← Book details Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 38

Sashe 17

Ni Da Prince Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salman kam yana fita ya kira wayar salma,itakam hartagaji da mitar goggo na tazo ta tafi, ganin kiran salman yasa ta mike da sauri ta d'aga, salman yace kinjini shiru ko? Tace wani abun ne ya tsare ka? Yai murmushi yace ganinan zuwa, kafin tai magana ya katse, ta girgiza kai sannan tai murmushi, goggo tace shi ne? Salma tace eh gashinan, goggo tace ah to gwara dai, dan naga akwai wata yarinya a garinmu daga zuwa ganin gida mijin bai kara komawa ba sai takarda tagani, salma tace shi ai ba haka yake ba😒goggo tace iye? Lalai su bera, salma ta juya zatai d'aki ganin kamal tai a tsaye da alama yaji me suka ce ta, dasauri tai d'aki.

Salman ya iso ya kira salma tafito, kamal na kallanta kamar yai kuka sai dai ba yanda zaiyi, salma ta shiga mota ta kalli salman tace irin wannan jirgawa?ya juya yace don't tell me harkin gaji da ganin gidan kinaso ki tafi naki🤔? Dasauri tace bafa haka nake nufi ba nufina ba kira🙄.

Wata sansanyar dariya yai yace abinda na dade bangani ba yau nagani shiyasa na sha'afa, duk da gaban salma ya fad'I amma tadaure tace da alama wannan abun nada matsayi, salman yace ehm sosai,yafad'a yana kallanta, ta bata rai tace mutum ne?yace eh, cikin tsoro tace mace?kallanta yai yace lawyer kika koma? Tace bahaka bane yanda kai maganar ne ai☹yace hmm.

By Ayusher Mohd📚
[11/13, 10:23] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.3⃣0⃣

Atare suka saho, har suka isa part d'insu, sai dai me? Suna shiga falo salma taga wata budurwa zaune tana kallo, mamaki yakamata, budurwar tana ganinsu ta mike da sauri tace yayana......sai dai maganar ta ta tsaya a wuya ganin salma, kallanta ta shiga yi, badai itace matar ba?wannan kyakyawar😳? Salma ma kallanta take, kamar tasan fuskar.

Salman ne ya karasa shigowa tare da cewa yaushe kika zo? Sai alokacin ta d'aure ta kalleshi, cikin sanyin jiki tace d'azu, ganinai baka dawo ba😕.

Salma ta kalleta sannan ta kalli salman tamai alama dakai wace? Murmushi yai sannan yamatsa gun farha yace kefa dadina dake kenan farha, ba hakuri.
Gaban salma ne yafad'I farha? Farha? Farha? Abinda zucuyarta keta maimaitawa kenan, da sauri tai hanyar d'aki, farha ta kalleta tace in_law ku nake jira muyi dinner fa?

Salma ta kalleta sannan ta d'auke kai riga da wando ne a jikinta 'yan kanti sai d'ankwalli data d'aura, salma bata amsa mata ba takara yin hanyar d'aki, salman yace magana take miki fa? Salma ta juyo kamar tai kuka tace ina zuwa, yace alright.

Salma nashiga d'aki ta zauna a gado dabass...ta rike kanta tace nashiga uku, meke faruwa? Can wata zuciyar tace kika sani ko kanwarsa ce uwa_daya uba_daya? Sai a lokacin tai _Hamdala_ sannan ta d'an mari fuskarta kad'an da hannu biyu tace hakane, salma kidaina tunanin komai.

Toilet ta shiga sannan ta fito, suna zaune a dinning farha na kusa da salman, ahankali salma ta karasa tazauna, farha kam ta tsorata dakyan salma sai dai bataso agane.

