← Book details ️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 27

Sashe 25

️Musayar Ruhi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kaka taitayin mita washegari sewajan 3 sannan Hanan tafarka Ammi da Siyama ne kawai cikin d'akin jin yadda Hanan keyin mutsumutsu yasa Ammi saurin qarasowa bakin gadon
kamo hannunta Ammi tayi cikin sanyin murya tace

" bud'e idonki Hanan nice Ammin ki Hussain bayanan kuma bazaizoba bakuma zakikoma gareshiba kinji "

Bud'e idonta Hanan tashigayi ahankali tasaukesu kan Ammi nannauyar ajiyar zuciya Hanan tasauke murmushi Ammi tasakar mata qarasowa Siyama tayi cikin farinciki tasumbaci goshin Hanan tasakar mata murmushi had'ida cemata " Hanan yajikin sannu kinji Allah yasa kaffarane "

Qoqarin miqewa tashigayi tananuna toilet kamata Siyama tayi takaita bayantafito Ammi dakanta tabata abinci babu jimawa su Sarki Jabir suka iso doctor yabasu sallama sukakoma gida part d'in Ammi akawuce da Hanan cikin bedroom d'in Siyama Siyaman tashiga da Hanan itakuma Ammi tanufi part d'in Sarki Jabir kusan tare sukashiga juyowa yayi cikin mamaki yace

" ah lafiya kuwa Hajiya kilishi ? "

Jinjina kai tayi cikin d'an damuwa taqarasa hannun shi takamo tasakacikin nata cikin matuqar damuwa tace

" dan Allah Maimartaba kajanye zancen maida Hanan cikin asalinta rabuwa da Hanan tamkar rabuwa da farinciki nane dan Allah "

Dubanta Sarki Jabir yayi sosai sannan yace

" kisani koda Hanan tabar cikin wannan masarautar tofa kuna tare Hanan bazata barkiba kamar yadda kema bazakibar Hanan ba ni kimar Hanan da darajarta nikeso nafito da ita bawai rabaku nikesonyiba zanjira taqara warwarewa "

Cikin yanayi marar dad'i Ammi tasakecewa
" to yaya zamuyi da igiyar Auran Hussain dake kanta ? "

Mameen Zarah & Sudees ce 👌🏻😊
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

*NA*

*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_

```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*

AND NOW
```MUSAYAR RUHI```

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PG 73 & 74*

*G* anin Hamut a parlour yasata sakin dogon tsaki qarasowa tayi tazauna tadubeshi tayatsina fuska tace " hmmm wanide ya iya aikata rashin lissafi amma yadinga nunama mutane shi d'in me cikakken hankali ne to kam magani "
Jin maganganun da Siyama keyi yasa Hamut jan qwafa yamiqe yadubi Hanan yasaki murmushi yace

" Hanan zanje zuwa anjima zan dawo kiyi tunani da kyau seki sanar dani zuwa anjima sabida ayanzu bazanji dad'in zama anan ba kinsan zamada mahaukaci se dole ko banza kasha duka idan kuma yasamu sa'a yacijeka tofa kaima kamuwa zakayi da haukan kinga kuwa garanabar gurin ko qanwata "

Duban Siyama Hanan tayi sabida tasan Hamut da ita yake dariya abin yabata sosai Hanan takeyin dariya sede sautin ta bayafita rabon dataji irin wannan dariyar tun sunatare da Ansar wato qanin su Hamut cikin fusata Siyama tamiqe tasha gaban Hamut amasife tace

" kenan kananufin ni mahaukacciyace ko to yau sekagayamin inda nata'bayin hauka ko nanunamaka qirqirarre yanzu k....."

Jin muryar Ammi yasaka Siyama yin shiru dubansu Ammi tayi tace " to kaji zakufara fad'an nakune ? kai nikam kilishi Allah yanunamin qarshen wannan fituna naku kai Hassan kaine babba amma kake biye mata ko ? "

Jin abinda Ammi kefad'a yasa Hamut fita daga part d'in bayan fitan Hamut Ammi tadubi Siyama tace

