Sashe 32
Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Salman ya d'ago idanunsa suka had'a ido, tace "har ka dawo?" Yace "Beauty ba inda ke miki ciwo dai ko?" Salma ta kalleshi har zatai magana ta fasa, can tace " ka fad'ama su Abba ne?" Salman yace " tun jiya nakesan sanar musu amma ina tsoron kar hankalinsu ya tashi." Tace "gwara da baka fad'aba dama banaso susani, hankali Abba tashi zaiyi."
Da yamma hajiya karama da kanta tazo ta taho dasu Salman, ba shiri suke ba hakan yasa daga gaisuwa da dubasu ba abinda yakara had'asu har suka isa.
Salman suna shiga ya kalli Salma yace "ina zuwa dear," Salma tace to.
Bangaren Fulani ya nufa, yana shiga ya wuce kilisarta, tana zaune itada Ishaq abin duniya ya damesu, jin sallamar Salman yasa suka kara shan jinin jikinsu, Salman ya shiga tare da neman guri ya zauna.
Cikin murmushinsa dabazaka tab'a gane me yake nufi ba yace" Umma tunda ke kin kasa zuwa dubo d'anki shi gashi yazo da kansa."
Fulani ta shiga in in na tace " Salman ba haka bane yanzu nake shirin fita, amma nikam ya akai hakan tafaru?" Tafad'a dan tabbatar da Salman yaga Ishaq
Salman ya kalleta yace " Hmmm to Nikaina bazance ga abinda yafaru ba, amma nikam kamar kana gun ko?" Yafad'a tare da nuna Ishaq, kan kace me? Ishaq ya rikice, jikinshi yafara rawa.
Salman yai wani murmushi yace " to ko ba kaina gani ba? Sai naga kamar kai ka taimakemu ka kaimu asibiti?"
Fulani jin haka yasa tai saurin cewa " shine mana, kasan halin Ishaq da rud'ewa, ya firgita ne ganin halin da kuka shiga."
Salman yace " ohhhh naga alama, nikam ina Farha?"
Fulani tace "tana d'akinta, hankalinta ya tashi dataji halin da kake ciki"
Salman yace "nasani ai." Yafad'a tare da mikewa, har yakai kofa yaji Fulani tace "Amma naji kamar ance kanada wani ciwo? Mai wuyar warkewa?"
Salman ya tsaya cak, tare da cizen leb'e, ya juyo inda suke ya saki murmushi yace " ba wani ciwo, kawai ganin matata tashiga wani yanayi ne yasa nima na shiga, ya akai? Kin shiga wani haline jin banida lafiya?"
Fulani tad'an tab'e baki tace "sosai ma, Alhamdulila da abun ba serious bane."
Salman ya juya batare daya mata magana ba.
D'akin farha ya isa tare da knocking, ta budemai, sai dai ganin Salman ya sa ta saki baki, Salman ya karasa d'akin yana cewa "to ko ba'ayi farin cikin ganina bane?"
Farha ta juya ciki da sauri tace "yayana, kaine?"
Yace "me? Bakiyi farin cikin ganina bane?"
Tace "inafa!!! Farin ciki yaimun yawa dai."
Salman ya karasa jikin madubi inda take yaga takardu, ya d'aga tare da cewa "badai anan kike ajiye passport d'inki ba?"
Farha tace a'a takarasa cikin jakarta tare da cirowa tace "ka ganshi nan"
Salman ya karasa ya ansa yace " banyarda adinga ajiyeshi a jaka ba, dan haka nizan ajiye miki daga yau."
Farha ta rufe ido tace " jinake kamar ka zama mijina yayana"
Salman ya buga mata wani kallo sannan ya karaso daf da ita, yace "lokacine ai."
Farha kam kamewa tai a tsaye har Salman ya fita bata sani ba, Salman na fita ya d'aga wayarsa ya kira wani friend d'insa, yace " zan kawo maka passport d'in gobe, please as soon as possible nakeso."
Ya kashe wayar tare da sakin wani murmushi, yace bazan bari ki kara canza hali ba anan garin.
