← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 38

Sashe 26

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin salma yasa ta zaro ido tare da janyo kofar, sai dai kafin takarasa rufewa salma ta hankad'a kofar da karfinta,😰😳 ganin salman a kwance ya baje yasa jikinta ya d'au rawa, gashi an cire mai riga an barshi da vest, wani mugun kishi ne ya taso mata, ta shiga d'akin rai a b'ace, farha kam jikinta sai b'ari yakeyi tai hanyar kofa da alama so take ta fita, salma na ganin haka tasa gudu ta rigata zuwa kofar ta datse da makulle sannan ta zare makullin, ta watsama farha wani kallo sannan takarasa gun salman.

Cikin kishi ya tabashi tace malam mike, tana fad'a hawaye na zubo mata, jin salman yayi shiru yakuma cigaba da baccinsa yasa haushi ya kamata ta jijigashi da karfinta kamar mahaukaciya tace malam ka tashi nace, sai dai salman taga ya koma duk abinnan datake wai bacci yake, tsoro ya kamata kardai mutuwa yai, kallan farha tai dake rakube a jikin bango tana tunanin abinyi, salma ta karaso gunta tana zuwa ta kalleta tace me ya sameshi😠? Farha ta hadI'ye wani yawo tace me yasameshi kuwa banda soyayyarmu da muka tuno? Batai auni ba taji salma ta kifa mata mari, farha ta rike kuncinta tace are u crazy? How dare yo.....salma ta kara mata wani ta d'aya kuncin, farfa ta zabura itama takai hannu, salma tai caraf ta rike hannun, tace baki kai matsayin marina ba, farha tace what? Salma ta kalleta tace farha karkiyi tunanin abinda kike yi tsorone yasa nake kyaleka a'a tausayin ki nake akan kina san maso wani, kuma bari in fad'a miki salman nawa ne wannan kalmar ki ajiyeta a cikin zuciyarki, farha kam jitake kamar ta mutu, salma ta kalli salman sannan ta kalleta tace magani kika samai ko? Farha ta fizge hannunta tace babu wani namiji dayakai matsayin insamai magani,sannan salman shi yakawo kanshi d'akin nan saboda ni, zancen salman nake ne wannan hasasshenki ne kawai, kuma kiyi gaggawar barmin d'aki yanzun nan.

Salma ta kalleta tasa dariya tace farha yanda naga alama kamar kanki ba d'aya ba, kinaso kicemin salman neman mata yake ko me? Sannan ke da ake nema kece idanki biyu shikuma mai neman har ya gama biyan bukatarsa ya kwanta? 😅 me kike tunani? Ni yarinyace? Ko kuwa 'yar kauyen dabatasan komai ba? Farha ta ce oho wannan matsalarki ce amma nidai kibarmin d'aki, salma ta riko wuyanta ta kaita bango tace zan buga miki last warning koda wasa kada ki kuskura ki kara had'a mijina da mazinaci, dan wlh I won't tolerate that.

Salma na gama fad'ar haka ta sake farha tare da karasawa gun salman, duk yanda ta jijigashi bai mekeba, haka kuma duk yanda taso ta d'agashi ta kasa, hawaye tasa tana jijigashi sai dai ina.....?salman baisan ma tana yi ba, gashi ba damar tanemi taimakon wasu kar a gane.

Salma ta sauko daga daga kan gadon, ta kalli farha tace is not a bad idea hakan da kikai, farha dake tsaye rike da kugu tace what? Salma ta karaso inda take tace canjin gurin kwana, farha tace mekike nufi😡? Salma tace ahhh me nake nufi? Nufina kibar mana d'akin mu kwana, farha tace me kika ce? Salma tace ohhh baki ganeba? Nufina ni da mijina😏 da alama ciwon fulani yasa mijina cikin damuwa shiyasa ya nemi mukwana a b'angarenta, farha tace ke me kike tunanin yi? Salma ta jawo hannunta tace kije ki kwanta ko a kusa da fulani ne mu zamu rufe d'aki🙂.

Farha jitai kamar ta shake salma ta kashe wani bakin ciki ne ke yawo akanta, a iya tarihin rayuwarta tana tunanin yaune rana ta farko da aka tab'a ci mata mutunci irin na yau, haka ta fita daga d'akin cikin tsananin bakin ciki.

Salma tai ajiyar zuciya tace dama inada zafi haka? Tafad'a tana kallan salman?

Karasawa tai ta kwanta kusa da salman ta shige jikinsa wasu zafafan hawayene suka zubo mata, ba shakka wannan abun da fulani aka had'a plan d'in amma wannan wace irin tsana ce? Kara shigewa jikisa tai tace *I WILL PROTECT YOU MY PRINCE*.

By AYUSHER MOHD📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.4⃣4⃣

Farha da gudu tai d'akin fulani tana hawaye, fulani kam harta fara bacci, ta mike zaune tace waye wannan?farha ta karasa cikin d'akin, fulani ta kunna fitila, ganin farha yasa tace farha ke kuma menene? Farha kam kuka take, fulani tace meye hakan zakizo kisani a gaba kina min kuka? Farha tace fulani salma ta ruguzamin plan d'ina😭, fulani tace ban gane ba? Wace salman? Farha nan ta shiha zayane mata sai dai bata fad'a salma ta mareta ba😛, ran fulani ya b'aci ta kalli farha bakin ciki da haushin salma yakamata, farha tace yanzu ni da wani idon zan kalli yayana? Fulani ta zuciya tace to ko kin hakura da auransa? Farha tace ban hakura ba, zuwa zanyi gobe infad'ama sarki ya auramin salman ai yayan mahaifinane, fulani tai tsaki tace ke a tunaninki sarki zaiji maganarki yabar ta d'an daya haifa? D'an ma kuma salman? Farha tace fulani yazanyi to? Fulani tace kibari yanzu gobe kiga mai shi salman d'in zai yi, farha tace to, fulani tace ki kwana anan gudun magana tace to.