Har salma takaraso ta zauna idan farha na kanta, daga d'an nesa dasu kad'an taxauna, farha tace in_law kin fito? Salma ta kakaro murmushi tace yp, salman ya kalleta sannan ya d'auke kai, farha ta fara jawo kwanuka tafara zubama salman abinci, salma naxaune na kallam ikon Allah, bayan farha ta gama sai ta bud'e kwanon karashe,tace kai kamar da tafarnuwa, tafad'a tare da d'an d'anawa, dasauri tasha ruwa ta kalli bayin dake gefe tace ke meyasa kuke sawa abincinsa tafarnuwa?salma tace bangane ba? Meye da ita? Bayan magani ce? Farha tace haba in_law yayana fa is allergy to tafarnuwa, jikin salma yai sanyi takalli salman sai dai takasa cewa komai.

Salman ya kalli farha yasaki murmushi yace ya isa, basu sani bane, farha tace nidai akula kar a jama wani abun, in rasa ya zan, salma dake kallan salman tuni ta maida idanta kan farha, cikin tsananin mamaki tace me kika ce? Farha tace bakomai, salman ya kalli salma yace kici abinci, salma dakyar ta zuba sai dai ko loma d'aya takasa ci, farha ta kalli salman tace yayana kasan nima nadainacin tafarnuwa? Yace why? Tace yaxa'ayi inci abinda baka ci☹?

Salma kam ranta yagama b'aci da karfi ta ajiye cukalin dake hannunta, dukansu suka juyo tamike tare da kallansu ko magana bata musu ba tanemi wucewa, tazo saitin salman, yasa hannu ya riko ta, ta tsaya cak,batare da ta juyo ba,idanunta taf kwalla, salman yace kI koma kici abinci,salma ta had'iyi wani abu, ta runtse ido tace na koshi banajin yunwa, salman zai magana farha da kishi ya zo mata wuya tai sarin tasowa ta raba hannunsu ta rike salma tace in_law kici abinci plz? Salma ta fizge hannunta tace nace miki na koshi, ko bakya fahimtar yaren? Tana kainan tai d'aki, farha ta kalli salman tace yayana matarka ta iya fad'a, sannan kamar kuka zatai, an ma.........kafin ta karasa taga salman ya mike, d'akin ya shige ya barta anan.

Salman na shiga ya salma azaune tana kuka, ya kalleta yace ke kuma fa? Dasauri tafara goge hawayenta ta mike zatai toilet da sauri ya jawota jikinsa ya rungume yace menene? Baki da lafiya? Bakin ciki ya kamata wato baimasan meke damunta ba? Salma ta kwace jikinta tace kaina ke ciwo, yace eyya akwai magani a drawer inkin fito kisha, yafad'a tare da juyawa, salma tace ina zaka? Yace gun farha,jitai kamar tasa ihu, tad'aure tace nikam farha ya kuke? Yace oh banfa fad'a miki bako? Cousin d'ina ce,'yar kanwar Abba ce.

Salma jitai kamar ta mutu sai dai gani tai salman ya bude kofa ya fita, komawa tai tazauna akasa, hutunansu ta tuno, tace shikenan nikam😰.

Salman na fita yaga baiga farha ba,dakinta ya wuce, tana kwance tana kuka, girgiza kai yai tare da karasawa, ya d'au tissue yazauna kusa da ita, yace ga tissue, zan fita inkin gama kukan nadawo, yafad'a tare dayin kamar zai mike, dasauri ta rungumoshi ta baya tace karka fita plz yaya, yace to meyasa ki kuka? Tace kawai gani nai kamar now I am useless in ur lyf, salman yace ya zaki fad'I haka bayan kinsan matsayinki? Yafad'a yana zare hannunta, kara kankameshi tai tace yaya naga fa yanda ka mike dazu, yace naji to sakeni sai muyi magana ko? Tace uhm uhm nidai a haka, nafijin dadi☹ tafad'a cikin shagwaba, murmushi yai yace badai haka kike taba mazan paris bako? Dasauri tasakeshi tace haba yaya😕nifa ban taba rike hannun wani ba bayan kai, ya kalleta yace anya kuwa? Tace 'yar iska kamaidani? Yace haka kalmar take nufi? Farha tace ohh yaya bakar magana fa kake fad'amin☹ yai murmushi yace kedai kin fassara kawai.

