← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 38

Sashe 21

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fulani zaune a kilisarta bakar maganar da salman ya fad'a wa d'anta ta dameta dayawa wata baiwa tasa ta kira mata ishaq ganin yau sam bai shigoba da alama shima haushin abinda fulani ta fad'a yake.

Salma ta shirya tsaf, dan salman ya fita makaranta kuma tafad'amai zataje gaida fulani, sun fito itada hanne, azahirin gaskiya gani take kamar bai kamata ace sai lokaci_lokaci take gaida fulani ba, ganin matan gidan kusan kullum sai sun gaidata, tana tsoron kar hakan yaja ma salman wani abun.

Sun isa bangaren, wata baiwa tace kishiga tana kilisarta,tace duk bayin su fita amma ke ai ba matsala, salma tace tom tare dayin hanyar.

Fulani zaune itada ishaq takalleshi tace wai haushi kaji? Yace umma ni narasa me kikeso inyi ki yabeni? Tace ina yabonka ishaq kawai banaso ne kadinga zama na karshe in aka had'aka da salman,ishaq yace nifa umma na tsani ganin yaron nan dan yana takuramin, daidai nan salma tazo shiga sai dai tasa hannu zatai knocking kofar taji fulani tace kodai musa amaidashi kasar waje? Ishaq yace ko? Tace eh mana ni kaina na tsani ganin salman gashi yai tamin kwarjini, inaji dai kawai musan yanda zamuyi yakoma can, dama acan yataso, salma da jikinta yashiga bari sai jitai ance in_law me kike anan? Salma ta juyo ad'an tsorace ta kalli farha, dakyar ta saisaita kanta ta kalli farha tace yanzu nazo tafad'a tare da kwankwasa kofar, fulani ta kalli kofar tace shigo? Salma ta d'aure murd'a kofar, farha ta kalleta tai tsaki tace da alama yau ranar ba sa'a tunda nafara karo da waccen.

Salma jiki a sanyaye ta shiga tazauna tare da gaida fulani,ta amsa itama a sanyaye dan tana tsoron ko taji, ishaq kam ya zuba mata ido kawai yana kallo,fulani ta kalli salma tace ina d'an nawa? Salma tad'aure tasaki murmushi tace yana makaranta, fulani tace salma ki kulamin da d'ana kinji? Kinga maraya ne😊 salma aranta tace lalai akwai 2face dayawa a duniya amma afili tace insha Allahu, ishaq ya kalleta yace ni naza'amin magana ba🤔 tad'an dago ganin kallan dayake mata yasa tamaida idanta kasa tace ban kula kana nan ba tuba nake, sai a lokacin hankalin fulani ya kwanta, indai tajisu to aikuwa tasan ishaq nanan, ishaq yace au hakane? Wato jikinki bai......dasauri fulani ta katse maganar da cewa salma kingadai sarki natsananin san salman dan Allah ki taimakamai karya dinga abinda ransa zai b'aci tace to, tare da kallan ishaq, tana mamakin me yakesan cewa d'azu.

Mikewa tai taredayi musu sallama, tana fitowa ta kalli kofar d'akin tace a waje kamar.......ta juya tai waje duk jikinta a sanyaye, tana shiga d'aki ta zauna abakin gado, lalai yau ta yarda in mutum ya rasa uwa to fa yayi babban rashi, idanta ya ciko da kwalla tausayin salman ne ke ratsata, tace ko ya sani? Can tace da alama ganin yanda
Yake musu.

Bayan isha'I salman ya dawo tana zaune tana game a waya, tanajin motsin kofa ta mike da sauri tad'au turare ta kara fesawa ta gyara zama, salman ya shigo da sallama salma ta amsa tare da murza iso, yashigo yace wai bacci? Tad'an kalli agogo tace kadad'e harna fara bacci☹ yakaraso yace uhmm anya kuwa baccin ake? Tace eh mana🙄, yai murmushi tare da sa hancinsa a wuyanta yace amma kamar yanzu akasa turaren na? Sannan ya sa hannunshi a bayanta yace kamar kuma wayarnan amfani ake da ita? Ta mike da sauri tare da ware ido ta turo baki tace ahhh wai kai ba'a fooling d'inka☹? Yajawota jikinsa yace inafa bayan baki iya pretending d'in ba? Kawai dai kice so kike ind'inga dawowa da wuri ko ba haka akeso acemin ba? Yafad'a yana kallanta, dasauri tashige jikinshi jin wani shock yai daga kansa har zuwa 'yan yatsun kafarsa, jiyai salma tace ni kad'ai d'in ne ba dadi☹ yai gyaran murya sanna yace insamomiki 'yan tayin zama? Tace suwa? Yace inada kanne mata ai ga farh.....tureshi tai tare da zama akan gado, ya kalleta ba shakka wannan kishi salma takeyi, kenan itama tana sanshi? Zama yai kusa da ita yace in mutum baisan abu yafad'a kawai bawai yad'inga had'e rai ba🤔 salma tad'an matsa tare da harde hannayenta tace eh banaso, happy? Yai murmushi batai auni ba taga kan salman a cinyarta, ta runtse ido inama salman na santa? Da gani zatai tafi kowa farin ciki a duniya, a hankali ta bude idanta, salman na kwance idanunsa ta kalla, shima kallanta yake, dasauri tad'auke idanta jin gabanta na fad'uwa, salman ya kalleta tare dasa hannu yadawo da fuskarya kansa yace yau nagaji shiyasa zan d'an kwanta anan, an bani pass? Ta kalleshi tai murmushi tace kunsha yawo kenan da najib ya kankance ido yace ummm da alama matar nan tasa ana bina🤔 salma tai dariya fararrn hakoranta suka fito, tace sai an dubamin? Bayan nasan me kuke a skul d'in? Yace ahh ashe fa hakane.

