← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 38

Sashe 10

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai naga yanada d'an manner nasan yanda zanyi yaban bargo,
Hijab din sallarta tad'auko tasa a tsakiyar gadon, yana fitowa ya kalleta yace baki sauka ba? Tace oho gashinan na raba mana ni nan bangaren kai nan, salman yai wata dariya yace what? Gadon nawa kika raba harda wani ni nan ke nan? Tace eh sannan kar wanda ya kuskura ya gangaro bangaren d'an uwansa😏 salman yace lalai kin girma dayawa tace da nid'in yarinya ce? Yace kin cire hijab dinnan kin sauko ko kuwa? Tace kazabi d'ayan uku, ko in koma falo na kwanta, ko kaban bargo ko kuma mu kwana a haka😏 salman yakalleta yace in zaba? Tace eh u have to choose a'a bama haka ba u most choose😎....

😳🙊nace lalai salma an zake😜

By Ayusher Mohd📚
[11/13, 10:23] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣8⃣

Salman yai ajiyar zuciya yace ke karki kuskura kib'atamin rai a daren nan dan zakisha mamaki, salma tad'an juyakai batare datayi magana ba, salman yace kwanta!in so kike mu kwana tare😏 dasauri ta juyo tace na'am? Yace eh ba haka kike son jiba? Ta mike daga kan gadon tace yaza'ayi mukwana tare😳? Salman ya matso inda take yasa hannunshi a kugunta ya janyota jikinshi, da sauri ta runtse ido, yai wani murmushin mugunta yace ba haka kike so ba? Ta d'aure tazare jikinta tace a'a ka kwanta😞.

Salman yace a'a mukwana taren ko? Dasauri ta girgiza kai tace a'a nabarma bargon da pillow d'in yaI kwafa aranshi yace kin d'aukan bansan burga zakimin ba? .

Kwanciya yai tare da jefo maya pillow din, ta amsa tarr da kallanshi☹, sunyi shiru dukansu kowa da abinda yake sakawa,can tad'aure tace sorry cikin sanyin murya, shima cikin magana mai sanyi yace 4 what? Tace maganar dana fad'a dazu I think bai kamata nafad'a ba, salman yad'anyi juyi yace at least kinsani, tace eh amma kaima u overreacted yace so kike nima in baki hakuri? Tace in mutum yai abinda bai daceba hakuri yake badawa ai, yace in hakane I can't zatai magana yace karki damen bacci nakeji🤔 aranta tace kamar nadamu muyi maganar😒.

Karfe 4 ta tashi tai alwala ta fara nafila batai minti goma da tashi ba salman ya mike ganin tana sallah kwarai yaji dadi aransa, mikewa yai yashiga toilet shima yad'auro alwala ya fita, harya dawo tana zaune tana karatun qur'ani sai dai a zuciyarta takeyi.

Wucewa yai ya hau gado sai dai ba bacci yai ba waya ya d'auko yana dannawa.

Wajen 7 ta kwanta yana kallanta sannan shima ya kwanta, basu tashiba sai da hanne tai musu knocking, salma ta mike tare da bude kofar, hanne tace ranki ya dade ku shirya zaku gaisuwa gun matan gidan, tace to nagode, hanne tace aikin nane ai.

Salma takoma ciki tare da kallan salman tace zamu gaisuwa, yai tsaki tare da juya mata baya ta makamai harara aranta tace so rude.

Kaya ta d'auka ta wuce toilet tai wanka ta goge jikinta tasa kayan, tana fitowa ya shiga ta kalleshi tace mutum sai isa🤔? Yace I can hear u dasauri ta rufe bakinta, ta shafa mai tare da murza hoda, ta zura kwalli tayi kyau dan dama mai kyan ce.

