← Book details ️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 27

Sashe 4

️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" idan kingama kifito parlour ina jiranki " zuyawa yayi yafita wajan abincin yanufa leder dayagani agefe yabud'e kajine manya guda 2 aciki da yoghurt mai sanyi sekuma nau'ikan abinci kalakala agurin kasa koda qwaqqwaran motsi yayi sabida yadda yaji zuciyarshi tasake shiga qunci sosai tuno maganar Ammi yayi da alqawarin dayayi mata akan zaici abinci hakan yasa yashiga zuba abincin cikin sanyin jiki yafara d'ibar abincin yanaci badan yanajin dad'in shiba sedan alqawarin dayayima Ammi kawai yasa yakeci dede lokacin Hamidat tafito ahankali take taku kamar maitausayin qasa sanye take cikin kayan bacci masu bin jiki sun bayayyana surar jikinta sosai tana qarasowa tazauna daf dashi sosai kwantar dakanta tayi saman kafadarshi tad'aura hannunta saman sumar kirjinshi wadda takwanta luf cikin lokaci kad'an taji kasala tamamaye jikinta ajiyar zuciya Hamut yasauke yace

" yakamata muci abinci ko ? " shagwa'be fuska tayi tace " jikina babu qarfi please kabani " rumtse idanunshi yayi sannan yace shikenan gyara zaman naki ahaka bazai yiwuba " gyara zamanta tayi ledar kajin yajawo yabud'e duban kaji tayi tace " a a my D wannan basuda amfani agareni ayau kabari sezuwa ranar daka warke aranarne zanjini amatsayin cikakkiyar amarya ba yauba yanzu irin abincinka zanci " sosai maganar tadaki zuciyar Hamut amma beko iya cewa komiba bata nashi abincin yashigayi har taqoshi sannan yamiqe yanufi bedroom batare dayacemata komiba yana shiga yakwanta saman bed idanunshi nakallon sama hawaye suka shiga gangarowa tagefan fuskarshi babu jimawa Hamidat tashigo cikin bedroom d'in hawa tayi saban bed d'in takwanta saban qirjinshi tashiga shafa sumar qirjinshi ganin hawaye nasauka tagefan fuskarshi tace

" haba my D nifa karkaga lefina iya gaskiyata nafad'a idan na'boyemaka najekuma na'aykata kuskurefa yaya zakad'aukeni ? Wallahi bazan iya jure lokaci maitsayi batare dasamun kulawar namijiba My D kafahimta naqosa namatsu dazuwan wannan ranar yawancin dare inakasayin bacci sabida tasowar shi'awata tunaka kawai zanyi naji yanayina yacanza My D balle yau gani gaka dan Allah kasanaji sassauci koyayane tunda har kaga na'iyafurtawa duk irin kunyar mace tabbas akwai matsala please help me my D "

Wani irin kunlewa yaji zuciyarshi tayi gawani irin zafi datashigayime jan numfashi yashigayi dasauri dasauri dafe setin zuciyar tashi yayi yashigayin magana cikin wahala

" karkidamu My B nayimiki alqawarin bazan bari kicutuba koda bansamu lafiyaba zansamar miki damafita in sha Allah kuma yau zanyi iya iyawata nasaki kibanbance sauran dararan dasukawuce abaya da wannan daran nayau " daga haka yajawota sosai yasaka bakinshi cikin nata yafara sarrafata sosai yake aykamata saqonni cikin salo ahaka kamar zai'iya aywatar dakomi amma kass itako Hamidat sosai tarikice sake mannewa takeyi ajikin shi sosai yatsinci kanshi dajin tausayinta Zameta yayi daga jikin shi yashiga toilet cikin Sauri tashi tayi zaune tanasauke numfashi sosai takecikin tsananin buqata Shiko yanashiga zama yayi yadafe kanshi yanasakin muguwar ajiyar zuciya gazafin zuciya yanaji sosai Kamar zuciyar tashi zata qone sabida zafi tsayin lokaci sannan yad'auro alwala yafito bai Kalli inda takeba yashinfid'a abin Sallah yatada sallah sauka Hamidat tayi daga bed d'in tabar cikin bedroom d'in Cikin wani yanayi Shiko Hamut kwana yayi sallah awannan daran hakama Hammat da Ammi duk sunayime addu'ar samun lafiya

