← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 38

Sashe 30

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ishaq ne yai sallama ya shigo da sauri, fulani ta kalleshi tace " yanzu nake nemanka ka tayani murna, Allah ya saukaka mana komai."
Ishaq ya zauna rai a b'ace yace " wani sauki koma? Banda tashin hankalin danake ciki?"

Fulani tace " wani bakin ciki bayan Salma da Salman na asibiti."
Ishaq yai tsaki yace "Umma nikam kibar wannan zancen, ni fa kishi ya ciwoni naso makeshi, amma Salma ta kare shi."

Fulani ta mike tsaye cikin kid'ima tace "mene? Ishaq kasan me kake fad'a kuwa? Ishaq bangane kai kaje make Salman ba."
Ishaq ya share zufa data ketomai yace " bama wannan ba Umma, Salman ya ganni yasan ninai."

Fulani tashiga tafa hannu tace "shikenan na shiga uku, Ishaq yanzu yazamuyi? Me yakaika? Nafad'amaka kad'inga tunani da hankalinka."

Ishaq yace "ni dan Allah Umma kidaina min wannan zancen abinda ke damuna ma ya isheni."
Fulani ta zabura yace "meke damunka? Akwai abinda zai dameka daya wuce wannan?."

Ishaq ma ya mike rai a b'ace yace "haba umma ya kikeso inyi da raina? Ina kallo yanzu Salma zata haifi d'an Salman?"
Cikin mamaki fulani ta kalleshi sai kuma ta had'e rai tace "da kanaso ne Salman d'in yasata agaba yai ta kallo ko me?"

Ishaq yace "ba ciki ne da Salma ba ko 'ya'ya d'ari gareta nidai ina santa bakuma abinda yadameni da wani Salman ko wani da zai kawomin matsala."

Fulani data rikece jin kalamansa tace "me kace? Ciki? Ishaq me kake nufi?"
Ishaq yace "ciki ne da salma yanzu aka fad'a a asibiti, menene?, kema kina tayani kishi ko?"
Fulani ta harzuka tace dalla gafara banza, shashasha, Salma nada ciki inta haifi namiji fa? Kai matanka biyi 'ya'yanka hudu amma duk mata, shine maimakon kai tunanin abin da zai faru gaba shine kakemin zancan wata banzar soyayyarka?"

Sai a lokacin ishaq yai shiru, yanzu in bai haifi namiji ba fa? Kenan za'a iya bashi mulki daga baya aba d'an salman, yazaiyi? Yanda ya tsani Salman d'in nan."

Fulani tazauna tare da dafe kai tace "yau nikam da wani hannu na tashi? Wannan bakin ciki kala_kala?"

Farha ce ta fito da sauri ta kalli Fulani tace " zanje asibiti ance Yayana bashida lafiya," Ishaq yai tsaki yace to salman ya ware, sai dai in Salma zakije ki dubo daganan sai ki tayashi murna tunda sun samu karuwa."

Farha takaraso tace "bangane ba? Karuwa kamar me?"
Ishaq yace "ciki gareta."
Farha tace "mene? Ciki? Bangane ciki ba?."
Fulani dake rike dakai tace " Farha yaz'amuyi Salma dai ciki gareta."
Farha ta zube agun ta d'aura hannu akai ta sa ihu tace " ciki? Shikenan nasan yaya Salman bazai kulani ba, Amma wannan Salmar akwai yar iska."

Nace ko kuma ku ba.....

Salmah kam tana kwance itakam rayuwa mai dadi take acikin baccinta, yau taga fuskar saurayin nan Salman ne suna zaune a bakin ruwa, ta kwanta akan cinyarsa shikuma yana rike da littafin story book yana karanta mata, sosai takejin dadin labarin sai lumshe ido take, Salman ya kalleta yai murmushi sannan ya rufo gefen fuskarta da littafin hannunsa, yakai bakinshi kan lebenta ya sumbata, ido ta rufe cikin murya kasa_kasa tace "in aka ganmu fa?"
Salman yace "menene aciki? Keba matata bace?"
Murmushi sukai ta kalleshi tace "ka cigaba," tai maganar cikin shagwaba nan ya cigaba da karatun.

