mik'ashine gamai daraja, dolene yakasance a waje mai daraja, ba Kaine kaima sauran maza zarraba, nice, ni Munaya ninaima sauran mata fintinkau wajen yin dace da samunka a matsayin miji, Uban y'ay'ana, Masoyina, cikon farincikina, I love you so more irin wadda bata k'arewa d'innan har a Aljanna....”
“Na gode Uwargidana a Duniya da Aljanna, kece shugabar Matan Muhammad Sameer anan duniya, kuma kece a Aljanna insha ALLAH, ALLAH yayi miki albarka wadda bata yankewa keda gudan jinina”.
Hannuna naima kisses uku Na hura masa.
Ya wani lumshe idanu yana dafe k'irjinsa alamar sak'ona ya isa.
Wata dariya mai ida kashe jiki murus nayi masa, aiko saiya zame ya kwanta kawai cikin kujerar yana kifa wayar a k'irjinsa ya lumshe ido.
Nakuma bashi wani kiss d'in mai k'arar sauti, babu shiri ya d'auki wayar da Sauri saidai kitt Na yanke kiran ina dariya.
Nima zubewa nayi a gadon k'irjinna Na dukan goma-goma, dayasan tsiyar da Na shirya masa dabai yarda dani hakaba😂🤭.
Dariya kawai da tafi naji akaina, nai saurin bud'e ido, sainaga Ayusher, Munubiya, da Feena akaina. Hararsu nayi ina juya fuska can gefe da fad'in, “y'an sa ido, Uwarmiye aka biyoni?”.
Ayusher tace, “Yo k'arshen munafurci da cika baki mukazo gani, yaudai munga abinda ake 6oye mana da cika baki”. Suka kwashe da dariya suna tafawa.
Banza namusu.
Feena tace, “Aini wlhy dama tun a asibiti nace muku gayunnanfa sun d'inke, wuya tayi wuya SIRRIN ZUCIYA ya fito fili, sun gama cika bakin da jan ajin, shi k'asaita da mulki, ita jan aji, Ashe harda Mulkin bamu saniba. Kai kusamana wak'a muyi murnan K'ulluwar k'auna”.
Ayusher ta saka wak'a a waya suka ko dage suna tik'ar rawa..
Dariya suka bani wlhy, nace, “y'an iska kwadaiji da munafurcinku wlhy, nan gani nan bari dai Munafuncin su innaro”..
Aiko mi zamuyi inba dariyaba gaba d'ayanmu, nikaina Innaro d'ince kawai tazomin abaki ban shiryaba.

**************************
Chapter 40 · 0% Book details