← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 38

Sashe 35

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waziri da sauri ya kashe wayar, dama yana zaune kusa da Sarki ne, tunda Sarki yaji ana Salman ba lafiya duk ya rikice, kawai dai yana zaune ne amma gaba d'aya hankalinsa yagama tashi, waziri ya d'aga waya ya kira likitansu, suna gama waya ya kalli Sarki yace " ko jokin ne?" Sarki ya kalleshi yace " kai sauri kaje ka dubashi, amma me ya faru dashi haka?"
Kafin waziri yai magana wanj bafade ya shigo yace waziri da matsala fa? Waziri ya kalleshi yace " matsalar me kuma?" Bafaden ya kalli Sarki sannan yai kasa dakai, Sarki yace " fad'i maganarka ba komai."
Bafaden da gulma ke cinsa yai kasa dakai yace " Ranka ya dade tuba ina kunyar sanar dakai wai an kama yarima mai jiran gado, a d'akin Salman."

Cikin rashin fahimta Sarki yace " ban fahimci me kake san fad'aba, an kamashi kamar ya?"
Waziri daya fahimci me maganar bafaden ta nufa, ya kalleshi yace tashi kaba mutane guri dama can munafirci kazoyi, ka kuma tsumayi hukuncin abinda kai."

Waziri yana ganin mutumin ya fita ya kalli Sarki yace " da alama Isahq ne dalilin tashin ciwon Salman." Sarki ya kalleshi yace " kana nufin d'akin da ake nufi ana nufin gun katar Salman ko me? Indai har ciwo ya tashi alamar ba karamar magana bace."
Waziri yai shiru, ganin haka yasa Sarki ya mike cikin tsananin tashin hankali yace "wani hauka da dabanci ne wannan?"
Waziri yai shiru aranshi yace " Salman kam ai yana ganin abu agun mutanen nan, badama nai magana ko na fad'ama, kar nima abu yashafe ni dan nasan halin fulani sarai."
Jiyai Sarki ya kalleshi cikin tsananin b'acin rai yace " wato ba wannan ne abu na farko da akemai ba kenan? "
Waziri ya d'ago cikin tausayi yace " yazanyi Ranka ya dad'e?"

Jin haka yasa Sarki yai baya tare da girgiza kai zama yai a kujerarsa, a runtse ido, a hankali yace "Salman mena aikata gareka?"
Waziri ya mik'e jiki a sanyaye yace " bari inje gun Salman kila likitan ya iso." Sarki ya mik'e yace "muje tare."

Salma kam duk tagama rud'ewa, banda kuka da rungume Salman ba abinda takeyi, Mik'ewa tai ta shiga duduba drawers tanayi tana hawaye, sai dai sam tarasa maganin Salman, jitai an kwakwasa d'akin cikin sauri ta bud'e, wani mutum tagani, da karamar jaka kamar akwati, ai bata tambayeshi ba kawai tai tunanin likitane tace gashi nan, cikin sauri ya shigo, ganin Salman a wani hali yasa ya shiga bashi taimakon gaggawa, Sarki da waziri ne suka shigo, Sarki yanda yaga Salman ranshi ya kara b'aci ya kuma ci alwashin ba Ishaq ba ko Fulani indai tanada hannu acikin abinda akema Ishaq wallahi bazai kyalesu ba.

Likitan ya dade akanshi kafin Salman ya samu nutsuwa, bacci ne ya d'aukeshi, Sarki cikin tausayin d'an nasa ya matsa kusa dashi, Salma ya kalla dake zaune akasa jikin gadon idanta harsun kumbura jiyai idanunshi naneman kawo kwalla, ace d'anshi da matarsa suna cikin wannan hali shi yanacan akan kujera baisan meke faruwa ba?
Kallan waziri yai yace "akira Ishaq da Fulani su sameni a fada, sannan a duba matarsa a tabbatar ba abinda ke damunta, sannan a kara kiran likitan da akace zai ma Salman aiki aji yaushe zai iso."
Likitan ya amsa da toh.
Sarki ya mik'e har yakai kofa ya juyo yakalli Salma yace " Salma taso inasan magana dake."
Salma ta amsa tare da mik'ewa.

A fali ya zauna, itama taje tare da zama a kasa, ya kalleta yace " Salma ki dubi Allab da matsayina agub mijinki na mahaifi, ki fad'amin meke faruwa tsakaninsa dasu fulani ko ince tsakaninku, tunda ance neman haik'e mike yaso yi."

Salma ta kalleshi hawaye ya zubo mata tace " Abba bansan kezance ba, nadaisan kawai basa kyauata mishi."
Sarki yace " hakan ma nagode tunda har baki karyata zuwan Ishaq bayau hakan ya tabbatarmin yayi abinda akace."
Salma ta share kwalla, ta daure tace " Abba in zamanmu zai zama matsala anan ka amince mu bar nan gidan dan Allah."
Sarki ya had'iyi wani abu yace " Salma bazan bari Salman yabar nan ba, dan kuwa shine magaji na, sai dai na miki alkwari ba abinda zai kara samunku daga ke har shi, kuma duk wanda yasan da hannunshi acikin abinda akamai ba shakka sai ya gamu da fishi na."

Ya mik'e tare dayin waje, Salma tabishi da kallo hawaye ya zubo mata.

