← Book details ️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 27

Sashe 9

️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta'be baki Hamidat tayi sannan tamiqe tanufi ciki binta yayi da kallo cikin damuwa misali 4:50 Hamut yashigo cikin parlour shi shida abokinshi zama sukayi bayan sun zauna Hamut yamiqe yace bari akawomaka abun jiqa maqoshi ko daga haka yamiqe yanufi ciki cikin bedroom d'in Hamidat yashiga zaune yasameta gaban dressing mirror sosai yashigayin mamakin yadda taci kwalliya kamar zata gasar sarauniyar kyau ajiyar zuciya yasauke mai nauyi sannan yace
" ga abokin nawa ya'iso kikawomai abun sha muna babban parlour " daga haka yajuyo yafito jiki babu qwari bayan yadawo parlour sukashiga hira shida abokin nashi babu jimawa sosai Hamidat tafito daga kitchen riqe da tire cike dakayan motsa baki taku takeyi ahankali mai d'aukar hankali aje tiran tayi agabansu nantake kamshin turaranta maijan hankali yagarwaye gurin lumashe ido muhseen yayi yasauke idon shi akanta sannan yadubi Hamut yace
"Abokina ashe kayi aure shine babu sanarwa haka wannan baby maizafi haka ? " kafin Hamut yayi magana Hamidat tayi saurin karyar damurya tace " ina ay yaya Hamut bai shiryayin aure ba ay dakaji nid'in qanwarshice tajini " miqamishi cup din ruwan kayan itatuwa tayi had'ida sauke mishi wani irin mayen kallo sannan takoma tazauna tana fesin dinshi binta dakallo Muhseen yayi yanajin wani irin yanayi nadaban duban Hamut yayi yasaki murmushi yace
" abokina inacikifa " murmushin yaqe Hamut yayi yace " ay babu matsala idan har ta'amince zanyi magana da'ita komi kenan zakaji " mido dubanshi yayi kan Hamidat yace " baby d'an bamu waje kad'an " miqewa Hamidat tayi takoma ciki bayan tavar parlour Muhseen yadubi Hamut yace " gaskiya abokina inason wannan qanwar taka amma sede akwai matsala dad d'ina yamaqale akan dole sena auri wata kucakar yarinya nikuma wallahi banaso kagama shiyasa nayi tahowata nan Ummy na tace nabar qasar kawai dan Allah kayimin jagora na auri sis d'inka batare dasanin iyayenaba "
Nisawa Hamut yayi sosai cikin zuciyar shi yanajin zafi sosai wai yau shine wani yake mai maganar auran matarshi wadda yake tsananin so maganar Muhseen tadawo dashi cikin wannan tunanin saurin dedeta natsuwarshi yayi yace
" karkadamu zanyi tunani akan hakan " hira sukacigabadayi segaf da magrip sannan Muhseen yabar gidan misalin 10pm Hamidat tashiga cikin bedroom d'in Hamut zaune yake saman abun sallah yayi jigum yanacikin matsananciyar damuwa ta'be baki tayi sannan tazauna tace " wai kai yaya Hamut maiye nufinka aykai gabama takaika tunda ga abokinka yanason aurena kuma gashi bayaso kowa nashi yasani kaga shikenan kaima seka'boyema kowa shikenan sirri kan sirri kenan ham........" dakatar da'ita Hamut yayi cikin zafin rai
" ke Hamidat dakata kibar ganin inakauda kaina akan duk wani abun dakikeso sabida inasonkine kawai dakuma darajar yan'uwantaka amma badan hakaba datuni najima damantawa dake seme dan kowa yaji lalurata aybanine nad'aurama kainaba Allah ne kuma in sha Allah zai yayemin nibazan goyi bayan wannan shirmanba amma zanbaki za'bi idan bazaki'iya zamadaniba har zuwa lokacin da Allah zaibani lafiya to nabaki dama dakinemi saki daga gareni nikuma zansakeki kinemi wani mijin wanda zai'iya yimiki maganin wannan jarabar taki "

