← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 38

Sashe 18

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salma kam tana zaune bacci take amma mai wuya, dan wani zazzafan zazzabine ya rufeta ga kanta ciwo yake tana zaune a takure kawai sai nishi takeyi.

A hankali salman ya shigo, gaban salma ya fad'I tare da d'agowa da kyar ta kalli agogon d'akin d'aya saura, ahankali ta maida kanta wasu kwalla suka sake zubo mata, salman ya shigo tare kallan inda take,kallanta yai tare da saurin karasawa inda take ya tsugunno kusa da ita, ahankali yace menene? Yanaganki a haka? Haushin tambayoyin nan ya kamata, salman ya sa hannunsa a goshinta tare da cewa kan ne? Sai dai me? Yanda yaji kanta yad'au zafi yasa ya d'ago fuskarta, hawaye ne ya gangaro mata, cikin rikecewa yace salma menene? Ya naganki haka? Y are u burning? Idanta ta runtse datake jin yamata nauyi, sannan ta girgiza mai kai ahankali tace dare yayi kaje ka kwanta, kallanta yai cikin tsananin tausayi yace wake zancen bacci kina cikin wannan yanayin?

Ta bude idanta ahankali batace komai ba, salman baisan sanda ya jawota jikinsa ba ya rungumeta, sai dai zafin jikinta har jikinshi yakeji, d'agata yai kamar 'yar tsana ya d'aurata akan gado sannan ya miko mata magani, kallansa kawai take dagaske san salman ne yaja mata ciwo? In haka ne ta shiga uku, zuciyarta bata mata adalci ba zata had'ata da san maso wanI.

Hure mata ido salman yai yace me kike tunani? Kallansa tai tare da amsar maganin tasa abaki ya mika mata ruwa ta sha.

Gyara mata pillow yai yace kwanta, kallansa tai inama wannan abun acikin soyayya ne?salman ganin tayi shiru yasa ya kwantar da ita da kansa, tace kaifa?yace don't worry.

Shiru tai tana kallansa sai hawaye, ganin haka yasa ya matso ya zauna kusa da ita yace da ciwon dake damunki zakiji ko da kuka me aka miki? Dasauri ta goge tace ba kuka fa nake ba, in ima zazzabi haka nake, yace au, sannu, juya baya tai ta runtse idanta, wannan wani irin bala'I ne?

Salman sai dayaga tayi bacci sannan ya kwanta a kasa, ranar kam makara sukai sallar asuba, sai 7:30 salma ta tashi dakyar tai alwala tai sallah sannan tazo kusa da salman ta tsuguna ta kura mai ido, hannu tasa akusa da kuncinsa, sannan takai hannun saitin bakinshi, gani tai salman ya bude ido ai kuwa idanunsu ya hadu, da sauri salma ta mike, jikinta duk ba karfi.

Salman ma ya mike yace haka ake tashin mutum? Ta kalleshi batai magana ba dan gabanta fad'uwa yake, salman ya karaso kusa da ita yasa hannu akan goshin ta sannan yai ajiyar zuciya, yace Alhamdulila naga zazzabin ya ragu sosai, salma kam kallanshi kawai take.

Kamo hannunta yai yazaunar akan gado sannan ya wuce toilet, ta bishi da kallo.

Ishaq yazo shiga bangaren fulani yaji masu gadin gun na gulma ya kallesu yace kuzo nan, suka karaso da sauri ishaq yace menene? Sukai shiru, yace kun fad'a kosai na sallameku?d'ayan yace dama jiya ne yarima salman sai d'aya saura ya fito daga gun fulani shine muke tunanin ko laifi yai akamaI fad'a kayi hakuri yarima mai jiran gado.

Ishaq ya shiga ciki da sauri, yazo shiga yaga farha na fitowa, yace farha? Jiya ance kinzo amma danazo ganinki bakya nan, tace muna tare da ya salman ya grn? Ishaq yace sai ina da safen nan? Tace zanje ganin yayana ne, ishaq yasa dariya yace da matar tasa zaki? Tace to meye? Tafad'a tarw da wucewa, ya bita da kallo yace tab amma wannan......sai kuma yace wait..to ai ni adadi na ko😬?nace a dadinka na me?.

