← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 66

Sashe 35

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shigowa su Ahmad suka k'araso gareshi suna gaidashi da jajanta masa.
Cikin k'arfin hali yace, “baku tafi gida bane?”.
Sarkin mota dake tsaye kusa dasu yace, “Ranka ya dad'e ai Ahmad shine ya taimakeni nakawo camera d'in kotu d'azun”.
Da mamaki Galadima ya kalli Ahmad yana nunashi da d'an yatsa alamar kaid'in?.
Murmushi Ahmad yayi yana gyara tsayuwa. yace, “Uncle bayan fitowa daga kotune za'a hutunnan sai naji wani yaron su Abbana yana waya akan atare su Aunty a kar6a Camera d'in, dan basa buk'atar ta k'araso Court d'in, to hakan danaji shine Na k'arasa garesa Na bigi cikinsa akan zancen”.
“nake cemasa zamuje ni da su Ahakam muma a kwato Camera d'in damu, so hakan dayaji saiya d'auka da gaske tare nake dasu, shine yabani key d'in mashin. Ina ajiye driver d'inka, sai mukazo asibiti ni da Yassar muka sanarma da Uncle d'ina, shine ya bimu da Ambulance har wajen da abun ya faru muka d'akkosu”.
Galadima ya kamo hannun Ahmad ya rungumesa, yayma su Yassar dake kallonsu alamar suma suzo, cike da farin ciki suma duk sukazo jikinsa.

__________________________

Hankalin mai martaba a matuk'ar tashe yake, jin wai dan kawai yayi mulki wasu suka bada gudunmawa domin durk'usar da d'an uwansa, “hazbinallahu wa ni'imal wakil” wannan wace iriyar masiface hakan?.
Sai safa da marwa yakeyi a bedroom d'insa, idanunsa Na kwarar da hawayen tausayin d'an uwansa da Galadima, ALLAH Sarki mahaifiyarsa, yadad'e yana zarginta akan ciwon d'an uwansa, Ashe babu hannunta a ciki, son zuciyar mahaifinta ne, Wanda a yanzu haka tsufa ya kamashi sosai. Waya ya d'auka ya kira Abba hayatuddeen danyaji wane hali d'an d'an uwansa yake cikine? Dan yayi tsumayen shigowarsu masarautar amma yaji shiru.
Bugu biyu Abba Hayatudden ya d'aga. Mai martaba ya tambayeshi suna inane?.
Abba hayatudden ya amsa masa da vewar gasu a cikin asibiti, Dan mutanen su Alhaji Mansur sun saka an tare matar galadima a hanya itada Nuridden yayin kawo Camera Court.
Kasa magana mai martaba yayi, saboda jin kuma wani sabon zaluncin, Wanda suka aikata baya baima ishesuba kenan.
Abba Hayatudden ma bai kuma cewa komaiba saboda yasan ran yayan nasa ya 6aci.

Mama Fulani kanta yau cikin damuwa take, bata ta6a tunanin mahaifinta zai iya aikata hakanba, dukda tsantsar son datake da burin y'ay'anta suyi mulki bazataso duk'usar da Saifudden akan hakanba, shekaru 26 bawan ALLAH Na kwance yana jiyya tamkar gawa, banbancinsa da gawar fitar numfashi, wannan wane irin son zuciyane su jinin sarauta sukeyi? Shikenan saboda sarauta sai aita halaka juna? “Ni Marawuyya wannan wane irin burine mai cutar da imani.......”

Lallai zato zunubine koda ya zama gaskiya😢, kiyi hak'uri mama Fulani munata zarginki Ashe ba haka bane🤔🤦🏻‍♀.

.............................★

A gidansu Munaya ma hankalinsu a matuk'ar tashe yake, gasu Abdurraheem nata kuka, dan tunda Munaya tabar gidan suke kuka, kukansu ya tada hankalin Munubiya dasu Inna sosai, lokacin da aka harbi Munaya bak'aramar fad'uwa gaban Munubiya tayiba, ta mik'e a zabure tana dafe k'irji, number Munaya tashiga nema, dan taji a jikinta wani mummunan abu ya faru da y'ar uwarta.

Lokacin da labarin abinda ya faru da Munayar ya iso garesu mafi yawan jama'ar gidan saida suka koka, Dady kuma ya hana kowa zuwa asibitin, saisu mazan kawai sukai shirin zuwa, gashi basusan wane asibitin bane.