Shewa Hamidat tayi tace " gara kasakeni zefimin zaman jiran tsammani " sosai Hamut yaji kanshi yashiga sarawa kamar zaifad'i dubanta yayi sosai da idanunshi wa'inda sukayi jajur yace tabbas zanyimiki abunda kikeso amma bazan sakeki ananba kibari semunkoma Nigeria in sha Allah zanmayar dake gabansu dady amatsayin qanwa ba mata ba " wani irin tsaki taja tace " hmmm ina sauraranka " daga haka tajuya tabar cikin bedroom d'in tana fita Hamut yadafe kanshi babu zato yaji wasu irin hawaye suna gangarowa daga idanunshi cikin rawar murya yashiga cewa " ya Allah kaine kajarafceni dawannan lalurar inaroqonka daka yayemin ya Allah kabani lafiya kabani ikon cinye wannan jaraftar taka " kuka yaci qarfinshi babu abinda yake tashi se sautin kukanshi kawai a wannan daran ko runtsawa baiyiba yana saman abin sallah yana gayama Allah damuwarshi

NIGERIA

Afusace hajiya wato mahaifiyar Sarki Jabir tanufi cikin parlour Maimartaba kishin gid'e yake Ammi tana daga gefanshi suna hira gabansu kayan marmarine kala kala tana shiga tanemi guri tazauna fuskarnan tata atamke tadubesu tace

" garama danasameku kuduka anan kai Jabir inaso kacire wannan qudirin naka nacewa wai Hammat zai auri Hanan sam hakan bazai ta'ba yiyuwaba sabida bazan yadda jikana ya auri tsintatciyar mageba babu tabbas d'in cewa Hanan marainiyace wama yasani ko cikin shege iyayenta sukayi suka jefar da'ita aka kaita gidan marayu shine ku kuka jajibo ko harma kuke shirin had'ata aure dajikana mai cikakken asali ko to banyardaba bakuma zanyardaba kunji nagayamuku kusamu wani can irinta kuhad'asu "

Ajiyar zuciya mainauyi Sarki Jabir yasauke yace " Allah yahuci zuciyarki ya mahaifiyata amma wayene yace zamuhad'a Hammat da Hanan aure ? nide banyi wannan maganar dakowaba amma kuma Hajiya ay baikamata ace munware Hanan cikin zuri'ar muba sabida idan akaduba bamakowane yasan cewa Hanan ba 'yata bace tamkar jinina takefa hj......." toni nasani idan kowa baisan cewa Hanan ba jininkabace toni nasani kuma bazan ta'ba yarda agur'batamin zuri'aba " nagamayin magana " daga haka tamiqe tabar parlour kallon juna sukayi sosai Ammi taji zuciyarta tayi babu dad'i kafin sarki jabir yace komi tamiqe tace " matsalar gidan saurauta kenan gulmar tsiya koda cikin uwar d'akinka zakashiga kayi magana se'ansamu waniyaji tabbas idan Hanan bata auri Hammat ko Hamut ba zuciyata zatadauwama cikin qunci babu ruwana da yadda Hanan tazo gareni har abada mai cikakken asali nike kallonta idan hajiya tahana d'aya dagacikin yarana auran Hanan in sha Allah Allah zaimaye mata gurbi da wanda yafisu alkairi agareta " daga haka tabar part din cikin damuwa

MARMYN ZARAH CE 🤝🏻👌🏻
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

*NA*

*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_

```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*

AND NOW
```MUSAYAR RUHI```

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PG 17 & 18*

*S* osai Sarki Jabir yaji babu dad'i cikin zuciyar shi to amma yaya zaiyi da hukuncin da Hajiya tazartar sede yana jinjina wani lamari kiran wayar Hammat yashigayi bugu 2 yad'aga gaidashi yayi cikin yanayinshi narashin son magana sannan yayi shiru yanajiran yaji abunda mahaifin nashi zaice cikin dakakkiyar murya yace
" Hammat inaso kajini dakyau kuma duk abinda zancemaka ayanzu babu shawara aciki umarnine kawai nasan harzuwa yanzu bakafidda matar aure ba don haka inaso kanemi izini wajan manyanka nawajan ayki kataho gida inaso kaje wajan hajiya bayan kadawo kasanar da'ita cewa kanabuqatar auran Hanan kuma inaso ka kafe akan haka idan kaine babu shakka zata amince Hammat kasani umarni nike baka ba shawaraba "
Kafin Hammat yace wani abu tuni Sarki Jabir yadatse kiran wurgi Hammat yayi dawayar cikin mugun 'bacinrai yace
" tabb lalle ni Hammat nine zan auri wannan qaramar yarinyar hmm lalle Hanan anashirin sakaki cikin wahala tabbas zanyi yadda kace maimartaba amma sekowa yayi nadamar wannan had'in "

