← Book details Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 66

Sashe 42

Raina Kama Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mukan bama musan sun shigoba balle fitarsu, motsawar da Abdurrahman yayi yana k'ananun kukane yasamu dai-daita, duk muka kalli inda suke.
Matsawa Galadima yayi inda suke dan sunfi kusa dashi, Ashe showal d'inne ya rufe masa hanci, ya gyara masa sannan ya juyo ya kalleni yana murmushi.
K'asa nayi da kaina nima ina murmushin. Nace, “Ina yini? Kazo lafiya?”.
“Kin fita daga mamakin yanzu dai kenan?”. Yay maganar tamkar bayaso.
Nanma Murmusawa nayi ina 6oye fuskata.
“Humm”. Ya fad'a yana gyara zama.
“Kayannan sun miki k'yau gaskiya my mata”.
Nad'an d'ago ina fad'in, “Da gaske?”.
Ido d'aya ya kashemin yana cizar lips.
Nima Na juya idanuna cikeda salo.
Har cikin ransa saida yaji wannan sak'on. Na katse masa tunanin da fad'in “Ya jikin Abie?”.
Zamansa ya gyara sosai, ya d'auki butar shayin zai zuba nai saurin d'aura hannuna akan nasa ina girgiza kai. “Aikin ai nawane yalla6ai”.
Murmusawa yayi yana sakarmin. Nima Na zuba masa fuskata d'auke da Murmushi, Na mik'a masa.
Cikin lumshe idanu yace, “Thanks”.
Kaina Na jinjina masa kawai, a nutse ya shiga bani labarin dukkan abinda ya faru, harda tsadar allurai da drugs d'in da Abie kesha, ya k'are maganar da fad'in ammafa Alhmdllh, bazan baki labarin komaiba sai kinje kinganema idonki yanda Abie yake yanzu, banta6a tafiya mai cike da nutsuwa ba irinta wannan karon, dan nasan nabaro farin ciki ne zan kuma iske farin ciki, lallai Na yarda da zancenki, HAK'URI shike bada komai, duk saurin Bawa saiya jirayi UBANGIJI, dan shine mai kowa da komai, a watanni biyu kacal da suka shud'e ganinake komai ma bazai zoba balle ya wuce, amma gashi harya zama labari, wataran muma masu bada labarin nemarmu za'ayi a rasa, mun shud'e saidai bayanmu, ALLAH ka rabamu da SON ZUCIYA, dan k'arshedai 6ACINTA, Ko'a yanzu akace babu Muhammad Sameer to naci ribar rayuwa, dan burina nason ganin mak'iyan mahaifina ya cika, Abie yasamu sauk'i, ga yarana, Na mallaki jarumar mace kamila Mumina wadda Na mallakama dukkan kaina da ZUCIYATA, To nikam minene ya ragemin kuma MATATA!?”.
'Dago idanuna dake cike da kwalla nai ina kallonsa, a hankali nace, “Sai addu'ar samun aljanna my King”.
Ya lumshe idanunsa yana murmushin daba koyaushe yake yinsaba yana min jinjina 👍🏻.
Nima na jinjina masa ina k'aramar dariya.
Muncigaba da hirarmu a tsanake cikin so da k'auna da nunama juna kulawa.
Yauma langaremin yayi saida nabashi abinci da kaina yaci, nima dai haka ya ciyar dani da kansa.
Ban bar sashenba sai wajen 12, shima su Yaa Marwan muka tausayamawa, dukda kowa da d'akinsa, falone kawai ya had'asu.
Da kansa ya d'akkomin Absurraheem da Amaturrahman, ya rakoni, aiko muna fitowa yace, “ya salam, my mata dama haka wajennan keda sanyi?”.
Cikin tausayawa Na kallesa, dan nima Na manta kayan dake jikinsa k'ananune, dan ciki akwai d'umi sosai, bama zaka tuna ana sanyiba, “kawosu kawai ka koma, kar mura ta kamaka”.
“No muje da sauri Na rakaki, dan sunmiki yawa ai”.
Har k'ofar sashen da muke ya min rakkiya, Na lek'a Na kira Wanda ke kusa danya taimaka min, Ayusher Ce ta fito itada Zuhuriyya, Na kar6esu d'ai-d'ai daga wajensa ina mik'a musu, yayinda suke gaisheshi sukuma yana amsawa da kulawa.
Suna shigewa ya jawoni jikinsa, waige-waige Na fara dan gudun kar wani ya gammu, shikam ko'a jikinsa, ya mannani da gini yana yanda yaso, kusan mintuna 2 sannan ya sakeni yana fad'in “Good night”. A hankali tare da d'agamin yatsunsa biyu.
Kasa magana nayi harya 6acema ganina, Na sauke ajiyar zuciya ina shiga ciki a sanyaye tamkar wadda tama sarki k'arya.
Duk sunyi barci, sai Ayusher da Maryamu da Zuhuriyya ne kawai ido biyu, sai bina da wani kallon tuhuma suke.
Na zauna ina fad'in, “waiku lafiya kukemin kallon har hanji?”.
Dariya suka sanyamin, Ayusher tace, “Hajiyata ina janbakin Dana Sanya miki?”.
Harara Na zuba mata nace, “oho miki sa idiniyya”. Natashi nai shigewata.
Aiko mizasuyi inba dariyaba, nima Na shige ina k'unshe tawa. Shirin barci nayi nai kwanciyata, har suka shigo suka kwantar da yaran ban kulasuba saima nayi tamkar barci nakeyi.
Dama Laraba Na iske tayi barci abinta ita tuni, Na dad'e banyi barciba, kasancewata tare da Galadima ta tsayamin arai, kai wannan Bawa akwai iya salon d'auke zuciya iri-iri, duk hanyar dazaibi ya dabaibayeki ya Sani.