__________________________

Iyalan su waziri hankalinsu a matuk'ar tashe yake, hakama su Alhaji Sageer, ga duniya tanata ALLAH wadai dasu, gaba d'aya yau kowacce kafar yad'a labarai da social media maganar kenan, su kansu sauran manyan kowa ya shiga hankalinsa, dan lamarin yayi matuk'ar girgozasu, suna yabama basirar Galadima matuk'a, gashi yabi ta hanyar da babu Wanda yata6a zaton zata 6ille masa yayi nasara, inhar za'a iya samun irinsa a yau, to lallai wataran za'a samo Wanda ya fisa ma.

....................★

Yanda masarautar su Galadima take a harmutse gameda wannan lamari haka tasu papi ma ta gama harmutsewa, dan lamarin ba'a cewa komai, cin amanar da waziransu sukayi yayi matuk'ar girgiza masarautun, bakajin komai sai gutsiri tsomar bayi da dogarai, harma da manyan gidan ba'a barsu a bayaba.
Tashin hankalin da papi da inno suke ciki ba'a magana, ga Sauban ya tasasu gaba yanata kukan son zuwa yaga halin da Munaya da Nuren suke ciki, harma da yayansa.

Dukda an hana fad'ama Su Momma amma saida labarin yakai musu, aranar aka nemama Aunty Mimi ticket d'in tahowa Nigeria, Samha nata kuka itada Khaleel zasu biyota, amma bata sauraresuba, dan hankalinta a matuk'ar tashe yake.

............................★

Doctor da kansa ya fito yayma Galadima iso cikin office nashi, bayan sun zauna doctor ya kalli Galadima cikin alamun damuwa, yace, “ranka ya dad'e da farko dai ina mai baka hak'uri akan zaluncinsu mijin y'ar uwata, ALLAH yay maka babban samako da sayya agaresu”.
Murmuahi kawai Galadima yayi amma baice komaiba.
Doctor ya kuma gyara zama yana fad'in “Alhmdllh jikin namijin babu wata babbar matsala, yanzuma mun saka masa alurar barcine cikin ruwan danya huta sosai yasamu nutsuwa, daya farka Normal zaku gansa. Ita kuma akwai harbi da akai mata a hannu, amma Alhadullh mun samu nasarar cire harsashin, tafin hannunta kuma shima anji mata ciwo, dan yatsunta Na tsakkiyama duk sun samu karaya, amma shima an gyarashi, maganar gaskiya ranka ya dad'e bazan 6oye makaba, tasamu buguwa akai, dan ALLAH ne ya tak'aita batasamu wata babbar Matsala a brain ba, saidai ahalin yanzu dukkan wani motsi mai k'arar sauti bama buk'atarsa kusa da ita, insha ALLAH inhar za'a kiyaye cikin kwanaki kad'an komai zai iya dai-daita, takuma dawo normal kamarma komai bai faruba, zamu bata dukkan kulawar daya dace da izinin Ubangiji. daganan har kwanaki uku zuwa hud'u zata kasance a halin barci, dan hakanne kawai zai girmama nutsuwar da muke buk'atar ta samu d'in, kai kad'aine kuma zaka ringa shiga d'akin”.
Galadima ya lumshe idonsa tausayin Munaya da yaransu Na kuma mamaye jinin jikinsa da kowanne ga6a, da k'yar ya iya bud'e baki yace, “Doctor! Kana ganin zaku bata dukkan kulawa?. Sannan tanada yara jinjirai, yaya kenan za'ayi?”.
Insha ALLAH ALLAH ranka ya dad'e, dan munada kayan aiki a asibitin mu, dakuma kwararrun likitocin da zasu iya aiki a kowacce k'asa, maganar yara inaga inhar akwai mai kulawa dasu acigaba da basu madara har ALLAH yasa ta farfad'o, saboda mu yanzu matsalarmu kawai shine motsin dazai iya farkar da ita ko wanda zaiyi tasiri cikin brain nata”.
Gyad'a kai kawai Galadima yayi, yabama doctor hannu sukayi musabaha, daganan ya fito.

Kuma ficewa yayi daga cikin asibitin, Sarkin mota yay saurin biyo bayansa, da hannu yamasa alamar yashiga mota suje.
Dukda sarkin mota baisan inda suka nufaba haka ya amsa cikin girmamawa.
Saida suka fara tafiya ya sanar masa inda zasuje.
yana nufi gidansu Munaya dan yaga halin da yaransa suke ciki.