Mayafi tad'auka tare da cewa dole insa akawomin Abba yad'inkon hijabai ko biyu ne ta yafa mayafin tai falo, shayi ta had'a ko kulolin bata budeba, ta kurba ruwan tea din jin daxafi yasa ta ajiye tashiga tunani, ko ina yaya kamal? Wai ahaka zata kare rayuwarta a gidan nan? Kwakwalwarta ta cunkushe da wannan tunanin da basu da amsa, batasan salman harya fito ya zauna a kujerar gefenta ta d'ayan bangaren, jin motsin bude kula ne yasata ta d'ago wata baiwa ce ke bude kwanukan tana tambayarshi abinda yakeso? Salma takalleshi ta tabe baki, a ranta tace abincin ma sai an budema? Ko kallanta baiyiba itama tad'auke kai tashanye shayinta ta mike da sauri hanne ta karaso tace ranki ya dade bakici abinciba ai😞? Salma tace banajin ci ne hanne karki damu, hanne tace jiyamafa bakice na safe ba, salma tace nakoshi ne, hanne zatai magana salman yace kin min shiru ko kuwa? Batace ta koshi ba? Hanne tai kasa tace yahkri ranka ya dade, salma ta kalleshi ranta in yayi dubu ya b'aci ta koma falo ta zauna a kujera batare datace komai ba.

Salman harya gama sannan, ya mike tare da kallanta dasauri hanne takarasa gunta tace ki taso, salma ta d'ago ganin salman na kalleta ta harareshi tare da d'auke kai, ya ce taso mana? Ta mike fuskarnan a hade suka fito a jere ya matso yace kin manta abinda nace miki ko? Karki bari wasu susan halin da muke ciki ta kalleshi tace kaikuma fa? Yace ni me? Tace shikenan.

Ya juya kai nan suka wuce bayi nata gaisuwa, salma na amsawa ya matso yace kidaina amsawa ki wuce kawai tace amm...yace bansan musu tad'an turo baki batarr datayI magana ba haka suka karasa bangaren hajiya karama tana zaune a kilisarta sun shiga sun gaisheta ta amsa tare da tambayar salma yazaman bakunta, daganan bata sake magana ba shima salman haka, nan suka taso sukai hanyar bangaren hajiya babba itama sun gaisa tad'an tambayi salma koda abinda takeso? Tace a'a nan ma taga sunyi shiru har suka taso, mamaki ya isheta haka ake rayuwa a gidan bad'an hirar rayuwa da shakuwa?

Sun isa bangaren fulani zasu shiha ishaq ya taho shida mannir tundaga nesa ishaq kebin salma da kallo har karkata kai yake, suna isowa kofa ya kura mata ido sam yamanta da salman, sai da mannir ya kula yadan tabashi sannan, itakam salma duk ta tsargu ganin irin kallan dayake mata, ishaq ya had'eyi yawo tare da cewa Ango kasha kanshi😁 salman yaI murmushi tare da cewa muje ciki ishaq ya kalli salma yace Amarya muje😁, takalleshi tareda yin murmushi ai jiyai kamar ya fad'I har salma ta shige ciki itada salman ishaq bai kula ba sai da mannir ya matso yace yaya me kake kitsimawa? Ishaq yace mannir waccen yarinyarce matar salman? Mannir yace eh mana dan ma baka ganta agun dinner ba🤔 ishaq yai ajiyar zuciya yace amma na cuci kaina ai dani ta dace gaskiya da sake😠.

Mannir yace sai hakuri dan tazama matar kanninka, haushi ya ishi ishaq yace bazan yarda ba kasan irin wannan matar nake dreaming arayuwata? Najib yace yaya mai kake shirin yi? Yace I have to think amma bazan bari ta kubcemin ba😕

ishaq😳

By Ayusher Mohd📚
[11/13, 10:23] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣9⃣

Salma da salman zaune a gaban fulani, sun gaisheta ta amsa fuska a sake tare da cewa salman da ai jiya kasa hakuri nai nafara tunanin inje inga salma da kaina dan randa aka kawota banganta sosai ba saboda mutane dake bangarena😀.