Salma kam ta dade batai bacci ba, tunani sun cika mata kwakwalwa, sai can cikin dare batasan yanda akai bacci yai gaba da ita ba, hartai sallah, salman bai farfad'o ba, ta shiga tasbihi, sai 8 sannan salman yai juyi, a hankali ya bud'e idansa tare da sa hannu a kai, jin kan yamai nauyi, salma dake zaune tana tasbihi ta mike da sauri tare da hawa gadon, salman ya mike zaune tare da kallan d'akin, me ya kawoshi nan? Dream ne? muryar salma yaji, ta taba shi tace prince ka tashi? Salman ya kalleta sannan ya kara kallan d'akin, dasauri ya diro daga kan gadon ya kalli salma yace me muke anan? Ta kalleshi ta daure sannan ta kakaro murmushi tace kamanta? Jiya anan muka kwana ai😊salman ya kalleta yace what? Sannan ya ka kalleta yace anan? Tace eh mana yai murmushi yace Do u expect me to believe that? Yafad'a yana nuna kansa, kallansa tai takasa magana, agogon bango dake d'akin ya kalla, 8am? Nan ya tuno shidai yasan an kawomai juice daga nan bazai iya tuna komai ba, dasauri ya matso kusa da salma, ya rike kafad'unta yace beauty? Hawayen datake b'oyewa ne suka zubo, ya kalleta yace me yafaro? Ki fad'an gaskiya, salma ta kalleshi tace ba abinda yafaru, salman ya rungumeta a jikinsa yace bakyaso raina ya b'aci ko? Ta d'aga kai yace amma karki manta nace mu daina b'oyema junanmu komai, salma tai shiru can tace maganin bacci aka sama, dama jikinshi ya bashi yai ajiyar zuciya yace anso amin sharri kenan? Ganina anan ba riga, salma tai shiru, salman ya kara kankameta yace and u protect me ko? Salma dai hawaye ke zubo mata, d'agota yai yasa harshe ya lashe hawayen dake zuba a idanunta, salma kam lumshe ido tai.

Salman ya kalleta bayan ya gama yace beauty banason hawaye su dinga zubowa daga kyawawan idanun nan naki, ta bude ido a hankali tana kallanshi, yace don't worry this time I will take care oh them, ya fad'a tare da saketa yace mu fita bazan iya sallah anan ba, salman yad'anyi gaba tare da zura rigarsa, a zahiri ji yake zuciyarsa kamar zata fashe dan bakin ciki, amma yana tunanin in ya nuna gazawarsa ya salma zatai? Wayasan jiya ya tai? Hamdalla yai, lalai shikam yaji dadi samun mata kamar salma sai an tona.

Sun fito harsunyi hanyar fita salman ya kalli salma yace beauty muje muga fulani, ta kalleshi tace da saffen nan? Yai murmushi yace ke kina tunanin jiya sun yi bacci? Tunda kin wargaza musu plan? Kasa tai da kanta, nan sukai d'akin fulani.

Ai kam fulani da farha tunda sukai asuba basu samu bacci ba suna zaune suna tunanin me zasu shirya gaba, salman yai knocking fulani tace waye? Salman bai magana ba ya tura kofar, fulani na zane a kan kujera farha na gefenta kad'an, salman yai murmushi ba shakka tare suka had'a, bai taba tunanin farha haka take ba, kallan kofa sukai a tsorace farha take kallan salman amma dayake fulani ta kware tace salman shigo mana, kofa ya kalla tare da cewa beauty ki shigo mana, salma ta shigo d'akin, salman ya kalli fulani yace umma da alama miracle ya faru? Tace name fa? Yai murmushi yace hmm jiya mun kwana anan saboda ke ashe ke kuma sauki har ya iso jikinki😊 fulani ta maimaita kalmar, mun kwana? Lalai yaron nan, salman ya kalli fulani tace baki tambayeni ya kwanan jiya ba? Fulani ta daure tace ya kwanan jiya? Salman yace eh to ba dadi dai, wasu miyagun mutane ne suka kawo min hari? Fulani ta kalleshi da mamaki, salman yai murmushi tare da kama hannun salma yace karki damu umma, ai matata jarumace ita tai yaki dasu, fulani ta makama salma harara, salma ya kula hakan yasa yace zan isar da sako, fulani tace name kuma🙄? Salman yace ki sanar da miyagun mutanen nan in suka kuskura koda wasa suka kara tunanin aikata abinda sukai, sai kuma yai wani murmushi yace umma bansan mezan musu ba dan wlh I won't tolerate it, ba fulani ba, ba farha ba, itakanta salma sai data kalli salman jin yanda ya karara maganar.

Ya kalli salma tare da mikewa yace beauty muje ko? Yafad'a tare da mika mata hannu, mikamai hannu tai cikin sanyin jiki ta mike, sun fara tafiya harsun je kofa su farha da fulani sun kafe kamar gunki, salman ya tsaya sannan yace ahhhh, tare da juyowa farka kam zuciyarta tagama tsinkewa, salman yace umma kisanar da mutanen nan duk Wanda ya taba matata sai kuma ya furzar da iskar bakinsa, yai kwafa kawai yai waje, salma suna fita ta rungumshi,salman ya d'agota yace beauty menene? Tace wait...1 min, salman ya dagota yace muje kin manta mijinki baiyi sallah ba? Takalleshi tace wani irin warning ne wannan? Ni wlh kamar ni kakewa, duk na tsorata, yai murmuhsi yace kyalesu muje kinji, tace to.
Chapter 26 · 0% Book details