← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 66

Sashe 22

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dak'ilesu da Galadima yayi ta hanyar kashe komai ya fusatasu suda William d'in, suna kuma kunna Computers d'in komai naciki ya goge, wannan Abu ya rikita William matuk'a, gashidai yagama proud d'in shi kwarone kuma bak'in fata d'an Africa ya masa kwaf d'aya, dukkan fushinsu saiya dawo kan Abba.
Ana cikin haka saiga Alhaji halluru da sauran tawagar y'an group d'in, wad'anda sai yanzune suka samu k'arasowa, da farko Abba ya zata Alhaji Halluru taimakonsa yazoyi, saida yaji suna masa izgilanci sannan ya fahimci komai, cikin tsantsar mamaki yace, “Alhaji Halliru da kanka?”.
Ta6e baki Alhaji Halluru yayi, yace, “zaka bani takarar Governor ne?”.
Abba yay murmushin takaici yana fad'in “Tir da kai Halluru, wannan ai jahilcine, ALLAH shikad'aine ke bada mulki ga Wanda yaso, akuma lokacin dayaso,, yanzu kana nufin duk shekarun daka d'auka a jikina kai dama da manufa kake tare dani?”.
Alhaji Halluru ya kuma ta6e baki yana murmushin mugunta, yace, “Alhaji Auwal kenan, ai bama zaka tabbatar da hakanba sai y'ay'anka da kansu sun d'akko min camera sun kawo, sannan mukuma kasheka a gabansu babu yanda zasuyi, yanzu haka suna gida, zuwa anjima kad'an kuma camera zatazo garemu”.
Zufa ta fara karyoma Abba a dukkan sassan jikinsa, danjin za'ayi amfani da gudan jininsa wajen tarwatsa abinda yad'au shekaru yana rik'ewa amana, k'ala baice da Alhaji Halluru ba, su kuma sai kiraye-kirayen waya suke Na had'ama Galadima tarko.🤦🏻‍♀
Abba ba tausayin kansa yakejiba, tausayin Galadima yakeji matuk'ar tik'ewa, Dan ganin rai kusan 15 kowa k'iyayyarsa akansa take da muguntarsa...

★★★★★★★★★★

Tunda Galadima ya shigo bai zaunaba, saida yagama had'a komai dazai buk'ata, yabama sarkin mota yakai cikin motar dazaiyi amfani da ita, alwala yay yafita salla massalacin masarautar, bai yarda sun had'u da Sarki ba, yay fitowarsa, koda ya dawo saiyasha magani ya kwanta, kaikace bashida wata matsalane, babu dad'ewa kuwa barci yay gaba dashi.
Bai tashiba saida aka kira sallar la'asar, nanma massalacin yaje, bayan ya dawo yay kiran Momma ta video call, duk suna asibitin hardasu Samha, d'aya bayan d'aya ya gaisa da kowa, Samha harda kukanta tanason zuwa Nigeria, ita missing nasu takeyi sosai. Galadima yace a'a ba yanzu ba, tashi tai tabar gaban lap-top d'in tana kuka, Galadima ya girgiza kai kawai.
Yasha hirarsa da Abie sosai, saboda Alhamdullah jikinsa saidai godiyar ALLAH, dama ciwo keshiga farat d'aya, sauk'i kam sai a hankaki. Addu'a kuma takobin muminice ako yaushe.
Bayan ya gama waya dasu Momma Sir Isa ya kirashi, ya tabbatar masa da komaifa is done, Dan ansami kowanne acikinsu, yanzu haka wasu sunma iso.
Galadima yay murmushi yana shafa fuskarsa. Yace, “Nama canja shawara, zamu canja gidan da zamu ajiyesu da, yanzu akwai wani gida annan kusada plaza d'ina, nagama magana da Saleem komai yayi ready, Ameer duk yakaisu can, insha ALLAH ana idar da sallar Isha'i zan fito”.
Sir Isa yace, hakan yayi, dan acikin yaran nasuma za'a iya samun munafukai, tunda duk sunsan gidan daza'a ajiyesun, yanzu kuwa shi Ameer kad'ai zaisan da wannan.