By *Ayusher Mohd*📚
© *NWA*
☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

No: 5⃣8⃣

Duk sun fita sun bar Salma agun Salman, hannunsa ta rike kam tana kallansa, bayan magrib taga a hankali Salman yad'anyi motsi da hannunsa, ta matso ta kalleshi tace " Prince!!!"
A hankali taga yafara bud'e idanunsa cikin kuka kuka_ dariya dariya tace " Prince are u alright? "
Salman ya kalleta tare da jawo hannun ta data rike nashi, daf tazo kusa dashi, Salman yasa hannu ya share mata hawaye sannan ahankali yace" wannan matar tawa akwai raguwa, tafiya saurin kuka."
Salma ta kalleshi sannan tasa d'ayan hannunta ta share kwallar data zubo mata tace " bakasan yanda na tsorata bane."
Salman ya mik'e zaune sannan yasa hannu a wuyanta yad'an jawota suka matso daf da juna dan suna iya jiyo numfashin d'ayansu, a hankali Salman yace " yanzu dai na warke ai sai adaina sa idanuwan danafiso a duniya sudaina zubar da hawaye."
Salma ta sa hannu ta rungumeshi, a hankali ya d'agota tare da tsotsen lebenta yace "I luv u Salmah." Lumshe ido tai wasu hawaye ne zuka zubo masu sanyi, murmushi Salman yai ya tsaya yana kallanta, ahankali ta bud'e idanunta,wani kallo tamai da ita kanta batasan tayi ba, ajiyar zuciya yai yace "ahh lalai na yarda matatace vitamin A d'ina da alama har naji karfin jikina ya dawo, Salma cikin shagwaba tace " kai Prince banda zolaya."
Salman yaja kunnenta da d'an karfi har saida tai kara yace " wayace ki d'inga bud'ema kowa kofar d'akin nan?"
Salma tace " Prince dazafi fa?"
Yace "nasani ai,
Laifi kikai ake hukuntaki ai , dabanzo bafa? Wayasan me shashashancan zaiyi?"
Salma ta riko hannunsa, ya saketa ta kalleshi tare da hararrar sa tace "ji kunnena fa yanda yai jaa."
Salman yace " au bama amsa zaki bani ba?"
Salma tace " nafa d'auka kaine, to da aka kwankwasa kuma na duba banga kowa ba, nifa banma san sanda yashigo ba, sannan kai ina kaje?"
Salman yace " daga yanzu kidaina bud'ema kowa sai kinji waye."
Tace naji " amma kai fa ina kaje?"
Yace " ina kuwa naje?"
Ta mik'e tace " anfa cemin kun fita da Farha? Ni ina nan na d'auka wani abu mai mahimanci kake ashe kanacan ka biyema Farha kuna yawo, duk sanda nakawo kaina damaka magana akanta sai naga kamar bazaka ji dadi ba, sai dai nafara tunanin kamar ina cutar kainane nayin shirun danake."

Salman ya kalleta yaga yanda ta had'e rai, yace " oh ni Beauty kema fa ba sauki, irin wannan rufeni da fad'a haka? Kamar wanda nai wani laifi?"
Tace "au wannan ba laifi bane Prince?"

Tafad'a tare da mik'ewa, dasauri Salman ya ruko hannunta, ta fizge tare da cewa " bari in d'auko ma ruwa kasha magani."
Salman ya bita da kallo, yasani sarai tamai kara sosai akan Farha, to amma bata tsaya taji ma ya maidata ba, yana zaune har ta dawo, ta bud'e robar ruwan ta tsiyaya a cup sannan ta b'allo magungunan ta mik'amai, yana kallanta ya amsa yasha, ta rufe rowan zata juya Salman ya riko hannunta, ta jiyo ta kalleshi ta kuma kasa magana, Salman ganin yanda ta had'e rai yasa kawai ya rike kirjinsa yace "ahh Beauty kirjina"

Salma ta matso a rikice tace " jikin ne? Nashina, ko inkira likitan? Wayyo ni?"

Salman ya kalleta yai murmushi yace " kin hakura?" Salma tace "what? Au tsokana ce? Pillow ta d'auka ta makamai ya rike pillow d'in yace " patient ne fa?" Ta zauna tare da cewa "amma nikam Prince tunda kake ka tab'a cema wani sorry ko yi hakuri?

Salman yai shiru yace " badai saboda haka kike ta wani kara had'e rai ba?" Ta juya kai tace " ni na fad'ama? Yai dariya yace " dagaske kuwa saboda hakan ne" Salma ta mik'e tace " nidai ban fad'aba, ammm mai martaba fa yazo."
Salman yace haba? Tace " yazo naji kuma yace a kira Fulani da Ishaq." Salma ya mik'e zaune yace " bari inje Beauty. "
Tace to.
Salman ya mik'e tare da fita.

Sarki kam zaune yake shida Fulani da Ishaq, ya kalli yanda fuskar Ishaq tai luhu luhu dan duka, ya kuma kalli Fulani dan da alama itama yanzu taga fuskar Ishaq d'in ganin yanda taketa kallansa da b'acin rai.
Sarki yai gyaran murya ya sallami kowa ya rage saura su uku, ya kalli Ishaq cikin d'aurewar fuska yace " kai me kajeyi d'akin Salman, cikin ma d'akin matarsa?"
Dasauri Fulani takalli Ishaq, d'akin matar Salman?
Ishaq yai kasa dakai gabanshi sai fad'uwa yake, cikin in ina yace " Abba ni ban tab'a zuwa ma d'akin Salman ba."
Sarki yace " kai ni zakama karya? To dukan fuskar ka fa? Waye yamaka?"
Ishaq yai tsuru_ tsuru yace " uhm uhm...."
Fulani tace " haba mai martaba yazaka tambayi d'anka wai ko ya shiga d'akin matar kaninsa, yama za'ayi hakan tafaru? Ko gulma aka kawoma ai bai kamata ka yarda ba, inma ahi Salman d'in me ya fad'i haka to yayi karya dan kuwa Ishaq yafi karfin yaje kwartanci d'akin sa."
Chapter 35 · 0% Book details