← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 38

Sashe 25

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isa gida sukai b'angarensu, bayi nata gaidasu, salman na shiga ya wuce toilet, ya watsa ruwa tare da d'auro alwala, yana fitowa itama tashiga tai wanka tai alwala, hanne ce tai knocking tasanar dasu an kawo abinci, salma dake tsaye ta kalli salman, ya jawo ta jikinsa ya rungumeta tana daga tsaye, salma tace abinci? Yace not now, ni abinda naci d'azu mai dadi bai bar cikina ba, salma tai murmushi, salman ya kamo hannunta ya zaunar da ita, sannan ya kwanta akan cinyarta, ta shafa kansa tace bacci? Yace eh beauty, tace tunda ka yi sallah, salman yace beauty? Tace naam? Yace bana tunanin zan iya bacci ba'akusa dake ba, salma ta kara shafa kansa sannan tazo daidai saitin kunnensa tace naji dadi, murmushi yai tare da lumshe ido, ita kuma tana shafa sumar kansa a hankali.

Salman bacci yake sosai, salma ta kura mai ido tana kallanshi, itakanta tasan sanda takema salma yamata yawa, tana zaune tana tunane_tunane har itama tafara bacci, sai wajen 5 salman ya mike tare da kallan salma data jingina da gado tana bacci, mikewa yai ya gyara mata kwanciya, tare da rufa mata bargo sannan ya fita.

Salman kam yana fitowa, yaga wasu fadawa biyu a kofarsa, suna ganinshi suka taho da sauri, suka gaidashi, yace menene? Sukace fulani ce tace musanar dakai tana jira, kallansu yai yace kuce ta jira inada uzuri tukun zan shigo😏, yai hanyar mota ya barsu anan, suma suka juya dan kai sako, fulani ta kwanta a gado ta daddage tana kakaro numfashi irin wacce takejin jiki d'in nan, tad'auka zataga salman, sai dai jitai ance wai yanada uzuri, bakin ciki ya isheta ta tashi zaune tare dayin kwafa, lalai itama ta kosa ai maganin d'an iskan yarancan.

Salman dama da saninsa ya fita daga gidan, gidan najib yaje Amir ma na gidan, nan suka shiga tsokanarshi wai ya honeymoon d'in nasa? Salman kam murmushi yai yace matsalarku duk jin kwakwaf d'inku yau sai dai ku hakura dan bazakuji komai ba🤔.

Salma bayan ta tashi,ta fita falo taci abinci sannan takira salman, ringing uku ya d'aga tace prince ka fita bakaci abinci ba? Ya kalle najib da Amir da suka matso kusa dashi dan jin kwakwaf, dasauri yace zan kiraki anjima ya katse wayar, salma tabi wayar da kallo tare da mamaki.

salman kam kallansu yai yace da alama nakusa daina zuwa nan tunda kun koma 'yan sa ido, dariya sukai sukace yarima kaga yanda kafara canza wa kuwa? Salman yace bansan iskanci, ba wani canzawa, Amir yace ga hasken Amarci nan😃 salman ya girgiza kai tare da mikewa yace mu fita ko? Sukace kai ya kamata dama an dade.

Salma kam duk gidan ba dadi haka tai tajinta, takosa salman ya dawo, waya tad'auka kamar ta kirashi sai kuma ta fasa tunda shi yace zai kirata.

Salman kam sunje yawo sai 9 sannan ya kamo hanya, waya ya d'aga yakira salma, da sauri ta d'aga, salman yace kinjini shiru ko?tace ina kashiga? Yace ina tare dasu najib ne sun takuramin, tai murmushi tace ka taho? Yace eh ganinan, kinyi missing d'inane?tai shiru, yace ohh da alama dai, tace kaje dubiyar? Nima inasan shiga amma bansan zuwa ni kad'ai, salman yai wani murmushi yace nakusa isowa nan da 5 mins ki fito sai mu shiga tare tace to sai ka iso, nan sukai sallama ta mike tare da d'an gyara fuskarta ta yafa mayafi ta fito.

Daga nesa ta hangoshi shima haka tun daga nesa sukema juna murmushi a hankali suka karaso kusa da juna, salman ya kalli salma, sannan ya kalli bayin dake biye da ita ya d'an sukunyo kad'an yace har naji relief dana ganki, murmushi tamai mai kashe zuciya, shima murmushin ya mata suka karasa b'angaren fulani.

Farha ta had'a juice d'in abarba ta zuba maganin bacci tun d'azu suna jiran salman sai dai salman shiru hakan yasa tasa a fridge, tai d'aki tana kokoni.

Jin sallamar salman yasa ta fito da sauri, sai dai tai turus, ganin salman da salma a kilisar fulani su biyu, salman yasa hannunsa a kugun salma tana ture hannun tana cewa prince a b'angaren fulani muke fa🙊? Salman yace to sai me? Ya matso daf da ita yace u are my wife, farha ta cika tai fam, tayi gyaran murya tare da karasowa, atare suka kalli gun salma ta had'e rai ganin farha, shima salman d'in fuska ya d'aure, farha kam aranta tace kyalesu,kin manta...hakan yasa ta saki murmushi takaraso tace yayana? Ina kashiga? Salman ya kalleta yace farha dama kinanan? Tad'an bata rai tace yaya yazaka cemin haka🙁? So kake intafi? Salman yace ba haka nake nufi ba, ina umma? Takalli salma tace sannu in_law, sannan tace yaya muje tana d'akinta, salman ya kalli salma yace beauty muje ko? Salma tai murmushi tare da d'aga kai, farha ta maimaita beauty? Tasan beyi karya ba amma kishi duk ya kara cika ta.

