← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 38

Sashe 36

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ran Sarki ya b'aci wato dama duk wani so datake nunamai nasan Salman agabanshi karyane, Sarki ya kalleta cikin b'acin rai yace" kin tabbatar in nai bincike aka tabbatar da hakan duk hukuncin danamai sai ya shafeki, kuma ba matsala?"
Fulani tai shiru ta kara kallan Ishaq zatai magana taji sallamar Salman, cikin kid'ima suka juya duk su biyun , Fulani ta had'iyi wani yawo, Ishaq kam jikinsa ya shiga b'ari, Salman ya karaso ya zauna kusa da Ishaq, ya gaida Abba sannan ya kalli Ishaq sannan ya kalli Fulani ya gaidata, ta amsa a d'am tsorace.
Salman ya kalli Ishaq yace "yaya ya akai kaji wannan ciwon? Badai neman matar wani kaje ba aka ma dukan tsiya?" Ishaq ya kalleshi yana kif kif da ido yace" wani irin neman matar wani kuma?" Salman yai wani mugun murmushi sannan ya kalli Fulani yace " Umma d'azu na kama wani yazo har cikin d'akina yana neman la lata da matata, banga fuskarshi sosai ba amma nasan namai bugu mai karfi, yaza'ayi? da alama sai an tara mutan gidan nan an nemoshi dan bama tunanin zan iya kyaleshi."

Fulani a tsorace ta kalli Ishaq sannan ta kalli Sarki ta kuma maida idanta kan Salman tace " uhmm bai kyautaba kuwa ko waye."
Salman yace "good ashe kin gane umma, ke a tunanin ki ni namijin da zan yafe hakan ne?" Fulani ta kara had'iyar yawo da kyar tace " a'a ammq ya kamata ka sassauta tun balle in wanda yama laifin d'an uwanka ne."

Salman ya kalleta yad'anyi murmushi yace " inafa! Ai in d'an uwa nane ma shine bazan yafe ba, balle wanda ya shigo d'akin nasan shine wanda ya kusan kad'eni a titi matata ta tare."

Ai a tare zuciyarsu ta buga da karfi, Ishaq da sauri ya tsugunna yace " Salman dama ka ganni sanda na kusa bigeka shine ka ki fad'amin ko? Sannan matarka wallahi tunda naganta naji........" dasauri Fulani ta katseshi da karfi tace " ISHAQ"

Sarki kam Salman ya gama burgeshi, gashi ta hanyar sauki yasa Ishaq ya fad'i abinda ya aikata lalai ba shakka wannan inya zama sarki mutane zasuji dadi dan da alama bazai yarda da injustice ba kuma duk inda mutum yakai da boye abu zai sa ya sanar dashi ta hanya mai sauki, kallan Salman yai cikin tsananin so sannan ya kalli Ishaq da duk ya rud'e ya kuma kalli Fulani da ke hararar Ishaq ta gefen ido.

By *AYUSHER MOHD*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

No: 5⃣9⃣

Salman ya kalli Ishaq yace " ahhh so matar kaninka kake so shine kaje d'akinsa?" Ishaq yace " nifa ba haka nake nufi ba."
Fulani tace " wai Salman meye hakan? Kasa yaro a gaba kanata bugar cikinsa, to bazan yarda ba, nasani sarai Ishaq d'ina bazaije gun wata matar ka ba mai kama da aljanna."
Salman yad'anyi dariya yace "Umma I feel hurt, wato ni ba naki bane bako?" Fulani takalli sarki tai kasa dakai tace "nifa ba haka nake nufi ba."

"Ohhhh nagane me kike nufi, amma umma bakya ganin bai kamata kice nasa yaro agaba ba? Yanzu kamar Ishaq a kira shi yaro? Yafa girmeni?"
Salman ya fad'a yana mata wani kallo.

Fulani kam ta tsani Salman yasata agaba duk ya rikitata haka, bare yau agaban Sarki tama rasa me zata ce.