" Siyama kinsan akwai wani shagali daza'a gudanar nanda kwanaki 2 a cikin masarautar nan kuma za'a had'ane da shagalin murnar kammala karatun ki dakuma bikin bud'e hospital d'in ki dan haka inaso ki gayyato duk wata qawa taki sannan na d'akko me gyaran jiki zata gyaramin ke kifito fes kamar amarya sannan zan shiryamiki kaya tamkar lefe irin na qayatacciyar amarya me cikken gata amma inaneman abu 1 agunki duk abinda zakiga nayi anan gaba to banason tambaya sabida nariga nasanar dake komi a yanzu ki d'auki duk wani abunda kike buqata kikoma part d'in Hajiya dazama sabida a can za ayi miki gyaran jikin "

Jin maganar komawa part d'in kaka yasa Siyama d'an zaro ido kafin tayi magana Ammi tadakatar da ita dafad'in " karkice komi ki lalla'bata kurabu lafiya tashi kije "

Komawa bedroom tayi da shiryawa tayi matuqar farincikin wannan shagalin amma zuwa part d'in kaka yasakata cikin mutuwar jiki tasan dekam zatasha masifa ne bayan tafiyar Siyama Ammi tazauna kusada Hanan jawota tayi takwanta dakanta saman cinyar ta shafa gashinta Ammi tashigayi cikin tausayawa da lallashi Ammi tafara dacewa

" Hanan kiyi haquri abisa tauye miki haqqi damukayi wajan aura miki Hussain tabbas bamusan zecutar dakeba munyi zaton zai bar komi ashe bahakabane damunsani dabamuyi wannan had'in ba amma yanzu babu mai mayar dake hannun shi banama tunanin zakisake ganin shi sabida tun a jiyan yabar qasar yakoma bakin aykinshi kimanta dashi kinji Hanan zakisake shiga cikin wata sabuwar rayuwa wadda tafi wacce kike ciki a yanzu nashi kije ki kwanta kihuta sabida doctor yace kidinga samun hutu "

Cikin sanyin jiki Hanan tamiqe tanufi bedroom zuciyar ta cike da tambayoyi bin bayanta Ammi tayi da kallo miqewa itama tayi tafita part d'in Maimartaba tasake komawa a wannan lokacin riqe yake da waya sefaman juyata yakeyi kallon shi sosai Ammi tayi kafin tace

" hmmmm kiranshi kakesonyi ko ? inagayamaka kabarshi dan Allah muma mununamishi cewa zamu'iya mantawa dashi kamar yadda shima yamanta damu yatafi ayanzu de baya cikin Nigeria balle kafita kaje kadawo dashi dukda cewa kasaba binshi har wata qasar kadawo dashi to ayanzu inaso karabu dashi dan Allah watarana dakanshi zedawo da qafafunshi "

Ajiyar zuciya Sarki Jabir yasauke yace

" hakane kilishi amma kinsan dolene nadamu ke kanki kinsan yadda nikeson Hussain bana iya jurar fushi daga gareshi " " haka nima bana'iya jurar damuwa daga zuciyar Hassan tunda nayi haquri najure a lokacin dayasamu lalura to kaima yazama dole kajure Hussain shine ya batamana bamune muka 'batamishi ba "

Tsayin lokaci suna tattaunawa akan hakan to bari muga shi Hammat d'in wace wainar yake toyawa

Turkiyya

Jirginsu yanasauka a filin sauka datashin jiragen sama na Istanbul akazo d'aukarshi sabida ansan dazuwanshi kimanin motoci 6 ne sukazo d'aukarshi ko wanne da kakin soja irin nashi saramai sukashigayi kafin akabud'e me mota yashiga fuskarnan a matuqar tamke sun d'anyi tafiya mai tsawo kafin suka isa wani kyakkyawan bene mai hawa 8 gidane wanda yaji komi namore rayuwa yana fitowa yashiga ciki kai tsaye shiga cikin Lenten yayi tasadashi da hawa na 6

tana tsayawa yafito nufar wata qofa me glass yayi password yashigar kafin qofar tabud'e yanashiga wani katafaran picture ne cikin wani qayatatten glass nashine shida Hamut kallon picture d'in yayi sosai yace

" bro na kenan zanyi kewarka natsayin lokaci "

Daga haka yabud'e bedroom yashiga toilet yafad'a alamu sunnuna ayanzu de Hammat bashida damuwa

Nigeria

Hidima takankama sosai cikin masarauta idan ka kalli Siyama hmmmm sekaqara kallonta sabida yadda taqarayin masifar kyau to dama akwai abun wato kyau a 'bangaran Hamut kuwa Sarki Jabir yakirashi babu 'bata lokaci ya amsa kiran Maimartaba gaidashi yayi cikin girmamawa sannan yazauna bayan Hamut yazauna Sarki Jabir yayi d'an jim nawasu lokuta kafin yafara dacewa