Shima a 6angaren Galadima da k'yar yay barci, da badan kar ace yayi abin kunyaba da babu inda matarsa zata ta barsa, yana buk'atarta a kusadashi ainun, amma ya zaiyi, dolene ya had'iye kwad'ayinsa harsu dawo kusa dashi. Haka yayta juye-juye harya samu barci ya d'aukesa.

*_Washe gari_*

Ban samu damar ganin Galadima ba har a zuhur, dama gashi an tashi da sanyin daya hana kowa sukuni, sai a waya muka gaisa dashi, bayan Azhur aka kaimasa yaransa dai, sunsha gayu cikin kayan sanyi.

Bayan sallar la'asar mukad'an fito ni da sauran y'an uwana domin mud'ansha iska dai, saidai kowa a cikin kayan sanyi yake, ina goye da Meenal, yayinda suma sauran yaran su Badeera duk suka goyasu.
Mun shiga sashen matan sarki mun gaishesu mun fito muka had'u da su Galadima sun fito daga masaukinsu zasu shiga mota, da alama dai fita zasuyi.
Ido muka had'a dashi ya sakarmin Murmushi da d'agemin gira d'aya.
Nima murmushin namasa ina juya idanu.
Da yake d'an nesa damu suke, basu zoba muma bamu k'arasaba, suka shiga motar da aka bud'e musu. Har suka fice inabin motar da kallo.

********

Tarbar da Galadima ya samu ta girma da mutuntawa tamasa dad'i ainun, Dan shima har wata sarauta suka bashi, sun Nuna farincikinsu Na had'a jini da babbar masarauta irintasu Galadima, shima kuma yayi farincikin kasancewarsu cikin yankin ahalin matarsa, shikam bashida abun fad'a sai godiya.

Washe gari Sarki da Kansa yasa aka kirani, naje har turakarsa Na samesa, nasiha yaymin mai ratsa jiki, ya k'ara nunamin Girman daraja da Kimar masarautar su Galadima dayake gani, dukda basu had'a k'asa d'ayaba, inhar Na aikata k'yak'yk'yawa martabarsu da darajarsu Na kare, domin su ahalinane, kuma dole ace daga tsatsonsu Na fito, Na kare musu mutuncinsu, shima bada dad'ewaba zai shigo Nigeria insha ALLAH.
Cikin girmamawa da share hawaye nace, “Insha ALLAH bazan baku kunyaba, zan zama d'iya tagari mai ado da tarbiyyar ahalinta Na kowanne 6angare,, da izinin ALLAH saikunyi alfahari dani”.
“ALLAH yayi miki albarka, Yakuma tsareku da dukkannin sharri keda y'an uwanki, yabaku zaman lafiya Na har abadan a gidajen aurenku”.
Nace, “Amin Abba mun gode sosai, ALLAH ya k'ara girma”.

A gurguje please🤗

*******************

Kwanakin Galadima uku a masarautar muka fara shirin tafiya, dan mura ta kama shi ram, gashi bata masa da sauk'i, a lokacin mu kwanakinmu 10, kowa yana cike da kewar tafiyarmu, jisuke kamar karmu tafi, mu kanmu a kewar rabuwa dasu muke ji sosai, dan Sabone maiban mamaki da shak'uwa ta shiga tsakaninmu, ba k'aramar hidima suka manaba, lamarin harma yayi yawa, sukace suma insha ALLAH suna tafe garemu nan kusa. Mussamman da kowa ya fahimci alak'a mai k'arfi dake tsakanin Yareema Issifu da Ayusher, wadda kowa yake cikin tsantsar farinciki da fatan ALLAH ya tabbatar da wannan had'i.

Yanzu kam tafiyar ta canja salo, dan Munubiya da Yaa Marwan, ni da Galadima.
Innarmu da Abba, mama Rabi'a da abbansu Ayusher, Feena da Ayusher, innaro, laraba, Yaa Fadeel dasu Aryaan aka had'asu a babbar mota guda d'aya (gwauraye kenan🤭🤣).
Chapter 42 · 0% Book details