Sashe 52
Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Itama Innaro na kirata namata ya jiki, daganan muka gaisa da gwaggo Safiyya da aunty Habiba.
Na kuma kira Munubiya, sosai mukasha hira, take kuma bani labarin auren Aunty Salamah dayazo kamar ha6o. Tace, “Alhajinan dai dayayta naci wanda muke cema Cingom Alhaji dai shine mijin”.
“Oni rayuwa, Sweetheart kinga hikimar Ubangiji ko, idan yazo muyita masa iskanci har ita aunty salamah d'in Ashe dai shine mijin, gaskiya ya cancanci ta auresa, wajen shekaru biyarfa bawan ALLAH nan baita6a gajiyawaba”.
“Wlhy kuwa Sweetheart, son gaskiya kenan ai, ga Ayusher nan anata soyewa itada Hamma Youseeff, duk wannan shan k'amshin nasa ya mace mata, Yaa Fadeel ma in fad'a miki shida Badeerah Ashe sun k'ulle”.
“Dan ALLAH da gaske ko wasa?”.
Cikin Dariya Munu tace, “Wlhy kuwa, waike bak'ya waya da kowama kenan?”.
“Wlhy ba haka bane kemakinsan d'an tsakaninan damuwar data hanani sukuni, amma yau dolene na kirasu nasha kanu, shegiya Ayusher bara itama na kirata, dukda kud'ina sun kusa k'arewa, a gaidamin da Sweetness babies d'ina da Yaa Marwan inya dawo”.
“Zasuji insh ALLAH, asha amarci lafiya, aidai kulamin da yara kar soyayya tasa abarminsu su rame”.
Kafim nayi magana ta yanke kiran.
Dariya kawai nayi ina girgiza kai, alokacinne Samha ta shigo.
“Ah lallai aunty gimbiya yau Uncle Sam ya 6oye mana ke, Momma Ce tace yau bazaki sakko bane?”.
“Dan ALLAH da gaske?”. Nai maganar cikin waro idanu.
Dariya ta sanya, “Wlhy kuwa da gaske nake”.
“Ni munaya naga idi, ALLAH kunya nakeji”.
“Kam kunyafa aunty gimbiya, to miye najin kunyar? Wlhy ALLAH yabani miji irin Uncle Sam a gabanki zan mak'alk'ale abina”.
Duka nakai mata ta kauce tana dariya.
**************
Cikeda jin kunyar su Momma na sakko k'asan, amma saisukayi tamkar basusan minike mawaba, tun ina sunne-sunnen kai hardai na warware nasaki jikina kamar yanda nasaba.
Momma da Aunty Mimi sunji dad'in haka, a zukatansu suna mana addu'ar d'orewar zaman lafiya nahar Abadan.................✍🏻
_Inaga sai Monday zakujini, kuyi fatan nama kammala gaba d'aya😅🤝🏻👌_
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭👏🏻
[8/22, 8:36 AM] Aysha Galadima: *_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITERS ASSO...._*
*_♦RAINA KAMA...!!♦_*
_(Kaga gayya)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BOOK 3_* 👉🏻2⃣9⃣
.................Gaba d'aya sun kasa yin breakfast, suna cikin zaman jigum-jigum suka jiyo bud'e gate da shigowar mota. Samha ta fita da hanzarinta danson ganin wanene, fitowar tata tayi dai-dai da fitowar Galadima daga cikin mota fuskarsa d'auke da wani irin k'ayataccen murmushi daya fidda sirrin k'yawunsa.
Da gudu ta taho garesa, yakan mata fad'a akan son rungumarsa ko Sauban amma yau saigashi ya bud'e mata hannu dakansa tazo ta shige jikinsa.
Ihun murnartace tasaka su Momma fitowa da hanzari suma
Ganin Galadima ai sai duk sukayo kansa itada aunty Mimi, itadai munaya gefe ta tsaya tana sharar hawayen farin ciki.
Abie dake kallonsu daga cikin mota ya saki murmushi yana share hawaye, yana k'asa d'aya da iyalansa amma bai ta6a sanin muhallinsu ba sai yau, dukda bai shigaba gidan yamasa k'yau.
Galadima ya ture Samha daga jikinsa ya rungume Momma da aunty Mimi yana sakin wani irin kuka daya matuk'ar tada hankalinsu.
Da sauri suka d'agosa hankali tashe suna tambayarsa mike faruwa? Kodai ALLAH yayima Abie rasuwane?.
Cikin kuka da dariya yace kowa ya rufe idonsa .