" Hassan a yanzu idan nace kabiyamawani sadakin aure dede da yadda zaka'iya biyama kanka zaka'iya ? sannan zaka'iya amsar mawani aure ba matsayin waliyi nike nufiba ina nufin kazama kamar matsayin ango komi da ango yakeyi kaima kayi kama daga yanayin shiga harma dasauran abubuwan Hassan nasan kanada biyayya to inaso kayimin biyayya akan wannan zuwa gode za ayi wani d'aurin aure a cikin masarautar nan hakan nikeso kayi akwai kaya namusamman dazakayi amfani dasu yanzu inaso kabada sadakin "

Sosai zuciyar Hamut tashiga rud'ani kanshi ya d'aure amma yakasa fahimtar komi bin umarnin Maimartaba yayi sannan yamiqe yafita

WASHEGARI
tun dawuri baqi sukafara hallara cikin masarautar Siyama kuwa tuni akashiga tsaramata shiri shiko Hamut yana cikin bedroom yafito wanka yanashafa maya mayan shi zuciyar shi cike take da tambayoyi amma babu mai bashi amsa ahaka har yagama shiryawa kya gaskiya Hamut yayi mugun kyau yau kam yake ango tunda ko a auran Hamidat baiyi irin wannan shigarba sede yaqare a asibiti yana fitowa daga bedroom kamshin turarukan shi suka daki hancin Hamidat juyowa tayi ganin irin shigar dayayi yasata saurin miqewa nufoshi tayi cikin mamaki tace

" D wannan irin shiga haka inazaka ? " tsaki Hamut yaja yace " au bakisan aure zanyiba yau ? "

Zaro ido Hamidat tayi cikin rud'ewa tace " au shiyasa naga an shirya sama ansaka komi sabo to wallahi baka'isaba hakan baze yuwuba kwata kwata aurena da kai wata nawane dahar zakayimin kishiya lalle kanaso nanunamaka hauka "

Tsaki Hamut yasake saki dukda maganar saka komi sabo a sama ta d'auremai kai amma se yace
" au wai ke kina tunanin ina daukarki a matsayin matata ne to ayko kimabari maganar nunamin hauka kuma ayni dama tuni nike kallon ki a shashasha " daga haka yasakai yafita abinshi

yau asabar 27 February 2021 damisalin 02:30 amsakuwar masallacin dake cikin masarautar tadauka dafad'in masha Allah a yau an d'aura auran Hassan Jabir Hassan da Siyama Aminu bashir Allah yabasu zaman lafiya Allah yabasu zuri'a d'ayyuba "

Hamut dake cikin masallacin ya zaro ido yakasa motsawa daga inda yake itako Siyama dake zaune cikin parlour Ammi tareda qawayenta tayi saurin miqewa cikin tashin hankali

Mameen Zarah & Sudees ce 😊👍🏻👌🏻💖
*⚜️MUSAYAR RUHI⚜️*

*NA*

*NPEEDY A AJI*
_(MARMIY ZARAH CE)_

```LITATTAFAN MARUBUCIYAR SUNE```
*1. NAYI RAYUWA DASHI*
*2. SANADIN ACCIDENT*
*3. SAKAYYAR CUTA*
*4. RUFAFFIYAR ZUCIYA*
*5. MUGUN SARTSE*
*6. FURUCI....*
*7. JUYI BIYU*
*8. HAYATUL MAHAYAT*

AND NOW
```MUSAYAR RUHI```

*_____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_____________________________________*

*PG 75 & 76*

*D* aya daga cikin qawayen tana tadubeta tarangad'a gud'a tace
" hmmm Siyama kenan ai dama ni wallahi jikina yabani cewa aure zakiyi shine kiketa wani 'boyemana to ay yanzu gashi mungani ammafa gaskiya kin mori miji "
Jin wannan maganganun da qawar tata keyi yasa Siyama qoqarin seseta kanta murmushin dole taqaqalo sannan tace
" dama ina sone nayimuku
bazata ina d'an zuwa "

Nufar bedroom d'in Ammi tayi takuwayi sa'a Ammi tanaciki yadda Ammi taga Siyama yasata saurin cewa
Chapter 25 · 0% Book details