Salman ya kalleta yasani sarai munafurci ne amma sai yai murmushi shima yace gashi ai tazo gaisheki, fulani ta kalli salma tace salman kayi dace yarinyar tamin sosai😊, ya kalleta sannan ya kalli salma yace nima tamin fulani😊, salma ta kalleshi tasan sarai karya yake amma batasan meyasa ta jin wani abu aranta? Salman ne ya kalli fulani zai yi magana yaji an turo kofa, baijuya ba dan yasan su ishaq ne, dasauri ishaq ya karaso ya zauna kusa da fulani, ishaq ya kalli salma yace Amaryarmu ya kike? Salma tad'ago ta kalleshi ganin yanda yake kallanta yasa tai kasa dakai tace lafiya, yace kanina dai baya wahalar dake ko? Takalli salman, tai murmushi tare da cewa a'a, ishaq yad'an hade rai yace salman akula da ita fa? Salman yace basai ka fad'aba, maganar taba ishaq haushi amma ya daure harsu salman suka fita yai tsaki yace ni wlh an cucen.

Fulani datasan halin d'anta sarai inyaga kyakyawa tace kul! Wlh ishaq ka fita daga idona, yace menai kuma? Tace nafad'amaka dai dan nasanka.

Salma kam suna isa d'aki ta kalli salman tace kai nafijin dadin fulani kamar kunfi shakuwa😀 gaskiya tanada mutunci, amma.....wani mugun kallo yawatsa mata yace will u keep ur mouth shut?tace me kuma nai? Dan nace fulani nada..karasowa yai ya jawota jikinsa yace what did u know? Idanta a runtse, ahankali ta bude idanunta ya kalleta jiyai wani abu na tsirgamai dasauri ya saketa, ya juya baya yace in bakisan komai ba kiyi shiru banasan magana😏 itama ta juya tace to.

Falo salman ya fita, ya kunna tv, ta fito ta tsaya a jikin labile tace aran waya please? Ya juyo yakalleta yace bangane ba? Tace uhm Abbana nakesan ma waya, yace sai kije kimai ai🤔tace to ai banda waya☹.

Kallenta yai tare da murmushi ya taso ya shigo d'akin tare da d'auko wayarsa dake kan side bed, ya kalleta yace baki da waya?tace eh mana baka kula ba? Yai dariya yace in these era? Tace to dole ne? Yace a'a ba dole bane amma in har kinaso inbaki aran wayata kidinga waya tofa dole kidinga bin umarnina😉 , tace da bana bi🙄? Yace inafa kike bI? Tai shiru can tace ai kai din ne, yace ni me? Tace kaima kasani ai yace bansani ba, tace to yanzu dai kaban nai waya sai musa rule din daga baya, yace a'a banyarda ba, ta turo baki tace to naji zan d'inga bi bani nai wayar, ya mika mata tare da zama akan gadon, takalleshi tace bazaka fita ba? Yace infita kimin bincike a waya? Tace ni😳? Yamata alama da ido yes, ta koma can jikin kujera ta danna number Abba, ringing biyu ya d'aga.

Tai sallama ya amsa tace Abba salma ce, yace salma nagane ya gida? Tace lafiya Abba yasu umma? Yace duk lafiya, tace Abba yaya kamal fa?

Salman dake zaune ya d'ago ya kalleta dama tanada yaya? Sai dai yanda yaga ta kalleshi ta kuma sa hannunta ta toshe wayar yasa jikinshi yabashi da wani abun, Abba yace salma meke damunki? Wani kamal kuma? Tai kasa da murya tace nasani Abba so nake naji ko yana gari ko ya koma? Abba yace bansanI ba kuma indai akanshi zaki dinga kira to karki sake kirana tace Abba.....jitai an kashe tace Abba☹.
Chapter 10 · 0% Book details