Ishaq yace" niba yaro bane, nasan kuma duk abunda nakeyi, yama za'ayi kid'inga kirana yaro agaban Salman?"
Sarki yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu,cikin b'acin rai ya kalli Ishaq yace "kenan dagaske ka shiga d'akin Salman kaje neman matarsa?"
Ishaq yace " Abba ba haka bane.."
"To ya ya ne? Ko inkira matar tawa ne? Ko kuma kanaso in kara maka dukan dana ma d'azu ne?" Jiyai Salman ya katseshi da wad'an nan kalmomin.
Ishaq ya kalli Salman a rikice yakuma kalli Fulani datake makama Salman harara ta gefe, yai kasa dakai tare da runtse ido.
Salman yad'an tab'e baki ya kalli Sarki, sannan ya kalli Ishaq yace " nikam yaya waye ya kaimu asibiti ranan da mukai karamin accidents d'inan?"
Ishaq cikin zumud'i ya d'auka wani abu ne yace " nine mana, nina kaiku."
Fulani zatai magana Sarki yace " kar inkuskura inkara jin bakinki anan tunda badake suke ba."

Salman yai murmushi yace " Ayya yaya nagode, dabadan Allah yakawo ka ba bansan mezai faru da Salma ba."

Ishaq ya sosa keya cikin farin ciki yace " ai duk lefinka ne, mezaisa ka bari Salma ta tarema, nifa kai........"
Kara Fulani ta saki, hakan yasa Ishaq yin shiru, Salman ya kalleta yace " aya Umma ta shiga wani hali, yazakiyi Umma gashidai Ishaq yafad'i komai da bakinsa."

Ishaq ya kalleta yace "Umma inafa da wayau hauka nake zan fad'amai, karyar Salman ne kawai yana za'ayi yasan nina je bigeshi bayan bai kula ba? Sai dai in yau yake nufi, wannan kuwa ai shiyakamani....."

Fulani mik'e wa tai cikin b'acin rai ta zo kusa dashi ta haska mai mari, tace wlh Ishaq nikam banyi sa'ar d'aba.

Sarki ya fusata yace ke Sakina! Ai duk fadar sai da kowa ya juyo, cikin sanyin jiki Fulani ta zauna Ishaq kam ido yai wuri wuri, Sarki cikin b'acin rai yace "banataraku anan bane kowa yai abinda yaga dama ba, kuma duk abinda kukama Salman dake da d'anki karkuyi tunanin zan kyaleku, ada na d'auka kina kula da Salman, a'a koma bakya kula dashi banyi tunanin zakuma ku had'u keda d'anki ku muzguna ma Salman ba, yanzu da sanda ya bige Salman ya mutu fa? Sannan ko kunya harya samu damar shiga d'akinsa neman matarsa? Gidana yakoma gidan dabobi kenan ko me? To wlh daga shi har ke dakike biyemai sai kun fuskanci hukunci mai tsanani."

Ishaq yasa kuka yace " Abba d'an Allah kayi hakuri nasan nayi laifi, wlh ni tun ina karami da k'in Salman na taso, kullum umma zancenta d'aya ne kar in kuskura in bari Salman ya wuceni akomai."

Sarki ya kalli Fulani datai kasa da ido, da alama itama kwalla ke zubo mata.

Sarki ya kalli Salman sannan ya kalli Ishaq yace " na cireka a matsayinka na yarima mai jiran gado, sannan nakuma bama Salman wannan mukamin."

Fulani ta d'ago ta kalleshi cikin tsananin b'acin rai tace me kake nufi mai martaba? Ishaq shine babban d'anka a tunanina duk abinda yai zaka yafemai tunda shine magajinka kuma ni danake uwar gida, Fulani nice ya kamata d'ana yazama Sarki."