Ta sauko tazo gabansa ta tsugunna tace yaya plz karka yada ni, yace yaza'ayi in ya da 'yar uwata🤔?tace bafa irin wannan ba, nasani sarai kai bakasan auren ko mace biyu shiyasa nake farin ciki,bazakamin kishiya ba to yanzu gashi kayi aure yazamuyi?salman ya kalleta tare da mikewa yace umarni kike nema ki bani ko me? Tace ba haka bane yaya, amma ai kaga ni kakeso, sai ka rabu da waccen ka aureni ko? Salman yakalleta yace farha kanki d'aya kuwa? Itama ta mike tace menai kuma? Yace bakisan niba kenan indai kinsan banasan kara aure ba, ban kuma fi tsanar saki ba😏 .

Yana kainan yai hanyar kofa binshi tai da sauri tasha gabanshi ta tare kofa da hannunta, yace me kike?tace to ya kake so inyi yaya? Yace bani gu farha akwai abinda zan? Hawaye ya zubo mata tace zakagun matarka?yace oh god farha meke damunki? Tace kishi tafada tare da tsugunnawa agun tasa kuka mai tsuma zuciya, tugunawa yai ya jawota jikinsa yana shafa bayanta, sai dai baice komai ba, farha kam kuka kawai takeyi.

Salma bayan tayi sallar isha'I tai shirin bacci, sai dai har lokacin salman bai dawoba, ahankali ta bude kofar falon, ga mamakinta ba kowa a falon, gabanta ya fad'I badai suna tare ba? Nikam na shiga ukuna🙆🏻 kanta taji ya shiha sarawa ta kalli maganin kawai taga bazata ma iya sha ba, ta rufe drawer tare da mikewa da kyar tai shimfid'a, ta zauna tana jiran salman saI dai har 1q ba labarinsa, har bacci yafara d'aukanta.

Salman kam nacan dakyar farha tai shiru nan tacemai ya tsaya ta nunamai wani abu, nantashiga kunnamai videos dinta a paris tana yawon inda suka saba zuwa da salman,dariya kawai suke sam abin yad'aukemai hankali.

Bai ankaraba sai ganin 12:30 yai yace farha dare yayi so sai😳sarai tasan time, amma sai tace inalilahi yaya yazamuyi?gashi 12 ake kulle ko ina ko? Salma yace eh, yanzu yazanyi? Tace yaya in akaga ka fito daga nan sai anyi gulmar abun, kawai kabari da safe tunda fulani ba fitowa takeba, in an sauko sai ka fita kamar irin daga gunta kake d'in nan, salman yai shiru, yace a'a idan na kira salma nace tazo mu tafi tare ba wanda zai zargi komai, yafad'a tare da laliban wayarsa, haushi yakama farha.

Sai dai me? Wayarsa nakan dinning🤔yakalli farha yace nabar wayar a gida, dadi yakamata tace yaya ka kwana anan kawai, yace me zaisa inkwana anan?tace yay.....ya katseta there must be another way bayan wannan🤔.

Nikam haushi duk ya ishen na d'auko sanda nace aikuwa ka kwana anan salman rad'a ma sandarnan zan😣😏.

By Ayusher Mohd📚
[11/13, 10:47] 💞Maman Binafah💞: ☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.3⃣1⃣

Farha tace yayana.....salman ya kalleta sannan yaja hannunta ya zaunar da ita akan gado, yace Farha ko za'ai maganata I can't sleep here, ko in cemiki I won't, kallansa tai idanta yai rau rau tace banaso ama magana ne, yace in banasan magana sai kuma inkwana d'aki d'aya da ke? Ba muharramata ba? Tace amma yaya ai ni.....yace farha please, yasaketa tare da juyawa takalleshi kwalla ta zubo mata, tana tsananin san salman kishin salma ne yashiga taso mata.

Salman kam fitowa yai kai tsaye yai hanyar kofa, masu kula da gun suka kalleshi sukace ranka ya dade ya muka ganka anan? Yace in d'a ya zauna agun mahaifiyarsa laifine? Ko in ishaq ne yazauna zakumai magana? Dasauri sukace kayi hakuri ranka ya dade, nan suka bude kofa, salman ya fita.
Chapter 17 · 0% Book details