Babu musu sukabi Umarninsa, har Munaya dake gefe.
Yace, “kun tabbatar kowa ya rufe?”.
A tare suka amsa masa da eh.
Ya murmusa da goge sauran hawayensa sannan ya juya ga motar ya bud'e, hannun Abie ya kama da taimakonsa ya fito rik'eda sandarsa mai k'yau dazata dinga taimaka masa wajen tafiya, Dan har yanzu tafiyar batai kwariba.
Saida Abie ya jingina jikin Mota ya tsaya da k'yau sannan Galadima yace, “Kowa ya bud'e idonsa”.
Har rige-rigen bud'ewa suke.
Akusan tare Aunty Mimi da Munaya da Samba suka kwalla k'ara, Momma kam sai tayi luuu sai gata a k'asa kawai ta sume.
Abie da Galadima dasu Munaya duk kanta sukai suna kiran sunanta, shima Abie ya tuzgud'e zai fad'i, Dr Ajay daya kawosu yay hanzari rik'esa yana fad'in “A sannu dai Sir, k'afafunka basukai k'warin wannan hanzarinba”.
Da gudu Munaya takoma ciki sai gata da ruwa, ta zuba a hannu tana shafama Momma, da k'arfi takawo Numfashi.
Bin yaran nata tayi da kallo tana fad'in “mafarki nakeyi ko yarana? Nasan irin mafarkin dana sabane dama, ba takawa Na bane ba”.
Cikin dariya da kuka Aunty Mimi tace, “Wlhy shine Momma, shine agabanki ba mafarki kikeba, Momma Abie d'inmune wlhy tallahi kinji Na rantse”.
Zumbur Momma ta tashi daga jikin Aunty Mimi, Abie dake tsaye har yanzu bisa taimakon su Galadima ya murmusa yana fad'in “Zeenah ki cire kokwanto, da gaske wannan Saifudden d'inkine ba Wanda yasaba zuwa miki a mafarkiba kinji”.
Tasowa Momma tayi garesa, ta shafa fuskarsa domin tabbatarwa, takuma binsa da kallo tundaga sama har k'asa, lallai da gaske wannan Saifudden d'intane bana mafarkiba, Ai sai kawai ta rungumeshi babu kunya ko tunawa dasu Galadima a wajen.
Sai duk'ar da Kansu duk sukai suna Murmushi.
Gaba d'ayansu kowanne soyake ya nuna ajintarsa ga Abie domin nuna masa gamsuwa da farincikin samun lafiyarsa, aka kawo masa y'an Uku ya had'a duka ya rungume yana maijin k'aunarsu har cikin jininsa, Khaleel ma yana nanik'e dashi.
Munaya dai nadaga gefe bata zak'eba.
Idon Abie ya sauka akanta, Murmushi yamata yana fad'in “'Diyata zo mana”.
Takowa tai cikeda jin kunya tazo gabansa ta durk'usa, cikin girmamawa ta gaisheshi da masa addu'ar k'arin samun lafiya mai d'orewa.
Ya amsa yana mai k'ara jin farin cikin kadancewarta suruka agaresa uwa ga jikokinsa.
Galadima ma yakasa d'auke ido daga gareta, sai yaga tamasa y'ar rama tsakanin jiya da yau.
Breakfast d'in dabai samu shigaba d'azun aka baje domin ci, amma shi Abie kasancewar an hanashi cin wasu Abubuwan Kuku yay azamar tanada masa Wanda yake buk'ata.
Daka gansu kasan suna tareda matsanancin farin ciki .
Koda suka kammala Galadima ya taimakawa Abie shiga d'akin Momma, shima ya haye sama shida matarsa.
Tun'a falo ya d'auketa cak yana juyi da ita cikin hajijiya, babu shiri Munaya tahau k'yalk'yata dariya da k'an k'ame wuyansa da hannayensa tana cusa kanta cikin k'irjinsa.
A haka suka k'arasa cikin bedroom, ya jefa abarsa saman gado yabita tareda jan bargo yay musu runfa.
An hanani ganin abinda akeyi🤨, sauk'inma inada mijin Nima😏🙄.
Farin cikin da wannan ahali suka tsinci Kansu wlhy 6ata lokacine, Momma kam sai ko ganinta bama ayi🤭🙈.
A gurguke please🥺😔.
Walwala da farin cikin wannan gida tadawo kam, ga nutsuwa mai saka zukata samun damar yawan ibada, ko yaushe suna manne da Abie, sai idan time d'in hutunsa ne yayi, Galadima yayma kowa gargad'i akan sanarda tashin Abie, burinsa kowa yaga abin mamaki, 100% Momma ta yarda da shawararsa, hakama Abie.