Washegari misalin 3pm doctor ya'iso Nigeria kasancewar tun jiya yataso Hammat neyaje filin jirgi dakanshi yataho dashi koda Suka'isa cikin masarautar nanfa gulma tatashi kowa yanatambaya me wannan d'an China yazoyi cikin masarauta ayau Kiran jakadiya hajiya Mariya tayi cikin part d'inta itama hajiya tana cikin part d'in duban jakadiya sukayi hajiya Mariya tace

" jakadiya tabbas akwai abinda ake 'boyemana acikin masarautar nan naga hajiya Salma tashigo cikin masarautar nan jiya afusace hadima larai tacemin taji tanacema gimbiya Hamidat bazai yiyuba bazatabari 'Yarta tazaunada namiji irin maimatsala ta Hamut ba tabbas akwai wata aqasa dubada daga airport akawuce dashi asibiti wai yasamu accident segashi yadawo babu alamar ciwo jikinshi Sekuma maimartaba yafara qoqarin hana aywatar da al'adar shinfid'a farin gyalle bayan haka gimbiya tace tanayin jini senan dakwanaki 6 bayan Kowa yasan yanzu ba'ayin haka anatsara komi a yadda yakamata Lalle akwai wani abu hmmmm ayau kam nizan rikita komi jakadiya inaso kiyi duk yadda zakiyi kigano mana wani abu idan kikayi hakan kinada kaso maitsoka nikuma zanje wajan hajiya nazugata Sena rikita komi "

Tashi jakadiya Tayi tace " nikuma sena ganomuku komi "fita tayi cikin sauri part d'in Hamut tanufa zaune tasamu Hamidat itada hadimanta gaidata tayi cikin girmamawa sannan tad'an zauna jim bataga alamar cewa Hamut yana cikin part d'in ba hakan yasa tatashi tafita zuwa part d'in Ammi nanma babu Hamut ba Hammat se Ansar da Hanan zaune gaida Ammi tayi sannan tace

" Allah shi taimakeki Allah yaqaramiki lafiya dama zuwanayi natambaya naga anyi baqo maiyakamata akawo mishi tunda naga shi bad'an Nigeria bane dole za'asamu banbancin cima "

dubanta Ammi tayi tasaki murmushi tace " a a wannan baqon Husain ne kuma lamarine na aykinsu dan haka shi yatanadar mishi komi kuma kinsan halin Husain bayason anashiga cikin harkarshi idan kuma zakishiga tojeki kitambayeshi babu ruwan hajiya kilishi "

zaro ido Jakadiya tayi tace " ina nina isa yarima Hammat a a nabarki lafiya " daga haka tamiqe tafita binta hanan tayi dakallo sannan tadubi Ammi tace " Ammina nifa gaskiya wannan jakadiyar banfa yarda da'itaba tafiye gulma " Murmushi Ammi tayi tace " ay bama itakad'eba akwasu dayawa kede shi'anin gidan sarautar se ahankali " tsaki Ansar yaja yamiqe yace " Allah yasa nakama mata tana gulmana wallahi daga ranar senasaka ancanzamata kamanni " daga haka yabar parlour afusace girgiza kai Ammin tayi tace " shegiyar zuciya kamar Husain shide hassan babu ruwanshi " murmushi Hanan tayi tace " hakane amma shikuma akwai jin kai da miskilanci " murmushi Ammin tasakeyi tace " ay wannan jinine Hanan sarauta gaba da baya kinga kuwa dole ayi jin kai " murmushi Hanan tasakeyi tace hakane kam

a part d'in Hammat doctor yake duba Hamut tundayazo yakeyin aykin har dare amma kamar babu nasara misalin 9:pm doctor yadubi Hamut da Hammat yace

" gaskiya sede kayi haquri nayi duk abinda yakamata nayi amma wa'innan jijiyoyin sunriga sun mutu kwata kwata bazasu sakeyin ayki ba kayi haquri zanbaka magani zakadenajin ciwon marar k......" kafin yaqarasa Hamut yamiqe yace banabuqatar maganin naka nagode Hammat kasallameshi kasa akaishi masaukinshi zuwa safe yakoma china kuje kudawo inason magana dakai "

ganin yadda ranshi ya'baci yasa Hammat yin abinda Hamut yace bayan yasallameshi yadawo zama yayi kusada Hamut d'in idanunshi sunyi jah sabida tsananin 'bacin rai kafin Hammat yayi magana Hamut yadubeshi cikin damuwa yace

