← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 38

Sashe 27

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farha kam da fulani sun dadw ba wanda yai magana fulani sai fila fila take da maganar daya gama dankara mata, itakam har kasan ranta tsoron salman da kwarjininsa take , farha kam jikinta gaba daya ya kame, itakam tad'aukama ta mutu ne.

Ohhh *SALMAN*

BY AYUSHER MOHD📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.4⃣5⃣

Bangarensu suka karasa salman bai magana ba, toilet kawai ya fad'a yai alwala, bayan yayi sallah ya mike tare da kallan salma dake zaune akan kujera da alama tunani take, murmushi yai sannan ya karaso inda take, a gabanta ya tsugunna ya kamo hannunta da sauri ta kalleshi, yace me beauty take tunani haka? Salma tai murmushi sannan ta ran gwad'ar da kai gefe tace zaka skul ne? Yai tsaki yace eh, ta kankame hannunshi tace prince? Ya kalleta yace ya akai? Mikewa tai daga zaunen datake tad'an d'agashi, ya mike tare da kallanta, kujerar data zauna ta maidashi ita kuma ta tsugunna, salman ya kalleta da mamaki yace beauty menene? Takwanto da kanta kan cinyarsa sannan tace my prince in rokeka wani abu? Ya kalleta yace mene? Tai shiru dan tana tsoron abinda zata fad'a can ta daure tace yanzu muyi karatu, kaji? Ya kalleta yace muyi karatu? Ban gane ba? Salma ta kara gyara kanta tace karatun skul nake nufi? Muyi karatun da gaske kaga muna bata lokacin mu ne, sai alokacin salman ya gane me take nufi wato yadage akan karatunshi, ya kalleta tare da shafa kanta yace bana so😏 beauty, salma ta d'ago tace why? Hannu yasa a lebenta alamar tai shiru, yace beauty banaso inyi wani abun da zai birge Abba, yana kai nan ya mike yai hanyar toilet.

Salma ta mike da sauri ta rungoshi ta baya, tace prince ba dan ka birgeshi nake nufi ba, dan ka gama ka huta nake nufi, salman ya juyo da ita gabansa yace beauty? Salma ta runtse ido tace please 👏🏻,salman ya kura mata ido ahankali ta bud'e idanta, salman yace inace banaso zaki daina min maganar? Salma tai shiru can tace a'a in kace bakaso yau, gobe zan kara tambayarka har sai nai convincing d'inka😕, salman ya kalleta yai shiru, salma idanta yai rau rau tace prince? Salman ya janyeta tare da shiga wanka.

A gun ta tsugunna tai shiru, dolene ta taimaki mijinta, amma ta ina? Shiru tai dan itakanta bata da amsar tambayarta.

Salman a toilet shaya kawai ya sakar ma kansa yai tsaye yana tunani, ruwa ne ke zuba ajikinsa, yasani maganar salma gaskiya ne, amma ina.....bayajin zai yi amfani da shawararta, ya dade a haka kafin yayi wankan ya fito.

Inda yabar salma anan ya tadda ita, dasauri ya d'agota yace beauty meye hakan? Ta kalleshi batace komai ba, sun dade suna kallan juna kafin salman ya daure yace naji, I will think about it, salma ta saki wani murmushi tare da rungumeshi, salman ya d'agota tare dakai bakinshi cikin nata, sun dade suna kaima juna sakonni da harshensu kafin su saki juna, a hankali suka bud'e idanuwansu, salman ya rungumeta tsam a jikinsa wani shauki ke kamashi, salma ahankali tace Thanks, salman yace for? Tace kace zakai tunani at least bakai rejecting ba, salman ya shafo bayanta baice komai ba sannan ya d'agota, takalleshi tace yanzu zaka fitan ai ko? yace eh tace bari induba abinci kafin ka gama, tafad'a tare da dan matsawa, salman ya riko hannunta yace baki fitomin da kaya ba🙁 takalleshi tace ni😳? Yace tunda bakyaso bari na.....dasauri tace a'a inaso, bari ind'aukoma, yai murmushi.

Itakuma ta bude drawer tafara duba kaya, kananam kaya ta d'auko rigar white ce anyi rubutu da dark blue a jiki sai wando jeans, salma ta kalleshi tace sunyi? Dariya yai yace in sun ma beauty nima sunmin, salma ta ajiye kayan akan gado tare da cewa godiya nake da wannan matsayi☺, tafad'a tare da yin waje.

Fulani zaune itada farha da ishaq sunyi shiru can fulani tace ya kamata mu fito da wani plan, ishaq ya kalleta yace umma wai da gaske salma na ita ta wargaza plan d'in namu? Farha ta kalleshi salmana? Tab, fulani itama da kalmar ta b'ata mata rai amma ta daure tace eh mana, ni yarinyarnan ina mata kallan mara wayau ashe green snake ce? Farha tai kwafa ta tuno da marin da aka maka mata, sannan bakin cikinta d'axu da safe salman ko kallanta baiyi ba har yagama jawabensa ya fita, fulani ce ta katsesu da cewa kunyi shiru, ishaq yace kawai musa a kamashi akaishi can wani kauye mai nisa a cillar dashi, farha ta kalleshi tace me kake nufi? Fulani ta harareshi tace kai fa haka kake baka tunani kake magana, ishaq ya zuciya yace ni dama ba'a taba d'aukan shawarata ba😏fulani ta zuciya tace duk shawarwarin naka da basuda kan gado? Ishaq ya hade rai tare da mikewa yace ni zan wuce, fulani tace koma ka zauna dan ban baka umarnin fita ba, ishaq ya kalleta sannan ya harari farha yai fitarsa.