Sarki yau farin ciki ba'a magana zuciyarshi kamar ta faso, sai dai yana tsakiyar murnar yin jika dazaiyi ta tsatson Salman waziri ya nisa yace "amma akwai wata 'yar matsala, Salman nafama da wani ciwo."
Cikin tsoro Sarki yace "ciwo? Wani iri kenan?"

Waziri yace "yarima Salman na fama da ciwon heart attack."

Cikin rud'ewa Sarki yace "heart attack? Kasan mai kake cewa kuwa waziri?"
Waziri ya tsugunna yace " tuba nake ranka ya dade."
Sarki ya rike kansa, yama kasa magana.

Waziri yace "amma akwai likita, ance inyazo insha Allahu da yardar Allah Salman zai warke."

Sarki yai shiru can yace " waziri kasani yaron nan kaf cikin 'ya'yana ba wanda nakejinshi har cikin jikina irinsa, in wani abun ya sameshi bansan yazanyi ba, da alama ciwonsa ma nine sila."

Waziri yace "ya kake fad'an haka ranka ya dade? Kaine sila?ciwo ne dai daga Allah."
Sarki yace "nasani ciwo me daga Allah amma nasan bakin cikin daya kunsa yana yaro shiya jamai wannan ciwo."
Waziri nan ya shiga bashi baki, sai dai Sarki jinsa kawai yake, can yace "naji waziri yanzu ana isha'I kazo ka kaini inga halin dasuke ciki, waye agunsu?"
Waziri yace "na kira zeenatu tace tana hanya."

Salman ne ya kallin likitan dayazo duba Salma yace "yanaga bata farka ba?"
Likitan yace "karka damu kila itama tanajin dadin rayuwar da takeyi ne acikin baccin, amma zata farka nan bada dadewa ba."
Salman ya kalli Salma cikin tsananin tausayi.
Likita yace "amma ina tunanin za'a kara mata jini kad'an." Salman ya kalleshi yace "akara mata nawa ko leda nawa ne dan kuwa O+ gareni bana tunanin akwai matsala."
Likita yai shiru can yace "amma ina ga kai da bakada lafiya bai kamata aragema jini ba."

Salman yace "jikinka ne ko nawa? Ko kuwa inwani abun yasameta zakai d'au responsibility?"

Likita ya had'iyi yawo yace "a'a ayi hakuri yarima, bansan kalmar zata b'atama raiba."
Salman yamaida idansa kan Salma tare da riko hannunta cikin zuciyarsa yace " Beauty please"
Tunowa yai yakamata ya kira Abban ta, to karkuma ya tada musu hankali, ajiyar zuciya yai yace "Beauty yazanyi?

By *AYUSHER MOHD*📚
© *NWA*
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.5⃣1⃣

Zeena tazo sai dai duk yanda ta roki Salman akan yaci abinci amma yaki, tai fad'an har ta gaji, shikam yama dags akan ta rakashi agwada jininsa su tabbatar zai iya bata, a d'eba asa mata.

Zeena ta kalleshi tace " haba Salman mai yasa kake haka? Kabari gobe in an kira 'yan uwanta sunzo sai a gwadaso asamu wanda yai a kara mata, amma kai baka da lafiya ina kai ina bada jini? Sannan gashi sam kakicin abinci."

Salman ya kalleta yace " Aunty zeena har dake? Nad'auka ke ba halinku d'aya dasu ba, taya zakice gobe in 'yan uwanta sunzo, Salma matatace kuma saboda wani abun dabai gagareni ba bazan nuna mata nafisan kaina akanta ba, abinci kuma inkinga naci abinci to tabbas naga matata taci." Yanakai nan ya fita, Zeena tausayinsa ya kamata, wani irin so Salman kema Salma haka? A da taga ko kallo bata isheshi ba, yaushe abu ya juya haka?.

Salman da kanshi yaje lab d'in suka gwadashi sun tabbatar O+ gareshi kuma zai iya bata, wucewa yai gun likita yace "tashi muje ko?"