Yanzu dai kam sun yanke shawarar Isa k'asarsu ta haihuwa ranar salla k'arama, zasu azumi na kwanaki 20 a india, su biya Saudiyya suyi Umrah ta kwana goma su isa Nigeria a ranar salla ayi idi dasu.
Gaba d'aya azumi saura kwanaki 6 a farashi.
******************
*_AZUMI_*
Alhmdllh kowanne musulmi yau ya tashi da azumin watan Ramadan mai mai albarka, saidai irin masu ak'idar saimun gani da suka kasance k'alilan acikin wasu k'asashe irin namu Na yankin Africa.
Duk da shayarwa hakan bai hana ni zama cikin jerin masuyiba, dan raino dai bani nakeba, tsakanina da yarannan idan sunji yunwa, koyaushe suna tare dasu Momma, sunyi 6ul-6ul dasu tamkar y'an watanni 6, amma har yanzu suna cikin wata Na hud'une ma kacal.
Tunda safe Galadima ya fice, Na d'an tashi nai gyaran saman sannan Na sakko, yau babu maganar shiga kitchen, Dan tunda Abie ya dawo nakoma nike mishi girkin abinda zaici, wataranma nakan had'a da namu muma, babu abinda zan cema wad'annan mutane sai godiya, soyayya dai mai cike da k'auna ina samunta a garesu, ni da mijina kam ai sai hamdala, yana tattalina da tarairayata, saidai d'an sa6ani Na yau da gobe Wanda baka Isa raba ma'autara da Shiba, shima kuwa bai wuce wasu awanni muke shiryawa ba, inko Momma ta lura ma takan kiramu tamana Nasiha, hakama Aunty Mimi.
A falo Na iske Abie daga can gefen falon inda wasu kujeru biyu suke da kanta mai d'aukeda buks Na karatu, tundaga kan Na addini har zuwa Na makaranta dadai sauransu, zaune yake yana nazarin wani littafi da banga sunansa ba saboda tazarar dake a tsakaninmu.
Sai Samha dake falon kwance a kujera tana kallon film, zaman gyalena Na gyara, Na taka a nutse zuwa garesa, saida Na durk'usa a gabansa sanann nace “Barka da safiya Abie”.
'Dago k'yawawan idanunsa da Galadima ya gado yay yana kallona, ya zare medical eyeglasses d'in idonsa yana Murmushi, “'Diyata barka dai, kin tashi lafiya?”.
Kaina a k'asa ina murnushi nace, “Lafiya lau Abie, ya ibada da k'arin k'arfin jiki?”.
“Alhmdllh d'iyata, ai jiki kam sai godiyar Ubangiji, Muhammad fa?”.
“Ya fita tunda safe”. Na fad'a cikin kuma duk'ar dakai.
Murmushi Abie yayi, ya maida eyeglasses d'insa yana fad'in “ALLAH ya dawo dashi lafiya to”.
A saman la66a Na amsa, sannan Na mik'e da k'yar zuwa d'akin Momma.
Abie ya bita kallo zuciyarsa cikeda k'aunar wannan yarinya, irinta yaytama y'ay'ansa addu'ar samu amatsayin abokiyar rayuwa, Alhmdlh Ubangiji ya amsa masa, saura Sauban kuma.
Nidai nashiga Na gaida Momma, Na iske tanama su Amaturrahman shiri, da alama wanka tamusu, Na gaisheta cikeda girmamawa kamar yanda Na saba, itama ta amsamin da kulawa tareda d'an jana da hira tamkar yanda ta saba, nad'an jima a d'akin, harta fito tabarni Na gyarashi tsaf kamar yanda nakeyi tun bayan dawowarmu, Dan tuni Na dakatar da Samha ni nakeyi.
Na fito da nufin shiga Na gaida aunty Mimi saina isketa tama fito falo, anan muka gaisa Na zauna muka d'ora da hira tamkar yanda muka saba, mafi yawama firar ta Sauban Ce, Dan kowa yayi missing d'insa, yace azumi da kwana 3 zai zo sai salla zai koma, Galadima bai hanashiba, dukda yana tareda tattalar kud'i a tsakaninnan saboda sun masa k'aranci, to saima papi ya d'auki nauyin zuwan Na Sauban da komawarsa.
Mund'an ja lokaci Muna hira barci yafara rinjayata, mik'ewa nayi Na gudu sama, nad'an rage kayan jikina Na haye gado sai barci.