← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 38

Sashe 37

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salman zaune a gaban Sarki, Sarki yace" hukuncin baiyi ba kome?" Salman ya kara kasa dakai yace "a'a ba haka nake nufi ba sai dai ina ganin kamar hukuncin ya musu tsauri. "
Sarki yai murmushi yace " mutanen da sukaso yin kisa? Da kuma hukuncin neman matar wani? Shine kake cewa d'an wannan hukuncin yai musu yawa? To ko kotu zan kaisu? Sai a banbance wanne yafi tsauri."
Dasauri Salman yace " a'a Abba masan can sai yafi tsauri."
Sarki yace " karka wani damu da wannan, ka maida hankalinka akan karatunka, inka gama kazo ka amshi mahaifinka."
Salman yai shiru.....
Hakan yasa Sarki yace " yaushe zaku fara jarabawa?"
Salman yace " saura sati d'aya."
Sarki yace " good gwara ku gama kafin lokacin da likitan nan zai iso."

Salman yai murmushi tare da cewa " amma Abba taron nad'in daza'amin a bari sai nagama ganin likitan." Sarki ya d'aga kai yace " hakan ma is a good idea."
Sunyi shiru kafin Salman yace "bari inkoma Abba, sai da safe."
Sarki ya amsa mai, nan ya mike yai waje.

Mutane sai tayashi murna suke, shidai tafiyarsa kawai yake ba wanda ya amsawa, b'angarensa ya nufa, Salma na zaune a falo duk da ba kallo takeyi ba amma ta kurama tv ido, hankalinta nakan abinda hanne tace mata wai anba Salman yarima mai jiran gado, batama san sanda Salman ya shigo ba ya tura kofar tare da matsowa saitin wuyanta ta baya yace " me Beauty take tunani?"
Da sauru ta juya d'an tad'an tsorata, tace "haba Prince nafa tsorata. " tai maganar cikin shagwab'a, shima kwaikwayar tata maganar yai yace " nima na tsorata" yasa mata d'ariya tad'an d'akeshi kad'an ya rike hannun tare da d'agota tayo jikinshi, hannunsa yasa a k'ugunta yace " bari mu gani ko Beauty tayi missing d'in mijinta sosai?" Yafad'a yana duba fuskarta, saurin rufe idanta tai, tace " ta ina ake gane wa?" Yace in nuna miki? Ta d'aga kai.
Batai auni ba taji bakinshi anata, sosai yau take maidamai sun shagala sosai, kafin su saki juna, ahankali suka bud'e ido tare dayima juna murmushi, Salman ya kamo hannunta yai d'aki da ita, suna shiga ya rufe kofar ya tsaya ajikin kofar, ta matso kusa dashi tace " Prince baka fad'amin. ......jawota yai yakara kai bakinsa nata, nan suka kara tsundumawa cikin shauki, nikam har yanzu ban manta da korar da Salman yamin ba hakan yasa nai sumsum sum nai waje, tare da kara rufo musu kofar.

Bayan sun gama Salman yad'au Salma ya kaita toilet tace " au toilet d'inma bazan iya zuwa ba ko me?" Salman yace "banaso a wahalar min da baby na." Tace uhmmm.....harzai fita ta riko hannunsa, ya kalleta tare da mata alamar tambaya, itama dakai ta nunamai, ya kara mata alama dakai na bai gane ba, murmushi tai tace " muyi tare, " shima murmushin yai yace "ahhhh yau naji dad'i na.

Sunyi wanka sun fito, Salma ta wuce falo tad'an zubo ma Salman abinci kad'an a plate, ita da kanta tabashi, sai daya gama yasha ruwa sannan ta maida tare da hawa kan gadon, Salman ya jawota jikinsa yace " Beauty akwai matsala fa? " ta kalleshi tace name? Nan ya sanar da ita abinda ke faruwa.