TURKEYA

Tsayin kwanaki 4 kenan dafaruwar wannan lamarin ga Hanan tun daga wannan lokaci tasake zama shiru batadawani kuzari kullum cikin damuwa kamar kullum safiya suna waya da Ammi cikin damuwa Ammi take tambayarta lafiya kuwa " Hanan tabbas kinacikin damuwa nifa mahaifiyarkice idan banji damuwarkiba waye zeji ko asuman takice take neman tashi ? ko'inzone ? "

Jin haka yasa Hanan qaqalo murmushi mai sauti tace " a a Ammi babu abinda yakedamuna karatune kawai kuma babu wata damuwa nasamu sauqin asuman sosai sabida inashan magungunana akan qa'ida " ajiyar zuciya Ammi tasauke tace " masha Allah in sha Allah kinatare danasara aduk inda kike Hanan kinji kidage akan karatunki sannan inasake sanar dake dakuma jan hankalinki akan kitsare mutuncinki idan kikayimin haka tabbas kinyimin halacci arayuwa ina alfahari dake Hanan auta ta " wani irin kuka Hanan taji yakwace mata sabida maganar Ammi cikin qarfin hali tadake harsukagama wayar bayan sungama kukan da Hanan take riqewa yakwace mata tunanin halin datake ciki ayanzu tashigayi afili tashiga furtacewa " tabbas kacutar dani komawaye kai bazan ta'ba yafemakaba har abada in sha Allah se Allah yasakamin mugu azzalumi dawane idon zandubi Ammi nasanar da'ita cewa anyimin wannan muguwar illar ya Allah kakawomi d'auki da mafita cikin rayuwata " sosai take kuka marar sauti tsayin lokaci dandanan wani irin mugun ciwon kai da zazza'bi yakamata hakan yasa tamiqe zuwa saman bed takwanta sosai tatakure tana tanarawar sanyi hatta haqoranta had'uwa sukeyi sabida tsabar mugun sanyin datakeji cikin shigar qananun kaya kasancewar qasar ma'abociyar sanyice Fadila tafito daga bedroom nufar bedroom d'in Hanan tayi tana shiga tahangeta saman bed qudundine sefaman rawar sanyi takeyi cikin sauri taqarasa gareta hawa saman bed d'in tayi tashiga tambayarta maikedamunta jin yadda jikinta yayi zafi sosai yasa Fadila sake rud'ewa wayar hannunta tashiga latsawa tana qoqarin kiran doctor ganin haka yasa Hanan saurin riqe hannunta cikin raunin murya tace

" a a Fadila banaso kikiramin doctor kibani magani kawai nasha " girgiza kai Fadila tayi tace " a a Hanan gaskiya gara akira doctor kusan kwana nawa inalure dake bakida lafiya amma kinqi yarda akira doctor kibari akirashi " sake girgiza kai tayi tace " a a Fadila inada tabbacin idan doctor yadubani to tabbas se Ammi tasan banida lafiya idan kuma tasani hankalinta tashi zaiyi banaso nahana zucuyarta natsauwa kibarashi kinji dan Allah zansha magani kawai in sha Allah zanji sauqi idan baisaukaba semukirashi kinji "

Jinjina kai Fadila tayi sannan tasauka taje takawomata magani tasha babu jimawa bacci mai nauyi yakwasheta

NIGERIA
misalin 5pm jiniyar motocin Hammat suka fara karad'e cikin masarautar kafin kace mai tuni kowa yafara shiga tetayinshi anayin parking baijira anbud'emai murfin qofar motar ba yabud'eta afusace yafito cikin sauri dogarawa suka shiga yimai kirari cikin tsawa yace " ya'isa!!!!!!! " babu shiri sukadakata takuyafarayi cikin izza da'isa cak yaja yatsaya yad'an juya kad'an yadubi masu takemai baya fuskarnan tamke yace " banabuqatar kowa " jin haka yasa dole kowa yajuya qarasawa ciki yayi kai tsaye part d'in hajiya yanufa yana shiga kuyangun dake yimata hidima sukashiga gaidashi cikin tsawa yace " banason ganin kowa cikin part d'innan kowayafita " jin haka yasa sukafara fita cikin sauri tashi zaune Hajiya tayi tasaki murmushi tace
Chapter 9 · 0% Book details