Munubiya da kanta ta fito masa dasu itada Ayusher, tausayin su ya kamashi matuk'a, musamman ma Munubiya, dan tayi wujiga-wujiga.
Cikin k'arfin hali yace, “kiyi hak'uri Sister, muyi musu addu'a ita kad'ai suke buk'ata a wajenmu, yanzu yaza'ayi dasu Amaturrahman? Dan nakula kamarma yunwa sukeji?”. ‘yay maganar yana kallon yaran da sukayi barcin wahala bayan sun gama shan kuka’.
Share hawaye Munubiya tayi. tace, “Yakamata a nemo musu madara, idan kuma Na shayar dasu to shikenan”.
Galadima ya jinjina kansa yana fad'in “Bamusan hikimar da ALLAH ya 6oyeba a gaba, karmuyi ganganci, bara kawai a nemo madarar, dan dolene su kwana anan, ita ba'ason mata hayaniya yanzun, maybe ma harnan da wasu kwanaki, saboda ta bugu a kanta, kuskuren kwakwkwaran motsi zai iya shafar brain nata”.
Munubiya takuma fashewa da kukan tausayin y'ar uwarta, hakama Ayusher, shi kansa Galadima dauriya kawai yakeyi, danma ya 6oye idanunsa cikin eyeglasses shiyyasa basa ganin nasa tsantsar damuwar.
Muftahu ya kira ya sanar masa a samoma su Abdurraheem Madarar da zasu ringa sha.

Daga nan gidan yabaro akan cewar Muftahu zai kawo, yakuma rok'esu akan Abdurraheem, dan ba'ason yacika yawan kuka.

A gurguje please😏😜

___________________________

*BAYAN KWANAKI UKU*

A kwanaki ukunnan fad'ar tashin hankalin da bayin ALLAH suke ciki 6ata lokacine, musamman ma Galadima da har wata uwar rama yayi lokaci d'aya, hakama Munubiya da innarsu, Nuren dai ya farka tun washe garin faruwar lamarin, kuma jikinsa Alhmdllh yanata murmurewa, saidai tausayin d'an uwansa daya addabi ransa.
Ko abinci Galadima bayasonci, sai Aunty Mimi ta turkesa tana bashi abaki, shima baifi yay lauma biyarba yace ya k'oshi. tayi-tayi kuma ya kafe, garama idan tea ne, shima sai an had'a da lallashi, babu abinda ke addabar ransa irin damuwar Munaya da yaransa, sukansu duksun rame, danma suna samun tsantsar kulawane ta kowanne fanni.
Papi yazo ya dubasu, hakama su mom da iyayen su Nuren d'in da y'an uwansa, mai martaba ma da daddare yazo cikin 6adda kama ya dubasu.
Mama Fulani ma kullum saitazo, a matan Sarki gimbiya Zulfah Ce kawai batazoba, Dan kunyama ta hanata walwala gaba d'aya a masarautar, Mai martaba kuwa ya hanata hanyar ganinsa gaba d'aya itada y'ay'anta, sai matawalle kawai daya nuna damuwa akan abinda kakansu da mahaifiyarsu suka bada gudunmawa wajen aikatawa wan mahaifinsa, sanan yay ALLAH wadai akan son zuciyarsu, koda yaushe yana tare da Galadima da Muftahu a asibitin, da wata buk'ata ta taso kafin Galadima yayi shi yayita.

A koda yaushe Momma cikin kira take taji yaya jikinsu Munaya, koda wasa ba'a sanarma Abie komaiba, Dan ana ganin cigaba da haske game da jikinsa sosai, ba'a fatan wani abinda zai maido da hannun agogo baya game da ciwon nasa.
Addu'oi kam sosai aka duk'ufa yinsu game da Munaya, wadda har yanzu Galadima ne kawai keda alhakin shiga ya dubata, shima sau d'aya a rana kawai, yau dai duk ake saka ran farkowarta, Dan an dakata damata dukkan wata allura dake sakata barci, saidai kuma har dare babu wani bayani.
Zasu tayar da hankalinsu doctor yace suyi hak'uri, maybe zuwa dare ko safiyar gobe ta farka d'in, danba a sume takeba, barcine kawai da sune suka sakata ta hanyar mata allurar.
Badan hankalin nasu ya kwantaba sukai shirun, har lokacin barinsu asibitin yayi babu wani bayani game da farkawar tata.

*Washe gari*.
Chapter 35 · 0% Book details