Suna shiga d'aki sukaga fulani a kwance cikin bargo, dama tunda taji sallamar salman tai saurin rufuwa, salman yakaraso kusa da ita da sauri, yace umma? Jikin ne? Fulani ta saki numfashi tare da d'aga kai, salman yace ayya sannu, har magana bakya iyayi? Ta kasa dakai, salman zai magana yaji muryar ishaq yana cewa umma kina d'aki ne? Yafad'a tare da bankad'a labulen d'akin,ganin salman da masoyiyarsa yasa ya had'iye maganar dayake shirin yi, yakalli salman yace ashe ka iso? Umma sai nemanka take, salman kam ba shakka yasan pretending ne daga yanda yaji ishaq yai magana daya shigo, amma a fili yai murmushi yace ba dole in dawo ba tunda umma ta matso tanasan ta ganni, da alama dai tafisan taganni akanka, ishaq yacd ban gane ba? Salman yace ni danake wani garin? Tunda tasa akirani ai kaga ta kosa ta gannine, ishaq ya d'aure fuska, salman ya kalli ishaq yace umma najin jiki yaya, ishaq yace sosai ma, salman yace ayya, dama haka ne, in mutum ya dade bai yi cuta ba ai da alama sai ya duba ibadunsa, ishaq yace bangane ba, salman ya kalli fulani sannan yace dama ba kowa bane zai gane😏, ran fulani dake kwance ya b'aci wato da ita yake ko wa? Abinciki ibadunsa? Sannan ta matsu ta ganshi? Salman ya kalli ishaq yace yaya ka kula da umma plz kar mu sake wani rashin😞 salma kam kallan salman kawai take tana mamaki mutum irinshi, sai magana cikin magana yake kwaba musu kuma fuskarsa d'auke da murmushi.

Farha ce tad'an taba fulani, salma na kallanta, salma sai ji tai fulani cikin dakucewar murya tace salman inasan magana dakai, salman ya kalleta sannan ya nuna kansa yace ni? Ta d'aga kai, farha da sauri takalli salma tace mu basu guri ko? Salma tace eh tafad'a tare dayin waje, farha tai murmushi.

Salma na fita ta kalli farha sam batasan zama da ita hakan yasa tace ni nayi gaba bansan how long hirar tasu zata kaiba, farha tace to in law, dama haka suke so, salma ta juya tanajin farha tad'anyi wani shewa itadai tai gaba.

Salman na zaune farha ta kawojuice, salman ya kalleta sannan ya kalli fulani yace ya akai? Fulani takalleshi tace salman kayi hakuri nasan kaji haushi danasa ka dawo,salman yace haushi? Wa? Ni? Fulani ta tsani rainin hankalin nan, tadaure tace to kasha lemon mana ko kana tunanin nasa ma wani abu ne? Salman yace wai umma meke damunki? Ban gane kinsa wai abu ba? Fulani ta zubo da kwalla, tace salman na sani bana kyautamaka kayi hakuri dan Allah, salman ya kalleta tare da kallan farha data zuba mai juice d'in tace yaya nina had'ama special, ya amsa tare da kurbar kad'an yace farha bansanki da haka ba shine kika ki d'aukowa tun matata tananan? Tace laa wlh mantawa nai, akwai dayawa inzaka tafi zan bada akaimata ko ibika dakaina in kaimata, salman yace gwara ki hada d'in dai bawai ki bini ba, yafad'a tare da shanye na cup d'in.

Farha ta kalli ishaq sukai wani murmushi salman ya kalleta yace meye.....sai dai ganin dishi_dishin daya fara yasa yai shiru, ai bai kara magana ba ya tun tsere agun, farha tasaki dariya suma haka, nan ishaq ya taimakama farha suka kai salman d'akim farhan suka kwantar.

Salma kam tana d'aki a tsaye, ganin har 11 shuru ba salman tsoro ya fara kamata kawai ganin text tai a waya, "am sry beauty, zanyi dare ki kwanta".

Da mamaki takara maimaita text din, hartayi cilli da wayar sai kuma ta d'auko, tare da kara karanta text d'in, zanyi dare? Ki kwanta? Salman d'in? Nan rayuwarsu ta jiya da yau tashuga fad'o mata, ta tuna a yanda tasan salman ba abinda zai zaunar dashi acan,tuno sanda farha ta taba fulani tai sannan shewar dataji farha tayi, dasauri ta jawo mayafita wajen 11:30 tai waje, su hanne basu masan tafita ba.

Farha kam tanacan tana murna harta hango an fad'ama sarki salman ya kwana da ita, ai ba makawa sai aure.

Nikam dariya ma taban dasauri nabi salma ganin tana zuba sauri.

*Masoya littafin nida prince kuyi hakuri plz jiya da yau bansamu na turo 2 pages ba kamar yanda nasaba, hakan ne yafaru saboda wani uzuri nawa.*
*Mutane sunmin complain akan hakan, kuyi hakuri amma insha Allahu gobe zan cigaba da turo 2 pages.*

Ayusher Mohd📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.4⃣3⃣

Salma na zuwa tai hanyar d'akin fulani, bayin suka tambayeta,salma ta kallesu yace farha fa? Suka nuna mata hanyar d'akinta, salma ta kallesu sannan tai d'akin farhan, batasan meyasa jikinta ke bata farha ce ke shirya wani abu, salma takarasa jikin kofar tare da knocking, farha da ke kwance kusa da salman ta kalleshi sannan ta mike, tace waye? Salma bata amsa ba, hakan yasa farha tai tunanin ko fulani ce, farha ta bude kofar.
Chapter 25 · 0% Book details