Jitai Sarki yace " ahh namanta, gwara da kika tunamin kema ina sanar dake matsayinki na Fulani na cireshi daga yau......."
Salman yace " Abba!!!"

Sarki yace " kamanta na sanarma bazan yafema duk wanda ya nemi kad'eka ba? Sannan ko kunya Ishaq ya nemi matarka? Kuma duk nasan lefin mahaifiyarshi ce."

Fulani cikin kuka tace" Alhaji ni zakawa haka? In ka cireni daga mukami na nida Ishaq alama ce ta mu mutu kawai, dama nasan ba sona kake ba, amma duk da haka bai kamata kamin haka ba."

Sarki yace " kin d'auka shi kad'ai ne? Nasani sarai in na kauda Ishaq zakiyi tunanin saka Mannir ko wani daga cikin d'anki, bazaki tab'ajin kunyar abinda d'anki ya aikata ba, dan haka na yanke hukuncin dolene kibar nan gidan ki koma can karshen gida( inda ake kai iyayen sarki insun tsufa sosai ) anan zaki zauna."

Salman yace " Abba? Hukuncin kamar yayi tsauri." Sarki bai bashi amsa ba ya kalli Fulani dake kuka sosai tana bada hakuri, sannan ya kalli Ishaq yace kaikuma kashirya kaida iyalanka kubar nan ku koma kasar Egypt dazama kada kuma kadawo har sai in nina bada izinin hakan."
Abba yana gama fad'ar haka ya mike yai cikin gida, Fulani tasa kuka, Ishaq ma kuka yake sosai yana cewa "Salman d'an Allah kataimakemu, ni wlh duk Umma ce, laifina d'aya danafara san Salma wannan kuma Salman kasan ba laifina bane laifin zuciya ne. "

Salman ya kalleshi shikanshi tausayin hukuncin da Abba ya yankr yakeyi.

By *Ayusher Mohd*📚

© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

No: 6⃣0⃣

Salman ya kalli Ishaq duk sai kuma yaji Ishaq d'in na bashi tausayi, Waziri ne ya shigo ya kalli Salman yace " Yarima mai martaba yace ka ciga ciki."
Salman ya kalli Waziri yace " Toh" mik'ewa yai ya d'an bugi kafad'ar Ishaq sannan ya kalli Fulani dake kuka yai ciki, Fulani tabishi da harara tare dacewa" niza'a wulakanta akan wani banza Salman? Wlh Sarki yayi kuskure."
Ishaq ya matso kus da ita ya riko hannunta yace "Umma kitaimakeni kisa abarni akasar nan, ni wlh na tsani wata kasar."
Fulani ta wafce hannunta tace " wato kanka ka sani kad'ai ko? Ni baka tausayin inda za'a kaini? A k'alla in na zauna acan kila sai nayi wajen sati 3 zuwa wata kafin 'ya'yana suzo su ganni."

Jisukai Waziri yace " ku fito daga fad'a ba gurin hira bane, sannan kai yarima Ishaq katabbatar ka shirya d'an gobe zaka wuce, sannan Fulani au hajiya kema ki had'a kayanki yau dan gobe da safe zaki koma."
Yana kainan yai waje, Fulani ta zuciya tace "me? Au hajiya? Sai na ci*********, "
Ishaq ya kalleta yace " nidai Umma yanzu ba lokacin wani zagi bane ya kike so nayi?"
Fulani ta watsamai wani kallo tace " duk ba kaikaja ba d'an rainin hankali, dalla matsamin." Ta fad'a tare da wucewa.
Ishaq ya dunkule hannu ya naushi bango, yace " ni dai rayuwa ta gama b'aci, bansamu Salma ba, bansami mulki ba, garin muma yanzu ya fi karfina."
Shima waje yai jiki a sanyaye.
Abinda zai baka mamaki kafin si fita zancen har ya yad'u agidan Sarki, suna tafiya bayi na kallansu suna d'an gulma.
Chapter 36 · 0% Book details