Ishaq ya shiga suka gaisa da fulani nan ya tambayeta jiya me salman yai?fulani tace name? Yace ance jiya sai d'aya saura ya fita badaga gunki yake ba? Fulani yace nI? Badai niba, ishaq yace badai yana........wata dariya yasaki itama fulani ta d'ago tasa dariya yace umma lokaci yayi inaji da Abba zai daina damuwa da salman😂.

Farha ce ta shiga bangaren su salma, sai dai ba kowa a falon, ga breakfast nan da alama ba wanda yaci, Haushi ya kamata badai salma tasa yayanta a d'aki ba abincin safen ma taki bari yaci?wani mugun kishi ya kamata kawai ta saki wani kara, salman wanda ya fito daga wanka yanzu, da salma dake cikin bargo, suka fito da sauri, da bayin dake bangaren duk suka fito,farha suka gani kwance tana murkususu akasa, hanne ta kalleta da mamaki, yanzu fa taganta a tsaye?farha kam sai murkususu take da sauri salman ya karasa ya d'agota yace farha menene? Duk ya rikice, salma ta kalli farha dake rike da ciki mamaki take bata fara ciwon cikim ba sai anan?haushin yanda salman ya rikice shine duk ya isheta, jiri ta faraji, ahankali ta juya tai d'aki batare datace musu komai ba, salman ya kalli farha datad'an rage murkususun yace sannu? Ya lafa? Tad'aga kai, nan bayin sukai waje, yataimaka mata ta zauna akan kujera.

Ishaq zaune agaban sarki yana hawaye, sarki yace menene? Kaki magana? Ishaq yace ranka ya dade bansan yaxanyi da kanina ba bayajin maganata sam, sarki yace salman ko?meyai kuma? Yace baya gudun magana yanzu jiya fa sai d'aya saura ya fito daga d'akin farha yanzu me mutane zasu ce😰? Ran sarki ya b'aci nan yasa akira salman.

Salma kam a d'aki kwanciya tai sai taji waya ahankali ta d'aga zee tace Amarya ya ango? Salma tace ni kyaleni dan Allah banajin dadi zee tace kodai laulayi kike? Jitai kamar ana magana a falo, dasauri tace zee ina zuwa.

Dasauri ta fito, fadawa tagani tace lafiya? Tafad'a tana kallan salman dake zaune ko ajikinsa wayama yake dannawa, ga farha a kusa dashi, bafaden yace umarni aka bamu mu taho da yarima salman, tace umarni? Laifi yai ko me? Bafaden yace bamu sani ba sakon sarki ne, farha ta harari salma sannan tace kaji yayana.

Salman ya shareta,salma ta karaso kusa dashi ta fizge wayar yad'ago rai abace yace meye hakan? Tace mahaifinka ke kiranka, salman zai magana sai kuma ya fasa, yace nasani ban wayata? Jitai jiri na d'ibarta ya kalleta yace lafiya? Daurewa tai tace please kaje prince, ya kalleta ganin ta juya tayi hanyar d'aki tana d'an tangadi.

Kallan fadawan yai ga mamakin farha jitai yace ina zuwa, ya wuce d'aki,a kwance ya ganta ya matso daf da ita yace lafiya? Jikin ne? Tace plz kaje gun mahaifinka, yace zanje kawai dai nasan gulmata aka kai, ta kalleshi tace wa? Mikewa yai yace wasu, sannan yace ki d'aure kici abinci, bansan how long zan kai acan ba, kafin tai magana ya fita, ko kallan farha baiyi ba yace muje, nan suka rufamai baya.