" d'an uwana ayau inaso kanunamin qarfin dangantaka nasan babu alfarma agaremu tsakanin ni dakuma kai amma ayau zanroqeka alfarma nakumasan zakayimin ita sabida girman alfarmarne yasa naroqeka nasan duk abinda nikeso kaima shi kakeso natabbatar dahakan ayauma zansake tabbatarwa!!!!!!!!!!! Hammat Inaso kayi auran sirri kaida matata Hamidat ko ita banaso tasan haka idan kayi haka zan......."

" dakata Hamut bazanyiba bakuma zan iyaba kai kasan banida ra'yin mace balle matarka Hamidat yarinyar danayi matuqar tsana ina gaskiya bazan iyaba "

miqewa Hamut yayi yashare hawayen fuskarshi yanufi hanyar fita ja yayi yatsaya yace " tabbas ayau natabbatar dacewa Hammat bazai iya yin musayar ruheey da Hamut ba kasani idan narasa Hamidat tabbas nima zakarasani dama iya haka qarfin dangantakarmu take dukda rayuwa damukayi a ciki d'aya kuma lokaci d'aya dama ba uwa d'ayace tahaifemuba dabazanji damuwaba dan kaqi ceto rayuwataba to amma kasani tabbas zantafi nabarka " hannu yasaka zai bud'e qofar Hammat yayi saurin kamo hannunshi dubanshi yayi yadda hawaye suka wankemai fuska sharemai hawayen yayi yace " zanyimaka duk yadda kakeso amma kasani zuciyata bazata ta'ba son Hamidat ba "

ajiyar zuciya Hamut yasauke yace " hakan nikeso duk ranar dakasota bazan iya yafe makaba inaji ajikina zanwarke nangaba in sha Allah zansaki Hamidat saki batare dakowa yasaniba zamuje ad'aura maka aure da'ita ayau tunda batada iddata akanta zandawo nace mata namayar da'ita kuma nasamu lafiya zakazama miji agareta amma nasirri duk dare zakajemata amatsayin nine kuma yazama dole kakusanceta amatsayin nine tabbas zanji babu dad'i cikin zuciyata amma hakan zaifimin sauqi akan ace wanine ta'aura duk ranar dana warke zakasaketa tadawo gareni komi dad'ewa "

rumtse ido Hammat yayi yace " tayaya Hamut idan bata ganeni takomiba zata ganeni ta yanayi dakuma launin idanuna Hamut tayaya zan'iya kusantar yarinyar dakabama zuciyarka tun tana 'yar qaramarta k........" dakatar dashi Hamut yayi dafad'in zan'iya sadaukar dakomi akan farincikin Hamidat kuma kai d'an'uwanane idan wanine yayi hakan to wallahi sena kasheshi sannan maganar lauyin idanu natanadi ledar dazakasama idanun naka yanayi kuma kayi qoqarin setashi yadawo irin nawa idan kayi haka zancigaba da rayuwa akasin haka kuma mutuwa zanyi zanje nayima Ammi bayanin komi ita kad'e nikeso tasani sabida banta'ba 'boyemata komiba bakumazanfara akan wannan ba "

Comments and shire please
[8/19, 5:55 AM] Aunty Fauza: *⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

*NA*

*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_

```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*

AND NOW
```MUSAYAR RUHI```

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*Page 9 & 10*

*Y* ana fita yanufi wajan Ammin yana shiga Hanan da Ansar dake parlour sukayi saurin miqewa suna gaidashi bai kallesuba baikumace komiba abinda bahalinshiba yana shiga yasamu Ammi tsaye da'alama tana cikin tunani sosai zama yayi sannan yace " Ammi " saurin juyowa tayi sabida ko sallamar shi batajiba sabida tana cikin tunani saurin zama tayi agefanshi kafin tayi magana yayi saurin cewa " shima wannan doctor yacemin bazan warkeba Ammai nikuma har yanzu bancire raiba inaji ajikina zanwarke ko Ammi? " yaqarashe fad'ar hakan cikin rawar murya " saurin kamo hannunshi Ammi tayi tashiga lallashin shi ajiyar zuciya yasauke mai qarfi yace
Chapter 4 · 0% Book details