Nace uhmmm🤔

By _*AYUSHER MOHD*_📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

_*This page is dedicated to all members of my group " The Queen Bee" thanks for ur love and care.... love u oll.*_

NO.4⃣6⃣

Salma haka ta zauna har saida salman yagama cin abinci tana kalansa, daya ce taci sai tai murmushi tace ni ba yanzu ba, nafisan in kalleka har ka gama, yace in na kware fa? Tace bazaka kware bama in kuma hakan tafaru sai in baka ruwa😊 tai maganar tare da nuna mai jug d'in ruwa, dariya yai yacigaba da cin abincinsa, bayan ya gama ya mike, salma tace ina zuwa, ya kalleta da mamaki, d'aki tai da sauri, ta d'auko jotting book d'inta sabo ta duba rubutun ciki baifi 3pages ba dasaurI tasa hannu ta yage, sannan ta d'au biro ta makala a littafin ta fito da sauri.

Salman na tsaye yana jiranta ta karaso tare da mikamai, yakalleta yace na menene? Tace na karatunka mana😉, salman yace what? Tad'an turo baki tace a class in anyi wani abun ai zakai jotting, salman yace wa? Ni? Salma tace kai my prince☹ irin wannan dizgi😢? Salman ya kalleta yai murmushi yace hakan ne dizgi? Ta juya baya cikin shagwaba tace eh mana gashinan☹, ajiyar zuciya yai ya juyo da ita sannan ya anshi littafin yace happy? Ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace alot😊, ya sunkuyo yamata kiss a goshi ya fita, ta dade a tsaye tare da shafa gun kafin ta shiga ciki.

Salman shikanshi a mota ya dade kafin yaja mota, yana isa gidan najib a waje ya tadda shi, bai fita ba najib ne yashigo, salman ya ja mota sukai skul, sai da sukai parking najib ya kalli salman yace yarima gaskita na yarda aure nacanza mutane😁 salman yace bangane ba? Najib yace da ace da ne da gudu zamu shigo muna tada kura amma yanzu baka gudu da mota nakula, ko dan......salman ya kalleshi yace kodan me? Yace ohh ka manta? First had'uwarku da salma ta hanyarne? Salman ya tureshi yace najib na kula kwanan nan gulma ke cinka dayawa, najib yai dariya yace Ango Ango, salma ya bud'e motar tare da ya fita, najib ya kalli kusa da inda salman ya mike ganin littafi da biro yasa shi wani tsananin mamaki, da sauri ya fito, sai dai baiga salman ba, can ya hangoshi yana tafiya, da sauri ya bishi.

Salman sai dayaje kusa da theater d'in dazasuyi lectures ya tsaya, najib ne ya karaso yace kai wasa wasa kana da sauri, salman yace ina zan tsaya ka bayan kana ganin rana ake, najib ya kalleshi yace muje, salman ya kalli hannunshi yace wannan? Da sauri yasa hannu ya fizge, najib yasa dariya yace najib dagaske ne abinda nake zargi? Naka ne littafin? Lalai in nakane da alama za'ai ruwa da kankara, salman yace to parrot sai kai tayi, na matatane menene? Najib ya bud'e baki yace da alama naka ne da gaske😳 u? Littafi? Ha ha ha .

Salman ya makamai littafin akai ya wuce ciki, to ba najib ba salman gani yai kowa na kallansa da sauri ya d'aga rigarsa yasa littafin a ransa yace yazanyi da beauty🤔?.

Fulani zaune tayi shiru, ta kalli farha tace farha ki bani yau zuwa gobe zan samo mana wani plan d'in farha tai kasa dakai, itadai tafara tsoro sai dai salman ne batajin zata iya hakura dashi, farha ta mike tace to fulani Allah yakaimu goben, fulani ce tace farha kirami hindu( baiwar fulani ce) farha tace to, hindu ta iso tare da tsugunnawa, tace gani ranki ya dade, fulani ta kalleta tace kinsanar da ishaq d'in inasan ganinsa? Hindu tai shiru, fulani tace dake nake, hindu tace nafad'a mai amma yace kiyi hakuri bazai samu zuwa ba, kuma bayasa ran har zuwa gobe zai samu dama, fulani ranta ya kara baci,takalli hindu tace fita, hindu tace to dasauri tai waje, fulani ta rike kanta tace ni? Ishaq? Hannunta ta dunkule, aranta tace da alama sai na lalaboshi.

Salman zaune a aji ana lectures, sai dai wayace a hannunsa yana dane_dane, najib yad'an zunguroshi yace yarima bazakai rubutu a littafin love d'in ba? Ga malan nata bayanai? Salman ya ture hannunsa yace kai rubutun kake? Najib yace yanzu nake tunani da alama gobe zan shigo da littafi tunda matar ka ta sa mu😊 salman ya makamai harara, najib yace kawo naku na love ni sai in muki rubutun, salman yace ka manta kana nufin littafin beauty d'in zan baka kamin jagwalgwalon rubutunka? Najib yace ahhh hmmm ayi hakuri, salman ya juya tare da kallan wayarsa jin karar text, dasauri ya bud'e ganin daga salma ne.

" My prince please concentrate".

Ya kalli text d'in , yace ya akai ta sani? Wani text ne yakara shigowa.

" please "

Salman ya karanta tare da murmushi, sai kuma ya ajiye wayar yad'an d'ago ya kalli malamin amma dayake bai sababa haushi ya kamashi yaga ina... kifa kai yai akan desk d'in.
Chapter 27 · 0% Book details