Galadima ya kira Munaya, dama tun d'azun kiran nashi take jira, ta d'aga tana shigewa cikin bayin d'akinsu Dan kar wani yaji.
Galadima yace, “haryanzu kukan?”.
“a'a” ta fad'a cikin share hawaye.
Yad'an murmusa kawai yana fad'in, “Akwai bak'in da sukazo gidanku?”.
“A'a babu Wanda yazo, sai Siyama da Zarah”.
Galadima yay murmushin gefen baki yana cigaba da danna lap-top, hasashensa yazama gaskiya kenan, gyaran murya yad'anyi kad'an yana fad'in, “kina jina?”.
Munaya tace, “eh”.
“Ki saka ido akan d'akin Abba, motsin kowa yazama akan idonki koda cikin matansane, ko yayyenki maza, Dan za'a iya yin amfani da kowa, inda da dama ma key d'in d'akin yazama a hannunki”.
Munaya tayi d'an jimm alamar tunani, zuwa can tace, “babu damuwa, zan gwada hakan insha ALLAH, amma kunji labarin Abban?”.
“Karki damu, insha ALLAH Abba zai dawo gida, addu'a muke buk'ata”.
Munaya ta jinjina masa kai tamkar tana ganinsa, ta share hawayenta dake zubowa.

Yana yanke wayar nafito, cikin dabara nashiga d'akin innarmu, key d'in d'akin Abba Na d'akko, dukda nasan kowama yana dashi cikin matansa, fitowa nayi naje cikin dabara da sauri-sauri Na saka key d'in cikin k'ofa d'in, cikin addu'ar Neman nasarar kozai karye a ciki, amma ko gezo baiyiba, hannuna sai azabar zogi yake, danma nayi amfani da wani abin sarrafa k'arfene, cirewa nayi nakoma ciki kozan samo wani k'aramin k'arfe dazai iya Shiga, saida nasha wahala nanma sosai kafin Na samo, gashi duk a tsorace nake kar wani ya fahimci abinda nakeyi, cikin kafar makullin Na turashi, Alhmdllh nasamu ya shige, nagwada saka key amma yak'i Shiga, nasan babu yanda za'ayi wani key ya sake shiga wajen harsai mai gyara yazo, tunda kuma Abba bayanan ai babu buk'atar hakan, Dan duk wanda zai buk'aci shiga yanzu lallai akwai manufa. Dukda haka saida nasamo kwad'o nakuma sakawa sannan hankalina yad'an kwanta.

**************************

*_9:00pm_*

Fitowarsa kenan daga wanka baiko tsaya shafa mai ba ya hau shiri cikin wandon da riga k'ananu, fuskarnan babu alamar walwala tattare dashi, komai yana yinsane cikin karsashin fushi da damuwa, ya kammala tsaf yad'an saka turare.
A k'ofar sashensa ya iske Nuren yana jiransa, sauran Hadeemansa dabasuyi barciba suka shiga masa barka da fitowa, kansa kawai ya d'aga musu, d'aya daga ciki ya bud'e masa bayan motar, amma sai bai shigaba ya d'aga masa hannu ya bud'e gaba da kansa ya Shiga, Nuren yay murmushi kawai, yasan yau mazan a wuya suke.
Shiga yay shima mazaunin driver yaja suka fice.