Tai shiru, kafin can tace"Allah yasa hakan ne mafi alkairi." Salman yace "Amin, amma Beauty nifa banasan harkar mulkin nan, duk abi a hana mutum sakewa, ni dake fa sai lokaci_ lokaci ni kuma banasan hakan." Gabanta ne ya fad'i tace "lokaci_ lokaci? Muna gida d'ayan?" Yace" hmm yanzu in akaban me jiran gado, nasan halin mai martaba abubuwa zai d'inga sani, kinga zama na dake dole zai rago."
Salma ta kalleshi jitake kamar tai kuka, sai dai tana tunanin ko bazata ji dad'i ba dolene ta karfafama mijinta, tace " to menene baga waya ba? " tafad'a tare da nuna wayarta, yace uhmmm, ta shige jikinshi tace " bacci nake ji.
Ta dade batai barci ba, har Salman yai bacci, tai shiru tare da kura mai ido itakad'ai tasan meke ranta.

Ishaq kam da Fulani da matan Ishaq bana tunani sunyi barci dan dukansu ba wanda yake farinciki.

By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

No: 6⃣1⃣

Da safe Salman yace Salma ta shirya yakaita gida, bayan ya kaita ya gaisa dasu Abba sannan yajuya ya koma gida, sam bayasan Salma takasance a gida arana irinta yau da gidan zai kasance a hargitse.

Waziri da wasu fadawan ne sukazo suka tsaya a b'angaren Ishaq har sai da matanshi suka gama had'a kaya, kana kallan fuskokinsu kasan tabbas suna cikin bakin ciki.

Fulani kam kuka sosai tai cikin dare sai dai da safe tana zaune tana kallan bayinta na had'a mata kayanta, ita kad'ai tasan bakin cikin dake damunta ga rabuwa da d'anta, matsayinta sannan korarta da akai, kana kallanta kasan bakin ciki ne fal zuciyarta.

Salman yafito yai b'angaren Ishaq, ganin su waziri a tsatsaye yasa shi mamaki, karasawa yai suka gaisa ya tambayesu meke faruwa yagansu haka? Waziri yace" mai martaba ne ya umarcemu da mu tabbatar mun tsaya harsai Ishaq ya bar gidan nan ya shiga jirgi."
Salman ya kalli Waziri yace " haba a tunanina ko ba'a tsareshi haka ba zai tafi dakansa tunda yasan umarni ne ba shawara ba."
Jiyai Ishaq yace " Salman inasan magana dakai." Salman ya juya ya kalleshi duk ya canza a kwana d'aya, binsa yai suka d'an keb'e, Ishaq ya kalli Salman yace " Salman nasani tunda kadawo kasarnan nake muzguna ma, bana kunyar yimaka sharri ko agaban mai martaba ne, ko ba'a fad'aba nasan bai kamata inma d'an uwana haka ba, amma azahiri kai kasan duk inda gidan sarauta yake to tabbas akwai hassada, kyashi da kuma san kai a ciki, sai dai bazan nemi yafiyar ka akan sharrin dana maka ba, dan nasan ko kaine ba shakka hakan zakayi, sai dai zan nemi yafiyarka akan abu biyu, na d'aya bigeka danaso yi, sannan neman matarka danai." Yana kai nan yai ajiyar zuciya idanunsa suka cika taf da kwalla.
Salman ya kalleshi cikin tsananin tausayi, ya runtse ido sannan ya bude tare da cewa" Mubar zancen nan, dana yanzu dana da banasan adinga tunowa, abu d'aya nakeso kasa aranka, a duk inda kake kazama mai so wa d'an uwanka abinda kake sowa kanka, karka manta wannan kalmar hadisi ne sahihi, duk wani abu daya shiga tsakanina dakai nayafe ma."