Farha jitai kamar ta mutu[truncated by WhatsApp]
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.3⃣2⃣

Salma naji sanda salman ya fita, kanta dake sara mata tadafa,jin ana knocking yasa ta mike da kyar, hanne ce tace hanne ya akai? Hanne tace yarima ya bani umarni dazai tafi insa kici abinci, salma ta daure ta karaso falo tazauna ta kalli hanne tace hanne kinsan abinda yai aka kirashi? Hanne tai shiru, salma tace kifad'amin koma miye ba komai.

Hanne tai shiru sannan tace naji ance wai jiya da daddare sai d'aya saura ko ya fito daga d'akin.....sai kuma tai shiru, salma tagane me ke faruwa, kwalla ya taru a idanunta, zatai magana taji hanne tace gimbiya nikam banasan matar nan, d'azu fa lafiya kalau tashigo naganta fa a tsaye amma wai ima fita naji kararta, nikam bata burgeni😞 salma tai shiru, can tace yanzu tana ina? Hanne tace ta bishi, salma najin haka ta mike tai d'aki tad'au waya takira zee, zee tace kingama? Salma tace zee ki bakin ciki zai kasheni, zee tace name? Nan salma tafad'a mata zee tai tsaki tacs kefa banza ce, zamq zakiyi ta kwace miki miji? Salma dake rike da kanta tace zee ba 'yar kasar nan bace☹salma tace ko 'yar inace nikin ban haushi ma, salma zatai magana taji zee ta katse layin.

Runtse ido tai, nikaina bansan meta tunoba sai ganinai salma ta mike ta shiga toilet wanka tai shaf_shaf ta zura kaya tasa mayafi,duk da batajin dadi amma cikin sauri tai shirin, ta fito.

A waje taga su hanne tace hanne muje, hanne tace ina? Salma tace muje gun mai martaba, hanne ta zaro ido, salma tace muje nace ko? Hanne jiki na rawa tace to, nan sukai hanyar bangaren sarki.

Salman na zaune sai da mai martaba ya sallami kowa sannan yadawo kan salman sai dai dul fad'an dayai salman baice kala ba, hakan yakara tunzura sarki, ya kalli salman yace san farha kake? Insan ta kake to ka aureta banasan iskanci, salman dai bai magana ba, sarki zaiyi magana wani bafade yace mai martaba hajiya farha na neman iso, da mamaki sarki ya kalli salman, sannan yace ta shigo, farha na shiga tafara hawayen munafurci sai dai kafin tai magana bafaden yakara cewa mai martaba gimbiya salma na neman iso? Sarki yace salma? Salman ma da tunda yazo bai d'ago ba amma jin ance salma yasa ya d'ago, farha ma haka, sarki yace ta shigo.

Salma ta shigo a nutse, ta tsugunna ta kwashi gaisuwa sannan takalli farha dake kukan munafirci sannan tai kasa dakai tace ranka ya dade duk laifinane😪,sarki yace laifinki? Kinsan me kike cewa salma? Mijinki ne fa ya munafurceki? Salma takara kasa dakai hawaye ya zubo mata tace jiya wajen 11:30 zazzabi ya rufeni muna tare da farha lokacin zata tafi, yanda taga ina zazzabi ga dare yayi, salman yace zai kira likita shine ita kuma tace tanada magani, shine ya bita ya amso, salman da farha a tare suka kalli salma cikin tsananin mamaki, sarki yace to 11:30 meyakaishi yin awa d'aya a d'akin? Salma tace mai martaba kasan jiya tazo, dole sai ta duba kayanta, sarki yai ajiyar zuciya wani dadi ya kamashi, ya kalli salman yace salman ai sai kamin bayani tun farko, yace kema haka farha, salman yai kasa dakai cike da mamakin furucin salma yace ayi hakuri, sarki yace na hakura ni abinda banaso inji ana gulmarka da zubar ma da k'ima, amma yanzu tunda na gane kowa ya fad'I abinda yaga dama bazan kula ba, salma tace mun gode mai martaba.
Chapter 18 · 0% Book details