Likitan yace "Yarima dan Allah....."
Cikin fad'a Salman ya katseshi yace "Karka bata min rai, inace inason abu to kamin kafin ranka ya b'aci, nagaji da ganin matata a kwance."

Likitan yace "kayi hakuri ranka ya dade amma matarka badan jini bane taki tashi."
Salman yace " Naji, amma wuce muje inka kara mata jinin sai nu jira in ta wuce hours d'in daka fad'a hmm bansan kuma mai zan ma ba."
Salman ya juya, da sauri likitan ya fito sukai shigo da kayan aiki d'akin, an saita komai sai da ba'a fara ba mai martaba ya iso shida waziri.

Salman na ganinshi ya had'iyi wani abu tare da kara d'aure fuska, Sarki ya karaso kusa dashi, waziri ya kalli Zeena dake gaida Sarki yace inkin gama kowa ya fito yabasu guri, tace to.

Kowa ya fita yabarsu su biyu sai Salma dake kwance, Sarki ya kamo hannun Salman ya rike yace "Salman na tsorata danaji ance bakada lafiya na d'auka kaima rasaka zanyi."

Salman ya kalleshi idanshi yai jaa, dasauri ya maida kanshi gefen da Salma take, Sarki yace " Salman meyasa baka sanar dani larurarka ba? Ina zaune bansan halin da d'ana yake ciki ba."
Salman ya kalleshi yace " Ina zaka sani Abba? Tunda mukamin ka yafini daraja? Tunda kake dani ka taba tambaya ta yana tashi? Meke damuna? Naci abinci? Bani da wata matsala dake damuna?"hawaye ya zuboma Salman a ido yacigaba" Kun rufe mutuwar Ummana saboda san mulki, kun turani wata kasar dan bazaku iya kula dani ba, sannan yanzu Abba katambayeni wai zancen ciwo na? Ban fad'ama ba?"
Ya share hawayen dake zubo masa yace " kasan wace irin rayuwa nayi? Kai dai kullum kana zaune akan kujerar mulki sai abinda aka fad'ama."
Salman na zuwa nan ya runtse ido, hawaye suka kara zubomai ya share tare da kallan Salma, yace "zan iya jure komai amma banda a tab'a matata."

Sarki da tunda Salman yafara magana kwalla ta cika taf a idanunsa yasani sarai abinda Salman ya fad'a duk gaskiya ne, amma ya zaiyi? Tunda haka mulki ya gada.
Kafad'ar Salman ya dafa, ya d'ago ya kalleshi cikin tsananin tausayin d'an yace Salman na sani duk wani abu dake damunka laifinane na sani amma dan Allah Salman ka cirema zuciyarka komai ko ka samu nutsuwa, kaduba matarka, ciki gareta ka taimakeni Salman ka cire komai aranka kafin d'anka ya taso da kiyayyata, Salman kayi hakuri akan duk abubuwan dana maka, nasani sarai abin na damunka amma zuciyata inta ganka sai inji tausayinka bazai bari in tada maganar ba."
Salman ya kalleshi yace " So nake ka bani izini ind'au matata in bar gidan, dan banasan zama a cikin gidan, nafisan inda zamuyi rayuwa kamar kowa nida abinda za'a haifarmin."

Sarki ya kalleshi tare da jijiga kai, yace Salman banda wannan, zan iyama komai Salman amma bazan iya barinka nesa dani ba, bayan kaine magaji na."

Salman yace "magaji? Magajin me fa?"
Sarki yace "mubar maganan nan Salman dan Allah."
Salman yace " Abba?"
Sarki ta rike hannun Salman yace "Salman kayi hakuri ka yafema wannan mahaifin naka, yasani yamaka laifufuka da dama, amma ka sani kullum kana ranshi dai dai da minti 1 bai tab'a mantawa dakai ba."

Salman hawate suka kara zubomai, yana tsananin san mahaifinsa yazaiyi? Idansa ya runtse baice komai ba, Sarki yai shiru can yace "ance hatsarine, bakasan waye mai wannan d'anyen aikin ba?"
Chapter 30 · 0% Book details