Salma kam d'akinsu ta shiga gyarawa, Salman ya bud'e kofar, tana tsaye jikin gado ta juyo ta kalleshi, Salman ya karaso tare da bud'e mata hannu, murmushi tai, takaraso ta shige jikinsa, riketa yai tsam yace beauty kamar munyi wata bama d'akin ko? Tad'aga kai, yace "ahhh naji dad'in ganin mu, mu biyu, Salman ta kara shigewa jikinsa, rikota yai ya zaunar da ita kan gado, tare da mikarmata da kafarta, yace "ki d'inga zama kina hutawa sosai, karki d'inga wahalarmin da babyna."
Salma ta rangwad'ar da kai tace "Prince gyaran d'akin ma wahala ne?" Yace "eh mana."
Tace " to ai sai jikina yai tsami in haka ne."
Mikewa yai ya zauna a bayanta sannan ya kwanto ta jikinsa, yace "Beauty?" Tace "naam."
Yace " nikad'ai nasan farin cikin danake ciki."
Tace "ummm to in haka ne abani gift"
Yace "toh!! me Beauty na takeso?"
Ta juya kanta tace " exams dazakuyi this year, karka m'ika farar takarda."
Salman ya sakar mata murmushi yace "daga sanda naji kina da ciki, na d'au wannan alkwarin, bazan bari d'ana yataso yaganni coward ba."
Salma ta kai bakinta zata sumbaci kuncinsa, matsowa yai hakan yasa bakinta ya shiga nashi, tad'an d'ago ta kalleshi, hannu yasa a gefen fuskarta yakara jawota kad'an, shima ya matso, tare dakai bakinshi cikin nata, sun shagala sosai, salo suke ma juna, dukansu idanunsu a rufe, sun dade kafin su saki juna, a hankali Suka bud'e idanunsu, Salman ya had'a gushinsa danata, suka saki murmushi, tace thanks dear.........murmushi ya sake mata.
A ranta tace Allah nagode maka daka had'ani da wannan bawa naka.
Farha kam tsalle ta daka, jitake kamar ranar auransu ta zo, waya ta d'aga takira mumynta, tace "mumy bana tunanin zan dawo yanzu, maybe ma kune zaku taho, bani ba."
Mumyn tace " bangane ba"
Farha tace " kedai bari mumy, burina ya kusa cika."tafad'a tare da kashe wayar, tace "hmm wayaga idanun Salma?"
Lol.....nace har na hango....
By *Ayusher Mohd*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄
*NA AYUSHER MOHD*
No.5⃣4⃣
Salman yashirya tsaf, Salma dakanta ta d'aukomai kaya ya saka, suka fito dinning Salma ta zauna ta zubamai abinci, Salman ya kalleta yace "yauma nikad'ai zanci?" Tace "a'a tarw zamuci" yai murmushi tare da kallan su hanne, ya musu alama da hannu su fita, nan sukai baya suka fita.
Salma ta sa spoon suka faracin abincin, Salman sai kallanta yake yana murmushi, suna gamawa ta d'auko mai littafinshi da mik'amai, yace "thanks dear" tace "Allah ya bada sa'a."
Salman ya mata kiss a kumatu sannan yai waje.
Direct school ya wuce, a hanya yama Najib waya yace "nashigo, ka karaso?" Najib yace " yanzu na shigo kana ina? Naji kace akwai magana."
Salman yace mu had'u a inda muka saba zama, ya kashe wayae tare da karasawa.
Sun had'u su uku da Amir, Salman ya kallesu sannan ya kalli agoggo yace "saura 5mins a shiga lectures, let me go straight to the point, daga yanzu no more play."
Najib da Amir suka kalleshi da mamaki, sukace yarima me kake nufi? Salman ya d'aga littafin hannunsa yace " Nadaina submitting d'in blank sheet, na kusa zama uba, ba zan bari d'ana ya taso yaganni a haka ba." Yana kainan yai cikin theater, suka bishi da kallo cikin tsananin mamaki, anya Salman ne kuwa? Sai dai Najib ya kalli Amir yace " kamar cewa yai ya kusa zama uba ko?"