Tace yaushe zaka fara karatu? Ya kalleta da mamaki yace da wasa nake? Tace nasani da saninka kake mika farar takarda, yace what? Mezai sani hakan inba rashin sanin amsa ba? Tace uhmm anya kuwa? No matter how much I think zuciyata ta kasa yarda da hakan,u are a smart person babu yanda za'ai kace ba ka fahimtar komai, salman ya juya kansa zuws cikinta yace mubar maganar, salma tasa hannu akansa tace why? Yace later, tai ajiyar zuciya tace to.

Salman yayi shiru a jikin salma, zuciyarsa na kwadaitamai kusantarta, sai dai yayi alkawarin a rayuwarsa bazai tab'a kusantar macen dabata sanshi ba, yazama dole yatantance meke ran salma.

Salma kam ta d'auka bacci yake tai shiru tana kallansa, maganar su fulani ce take dawo mata, shafa kan salman tai tausayinsa na ratsata.

Salman ganin bazai iya bacci a haka ba yasa yai kamar yana bacci, yad'an mirgina, salma ta matso daf da fuskarsa tana kallansa a fili tace
*Sweet one time, cold one time, rude one time, mean one time and romantic one time*
Tai ajiyar zuciya tare da rufe ido, can ta mike tai shimfid'a ta kwanta.

Salman ya bud'e ido ahankali ya maimaita kalaman data fad'a yai murmushi tare da kwanciya wani farinciki yakamashi da alama salma nasansa.

By Ayusher Mohd📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.3⃣7⃣

Yau juma'a salman na kwance har wajen 10, salma tad'an tabashi ya motsa tare da bud'e ido cikin kalar bacci, yace ya? Tace skul fa? Yace bazani ba, yafad'a tare da juyawa tai ajiyar zuciya tare da mikewa,jawota yai takoma ta zauna tare da kallanshi, ya d'ago a hankali yace kishirya zamuyi tafiya bayan an sauko, takalleshi tace zuwa ina? Ya saketa tare da juya baya ta kalleshi aranta tace ko ina zamu?

Mikewa tai ta fita falo, tana zaune tana kallo, salman ya fito, ta kalleshi har yayi wanka tace ka tashi? Yace umm tare da zama, farha ce ta shigo salma ta harareta aranta tace yau kuma? Salman ya kalli farha yace kin iso? Salma ta kalli farha kin iso? Farha ta kalleshi tace na iso yayana😊, takalli salma tace hi in law salma tace sannu, farha ta kalli salman tace yaya rakani zakai fa☹? Salman yace ina? Tace kai yaya kafa sani, salman yace yanzu? Yafad'a tare da kallan salma dataci magani ta kafeshi da ido, salman yad'auke kai yace muje, farha ta kalli salma ta saki wani murmurshi, tai gaba.

Salma ta makama salman harara tai d'aki, d'aki da sauri ya kalleta yai murmushi tare dayin waje.

Salma tai d'aki tare da kwanciya tad'au pillow ta d'aura akanta.

Salman na fita suka karasa gun mota da farha, yad'au waya yakira wani, suna zuwa bakin mota farha taga driver takalli salman, salman yakalli driver yace habu kiranka nai zaka kai farha unguwa, dasauri farha takalleshi tace yayana😳? Salman yace inzaki fita kid'inga neman habu zai dinga kaiki, yana kainan yai gaba.

Farha tabi bayanshi da kallo tana kiranshi ko kulata baiyi ba, habu yace muje hajiya? Farha cikin masifa tace bazani ba😡 tai cikin gida da sauri tana shiga tad'auko akwati ta shiga zuba kaya tana hawaye.

Salman na shiga yai d'aki, a kwance yaga salman ta rufe kanta murmushi yai tare da zama kusa da ita, ya zare pillow din, ta d'ago a hankali ta kalli salman, cike da mamaki tace har ka dawo? Ya kalleta yace ina zani da? Tace ba fita zakuyi ba? Yace ahh yazanyi? Matata sai kishi? Tace bafa kishi bane☹ yace ummm to menene? Tace kawai dai.....yace hmm kinshirya mana kayan? Tace bakace sai an sako ba? Yace nafasa mutafi yanzu.

Tace wai ka fad'a? Yace na sanarwa mahaifina ko akwai wanda yazama dole infad'amai bayan nan? Takalleshi sannan tai murmushi tace nibance ba, ahankali ta mike ta jawo karamar jaka, tafara zuba kaya tana gamawa yace muje, tace wai saurin nameye?yace so nake insami sallah acan, tace to.

Sunfito tasanar da hanne, nan sukai waje suka shiga mota, suka fara tafiya, sunyi tafiya mai nisa harta daina ganin gari, wudil taga ansa ta kalleshi tace wudil? Yai murmushi tare da gangararawa, sai da suka je karshen garin wani d'an karamin had'adden flat suka isa, ahankali mai gadi ya bud'e gate d'in salman ya karasa yai parking, salma ta shiga kallan gida sosai gidan ya burgeta gashi ba girma gareshi ba, sai kyau da tsari, mai gadin ya iso da sauri ya kalli salman yace yarima barka da isowa, shekaru dayawa? Salman yace ashe zaka gane? Yace ina na isa namanta dakai? Bayan nasan bamai zuwa sai kai? Salman yai murmushi ya fito,mai gadin yai saurin budewa salma kofa tare da gaisheta yace kai uban gidana masha Allah, salman ya kalli baba tsoho yace kai baba? Nan yad'au jakarsu yai ciki, salman ya kalli salma yace kishiga bari nai sallah tace to.
Chapter 21 · 0% Book details