Ishaq ya kalleshi cikin hawaye ya riko hannunsa cikin kuka yace "Salman please take care of my mother, nasani she is so greedy, amma tunda nake da ita bata tab'a bani shawarar neman Salma ko kad'eka ba, duk da batasanka."
Salman ya dafashi yace " karka damu I will take care of her, amma inkaje can me zakayi?"
Ishaq yace " ban mayi wannan tunanin ba."
Murmushi Salman yai yace " u have to make plan, dan karkaje kawai kace zama zakai kaga dai zama ne bama shekara ba, mayb inka tafi ba dawowa zakai ba."
Ishaq yace " nagode Salman."
Salman dakanshi yakaisu airport da azahar suka tashi, baiji dad'in yanda Sarki ya had'ema Ishaq rai ba dayaje masa sallama.

Yana dawowa gida yatadda Fulani har ta tattara ta koma, yai ajiyar zuciya yace " why am I feeling so empty? "

Salma kam taji dad'in zuwa gidan nan tayi mamakin yanda aka gyara gidan, sam bazakace gidansu ne na da ba, goggo sai janta a jiki take, sun sha hira da Abbanta, nan ya fad'a mata ai kamal ya kusa komawa kasar waje d'an yin masters d'inshi, takalli Abba tace " Abba zanma Salman magana, akwai naga mutanen da ake d'eba na scholarship a gidan Sarki, duk da dai naga 'yan uwane yawanci amma nasan in namai magana zaisa sunanshi"
Abba yace kina ganin ba matsala?
Tai dariya tace " yasan komai Abba ba wata matsala. "

Salma duk yanda taso suyi hira da umma amma abin ya gaggara hakan yasa ta hakura ta koma gun Abbanta.

Sai bayan magrib Salman yazo, sun gaisa da Abba sai daya shigo yaga gyaram gidan da akai lalai komai yayi kyau, Abba ya kara mai godiya sosai sannan yagaudasu umma da goggo, sannan suka fito.

A hanya ne Salma ta sanar dashi zancen kamal, Salman ya mata wani kallo yace " tsohuwar zuma ce ta motsa?" Dariya tai tace " ai kafi kowa sanin ba wata tsohuwar zuma araina, daga sabuwae har tsohuwar mutum d'aya kawai nasani."

Kallanta yai yad'an d'age gira yace "mutum d'ayan dai ko ba'a fad'a ba nasa nine."
Tad'an murgud'a baki tace "irin wannan confidence haka?"

Yace "kinsan nayarda dakaina, no doubt. "

Tace "ahhhh namanta ne, but what can we do? Sai kuma yakasance bakai bane Mr self-assurance?"

Salman ya kalleta yace "ban gane ba?"

Tad'an langwab'ar da kanta batace komai ba.

Salman cikin b'acin rai yai gefe da motar yai parking, ta guntse dariyata tare da maida kanta tana kallan window, Salman yasa hannu ya juyo da fuskarta, yace " Beauty magana nake." Juyowa tai ta had'e rai tace " inaji Mr self-assurance."
Yace " me kike nufi da kalamanki?"
Tace " me nake nufi kuwa?"
Yace " karkisa naje na fasama kamal baki wlh, dama inajin haushi banine first love d'inki ba kar ki kara b'atan rai."
Dariya ta kwashe dashi tace " Prince kanada abin dariya wlh, ni fa matarka ce banasan mud'inga zancen wani kamal inbadai aharkar 'yan uwan taka ba."
Yace " to ai kece kika zo min da magana abaibai."
Salma tace "uhmm nad'auka Mr Prince duk abaibai d'in danai magana zai gane, tunda dai shi ya koyamin."

Salman yace " ohhh dama saboda ni kikai? Band'auka kema kin koyaba ai."
Tace "ina zaune dakai ai dole ne."
Kunnenta yad'an ja tace ahhh, yace " ramawa nai......dariya sukai atare, nan suka wuce gida.

Yau Salman sun gama jarabawa kuma a yau akesa ran za'a kwantar dashi a asibiti danyin treatment, dan yau da yamma akesa ran zuwan Dr Bilal da matarsa Dr Ilham.
Chapter 37 · 0% Book details