Amir yace "haka naji."
Najib yai murmushi yace "wow da alama Salma ciki gareta."
Shima yai sauri ya shiga yana murna.
Amir ya bisu da kallo, shikam sam baisan karatu, haka dai ya shiga ranshi a b'ace.
Yan class gaba d'ayansu suka zuboma Salman ido, harda malamin, mamaki suke yau Salman ne ya shigo akan lokaci? Sannan kuma rike da littafi? Salman ko kulasu baiyi ba ya wuce ya zauna.
Malamin ya saki baki, sai da Salman ya kulu yad'an daki desk kad'an, sannan kowa ya juya, malamin ya d'auko biro a aljihunsa a rikice ya d'auka maker ce, sai dayaje rubutu ya gani, yan class suka kwashe da dariya, sannan yai saurin d'auko maker ya fara rubutu.
Salman rashin sabo yasa duk yaji ajin ya isheshi, yadaure sai gyara zama yake, yakai hannu kamar zai d'auko waya, Najib yace "ka manta ne baban baby?" Salman najin haka ya fito da hannunshi, har aka gama lectures kafin su fito.
Yana fitowa yad'au wayarsa ya kunna, text ne ya shigo daga Beauty "My prince ya karatun?"
Murmushi Salman yai sai dai maimakon ya kirata kawai sai ya kira wata number, yace "Asim ina zamu had'u? Na taho da passport d'in."
Sai kuma yace "alright" tare da kashe wayar.
Najib ya kalleshi yace "badai honeymoon zaku kara guduwa ba?" Salman yace to baban sa ido, mun kusa fara exam inafa zani wani gun?" Najib yace "kai abin nan na bani mamaki."
Salman ya d'an bige kafad'arsa yace " gwara ya daina ma baka, muje ka rakani."
Nan suka shiga mota suka fita.
Farha zaune kusa da fulani da ishaq, Fulani tace "yanzu wace shawarar zamu b'ulo?" Farha ta kallesu tace "ni ba wani plan da za'ayi dani, dan yanzu yayana yana sona banason nasake wani abu dazaisa ya kara jin haushina."
Fulani tace " ke yanzu kina tunanin Salman dagaske sanki yake."
Farha ta mike tace" ni ba abinda yadamen, abinda yayana Yafad'a dashi kad'ai zan d'inga amfani." Takarashe maganarta tare da mikewa tai d'akinta.
Ishaq yace "good haka akesan soyayya da confidence, da alama nima zan tari Salma in fad'a mata abinda ke raina, wayasani ko itama tana sona? Ganin na basar ne yasa ta share?"
Fulani ta kalleshi shekeke, tace "lalai Ishaq baka da hankali, matar kanin taka zakace kana so? "
Ishaq ya mike yace "nidai nagaji da biye miki abubuwa na basa tafiya daidai."shima ya juya yai waje.
Tai tsaki tace "ace duk cikinsu bada wanda zakai shawara? Ga ragowar 'yayanta maza bata saba irin wannan had'in dasu ba.
Salman sai bayan magrib ya dawo, yana parking yaga wayar farha, tsaki yad'anyi kafin ya d'aga, cikin salo da kisisina take maganar, tace "yayana baka dawo ba?" Salman yace "ya akai? Kanwata ta damu ta ganni ne?" Farha tace "sosai ma." Yace na shigo yanzu, anma zan tsaya gun mai martaba"
Tace " to sai ka gama." Ya kashe wayar batare da ya amsa ba.
Tsaki yakari yi, sannan ya kira Beauty, Salma ta d'aga tare dayin sallama, wani sanyine ya ratsashi, yace Beauty kinjini shiru ko? Tai murmushi tace " eh mana duk ba dadi." Salman yace "uhmmm lalai an damu dani dayawa, Me aka tanadarmin to?" Salma tace "komai ma, nidai ka dawo please"