Gidane matsakaici sabo, dagani ko dad'ewa da gama gininsa ba'ayiba, saidai anzuba komai Na amfanin gida, ahaka suke buk'atar badashi haya. Dan haka da saleem yanemi hayar suka bashi kai tsaye.
Suna isowa Muftahu ma ya iso d'auke da su Harun, Alhj Darma, Farhat d'iyar Minister sai mal. Saminu driver Alhaji balala, kusan shima yana hannunsu har yanzun.
Ameer ya mik'e da Sauri yana salute d'in Galadima, hararsa yayi, Ameer yay murmushi yana yin k'asa da kansa. Cikin girmamawa yace, “Ranka ya dad'e wad'annan sune phones d'in yaran da tarkacen kayamsu”.
Jinjina kai Galadima yayi, hannunsa duk biyu goye a bayansa yana zagaya table d'in da aka zube wayoyi, da lap-tops, iPad's dukna wad'anda aka kawo d'in, ya kalli Ameer cikeda k'asaitarnan tasa yace, “Suna INA?”.
“Duk suna sama ranka ya dad'e, Dan inaga yakamata kazauna acan, danka ke ganin motsin kowa daga waje, dukda ansaka cctv a ko ina na wajen”.
Galadima ya kad'a kai alamar gamsuwa da bayanin Ameer.
Cikin takunsa na izza da lafiya ya nufi saman benen dake gidan, Muftahu da Nuren suka kalli Ameer cikin neman k'arin bayani, murmushi yamusu, yana tattare wayoyin yabi bayan Galadima dasu.
A k'aramin falon k'asan ya iskeshi tsaye yanabin komai da kallo, Ameer yace, “ranka ya dad'e yazamuyi da wad'annan phones d'in nasu?”.
Galadima yad'an ciza lips yana kallon Ameer, yace, “inasu Nuren d'in?”.
“Suna k'asa”.
Galadima baice komaiba, hakan da yayi ya saka Ameer fahimta su shigo kenan, saiya ajiye abin hannunsa ya sauka k'asan Dan kiransu.
Saleem yafito daga wani d'aki ya taso k'eyar wani matashin Saurayi k'yak'yk'yawa, daka gansa kasan hutu yagama ratsashi, kallo d'aya Galadima yamasa ya d'auke kansa, Saleem yaja kujerar dining d'aya ya zaunar dashi, sannan yasaka igiyar daya d'auka ya d'auresa jikin kujerar, saurayin sai zaginsa yakeyi, amma Saleem ko kulashi baiyiba, saida yagama tsaf sannan ya kalli Galadima, wata alama yamasa da ido.
Sai kawai naga Saleem ya d'auke saurayi da wani shegen mari, Wanda yasaka su Nuren dake shigowa jan birki suna kallon Saleem, bakin saurayi bai mutuba, Dan haka Saleem yakuma zuba masa wani har hancinsa Na fashewa, azaba ta sakashi kama bakinsa yay shiru yana huci da had'iye hawaye.
Galadima ya ta6e baki yana d'age kafad'a. Alamar sudai suka sani.
Haka Saleem yayta fiddosu d'aya bayan d'aya harsu 7, maza 5 mata 2, sai Farhat cikon ta takwas, amma su matan babu wacce aka d'aure, mazanma idan har bakayi gardama ba ba'a ta6asu.
Saleem yagama jerasu reras gaban Galadima daya d'ora k'afa d'aya kan d'aya cikin kujera yana danna lap-top hankali kwance.
Muftahu da Nuren dai sunyi mutuwar zaune, basu ta6a tunanin Galadima zaibi wannan hanyarba, gashi yak'i basu wata fuska dazasu masa magana ko tambaya.
Saleem da Ameer suka kamo Harun shima aka d'aureshi a gefe ba cikin yaranba, shi baima cikin hayyacinsa, Dan su Nuren saida suka shak'a masa Abu, Alhj Darma da m. Saminu ne kawai ba'a d'aureba, suma dai aka kawosu gabansa aka zube.
Galadima ya d'ago yana kallon su Muftahu dasuka Gaza barin kallonsa, cikin ta6e baki yace, “kallonfa?”.
Ajiyar zuciya suka saki a tare, Nuren yace, “Brother mufa bamu fahimtaba”.
Lips yad'an ciza yana ta6e baki da fad'in “Duk wannan dalla-dalla d'in da akai muku?”.
Shiru sukayi Dan inhar a fahimtarsuce dai yau sunzama Kidnappers Na gaskiya kenan🤭😂.
Galadima yace, “Well, Ku ajiye zancen fahimta gefe, kuduba phones d'in su Wanda babu charge a saka, Dan zuwa safiya duk za a fara aiki dasu, daganan mai buk'atar barci yaje ya kwanta kawai, sauran aiki sai safiyar gobe”.
Babu Wanda ya iya cewa komai, dan sunsan dai Galadima bazai sakasu a had'ariba saboda son zuciya, Ameer ya fidda Chargers suka saka dukkan wayoyi ajikin caji, Dan akwai wuta.

A wannan daren Galadima ya tura sak'o ga dukkan iyayen yaran, lokacin duk sunbar wajen Abba sun koma gida, anbarsa da garadan samarinnan akan sai washe gari, Dan sun tsarama su Zarah duk yanda zasuyi.
Chapter 22 · 0% Book details